← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 238

Sashe 8

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kusan ƙarfe shida na marece, A haka Har kike tambaya, toh abincin dare ne, mu da cin wani abincin sai gobe da safe in Allah yakaimu" javed ne Ya bata amsa Yayin da yake kur6ar lemu me sanyi.

"Ba'a magana idan Ana cin abinci," Boss ne ya faɗa yana duban su.

"Dariya fa da murmushi suma ba'ayi"?

Jemimah ce ta jefa mashi tambayar yayin da take cunkusa abinci abaki tana tauna.

Dariya suka sanya gaba ɗayansu cikin raha.

"sajeed Ina wayata"

Dafe kai Yai da hannu ɗaya"Am sorry sister, Na cinye maki chargy, bansan ko kina da charger ba"

"Akwai charger bani wayar" da sauri ta miƙe taje gaban sofa din da yake a zaune, Wayar Ya zaro daga trouser pocket nasa ya miƙa mata ita.

Tasa hannu ta kar6a, kafin ta nufi bedroom dinsu, shigarta keda wuya wayar hannunta ta soma ringing, tana kokarin ɗaga Wayar ta kashe kanta kamar tayi hauka saboda ta gane number da suka kirane ita da sajeed.'

Cikin takun sauri ta nufi backpack din su, ta buɗe ta dauko cazar wayar ta jona a socket, akan idonta wayar tayi haske alamar ya ɗauka, lumshe idanunta tayi tare da jingina bayanta jikin gadon, zuciyarta a cike fal da tunanin shi.

*💋NAZLI👑*

Sautin daddaɗan kiɗa ne da ke tashi a katafaren gym room (ɗakin motsa jiki) da ke a gidan prime minister, an ƙawata shi da manyan injinan motsa jiki, a tsaye take saman thread mill tana gudu cikin shiga ta kayan motsa jiki, sport bra tare da short launin black colour, sunyi bala'in yi mata kyau, sun bayyana farar fatarta sol ko kwarzane babu, tamkar bata ta6a yin rarrafe ba arayuwarta saboda hasken fatarta harta gwiwar ƙafarta tayi jawur da ita, dirar mace doguwa ga kyan sura, ta ɗaure lallausar baƙar sumar kanta sai salƙi take yi da sheƙi ta sauko har saitin waist din ta, gaba ɗaya ta tattara nutsuwarta akan abun da take yi, sautin music din ba ƙaramin ni'ima yake samar mata ba, kyawawan idanunta na akan tanƙameman madubin dake manne da bango, zufa ce ta soma tsastsafo mata ta ko'ina ta jiƙe sharkaf da ita, babu alamun gajiya atattare da ita, daga gani ta ƙware a 6angaren gym.

Bakomai ne acikin zuciyarta ba, face zallar begensa, duk yadda taso ta hana kanta tunawa da shi abun yaci tura, tayi tunanin zata iya sarrafa zuciyarta wurin hana ta tunaninsa sai dai abun yaci tura, a kowani daƙiƙa son shi ƙara ninkuwa yake yi a zuciyarta, ga dukkan alamu Nazli batasan menene So ba, ko da yake girman kai da izza sun hana ta gane cutarwar da take yima kanta, shiyasa ta kasa miƙa wuya"

Tunanin shi ne ya haifar mata da jin Kasala, ba arziƙi ta dakata da motsa jikin, ta kai hannu ta ɗauki short towel fari ƙal ta soma tsane jikin ta da shi, bayan ta kammala fitowa tayi daga gym room din ta nufi bedroom dinta, kai tsaye ta shiga bathroom domin yin wanka.

Shigowa ɗakin Yazrin tayi cikin shiga ta riga da wando black and white, tayi rolling veil akanta, hannunta ruƙe da wayarta.

Ganin babu ita a dakin yasa tayi tsammanin ko ta fita ne har zata juya ta juyo motsin ta a toilet da sauri ta la6e a bayan labule.

Gently ta zuro ƙafafunta dake sanye cikin slippers, bathrobe ce a jikinta fara ƙyal, hannunta ɗaya ruƙe da towel sai faman tsane sumar kanta take yi.

