← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 207 OF 238

Sashe 207

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata yi aune ba, unexpectedly glass din madubin da take fuskanta ya fara tsattsagewa, a razane ta ƙura ido tana kallon abun mamakin gani take kamar idanunta ne ke nuna mata ba dai dai ba, dama bata a cikin hayyacinta damuwa ta fara zautar da ita, miƙa hannu ta yi da niyar ta shafa madubin don ta tabbatarwa kanta abunda take gani gaske ne ko ƙarya kwatsam! madubin ya tarwatse da kan shi glass din ya zubo kan floor, har ta kware baki zata fasa ƙara ta ji an fusgo hannuwanta izuwa cikin madubin, ta ƙarfi da yaji ake kokarin janta cikin shi, fashewa ta yi da matsanancin kuka na tashin hankali ta dinga yan buge-buge tana ƙoƙarin kufcewa yayin da hannayen da suka rurruke nata suka ja kusan rabin jikinta cikin madubin, daddagewa tayi da iya ƙarfinta na ƙarshe ta shiga karanta ayatul kursiyu bata kaiga direta ba ta ji an wurgo da ita gaba ɗaya gangar jikinta ta dawo cikin toilet ɗin kanta ya daki floor, A zabure ta miƙe ta watsa a guje ta nufi ƙofa sai dai me? Kafin ta ƙarasa ƙiiiii taji kofar ta datse kanta, fasa ƙara ta yi da ƙarfi take ambaton sunan Yaya shyureim dana Mommyn su don su kawo mata a gaji, bugun kofar ta dinga yi kamar zata 6alle ta, gurnanin mutun ta jiyo a bayanta jiyowar da zata yi keda wuya tayi arba da wani gabjejejn mutun ƙaƙƙarfa jikinshi sanye da baƙaƙen kaya ya rufe ko'ina na jikin shi, zazzare mashi idanu ta yi kamar mai fama da farfaɗiya ta dinga farfari zuciyarta na bugawa da tsananin fargaba ta dinga sambatu tana fadin, "Na shiga Uku!!! Wanene kai? Wallahi kada ka ta6a ni, kada ka matso kusa dani, zan ƙona ka da ayar Allah..., bata ƙare maganar ba ya ɗaura gabjejen tafin hannunsa kan wuyanta ya damƙe shi ya jata tana kuka da yan buge-buge ya nufi bathtube da ita, wani irin ruwan zafi ne ya kwararo ta cikin faucet har tiriri yake yi kamar za'a zabka kaza haka ya soma ƙoƙarin tura kanta cikin ruwan, wanda hucinsa kaɗai bala'e ne tsaf zai ƙona fatar mutun, fashewa tayi da kuka tana ihu ga bleeding da hancinta ya fara yi,

Sai yakushin hannunshi take yi don ya saketa, yana gab da zai tsumbula kanta cikin ruwan, ta furta wata addu'ar neman tsari da Dr Shureim ya koya mata, wallahi ko second ba a ƙara ba mutumin ya 6ace 6aat hasken toilet din ya daidaita, madubin ma ya maida kansa yadda yake, hannunta dafe da wuyanta dake mata raɗaɗi take kallon Ikon Allah, Wato addu'a tayi a rayuwa musamman in kayi imani ba tare da kokwanto ba, ganin ya 6ace yasa ta zabura aguje ta nufi kofar toilet ɗin ta dinga bugunta daƙyar ta samu ƙofar ta buɗe sai dai kafin ta fuce wani irin jiri ya ɗebeta gaba ɗaya ta yanke jiki ta faɗi yaraf har goshinta ya fashe sakamakon dakar floor da kanta ya yi.

Hankalin Anila dana Taj ba ƙaramin tashi ya yi ba, Sun yi matuƙar girgiza da jin abunda ke faruwa da Benazir.

