← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 159 OF 238

Sashe 159

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuciyarshi ta karaya da jin furucinta, ta bashi tausayi ba kadan ba, ga kaunarta dake kara ninkuwa cikin zuciyarshi, jiya dakyar ya runtsa hatta Danejo saida ta lura da yanayin shi ba irin magiyar da batai mashi ba akan ya fada mata gaskiyar abunda ke damunshi amma yakiyi saboda bazai iya tona ma yarsa asiri ba, kamar tona ma kansa ne..

Baiwar Allah muryarta harta disashe, Unxpectedly taji ya ɗaura tafukan hannyenshi akan sumar kanta ya ɗan shafa bayanta cikin sigar lallashi

Kafin ya fara magana
"Unaisah, kin bani mamamki, kinyi min abunda ban ta6a zato ba..." a firguce ta dago tana kallon fuskar shi

"Ina yi maki kallon mai hankali, kuma mai jin tsoron sabawa Allah ashe nayi kuskure Unaisah, na yaudari kaina.." cike da tashin hankali ta furta"daddy ni din? Me nayi maka"? girgiza kai ya danyi cike da takaici ya zayyana mata abunda Ya taras sunayi adakin Danish...

Dafe kai ta yi da tafin hannunta, wani irin faduwar gaba da tashin hankali taji

"Idan shi jahili ne baida addini, ke ay ba irinsa bace, Kinsan babu kyau unaisah, ina tarbiyar dana baki? Baki ji komai ba kika biye mashi kuka rungume juna, haba Unaisah baki kyauta ma kanki ba, nima kuma baki kyauta min ba, wlh kin karya min zuciyata, kin samin fargaba saboda zullumin kada ya lallata min rayuwar yata...."

kusan suman tsaye tayi, jikinta ya fara kakarwa kamar mazari ga kunyar shi data lullu6e ta, tasan bata da gaskiya shiyasa ta sunnar da kanta ƙasa cikin sanyin murya ta furta"daddy, na kar6i laifina, amma dan Allah kada ka zarge mu, wlh bamu ta6a aikata wani abu daya sabama Allah ba, duk da Danish baida addini ba ɗan iska bane daddy, bazaiyi abunda zai cutar dani ba, idan yayi ba daidai ba ina faɗa masa babu kyau a addinina kuma baya musa min, abun da ya faru ranar bana a cikin hayyacina daddy, hankalina ya tashine naji matuƙar tausayin shi kuma naji tsoron kada na rasa shi shiyasa na rungume shi, amma wlh ba shine ya fara rungumata ba, ni ce daddy...."

yanayin yadda take yi mashi magana jikinta na kerma ba karamin rauni ta sanya mashi ba, yayi niyar yayi mata fada sosai amma sai yaji bazai iya ba, ya yarda da maganarta yasan Unaisah bazatai mashi karya ba.

"Meke atsakaninki da shi"? Ya tambaya yana kallon ta

Kamar mai in ina ta fara yan kame kame tana fadin"amm..umm..dama.."ta ɗan kau da idonta gefe kamar bazata karasa maganar ba tace"bazan boye maka ba, dama najima inason in faɗa maka, nasan zaka goya min baya akan abunda nakeso...." tashin hankali idanun shi aware yake kallon ta.

"Daddy Allah ya jarabce mu da son juna ni da danish, soyayyar dake tsakaninmu bazata misaltu ba, har rayukan mu zamu iya sadaukarwa akan junanmu, daddy wlh ina son danish, shi kadai ne namijin da nake da burin in aura..." bata ƙare maganar ba, sakamakon tsawar da Taj Ya daka mata wadda tay silar rikicewarta arazane Ta zazzare grey eyes dinta akan fuskar shi Yana faman fitar da huci yace"Impossible Unaisah! Wlh bazan lamunta ba, ba zaki sa nayi karamar magana ba, baki isa ki kunyata ni ba, kina hauka ne unaisah? Meye abunso atare da shi? Yaron da baida adinini arne ne, ga jahilci cike da kai, sannan bashi da wani galihu, bayan haka ina yake da halin da zai iya ruke min ke!?

wani irin jiri jirin tashin hankali ta gani acikin idanunta kalaman daddynta sunyi matuƙar ɗaga hankalin ta, tayi mamakin furucin da yayi akan danish kamar dai ya manta cewa komai ya faru arayuwar shi bayin kan shi ba ne...

