Sashe 33
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Shikenan, yanzu ki faɗa min ina ƴar uwarku Unaisah? Muna cikin magana da ita ɗazu aka kirani awaya sai naje amsa kiran kafin nadawo na taras bata nan, Ko kinsan inda take"!?
Sai da ta ambaci sunan Unaisah batool tafara kyafkyafta idanunta tana bin dakin taron da kallo, sai yanzu ta tuna da tsawon lokacin da bata ga gifcin unaisah ba, kuma bata cikin masu yin rawa, nan fa hankalin Batool Ya fara tashi ta fara ƴan waige waige fuskarta a yamutse babu nutsuwa
Ganin yadda ta ɗaga hankalinta ne yasa Zahra cewa"ko kema bakisan inda taje bane" ɗaga mata kai batool tayi muryarta adabarbace ta furta"ban..bansani ba, bamu jima da rabuwa da juna ba, atare muke zaune can mu da su chief kafin tashin ta" ta fada Tana nuna mata wurin..
Ruƙo hannun batool zahra tayi "zo muje mu nemo ta," da sauri batool tabi zahra suka soma bi sako da lungu na hall din suna neman Unaisah, ba tare da sun fada ma kowa ba ...
____________________________💋✍️
Jin ta ruƙo hannunshi yasa shi yin sauri fusgewa Yana bin ta da kallo mai cike da fargaba
Jikinshi har kerma yake yi saboda matar bata kwanta mashi aran shi ba,
Murmushi ta ɗan sakarmashi cike da fargabansa ta furta"kayi haƙuri dan Allah, bawani abu zanyi maka ba, Inaso mu yi hoto ne" ta fada tana nuna masa i phone din hannunta, maƙe mata kafaɗa naufal yayi muryarshi da yar tsiwa tamkar zai fashe da kuka yace"banso, Ni ki ƙyale ni, kuma wallahi ki daina kallona," Ranshi a6ace yayi maganar, arude hajjaty ta soma lallashin shi gudun kada ya janyo hankalin mutane gare su.
"Dan Allah ka yi hakuri, Idan na bata maka rai, alfarma ɗaya nake nema a wurinka, Ka fada min sunanka"?
Harara naufal ya wurga mata, Yana faman haɗe rai yace"sunana Sajeed"
Tuni yanayin fuskarta ya canza, tayi zaton zataji irin sunan ɗanta,
Gyaɗa kai tayi"masha Allah, Allah yayiwa rayuwarka albarka, amma baka ga muna kama da juna ba"? ta faɗa da fara'a akan fuskarta, Ta6e baki naufal yayi alamar ta takura masa hada ɗan bubbuga kafafunsa"Ni bani kama dake, bansanki ba, dan Allah ki ƙyale ni, In shaƙi iska" yanayin yadda yayi maganar yaso bata dariya,
"Naji zan ƙyaleka, ka shaƙi iska but pls ka bari na dauki hoto dakai"!
Juya mata ƙeya yayi atakure yace"sai dai ki ɗauki bayana" dariya tayi sosai tana kallon bayan shi.
"Kaga dan Allah ka juyo na dauki fuskarka, Ita nakeson gani, Harma In nunawa Mijina shima yaga mai kama dani" maƙe mata kafaɗa naufal yayi alamar a'a.
Magiya tadinga yi mashi amma yaƙi juyawa, ta rasa ya zatayi da shi.
