← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 238

Sashe 90

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Daddy me kakeso na baka? Ka fada min koma menene...." dariya sir mubarak yayi

"Farin cikin ka da kwanciyar hankalin ka nakeso .." dariya zaki yayi

"Ka bani mamaki son, ji bi yadda soyayya ta jigata ka, kamar ba dan sir mubarak ba...." sunnar da kanshi kasa yayi cike da jin kunyar daddynsa

"Ni kamarma na ta6a ganin yarinyar? Halan 6oye ta kake yi idan naje canada don kada na ganta ." girgiza kai yayi"a'a daddy, bana 6oyanta zaka iya saninta, duk wanda yaje gida sai yayi tsammanin yar aiki na ce, shiyasa baku ta6a lura da shakuwar dake atsakanin mu ba..."

"Gaskiya zanso inji meya faru da ita? Meyasa ta gudu tabar Yarta? Amma kaima da laifinka, fisabilillah ina maka kallon uztaz ashe har mace kake 6oyo agidanka, almost 16years haba zakina! Kunyi ma kanku adalci kuwa? Da hankalin ka ka ajiye matar aure kuma kasan guduwa tayi daga gida bakayi yunkurin neman danginta ka fada masu ba!meyasa"?

Ya faɗa fuskarsa adaure alamar baiji dadi ba

"Daddy sonta ne Ya rufe min ido na, nasan na aikata babban kuskure amma nayi nadama, kuma ni harga Allah ban ta6a neman ta ba, abun dayasa ban nemi kowa nata ba saboda ta faɗamin ta tsani danginta, bata son ta dawo Nigeria, nayi kokarin shawo kanta donta amince in dawo da ita amma sai tace idan na matsa mata zata kashe kanta ne, shiyasa na kyale ta, daga baya mijinta ya turo mata sakon saki ta wayarta, daga ganin hakan saina kara samun kwarin gwiwar killace ta agidana saboda in mallake ta........." cikin sanyin murya ya kare maganar yana kallon daddyn nasa,

"Kayi kuskure da baka sanar dani ba, ay da nayi maka hanyar auranta, yanzu koda ka hadu da ita zata iya bijire maka ta koma ma tsohon mijinta...." dafe kanshi yayi da hannu ɗaya"daddy ka tayani da addu'a, Allah yasa rabona ce..."

"In sha Allah zanyi iyakar bakin kokarina don ganin ka samu abunda kakeso.." ajiyar zuciya ya sauke, kafin wani ya kara magana a cikin su,

Sallamar hajiya turai ta katse su, atare suka amsa mata, ta shigo fuskarta dauke da murmushi"i'm sorry na katse maku firarku, my son barka dai, fatan ka tashi lafiya" da fara'a ya amsa mata"lafiyalou mommy,

Kallon sir mubarak tayi"na kammala shirya mana breakfast, ka taso muje kaci kada ka makara" ruko hannun zaki yayi acikin nashi atare suka mike suka nufi dining din

Adai dai lokacin, dr Jazz ya fito sanye cikin black trouser da shirt, Ya daura lapcoat akan kayansa, idanunsa manne da farin glass

"Barka da safiya daddy..."

"Yawwa Son, Harka shirya kenan"

"Eh,"

Ya faɗa tare da samun wuri kan dining chairs suka zauna, turai ta fara yin serving nasu

"Big bro Ina kwana.." murmushi ya sakar mashi kafin yace"lafiyalou, ina fata kaima haka" ya ɗaya masa kai alamar eh,

Har sun fara cin abinci, Ibad Ya fito daga shi sai ɗan short,

"Mommy ni an manta dani, shine ba a kirani inzo inci abincin ba . " ashagwa6e yayi maganar

Turai tace"sorry babyn zaki, Ay nayi zaton zaka jira ne Ya kammala in ya rage sai ka ci.." murmushi sukayi

"Oh wai har yanzu bai daina wannan ɗabi'ar ba"? Sir mubarak ya tambaya yana kallon zaki

"Daddy bai daina, abun nasa kullum ƙara gaba yakeyi, bansan ya zanyi da shi ba, har friends dina sun gane halinsa, Na cin sauran abincin da na rage...."kallon shi sir mubarak yayi da sauri ya juya baya yana faman noke kai