"Unaisah Ina burin da kike shi na son auran attajirin me kuɗi? Mai ilmin addini dana zamani mai cikakken asali wanda zai gatantaki Ya tarairayeki ya baki kyakkyawar kulawa?

"Daddy, na jima da soke wannan burin, ba dole sai na auri miji mai kudi zan samu farin ciki ba, sau dayawa wasu masu ilmin basu aiki da shi daddy, ni kawai miji na gari nake nema kuma na samu daddy, duk abunda ka lissafa Danish zai iya bani fin su, saboda yanayi min soyayyar da bazai iya cutar dani ba, yana yi min son da zai iya hana kanshi farin ciki saboda farin ciki"

Ta ɗan numfasa kafin taci gaba da cewa" ka kira shi jahili daddy banji dadi ba, bayan kasan ba shi yaja ma kanshi hakan ba, idan ka amince min, zanyi amfani da son da yakeyi min in musuluntar da shi..."

bata ƙare maganar ba, Ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu! wani irin kululun bakin cikine Ya tokare makogwaronsa, Ya ma rasa me zaiyi ya huce haushin sa, Yayi mamaki wai har Unaisah ta iya gaya mashi da bakinta bata ji kunyar shi ba lallai ba karamin so take ma shi ba, zata iya komai akan shi..

Kafadunta Ya dafa da tafukansa Ya jijjigata har saida Sumar kanta ta yarfo ta gaban fuskarta fashewa tayi da kuka don ta gane bai fahimce ta ba..

Da kakkausar murya ya furta"Bazan ta6a amince ma soyayyarku ba, ba son shi kike ba, tausayin shi kike ji, tun wuri ki cire zancen zaki aure shi, saboda na riga da nayi maki miji sadakinki ne kadai bai biya ba, kuma yana sonki, shine za6ina unaisah in har ba bijiremin zakiyi ba, bana so ki bani kunya kada kisa na karya alkawarin da nayi masa, ki cika min burina Unaisah, danish ba dole saida ke zai iya rayuwa ba, ga sauran yan uwanki nan sai ya zabi daya acikin su, Unaisah burin kowace uwa ta sama ma ya'yanta uba nagari ba jihili ba.

abun da Taj bai sani ba tuni tajima da sumewa, idanunta daya gani a kakkafe shi yasa shi gane hakan..cikin jin faduwar gaba ya hadiye sauran maganarshi da bai amayar ba, saboda tashin hankali, Ashe nashi wasane bai ta6a ganin true love ba sai yau, ay yayi zaton daga layla da majnoon andaina samun irin soyayyar nan, sungumarta yayi kan fadar shi ya kwantar da ita kan gadon su, Ya fito daga dakin jiki na kerma Ya tafi dauko ruwa kafin dawowar shi, Batool ta shigo dakin fuskarta dauke da murmushi ta zauna gefen gadon tana kallon wani sabon salon kwanciya agurin Unaisah, tayi zaton dadin baccine yasa ta dauki tsawon lokaci bata leko waje ba.

"Sister Ya kamata ki tashi, Aunty Ummi ta hanamu baccin marece.."

ta fada tare dakai hannu ta ɗan bubbuga ƙafar Unaish shiru bata farka ba,

"Unaisah wani irin bacci ne wannan kamar mai fama da cutar bacci" ta fada tana kara bubbuga legs din ta.

Adaidai lokacin Taj ya fado dakin hannun shi ruke da robar ruwa me sanyi, Yana ganin Batool yaci burki gaban shi na faduwa yasan muddin tasan Unaisah suma tayi sai ta yi kukan da zai jawo hankalin sauran yan uwanta.