Yazrin dake a la6e bayan labule, wayarta ta danna ta shiga camera ta ɗage labulen a hankali ta soma ɗaukar Nazli video batare da sanin ta ba.

Dressing mirror ta nufa cikin takun qasaita, wasu tsadaddun mayukan gyaran jiki ne asaman mirror din, bayan ta zauna ta soma bin ko'ina tana shafe shi a tsanake, kafin ta dauko bakhhoor burner ( turaren wuta) ta soma turara jikinta da sumar kanta, komai nata cikin aji take yin shi, Nazli macece mai tsafta ga son gayu, kuma ma'abociya son ƙamshi.

Duk wani motsinta, Yazrin na kallonta ta cikin camera, bayan ta gama gyaran jikin nata, closet ta nufa jim kaɗan ta fito, har ta canza kayan jikin ta zuwa kimono robe, yazrin da ke ta daukar ta video kayataccen murmushi ne kan face dinta, aranta ta ayyana ukhty Nazli badai iya gayu ba, bata gama zancen zucin nata ba, taga Nazli ta haye saman Royal bed dinta hannun ta ruƙe da wayarta, bakomai take kallo ba face hotonsa, har zooming dinshi take yi da zira ziran yatsun hannunta, hoton da take kallo tsohuwar ajiyace a kalla yakai shekara biyar, lokacin yakai masu ziraya a canada, ba tare da sanin shi ba ta dauki hotan, dama duk in yaje basa jituwa da Nazli, har ya bar ƙasar basa sakarma juna fuska kai kace makiyane, Yazrin ce kadai suke mutunci da juna, kuma a lokacin suna matuƙar ƙaunar junansu, amma izza ta hanasu bama juna kulawa sai dai su yi magana ta text message, tamkar basa a gida ɗaya.

fita tai daga gallery ta shiga wurin messages dinsu

Har ta rubuta "I miss u.... ' sai kuma ta goge, zuciyarta na raya mata zubda aji ne ta nuna ta damu dashi, shi ne yakamata yafara yi mata magana

Jefar da wayar tayi gefenta, tare da kai hannu taja lallausan duvet dinta ta lullu6e fuskanta, ganin hakan yasa Yazrin fitowa daga bayan labulen cikin sanɗa ta nufi gadon, tare da hayewa ta janyo wayar Nazli cike da fargaba cikin sa'a ta ɗauko ta batare da security din wayar ya shiga ba, hakan ba karamin dadi yayi mata ba.

Whatsapp dinta taso ta shiga sai dai kash password Ya hanata, tunani ta soma yi me Nazli ta rubuta a matsayin password dinta?

Gudun kada ta tayi mistake ta samu matsal

Zurfi tunani ta shiga, can zuciyarta ta raya mata cewar ta jaraba rubuta date of birth din Aki Owais saboda ta ta6a ganin ta rubuta shi a diary din ta amatsayin rana mafi mahimmanci agare ta.

Wani irin tsalle ta daka ganin Ya buɗe, da sauri ta shiga nutsuwarta tana leƙen Nazli, wadda tuni bacci yayi awon gaba da ita

Yazrin tayi mamakin ganin tsawon lokacin da suka dauka ba suyi magana wa junansu ba, Ranta ya sosu bata ji daɗi ba, ji take kamar ta dauki pillow ta bubbuga mata akanta tsabar haushin da taji.

"Ƴar bakin ciki, In sha Allah baki da miji a duniyar nan daya wuce big bro, bazan zauna na zuba maki ido kina cutar kanki ba, Akhi Owais shi ya dace ya mallake ki, nayi maki sha'awar auran shi saboda samun miji nagari irin shi ba abu ne mai sauƙi ba, Ina son kiyi rayuwar farin ciki yar uwata, dole na shirya tsakaninku.... " acikin zuciyarta ta furta maganar tare da cigaba da danna wayar, daga wayarta ta tura video din data dauka, kaitsaye ta yi mashi sending, shaf shaf ta rubuta mashi text message da harshen turanci kamar haka