"Kin taba faɗa ma wani?" Ɗaga kai ta yi,"Eh, Yaya Shureim ne kadai ya sani, amma ban faɗa masa na ranar dana shiga toilet ba saboda ban farfado cikin hayyacina ba.

Cike da al'ajabi yake ɗan jinjina kanshi yayin da zuciyarshi ta cika fam da tashin hankali, Komai da suka faɗa yayi shige da case din da suke aiki akai, yanzu ya fara yarda da abunda Anila ta faɗa masa akan Benazir.

Chief ya kira bayan ya yi picking gaba daya ya fayyace masa abun da su Aneelarh suka sanar da shi, tashin farko ya ce wannan babban al'amari ne, kuma ya ji dadin zuwan su, in ba damuwa su jira shi ya dawo yana son yin magana da su.

Ɗagowa ya yi tare da kallon su Aneelerh, "Ya buƙaci yana son magana daku, zaku iya jira har lokacin da zai dawo?"

Aneeleerh ta ce, "Ba damuwa zamu jira shi"

Faɗa mashi ya yi kafin su ka yi sallama ya aje wayar gefen ta Ana...

"Naga baku sha fruit din ba," Ya ɗan tambaya idanunsa akan Benazir dake ta kallon shi..

"Ni wlh hankalina kwata kwata ba a kwance yake ba, bana jin cin komai"

"Look Aneelerh, Ki kwantar da hankalin ki, tun da har ku ka yi dubarar tuntu6armu in sha Allah komai zai tafi dai dai" jinjina kai ta yi ..

"Ina su Unaisah ne?" Benazir ce ta tambaya

"Suna a daki" ya bata amsa batare da ya dubeta ba...

"Zan iya ganin ta" girgiza mata kai ya yi"A'a!"

"Meyasa? pls Taj, almost one month ban ji muryar ƴata ba? Dan Allah meyasa ka ke yi min haka? Laifin da na yi maka tsakanina da kai ne, banga dalilin da zaisa ka shiga tsakanina da ƴata ba, saboda ni na yi wahalar naƙudarta na kuma haifa maka ita..." ranta a 6ace ta yi maganar tana aika masa da harara.

"Sau nawa kina yunƙurin zubar da cikin nata don kada ya 6ata maki shape?"

Bai ƙare maganar ba Anila ta yi saurin furta, "Dan Allah Taj ku daina, ba girman ku bane, bai kamata aji maganar nan daga bakin ka ba, Benazir koda da son ranta ta gudu tabar Unaisah amma ai tayi nadama ko? Allah ma muna yi masa laifi ya yafe mana yakamata kaima ka yafe mata."

Murmushin gefen fuska ya ɗan saki, "Ni zolayarta nake yi, amma komai ya wuce awurina, sannan ni ba hanata Unaisah na ke yi ba, tayi rashin lafiyane har kwantar da ita asibiti saida aka yi, bana so na ɗaga maki hankali ne shiyasa ko kin kira bana ɗagawa ....."

Bai ƙare maganar ba sakamakon kalmar Innalillahi wa'inna ilaihirraji"un da Benazir ta furta tare da miƙewa tana yarfa hannu ta furta "Meke damunta ne? Wani irin ciwo ne ta yi? Don Allah ka haɗa ni da ita! Dama saida na ji a raina wani abu na faruwa da ita, har mafarkinta nake yi ashe bata da lafiya...." Ta faɗa har hawaye sun zubo kan fuskarta,

Da damuwa akan fuskar Anila ta ce, "Taj, meke damun Unaisah ne? Meyasa baka sanar dani ba?"

"Calm down your mind, Unaisah ta ji sauƙi yanzu, bari na kirata ku gaisa."

Ya faɗa tare da ɗaukar wayarsa yana ƙoƙarin danna mata kira Unexpectedly suka jiyo shesshekar kukanta!

Kusan a tare suka kai duban su gare ta, tana a tsaye jikinta sanye da Satin fitted gown black colour tabi shape dinta, bata ɗaure sumar kanta ba,ta sake ta har mid back dinta, ƙafafunta na sanye da highhill masu ɗan banzan tsini....