Jin motsin adakin yasa Batool ta juyo ganin daddyn Unaisah yasa ta miƙe da fara'a tace"ina wuni daddy, i'm sorry watakil ka yi sallama banji shigowarka ba..." yawu ya haɗiya dakyar ya tattara nutsuwarsa yana kokarin danne damuwar shi yace"lafiya lou daughter.." da alamun rudu kan fuskarta tace"daddy naga water bottle a hannunka.." washe baki yayi"eh ni zan sha ne, kishi nake ji" murmushi tayi"ko kazo ganin Unaisah ne" a kagare ya daga mata gira"bacci take, yanzu nake kokarin tadata" da sauri yace"kinga bari ni in tashe ta, kije gurin ummi naji kamar tana nemanki..." kamar taso ta ɗago shi, ta lura kamar wani abu badaidai ba, amma sai batayi mashi gaddama ba, ta fuce daga dakin, ajiyar zuciya ya sauke bayan ya datse ƙofar dakin, ya zauna gefen gadon da sauri ya cire murfin robar ya yayyayafa mata ruwan kan fuskarta.

dogon numfashi taja tare da sauke ajiyar zuciya..

"Unaisah, Pls ki yi hakuri ki tashi, kinji! I won't hurt you anymore..."

dakyar ta iya buɗe idanunta wadanda suka kada jawur ta dube shi

Wani irin ciwon kaine Ya far mata...
Cikin disasshiyar murya tace"daddy, kada ka raba ni da Danish, zan iya rasa raina.."

Kwata kawata baya son tana fadin zata rasa ranta akan Danish, Ranshi baci yake kamar ya hadiyi zuciya, kuma yana akan bakanshi bazai janye ba.

"I'll think about it, Yanzu bana son duk wani abu da zai ɗaga hankalinki, kwanciyar hankalinki nakeso..." hankalin ta ya ɗan kwanta, gani take kamar daddynta zai duba mata ne.

"Amma daddy, baka son Danish ko"? Girgiza mata kai yai"Ina son shi Unaisah, Kuma ina jin tausayin rayuwar shi, maganganun da kikaji nayi ɗazu rainane Ya 6aci bawai don ina nufin hakan ba, ni kawai banaso kina sakar mashi jikin ki ne"

cikin kwantar da murya ya faɗa.

Ruko hannun shi tayi a cikin nata"daddy pls ka min alkawarin ba zaka raba ni da shi ba"!

Dafe kai yai da tafin hannun shi, ji yake kamar ya kifa mata mari saboda haushin da yake ji in ta ambaci sunan Danish

"Kina so In amince ma Soyayyarku?In kuma ba shi damar Auren ki"? jin wannan maganar daga bakin daddyn nata yasa ta miƙe zaune cike da zumudi tace"Eh daddy..."

Numfasawa yayi kafin yace"Zan baki Umarni, If you do what I say, I promise to fulfill your dream of marrying your choice".

gabanta ne ya ɗan faɗi duk da batasan umarni da zai bata ba, taji fargaba sosai..

"Daddy, wani irin Umarni ne? Ka faɗa min in sha Allah zan yi maka biyayya" ta faɗa cike da jin fargaban amsar da zai bata..

Ido cikin ido su ke kallon jun.

"ki bashi Umarnin, ya yi mana jagora zuwa Gidan Kurkukun ƙaddara..."

wata irin razananniyar faduwar gaba taji, kamar zata zauce ta daddafe kanta da tafukanta dama saida ranta ya ayyana mata abun da zai umarce ta da tay...

"Inaso in tabbatar da kaunar da ya ke yi maki, ta hakanne zan gane shin jarumtakarsa takai in mallaka mashi lu'u lu'u na?

ya faɗa yana kallon idanunta da suka rune zuwa Jajawur kamar Jan gauta.

Cikin shesshekar kuka tace"daddy, pls ka bani wani umarnin daban, wannan is too hard for me! I can't force him I don't wanna put his life in danger"

Kwata kwata babu annuri akan fuskarshi, ya haɗe rai sosai saboda yana son ta ɗauki maganar shi serious
Chapter 159 · 0% Book details