← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 238

Sashe 83

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aneelerh na karasawa ta rungume hajiya layla batasan sa'adda kuka Ya balle mata ba

Shafa kanta hajiya layla tayi tana ɗan rarrashin ta, hakika tayi mamakin ganin yadda ta kara girma rayuwa kenan andade ba'a hadu ba, tun da zumuncin su Ya watse

Tsawon mintuna hajiya layla tana lallashinta, kafin ta dago idanu jawur ta gaishe da Alhaji ubaid fuskarsa da fara'a ya amsa mata har yana ɗan zolayarta

Aneelatu kece kika koma haka? Ƴayanki nawa? Cikin shesshekar kuka tace Yarona dayane Yana a school,

"Allah shi raya shi,

Tace"ameen"

"Ya hakurin abun da ya faru da su Uzair"?

"Mungode Allah"

"Ubangiji Allah Ya bayyanar da su" ta amsa mashi da ameen

Hajiya layla tace"ki shiga ciki," da sauri ta shiga dakin,

Su zahra dake atsaye har suna haɗa baki wurin Gaishe da su ita da mahboob suka kuma yi masu ya mai jiki

"Jikin da sauki bacci take, amma ku yan uwanta ne"?

"Ƴaƴan uncle dinta ne mu"

"Allahu akhbar kamar na ta6a ganinku da jimawa lokacin baku kai haka ba.."

Zahra tace"eh ay muna yawan zuwa joss lokacin baya..."

"Allah sarki ku shiga daga Ciki dan Allah kuyi mata addu'a' amsa mata sukai da toh

Bayan sun shiga, agaban gadon suka iska Aneelerh ta zuƙunna kan gwiwowin ta, kanta akan gadon, hannunta acikin na Benazir, jikinsu duk sai yayi sanyi ganin yadda benazir ta faɗa daga jiya zuwa yau har ta canza...

Har lokacin hajiya sarah na zaune kan kujera sallah kadai ke tada ta..

Gaishe da ita su zahra sukayi tare da yi mata ya mai jiki tace masu da sauki,

"Ubangiji Allah Ya bata lafiya, Allah yasa kaffarane" ta amsa masu da aneen

Gaban gadon suka tsaya kafin suka fara yi mata addu'o'i suna tofe mata jiki da su,.....

Kamar masu zaman makoki haka suka tasa ta agaba suna kallon ta.

Wureran karfe biyu da rabi ta farka kamar mai ta6in hankali haka ta dinga fusge fusge tana ambaton sunan taj da Angel, ta makance bata ji bata gani bata sauraren kowa hauka kawai takeyi masu, haka suka dinga rurruƙe ta don kokari ma take ta sauko daga kan gado, su Aneelerh sun sha kuka ba kamar da ta furta"kada su bari ta mutu bata sanya yarta a idon ta ba, bata son ta mutu bata ganta ba, su taimaka ma rayuwarta....."

babu wanda bai zubar mata da kwalla ba, hatta mahboob Yaji tausayinta

Likitan dake kula da ita ne Ya shiga dakin tare da wasu nurses Ya bukaci su hajiya sarah su fita daga waje

Nan suka fito kowa Ya zauna kan waiting seat suna ta jiran tsammani

Tsawon mintuna ɗuff suka daina jin sautin koke koken benazir, har sun fara fargaban meke faruwane sai ga dr adam Ya fito daga dakin tare da nurses din

Suna ganin shi kowa Ya mike suka nufe shi suna tambayar awani hali take ciki"?

Fuskarsa babu walwala Yace masu suci gaba da yi mata addu'a sannan su yi kokarin samo yarinyar da zata iya pretending amatsayin yarta daga yau zuwa gobe in ba haka ba sakamakon ba lallai Yayi masu dadi ba, don sunyi iyakar bakin kokarinsu amma abun yaci tura, Yanzu haka allurar bacci suka ƙara Yi mata....."

Hankulansu ba karamin tashi Yayi ba, nan fa suka fara shawarar Yadda za su samo Yarinyar dake kama da Angel ƴar fara mai launin ido ruwan toka..