Jikinta sai kerma yake yi kamar mazari, yayin da idanunta dake fitar da hawaye ta tsayar da su akan Benazir, ashe tunda Taj da Benazir suka fara sa'insa ta fito daga daki kaitsaye maganganunsu suka sauka acikin kunnanta.

"Daughter meyasa kike kuka? Ko jikin ne?" Da damuwa akan fuskar Taj ya tambaya.....

Da index finger ɗinta ta nuna Benazir,

"Dama kece mahaifiyata wadda ta haifeni a wulakance! ta barni a cikin kwamin wanka sannan ta gudu ta tafi ta barni! Dagaske kece Aunty Benazir?"

Rai a matuƙar 6ace ta faɗa da tsiwa tana fitar da numfashi mai huci.

"Ki amsa min tambayata??" Ta faɗa tana zare mata gray eyes dinta...

Tsabar ruɗu da tashin hankali ya hana Benazir furta kalma, wani irin shakkarta take ji....

"Shirun da kika yi ya tabbatarmin da abunda kunnuwana suka jiye min."

Ta faɗa tare da maida kallonta akan Aunty Aneelerh cikin jin ƙunar rai ta ce,"Aunty Aneelerh, I know you won't lie to me tell me, who is she?"

Yawu Aneelerh ta haɗiya ƙutt, cikin sanyin murya ta ce,"Pls Unaisah, zo ki zauna za mu yi maki bayanin komai..."

Fashewa tayi da kuka tare da girgiza kanta, "Daddy, Aunty Aneelerh meyasa kuka 6oyemin cewa itace matar nan data gudu ta barni? Kuka sani na je nayi jinyarta a asibiti, bayan kunsan irin tsanar da tayi mini, bata taba sona ba, wallahi dana san kece bazan taba yin jinyarki ba koda zaki rasa ranki ne" with a burning heart ta faɗa tana aika mata harara.

"Why didn't you kill me at birth if you couldn't care for me? You left me in the bathtub and abandoned me for years, You never thought to return and check on the child you left behind!, wlh hakkina kaɗai bazai bari ki gama da duniya lafiya ba...."

Bata ƙare maganar ba sakamakon tsawar da Aunty Aneelerh ta doka mata, "Unaisah ya isa! Ya isa haka!! Har yanzu ita mahaifiyar kice, karna kuskura na ƙara jin kin gaya mata maganganu marasa daɗi"

Fashewa da kuka Benazir tayi, baiwar Allah tama rasa ina zata tsoma ranta taji dadi.

"This woman will never be my mother! I don't like her, I hate her, I don't want to see her, You're heartless and don't deserve to be called a mother! Dan Allah na roƙe ki ki fuce daga gidan nan in har ba so kike ni in bar maki gidan ba"

Cike da takaici Taj ya dafe forehead ɗinsa da tafinsa, dama saida yayi fargaban zuwan ranar nan, shi yasan za'a rina saboda Unaisah ta ƙullaci Benazir aranta, haushinta take ji sosai, tsanar ta samo asali ne tun daga kuruciyarta.

Bata saurari kowannan su ba ta juya a zafafe ta nufi kofar dakinsu, da gudu Benazir tabi bayanta ta kai hannu tare da ruƙo hannun rigarta, aikuwa cikin fushi Unaisah ɗin ta bangajeta har saida ta yi taga taga zata faɗi, cikin sauri Aneelerh da ta biyo bayanta tayi saurin tallabota.

Rushewa ta yi da matsanancin kuka tana fadin wai ƴar da ta haifa ce ta ke gaya mata magana kamar zata doke ta? "My own daughter calls me heartless! Na shiga Uku Aneelerh ta tsaneni bata son ganina! Wayyo Aneelerh zuciyata zafi ta ke yi min..."
Chapter 207 · 0% Book details