← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 238

Sashe 91

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana shuga ciki ta iske shi akan hanger, tunawa tayi da jinin daya dawo mata gadan gadan adaren jira aranta ta ayyana shima dagaske ne ko duk cikin mafarkin ne"? Ta kare maganar tare da buɗe laps dinta ta laluba jikin ta, bata ga komai ba, sai dai wani farin ruwa mai yauƙi yauƙi dake gangarowa...

Gaba ɗaya ta gama rikicewa, tunaninta ya kasu gida biyu, ta jima a toilet din kafin ta fara tunanin yin wankan

Bada jimawa ba, ta fito sanye da rigar wanka, har ta kusa isa gaban mirror tajiyo bugun kofa,

"Wanene"? ta fada tare da kallon ƙofar

"Daddyn ki ne..." sanyi taji ya ratsa zuciyarta, da sauri ta nufi kofar ta buɗe mashi

Tun daga kasa ta fara kallon shi, jallabiya ce a jikin shi maroon colour, sai kamshin turare ke tashi a jikin shi

"Daddy, Ina kwana..." bata ƙare maganarba, ganin yadda yake binta da kallo mai tattare da ruɗani

"Unaisah! Baki da lafiya ne? Meya faru naga fuskarki ta kumbura tayi ja, kamar kinyi kuka..." wani irin mugun bugu kirjinta yayi, babban tashin hankalinta kada ace abunda Ya faru jiya dagaske ne, ba mafarki ba

Muryarta adabarbace ta furta"da.. ddy.. lafiyana lou, meka gani ne."?

girgiza kai taj yayi"no ban yarda ba, fada min ko dai wani ya buge ki ne"?

"Wallahi daddy ba komai, watakil ko dan saboda firar da muka tsaya yi jiyane ban samu isasshen bacci ba shiyasa fuskata ta kumbura..." kwata kwata hankalinsa bai kwanta da yanayin ta ba, janyota yayi tare huggin dinta, ya daura hanneyensa akan bayanta

"Nayi missing dinki my daugher, ina fata kin tashi lafiya.."

"Lafiyalou daddy ..." dago da kanta yayi"baki jin ciwon kai? Ko zazza6i haka"

Ƙaƙaro murmushi tayi akan fuskarta duk don ta kwantar mashi da hankalin shi

"Bana jin komai daddy, ni yau da karfina na tashi..." ajiyar zuciya ya sauke

"Okey, ki shiga ciki ki karasa shiryawa, Chief Yana son ganin ki" waro idanu waje tayi alamar mamaki

"Daddy ni kuma? ɗaga mata gira yai alamar eh

"Ki sanya kaya masu kyau, zan jira ki awaje" cike da mamaki ta amsa mashi da toh,

Bayan fitarshi cikin sauri ta nufi closet dinsu, ta dauko wasu hadaddun riga da wando ƴan pakistan, rigar fara wandon yellow, veil din kayan yellow, ita kanta data sanya kayan saida ta jinjina ma kyan da sukai mata, gaban mirror ta zauna ta fara gyara sumar kanta dakyar take sharce ta da comb, bayan ta kammala gyara gashin, ta shafa powder da lipstick, kafin tayi rolling veil din akanta, takalma ta dauko masu tsini ta zura su a kafafunta,

Komawa tayi gaban mirror ta feshe jikin ta da turare

Har lokacin bata daina tunanin abun da ya faru a daren jiya ba, was wasi take tayi aranta.., kwata kwata bata so ya zamana gaskiyane abun da ya faru da ita....

A hankali ta zura kafarta ta fito daga dakin,

Walking slowly ta nufi daddyn ta dake atsaye yana jiran ta, babu kowa a falon da alama basu kaiga fitowa ba

"Daddy yunwa nake ji, Ciki na babu komai.." ta fada yayin da ta ruko hannunsa acikin nashi

"Kada ki damu, nima banyi breakfast ba, idan munje wurin chief din zamuyi atare da shi..." amsa mashi tayi da toh

Kaitsaye suka nufi walkway bata san ina za su bula ba

"Daddy ba part dinsa zamuje ba"?