_Nayi kewarka bugun zuciyata, ina mai baka haƙurin nuna halin ko'in kula da nayi, ba'asan raina ba, nayi danasanin hakan don ba ƙaramin cutuwa nake yi ba na rashin jin ɗumin jikinka a kusa dani, ka duba whatsapp in ka, na tura maka video dina don ya ɗebe maka kewar rashi na, nasan zaka ji dadin kallon shi_

fuskar yazrin dauke da murmushin mugunta ta tura mashi message din, bayan ta gama ta ajiye mata wayarta, ta nufi kofar fita daga dakin tana faman sakin dariya, ta riga da tasan me zai biyo baya muddin Nazli taga aika aikan da tayi mata ba ƙaramin husuma zata tada ba, zata ce ta zubda mata aji awurin chief owais.

*A GIDAN UNCLE ƊAN IYA*

Kusan Atare Su ka yi Parking din motocin su, Mahboob ne Ya fara fitowa daga front seat hannun shi ɗaya ruƙe da key din Motarshi, fuskarshi dauke da murmushi yake kallon Motar zahra.

"Sannu da dawowa Hajiya Zahra Surukar Kaka Obinna" Ya faɗa tare da buɗe Back Seat din Motar Shi Ya duƙar da kai Yana leƙan Baby Junaid dake zaune Hannayenshi rungume da Food basket dinshi, Ga school bag din shi a gefe, Sai faman ɗaure fuska Yake, Da alama rigimar tashi ce ta motsa.

"Ranka Shi daɗe, Mun ƙaraso gidan, zaka iya takawa da kafarka ne mu shiga ciki ko kuwa ni kake so In goyaka"? Da zolaya mahboob yayi maganar yana dariya.

Yamutsa mashi fuska baby junaid yayi "ni ka goyani" Ya fada A kule.

Juya mashi baya Mahboob Yayi Ya ɗan zuƙunna Baby Junaid Ya Haye bayan nashi, Bayan Ya miƙe Ya ɗauko mashi Backpack dinsa tare da kwandonsa

Adai dai Lokacin Zahra Ta fito daga motarta, tayi shiga cikin Lafaya, Hannunta ɗaya ruƙe da Ƴar purse dinta

Fuskarta da fara'a take duban Baby Junaid Da Mahboob

"yau wata rana mun dawo gida atare, baby junaid dina zo nan" ta faɗa tare da miƙa mashi hannu, babu musu Ya soma kiciniyar saukowa daga saman bayan mahboob, daukarshi tayi Mahboob yace"Wato ni kake gudu? Zamu hadune ɗan rainin wayau, tun da naje dauko shi Daga school Yake ta jin haushina saboda naje amakare shi kaɗai Ya rage ba'aje daukarsa ba, baisan nima bada son raina ba, Motarce ta samu matasala sai da nakaita gyara tukunna naje daukoshi da ita"

Dariya zahra tayi"Gaskiya baka kyauta ba, taya zaka bar mana Baby Shi kadai Ga yunwa, meyasa baka kirani awaya naje daukosa ba"

"Banyi dabarar yin Hakan ba, Yanzu dai tun da mun dawo gida, gashi nan ki kaima jatumarsa, nagaji da kallon kumburarran fuskarshi"

"Mahboob baka da mutunci, zamu rama ne" ta faɗa tana dariya, baby junaid kuwa Ya ɗaure fuska, Kumatunshi sunyi jawur da su, da alama kuka Yake so yayi.

Atare suka nufi cikin gidan, tana agaba mahboob Yana abayanta

Bayan shigarsu Falo, Suka taras da mami da Ummi zaune suna kallo a plasma tv din falo, Cikin girmamawa suka gaishe da su.

"Sannun ku da dawowa, Ya gajiyar aiki"? Cikin Kulawa mami tayi maganar, atare suka hada baki wurin cewa"yawwa mami"

Ummi dake kallon Baby junaid tace"to fa, Me akayi masa ne naga yana ɗaure fuska"

Mahboob Na dariya Yace"wallahi Ummi Rigimarshi ce ta motsa, Kinsan Halin shi.
Chapter 8 · 0% Book details