← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 238

Sashe 38

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin wannan maganar yasa unaisah yin saurin miƙewa, yatsun hannunta na kerma ta soma kiciniyar buɗe kofar, a fujajen ta fado dakin, ganinta yasa suka bata hanya, ta faɗa jikin tajuddeen ta ƙanƙame shi tana kuka take fadin daddy dan Allah kayi hakuri nasan nice na bata maka rai, ka tashi ka ji daddyna abun alfahari na, la66anta na kerma takeyin maganar, hawayen fuskarta tuni sun wanke fuskarshi, sumbatar goshin shi tayi, tare da manna masa wani kiss din kan kuncinsa ...." sai da taj ya bari ta gama firgita, tukunna ya buɗe idanunsa fuskarshi dauke da murmushi, fashe mashi tayi da kuka da sauri ya janyota jikinsa suka rungume juna tamkar zasu koma mutun ɗaya tsabar yadda suka matse junan su lallashinta yaci gaba dayi yana fadin"am sorry my angel, ki yafe ni, nasan bankyauta maki ba, wlh kina araina, kamar yadda kike fadin kin yi kewata nima haka nayi kewarki, angel rashinki ba karamin gi6i yayi min ba rayuwata sai da nakusa zaucewa saboda haukan rashin ki a kusa da ni, Angel bana iya bacci batare da nayi mafarkin ki ba, duk dare na Allah sai na tashi nayi salla saboda inyi maki addu'a Allah ya kare min ke duk da bani da tabbacin kina araye ko kin mutu......" dakatawa yai da yin maganar, idanunsa acikin na Angel dinsa, sai da ya fara tattara nutsuwarsa kafin cikin sanyin murya ya fara basu labarin abun da Ya faru dashi bayan ya jefa Angel cikin ruwa.

_______________________________✍️

Abun da ya faru lokacin da wadannan migayun dattawan su ka ƙyasta lighter bayan sun zazzaga mashi fetur a jikin shi, idan ba zaku manta ba, ba su kaiga jefa mashi lighter din ba, har sai da suka kusa shiga motocinsu tukunna suka cinna wutar, sannan ba su tsaya sunga wutar ta kone sa ba, suka shiga cikin motocinsu tare da fusgarsu suka bar dajin a guje, bayan tafiyarsu hucin wutar Ya daki fatar jikinsa wani irin radadin azaba ne ya ziyarci sassan jikinsa, nan take ya farfaɗo daga suman da yayi ko da yaga wutar dake ci, cikin matsanancin tashin hankali ya yi wani irin kwakkwaran juyi da dukkan karfinsa gaba ɗaya ya rubza cikin Kogon ruwan daya jefa Angel, tsulundun Ya rubza cikinsa ya nutse can kasan ruwan kuma nan take ya sake sumewa.

Suna acikin ruwa ɗaya da Unaisah sai dai akwai tazara tsakaninshi da unaisah, wanda silar hakan yasa har danejo ta ceto rayuwar unaisah ba tare da tasan cewa akwai mutun acikin ruwan ba saboda ruwa daya ja shi... A kalla taj ya kwashe tsawon kwana uku acikin ruwan ba tare da ya samu taimako ba.

Ana haka cikin ikon Allah, Wasu fulanin daji dake kiwo daga can wata ruga dake a cikin dajin, su biyu matasa suka koro shanayensu zuwa wurin da ruwan nan yake, Anan suka yaɗa zango, to ɗaya daga cikin su mai suna habu mayen ruwa ne duk in suka zo bakin ruwan sai ya shiga yin wanka, babu irin gargadin da ɗan uwansa garbati baiyi mashi ba akan yadaina shiga ruwa saboda hatsarin dake gare shi amma yai kunnan uwar shegu da shi saboda taurin kansa da kafiyarshi, Abun ne yabi jikin shi tun suna kanana Yake shiga ruwa yin wanka har izuwa girmansa, shi kuma garbati mugun tsoron ruwane da shi, ko kusa da ruwa baison zuwa jikin shi kerma yakeyi saboda Labaran da yake ji daga wurin mutane dangane da mugayen halittun ruwa dake cinye mutun shiyasa yake jin shakkar kusan ta kanshi da ruwa, aranar da suka je bakin ruwan, habu na kokarin cire kayan shi don yashiga yayi wanka, garbati yayi saurin damƙar rigarsa suka soma kokawa a tsakaninsu, cikin harshen fulatanci suke magana garbati yace wlh bazaka shiga ruwan nan ba, ka manta da gargadin da baffa yayi mana akan shiga ruwa? Ko so kake ka mutu ne kafin lokacin ka yayi?