"Eh, yace mu same shi a backyard..

Zazzaune suke akan wasu jigunannun sofas ƴan ubansu, backyard din ya Haɗu an ƙawata shi sosai, chief da hajiya saratu suna a zaune kan sofa daya, Aneelerh da zahra suna fuskantar su, tun da suka zauna Aneelerh take ta jinjina ma haduwar gidan da shi kanshi mamallakin gidan wato chief, kallo ɗaya tayi mashi saida gabanta Ya faɗi, ya ɗauki wankan suit navy blue sunyi bala'en yi mashi kyau

Zahra dake satar kallon shi, gani take kamar a mafarki yau gata ga director general na isod, crush ɗinta, mutumin da tayi haukan son shi a lokacin baya..

Round table din dake a tsakiyarsu, cool drinks ne da Snacks asaman hadadden wooden tray

"Idan muka baku aron yarinyar sai yaushe ne zaku dawo mana da ita.."? Hajiya saratuce tayi masu tambayar

"Idan da hali har zuwa lokacin da benazir din zata ji sauƙi, dan Allah ayi mana alfarmar nan..." gyaɗa kai hajiya saratu tayi"okey, amma fa zaku bani tukuici tun da ni nayi maku hanya a wurin chief..." ta faɗa da yar zolaya tana kallon su

Murmushi suka saki zahra tace"bakomai mommy, ay duk abunda kikeso zamu baki.." yar dariya tayi"zolayarku nakeyi..." dariya sukai su kansu sun san tafi karfin tukuici, ta dai faɗi ne don ayi raha...

Kwas kwas sautin takalmanta Ya ratsa kunnuwansu, kusan atare su Aneelerh suka dago tare da kallon inda sautin ke fitowa....❓

*Daga alkalamin Boss Bature mu haɗu next page on monday idan Allah yakaimu da rai da lafiya✍️*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne dukanshi za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*

Sponsored Post
Tags
Kurkukun Kaddara
YOU MIGHT LIKE
POST A COMMENT
Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post
Next Post
GET IN TOUCH
Facebook
twitter
YouTube
Instagram
Whatsapp
SUBSCRIBE US

OPINION
FACEBOOK

COMMENTS
CATEGORIES
Africa
(1)
Al'adu
(1)
Alkamawa
(3)
Article
(3)
Blogger Tips
(1)
Economy
(5)
Education
(2)
Entertainment Gist
(1)
Gyaran-Jiki
(5)
Health
(13)
Jikar Iya
(11)
Kimiya
(1)
Kiwon Lafiya
(54)
Kukan Zuci
(5)
Kwalliya
(4)
Labaru
(23)
Lifestyle
(1)
Ma'aurata
(1)
News
(300)
Nigeria
(5)
Noma
(1)
Opinion
(3)
Picture
(3)
Politics
(15)
Profile
(2)
Q&A
(1)
Ramadan
(9)
Ramadan Tafsair
(1)
Siyasa
(1)
Sports
(72)
Tarihi
(5)
Technology
(1)
Tips
(3)
Video
(3)
YouTube
(5)
Zain Abeed
(1)
Zamantakewa
(1)
Novels Elite
Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content.

Novels Elite
SUBSCRIBE
Posts
Comments
Links
Post a Job

LATEST POSTS

ADVERT
Novels Elite
Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved
DMCA.com Protection Status
Disclaimer
Privacy Policy
Terms and Conditions

Buy bestselling books online
[14/10, 6:05 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite

Home
Kurkukun Kaddara
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 30
by
Novels Elite Admin
August 11, 2024
Sponsored Link
Novels Elite English
Kwas! kwas !! sautin takalmanta Ya ratsa kunnuwansu, kusan atare su Aneelerh suka ɗago tare da kallon inda sautin ke fitowa...