Sajeed da ke ta kallon su, baisan me suke tattaunawa ba, A hankali Ya nufo su,
"Bro, meke faru ne"? Ya faɗa yana kalon fuskarshi dake a daure
Da yatsan hannu ya nuna mashi hajjaty dake abayn shi"matar nan ce ta ɗazu da take ta kalllona, shine ta biyu ni wai dole sai ta dauke ni hoto ni kuma nace mata bana so"
Ɗagowa naufal yayi su ka haɗa ido da Hajjaty, harta bude baki zatayi mashi magana sai kuma ta fasa, saboda ganin suffar Sajeed kamar zaifi naufal din taurin kai, a tunaninta amma ga mamakinta sai ji tayi yace mashi"to meye aciki? Ba hoto kawai ta buƙata ba"? Ɗaga mashi kai naufal yai, Ruƙo hannunshi sajeed yayi" dallah juya kaje ku ɗauki hoton, In ba haka ba bazan ƙara taimaka ba wurin koya maka karatu" ba don yaso ba, ya juya yana jifar hajjaty da harara kwayar idanunsa kamar zasu faɗo ƙasa,
"Nagode sosai, Kai meye sunanka"? fuskarta dauke da murmushi ta tambayi Sajeed, Kafin yai yunkurin bata amsa naufal yai sautin cewa Sunan shi Naufal, Wani kallo Sajeed Yayi mashi da ruɗani akan fuskarsa jin Ya canza mshi suna, da ido yai mashi alamar da nan take ya gane me yake nufi wato Ya faɗa mata sunan sa amatsayin nashi, shine yace shi sunansa Naufal
Jim ta ɗanyi har cikin zuciyarta sunan ya dake ta, Taso ace mai kama da itan ne yake da suna Naufal sai dai kash shi sunan shi Sajeed.
"Kawo wayar nayi maku hoton" da sauri ta miƙa ma sajeed wayar ya kar6a, ya soma daukarsu hoto, Hada kokarin Jan naufal Ya matsar dashi jikin hajjaty gaba ɗaya ya takura mashi, duka hotunan sunyi bala'en kyau kamar ɗan ta, sai dai fa babu fara'a akan fuskar naufal har ya kammala daukar su, hajjaty ta kar6i wayar tana yi masu godiya.
Suma su jamimah anyi masu hotuna tare da Sir mubarak da Mom turai, harta su Zaki sai da su kayi hotuna da su, kamar ƴan uwan juna.
Haka zalika Su Haris da Javed suma hada su akayi hotunan, kowa ya yi kyau ana ta kwasar shagali.
Hajiya saratu dake ta faman satar kallon parveen duk in da tayi akan idonta, ta sanya mata ido sosai, tsabar ji da kai ne ya hana ta nemi alfarmar ta su dauki hoto atare, sai ta koma tana daukarta a fakaice da wayar hannun ta ba tare da ta ankara ba.
Hankalin Batool ba karamin tashi yayi ba, Ko'ina sun duba ita da zahra babu Unaisah, Jikin ta har Ya fara kerma tsabar tashin Hankali, sune har wajen hall din neman Unaisah, Dawowa ciki su kayi cike da fargaba, can zahra ta tuna da akwai restrooms a dakin taron, ajiyar zuciya ta sauke tare da kallon batul tace su ɗan jirata, watakil ta shiga toilet ne, zama sukayi a table daya ita da batool suna jiran unaisah ta fito.. ..
*Chief Owai*
A tsaye yake a wani area dake a hall din, Ya juya bayansa, hannunsa ɗaya ruke da phone dinsa yayin da dayan hannun ya zuba sa a trouser pocket dinsa, bai jima da kammala yin wayar da ta yi silar tada sa daga wurin zaman sa ba.
Layin boss Ya danna ma kira bugu ɗaya yayi picking.
Muryarsa ƙasa ƙasa tamkar ta me yin raɗa ya furta" ina fata ka same su lafiya"?
On the other hand muryar boss ta karade kunnansa"tun dazu na shigo gidan, suna nan cikin koshin lafiya yalla6ai, yanzu haka ina atare da salsabeel sai fada yake min wai jiya hankalinsa ba akwance yake ba, sun ji shiru Dr jazz bai leƙo su ba, sannan mu ma bamu kira ba kamar yadda muka sama"
Daga can cikin wayar yajiyo muryar salsabeel yana fadin"ka fada masa jiya ko isasshen bacci ban samu ba, deeja ta hanamu sukuni daga ni har ƴan uwanta daƙyar na samu yarinyar nan tayi bacci".