Aneelerh tayi saurin cewa akwai wata yarinya da ta sani mai kama da unaisah, amma ko za'a same ta sai ya kai zuwa gobe...." ta fadi hakanne saboda tana sa ran gobe hajiya saratu zata kirasu inyaso koda yarinyar ba unaisah bace sai su nemi alfarmar abasu ita aro har zuwa time ɗin da benazir zata ji sauki...

Hankalinsu ba karamin kwanciya yayi ba, hajiya layla tsabar zumudi hada cewa me zai hana yarinyar tazo yanzu? In ma da bukatar suje gidan iyayenta neman alfarma sai suje..tace masu ay yarinyar ba'a kusa take ba, suyi hakuri zuwa gobe sai a sanar da iyayenta amsa mata sukai da toh ..........

Bayan komai ya lafa, Aneelerh ta kira mami awaya don ta sanar da ita halin da ake ciki, a lokacin tana a falo zaune zuciyarta cike fal da tunanin kome Ya tsayar da su aneelerh har yanzu basu dawo ba? Ko dai sun samu shiga gidanne? Ita kadai take ta tufka da warwara, kiran na shigowa a hanzarce ta dau wayar dake akan sofa hand, ganin sunan aneelerh yasa tay saurin dagawa

"Aneelerh! Ina fata kuna lafiya? Naji shiru baku dawo ba, ba sai da nace maku in baku samu shiga gidan ba kada ku takura kanku?

On the other hand Aneelerh tace"mun samu shiga mami, amma bamu samu damar yarinyar ba...." a tsanake ta sanar da ita komai ta kara da cewa"tace zuwa gobe zata tuntu6e mu,..."

Mami tace"to kuyi hakuri ku dawo gida, wani jinkirin alkhairi ne..."

"Mami, Yanzu haka muna asibiti, benazir ba lafiya..." tunkafin ta kare maganar mami ta doka salati tana fadin wata benazir din? Meya same ta"? Gaba daya hankalin ta ya tashi

Shigowa ummi tayi falon tana kallon mami dake ta zagba salati tana sauraron Aneelerh dake bata labarin abun da Ya faru bayan komawarsu dr shurem gida,

"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'i abu baiyi dadi ba, kai jama'a baiwar Allahn nan tana jin jiki, ubangiji Allah Ya tashi kafadunta, Anerlerh gani nan zuwa asibitin, kice wa mahboob kada ya manta da junaid karfe shida Yaje ya daukosa" amsa mata aneelerh tayi da toh

Bayan ta katse kiran, fuska A yamutse ta kalli ummi dake tambayar ta lafiya meya faru taji ta ambaci sunan benzair

Girgiza kai tayi kafin ta kwashe komai ta sanar da ita, hankalin ummi ba karamun tashi yayi ba.

"Yanzu zanje asibitin, ki zauna ke inyaso gobe sai kije kada abar gidan ba kowa, duk da Ana tana nan ba lallai junaid Ya yarda da ita ba kinsan shi da rigima."

Amsa mata ummi tayi da toh, cike da Alhinin abun da Ya faru, da sassarfa mami ta dauko hijabi ta zubla ta fito daga daki, ummi tayi mata adawo lafiy sanna tace agaishe mata da mai jiki, kafin taje goben

Mami na fitowa daga gidan saiga motar abie ta shigo, hakan ba karamin dadi yayi mata ba, dama abun hawa zata tsayar akaita can, sai gashi Allah ya dawo da shi, Agabanta Yayi parking motar bata jira Ya fito ba, ta bude motar ta shige sai da ta zauna yake tambayarta ina zataje yaga kamar bata acikin nutsuwarta, nan ta sanar da shi abun da ya faru na rashin lafiyar benazir, har faɗa sai da yayi akan fada matan da aneelerh tayi mami tace bafa laifin ta bane, itace ta matsa mata, kuskure daine an riga anyi sai dai ayi fatan Allah Ya tashi kafadunta....