"Daddy pls kada kamin faɗa, ni wlh na saba, kuma nafi jin dadin cin ragowar abincinsa, daɗi Allah" dariya suka sanya gaba dayansu

"Calm down Your mind, kai fa last born ne, shalelan mommy da daddy, ba wanda zaiyi maka faɗa, kayi abunda kakeso" yaji dadin maganar turai,

"Zo ka zauna in zuba maka abinci.." da sauri ya samu guri ya zauna, Yana satar kallon daddyn su da jazz wanda tun ya zauna, hankalin shi baya atare da su, gangar jikinsa ce kadai atare da su ruhinsa yana wurin faryat daya kwallafa rai akai.

"Jazz kaci abinci mana! Salon sai ka makara ko"? Cikin kulawa Sir mubarak yayi masa magana

Kamar baisan cin abincin Ya dauki cuf of tea mai zafi Ya ɗan kur6a

"Daddy dan Allah kace ma yaya zaki mu koma toronto, ko dan saboda karatuna, in ba haka ba zaija amaida ni baya..." da damuwa akan fuskarsa yayi maganar

Harara zaki ya dan watsa mashi"kada na sake ji kayi magana!..."

Sir mubarak ya katse shi da cewa"ba haka yakamata kace mashi ba.." ya faɗa tare da maida dubansa ga ibad wanda Ya haɗe rai.

"Next month zaku tafi, in sha Allah"

Murmushi ibad yayi"yawwa daddy thank you.."

"Wato na lura gudunmu kake Yi ibad..

"No momy wlh saboda school, kuma na manta bibina a gida..." Yana nufi magensa, miƙewa jazz yayi"zan wuce" atare suka haɗa baki wurin yi mashi Allah kiyaye hanya, sai da yabi kowan nan su ya manna masu peck kafin ya tafi......

________________________________✍️

Tun da garin Allah ya waya, Aneeleeh ta rasa kwanciyar hankalin ta, ta kasa tsaye taka zaune kamar mai fama da ta6in hankali, tayi matuƙar kagara ta kosa hajiya Saratu ta kira zahra, duk bayan yan mintuna sai ta leƙa dakin zahra don ta ji ko ta kirata shiru har yanzu babu wani labari, kamar yadda ta matsu haka hajiya layla ta matsu suzo da yarinyar, itace ta fara farkar da ita daga bacci da sanyin safiya ta kira ta awaya, tana kara jaddada mata akan kada ta manta tayi kokari su yi magana da iyayen yarinyar, ta rasa ya zatayi gaba daya ta daura ma kanta damuwa, daren jiya dakyar ta runtsa..

"Aunty Aneelerh"muryar zahrce ta ratsa kunnanta, Jiki na rawa ta juya da sauri ta nufi zahra dake shugowa dakin, tana sanye da hijab, hannunta ruko da wayarta...

"Zahra ta kira? Ko har yanzu"? shiru zahra tayi fuskarta babu walwala.. Hakan ba karamin ɗaga hankalin Aneelerh yayi ba

"Kinyi shiru baki ce komai ba"? fuskarta dauke da matsananciyar damuwa ta furta"muyi hakuri aunty Aneelerh, ta kira tace wai yarinyar ba unaisah ɗinmu bace....."

"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..." Hankali atashe Aneelerh ta zabga salati tare da ɗaura hannayenta biyu akanta

"Nashiga uku zahra! Ya zanyi? Ga shi nayi masu alkawarin yau zanzo da yarinyar, dan Allah ki taimaka min zahra, ki nema mana alfarma awurin hajiya saratun su bamu aronta...." gaba daya tabi ta ɗaga hankalin ta...

"Aunty Aneelerh, ki kwantar da hankalin ki, tace muje gida mu same ta yanzu watakil ko zasu ba mu aronta ne.." nauyayyar ajiyar zuciya Aneelerh ta sauke, jiki na 6ari tace"bari na shirya sai mu tafi, mahboob Ya dawo ne"?