Lumshe ido yayi ahankali Ya furta" Please tell him I'm sorry. It won't happen again. We were busy with dinner preparations yesterday. in sha Allah, cikin kwanan nan zasu baro anguwar nan su dawo cikin ƴan uwan su"
Taj yace"amma naji dadi Yalla6ai, saboda bani da burin daya wuce inga an haɗa kan yaran nan, su gana da ƴan uwansu, hankalin su sai yafi kwanciya"
Sun ɗan jima suna yin wayar, kafin daga bisani su ka yi sallama, tunkafin ya sauke wayar daga kunnansa daddaɗan ƙamshin turarenta ya daki hancinsa har sai da lumshe idanunsa saboda yadda fragrance din Ya ratsa shi, tuni ranshi ya bashi cewar itace saboda haddar turarenta da yayi
Shiru yayi batare daya juya sun fuskanci juna ba, sai ma ya ci gaba da danna wayarsa.
Sautin tarin ta da yaji ne yasa shi saurin juyawa yakai idanunsa saitin inda take, hannunta ɗaya dafe da gefen cikin ta, ɗayan hannun kuma yana ruƙe da Mayafinta da ya zame, lallausar sumar kanta ta lullu6e bayanta baƙa wulik da ita, babu alamun tasan da zaman shi a wurin, yanayin ta kamar bata a hayyacin ta, ganin tana kokarin faɗuwa kan fillow yasa shi yin saurin nufarta, ya sanya hannu ya janyota gaba ɗaya ta fada kan broad chest dinsa, luf ta kwanta masa, ta daddafe waist dinsa da hannunta, yana iya juyo fitar numfashin ta da sauri da sauri, hankalinsa ba karamin tashi yayi ba.
"Nazli! Are you okay? What's wrong? Are you alright?" a ɗan ruɗe ya yi maganar.
Ƙara ƙanƙameshi tayi muryarta da wani irin sanyi da zaƙi ta furta"bana jin daɗi, kaina da ciki na ciwo su ke min, sannan bana son hayaniya, kwata kwata bana son zama awurin nan" yanayin yadda take yin maganar ba karamin narkar masa da zuciya yayi ba, ƙamshin turarenta ya kanainayesa.
"Bana son zama anan, rikicewa nakeyi" cikin wani irin salo take maganar, Nazli karshe ce, babu namijin da zai haɗa jiki da ita batare dayaji sauyi atare da shi ba, koda kuwa zuciyarsa dutse ce.
bakomai yasa shi yadda da kalamanta ba, face sanin lalurarta na rashin son hayaniya, tun da kuruciyarta, daga bayane ta samu sauƙi bayada likitoci suka tsaya tsayin daka don ganin ta dawo normal, tunaninsa abunne ya dawo mata yan zu shiyasa ya aminta da ita......
Yanke shawarar fita yayi da ita daga hall din kota samu lafiyar jikin ta,
"It's okay, Let's go. I'll take you home and you can rest."
maƙe mashi kafaɗa tayi tana fadin"I can't walk. My legs hurt."
Kallon takalman kafarta yayi wasu matsiyatan high hills ne masu tsini na fitar shariya, irin takalman da tafi sha'awar sanyawa kenan, mafi yawan lokutta suna jaza mata ciwon ƙafa, sai da ya fara duddubawa ya tabbatar babu mai kallon su, kafin ya sanya hannu ya ɗauketa gaba ɗayanta Ya nufi second door da ake fita hall din bai bi ta ainihin kofar fita ba, don bayason wani yagansu.
Bayan sun fita, yayiwa ɗaya daga cikin sojojin dake tsaron ƙofar magana akan ya kawo mashi motarsa, bayan ya miƙa masa key, jim kadai sai gashi ya kawo motar, ya fito tare da buɗe masu, a backseat ya shigar da Nazli, sai faman lumshe idanunta takeyi masu kama dana ɗawisu saboda kyau
Cikin kulawa yace"Calm down, He will take you home."
ya fada yana nuna mata sojan daya kawo masa motar, girgiza mashi kai tayi da wata irin kasalalliyar murya tace"I want you to take me. Don't you have time for me?" She bit her soft, pinkish lips.
"Tomorrow, I will leave the country. I am not sure if we will meet again,"