Karya kwana yayi da gudu motarsu ta fuce daga gidan kai tsaye suka nufi asibitin.

_________________________________✍️

Slowly motar dr shureim ta kunna kai cikin gidan, bayan yai parking ya dago ya kalli zeenatu da ta kifa kai bisa gwiwa tana ta shesshekar kuka

"Bazan gaji da lallashinki ba, dan Allah ki hakuri ki jure ya shurem bayason ganin hawayen babynsa, na fada maki addu'armu take bukata, kuka ba abunda zaiyi mata...." tun da yafara maganar bata dago dakai ba

Fitowa yai daga motar ya zagaya dayan bangaren da take ya buɗe mata"fito mu shiga" still bata tanka mashi ba, dama dakyar ya rabata da asibitin. Ba karamar badakala suka sha da ita ba. Kuka tadinga yi akan bazata koma gidan ba, dakyar suka lalla6ata.

Ganin zata bata lokaci Yasa shi kai hannayensa ya tuttu6eta kamar yar tsana Yai mata irin daukar da ake ma jariri Ya nufi cikin gidan da ita.

Tana kuka tana fadin yaya shureim bazanje ba ni ka sauke ni, wurin aunty benazir zan koma...bai saurareta ba har ya karasa katafaren falon, Alhaji musa na azaune kan sofa ya daura kafa ɗaya bisa ɗaya, idanunsa na akan laptop dinsa, hada mug din coffee a gefe yana sha babu alamun damuwa akan fuskarsa hankalinsa kwance

Shigowarsu ne Yasa shi dago da ido Ya kallesu Fuskar shureim a daure Ya dira zeenatu, ransa Ya baci da ganin uncle din nasa kamar baisan halin da suke aciki ba.

"Shureim..." har ya kusa Fita ya dakatar da shi waiwayowa yayi babu walwala Ya ke kallonsa, shi kanshi alhaji musan Ya fahimci fushi Yake da shi

"Ya jikin benazir din? Kamar bazai tanka masa ba ya furta"da sauki"

"Menene sakamakon abunda ke damunta"?

Sai da ya ɗanyi jim kafin yace"It's depression and panic attack...." bai kare maganar ba yai hanzarin fucewa daga falon don baya jin zai iya jurar kallon uncle musa tsaf zai Iya gaya masa magana

Har ya kusa fita daga entry hall din kwatsam sautin muryar zeenatu Ya dakatar da shi Ya kasa kunne Yana sauraronta

Cikin muryar kuka take fadin"Wallahi daddy baka da tausayi, kowa ya damu da halin da aunty benazir take aciki ban da kai! Jiya kana gani haka ta kwana akulle kaki taimakawa ka buɗe mata kofa, har sai da ta kwana, why daddy? Baka sonta ne? Ko tayi maka wani laifi ne da yaja har kake nuna halin ko'in kula akan ta, ni wlh ka 6ata min rai daddy tun da har baka damu da rashin lafiyar aunty benazir ba, hankalinka kwance kana agida sai kace ba ɗiyar yayanka ba,....." kamar daga sama dr shureim yaji saukar mari ji kake tasss

A matuƙar furgice ya ware dara daran idanunsa, jikinsa na 6ari a sukwane Ya juya cikin takun sauri Ya nufi falon Har zai shiga wata zuciyar ta gargadesa akan kada Yaje Tsayawa yayi yana sauraron su daga inda yake yana iya hangen zeenatu wadda tunda daddynta ya kwasa mata mari gaba daya ta jirkice ta kife kan hannun sofa, jikinta yadinga bari kusan wannan ne karo na farko daya fara ta6a lafiyar jikin ta....baiwar Allah gaba ɗaya ta furgice ta kasa dagowa ta dinga tsala kuka tana fadin na tsane ka daddy, da kanka ka sa hannu ka buge ni? Daddy ka makance ne? Wlh sai dai ka kashe ni daddy..." masifa ta dinga zazzaga mashi
Chapter 83 · 0% Book details