Ƙura idanu sukayi suna kallon su, kafin Aneelerh tayi wani irin yunkuri ta miƙe jikin ta na 6ari, zuciyarta na dakan uku uku, gaba ɗaya tabi ta rikice gani take kamar a mafarki take kallon su!! Kokwanto ta farayi anya kuwa sune? Tajudeen da Angel? Ko dai idanunta ne suke nuna mata badai dai ba? Tayaya mutanan da suka 6ace almost 16years yau kwatsam ta gansu, da ransu da lafiyar su, kanta ne ya wani irin sara mata da sauri ta dafe goshin ta, ganin hakan yasa Zahra ta miƙe a matuƙar ruɗe take kallon Aneelerh...

Lokacin da unaisah ta ɗaura kwayar idanunta akan fuskar Aneelerh, Ras taji gabanta Ya faɗi, wani irin burki taci ta dakata da yin tafiyar, idanunta azare take kallon ta, wlh ko amafarki taga fuskar Aneelerh sai ta shaida ta balle kuma azahiri, La66anta na kerma ta furta"Aunty Aneelerh? Daddy! Auntyna ne? Ita ne nake gani azahiri ba mafarki ba? Daddy wallahi itace aunty Aneelerh ce...." kalamanta ne suka dira akan kunnan Aneelerh, baiwar Allah jiki na 6ari ta watso da gudu mayafin ta har yana ƙoƙarin zamewa, da gudu unaisah ta nufe ta, takalman kafarta suka kusa kayar da ita kasa, amma ahaka ta jure don bazata iya jira aunty Aneeleeh ta karaso gareta ba, zubewa Aneelerh tayi akan gwiwowinta tare da ware hannayenta biyu ta rungume unaisah, tayi hugging dinta tightly lokaci ɗaya suka fashe da matsanancin kukan farin ciki mai tsuma zuciya 😖

A hankali taj ya ƙaraso Ya tsaya daga bayansu, tare da goya hannayensa bisa kirjinsa.

A sukwane hajiya saratu da chief suka miƙe tsaye suna kallon su, fuskokin kowan nan su ɗauke da murmushi su kansu da suka sake haɗa wannan zumunci ba karamin dadi suka ji ba, farin cikin da suka gani akan fuskar Aneelerh da unaisah ba zai misaltu ba.

Yadda Aneelerh ta rungume unaisah, kamar zata mayar da ita cikin cikinta, a kalla sun shafe mintuna goma manne da juna, kafin Aneelerh ta raba jikin ta daga na Angel, a lokacin itama ta durƙusa kan gwiwowinta, Aneelerh ta sanya tafukan hannayenta biyu ta tallabo fuskar unaisah da su, itama unaisah ta tallabo fuskar Aneelerh da nata tafukan hannun, suka kurawa juna ido yayin da hawaye ke sintiri kan fuskokinsu, cikin shesshekar kuka Aneeleeh take fadin"Angel dina! Kece nake gani? Dan Allah ki fahimtar dani nagaza yarda da abun da idanuna suke gane min! Wayyo Allahana.." ta fada tana jan numfashi.

"inna lillahi Ya Allah Idan Mafarki nake kada ku tada ni, kubarni kawai inci gaba da yin shi, Ya ilahi Angel dina ce..Ina kika shiga? Kika bar auntynki da ciwon rashin ki? Angel wayyo Allah...duk tabi ta susuce

Cikin muryar kuka unaisah tace"Aunty Aneeleeh, ni ce Angel dinki, ƴarki, Aunty Aneeleehna, ba mafarki kike Yi ba, ni ce dagaske, Angel dinki abokiyar firarki, mai sanyaki nishadi..." ƙara rungumeta Aneeleerh tayi.

Gyaran murya taj yayi cikin karayar zuciya ya firta"Aneelerh!.." kamar jira take yayi magana, a zabure ta mike ta tsaya agabanshi idanunta jawur ta furta"taj! kasan irin haukan rashin ku da nayi? Me nayi maka dana tsantsanci haka daga gareka?..." kwalar rigarshi ta damƙa da hannayenta biyu ta jijjiga shi kamar zata rufe shi da bugu taci gaba da fadin"taj meyasa kayi min haka? Meyasa ka gudu da unaisah kuka barni da kewarku? Taj kasan irin kunci da radadin dana naji a lokacin dana farka naga babu ku"?
Chapter 91 · 0% Book details