"Bai kaiga dawo ba" amsawa tayi da toh, da sauri ta nufi toilet ta shige don tayi wanka

Fitowa zahra tayi daga dakin, jikin ta duk yai sanyi,

Bayan sun kammala shiryawa,sai da suka fara zuwa dakin mami suka sanar da ita kiran da hajiya saratu tayi masu, mami tace Allah Yasa muji alkhairi, idan kun isa komai ake ciki ku kira ku sanar dani,suka amsa mata da toh...

Da matsakaicin gudu motarsu ta haura kan titi, Aneeleerh ce ke driving dinsu, zahara na zaune gefen ta..

"Auntyna ki bi a hankali mana, naga sai zura uban gudu kike kamar zamu tashi sama!

"Ba zaki gane ba Zahra, wallahi ji nake kamar inyi fiffike in karasa estate din, gani nake kamar bana sauri, ni dai burina Allah yasa su taimaka su bamu yarinyar..." zahra ta amsa mata da ameen,

Lokacin da motarsu ta karaso estate din, da sauri Aneelerh ta rage gudun motar, sunyi tsammanin security officers din zasu dakatar da su irin na jiya amma abin mamaki suna isa, da hannu sojojon suka yi masu alamar su wuce, gaba daya suka sauke ajiyar zuciya

Bayan sunyi parking din motar, suka fito daga ciki, adai dai lokacin Hajiya saratu ta fito daga entry hall na gidan, ta dauki wankan leshi, idanunta sanye da farin glass

Cike da zumudi suka nufeta, with respect suka gaishe da ita, fuskarta asake ta amsa masu kafin tace"bismilla muje" ta nuna masu motarta da hannu, su biyu suka shiga back seat, security din da zai yi driving dinsu yana a mazaunin driver, Hajiya saratu na daga gefen shi...

Kaitsaye motar ta nufi cikin estate din

"Kamar yadda nake fada maku, munyi magana da shi jiya, nayi masa bayanin komai dangane da zuwan ku, to a gaskiya yarinyar bata wurin ku ba ce, amma yace zai iya baku ita har zuwa time da ita patient din naku zata ji sauƙi...." fuskarta babu fara'a tayi maganar.

kallon juna zahra da Aneelerh su ka yi jikin su yayi sanyi lakwas...

Cikin karyayyar murya Aneelerh tace"hakan ma yayi mungode sosai..."

___________________________________✍️

Firgigit ta farka daga bacci tana faman zazzare gray eyes dinta tamkar kwayar idanunta zata faɗo kasa, hannun ta ɗaya dafe da goshin ta, numfashin ta na fita da sauri, kwata kwata babu kuzari a jikinta kamar wadda aka zarewa laka, ga wata kasala data baibaye sassan jikin ta, dakyar ta yunkura ta miƙe zaune tare da jingina bayanta jikin pillow, fuskarta ta kumbura suntum, kumatun sunyi jawur, haka la66anta ma sun dan kumbura, idanunta sun ƙanƙance kwarmin idon yayi ja daga gani ta jigata ba kaɗan ba...

Lokaci ɗaya ƙwaƙwalwarta ta fara tariyo mata abunda Ya faru da ita adaren jiya, runtse idanunta tayi sosai kwallar da ta taru acikin su ta fara ƴar tseral kan kuncin ta, ta rasa gane meya faru? Shin mafarki ne ko gaske? Kokwanto ta soma yi saboda zuciyarta tagaza yarda da abun da ya faru, was wasi ta kama yi tana faman tariyo komai daya wakana adaren jiya, babu wata alama da zata tabbatar mata da abun ya faru dagaske, da sauri ta dubi yar rigar jikin ta, tayi uban squeezing kamar an ƙwatota daga bakin kura, da sauri taja rigar ta rufe santala santalan laps dinta, ta sauko daga kan gado tana faman bin dakin da kallo, mirror chair ta gani yashe ta jirkice kan floor

"Ina wandona Yake"? Ta jefa ma kanta tambayar,

Ringing din wayarta ne Ya doki dodon kunnanta, jiki na rawa ta nufi toilet saboda tana tunanin kamar anan ta cire wandon
Chapter 90 · 0% Book details