Habu da ya gama hasala Ranshi a6ace yace"Aradun Allah garbati baka isa ka hanani shiga yin wanka ba, ko da kuwa sama da kasa zasu hade saina shiga, idan ma wani abu ya same ni, ni naja ma kaina kai dai naka kallone kawai" duk yadda garbati yaso ya hanashi amma yaki ji, a karshe sai yasa hannu ya hankaɗe garbati gefe daya ya kife kan ciyayi da sauri habu ya bi ta hanyar da ya ke shiga ruwan ta cikin sauki yabi duwatsun dake kewayen da ruwan ya tsunbula cikinsa Ya cigaba da yin wanka yana raira waka cikin harshen fulatanci.

Mikewa garbati yayi zuciyarshi a 6ace yaci gaba da kula da shanayensu yana jiyo muryar habu dake acikin ruwa yana raira mashi wakar habaici har yana kiran shi da ragon namiji, zaifi dacewa ya koma ɗaura zani maimakon wando, har ma ya dinga taya su Inno surfen Gero, ranshi ya 6ace jin wannan maganar, amma saboda hakurin dake gare shi sai ya share shi yaci gaba da kula da shanayensu

Habu yana cikin yin nutso ya shige can kasan ruwan yana shawagi ba zato ba tsammani idanunsa suka sauka akan mutumin dake kwance kasan ruwa rai hannun Allah, kasancewar kasan ruwane idanunsa sunyi mashi biji biji sai ya dinga ganin kamar wata halittar ruwace me girman gaske, bakomaine ya fado mashi aranshi ba face gargadin da garbati keyi mashi akan ya daina shiga ruwa akwai mugayen halittun dake cinye naman mutun, nan fa hankalin shi yayi mugun tashi, zuciyarshi ta soma yi mashi dakan uku uku, Jiki na bari ya soma yin sama ya fiddo kanshi yana ihu na fitar hayyacin tamkar zai fasa makoshin sa, ko da garbati yajiyo ihun Habu abunka ga firgitacce bai tsaya tambayarshi menene ba, ya watsa aguje kamar karan farauta Ya nufi rigarsu.... Ya bar habu acikin ruwa Yana ta Zagba ihu tsabar rudu Ya hana ya fito daga ruwan gaba daya ya gama rikicewa.

Da gudun gaske Fulanin Rigarsu suka nufo wurin ruwan wasu ko takalma babu a kafafuwansu, wasu kuwa hannayensu ruke da makamai saboda su ceto dan uwansu, bayan sun karaso gaban ruwa wasu dattijai daga cikin kakanninsu irin wadanda suka daɗe suna gwagwarmaya ne, basu da tsoro ko miskala zarratin, sun saba da duk wani abu daya shafi daji suna da kwarewa akansa

Basu tsaya bata lokaci ba suka afka cikin ruwan don su ceto rayuwar dan su, ko da suka shiga, Habu Ya kankame kakansu Yana sambatu iri iri, ya dinga nuna masu saitin inda yaga halittar da hannun shi, da sauri ɗaya daga cikin kakannin nasa mai karfin Hali ya kutsa kai cikin don ya kashe halittar, aikuwa yana shiga yayi tozali da mutumin dake a kwance kasan ruwan, lamarin ya daure mashi kai, ganin ɗan mutun acikin ruwa, aranshi ya dinga tunanin mutunne ko aljan? Watakil aljanin ruwa ne" Wasi wasi yaci gaba dayi, har zai tafi sai kuma zuciyarsa ta dinga azalzalarshi akan ya dauko mutumin watakil tsautsayine ya afka da shi... Baiyi kasa a gwiwa ba yaje ya kinkimo tajuddeen abunka ga tsohon kashi na majiya karfi wadanda suke da shirinsu baiji nauyin taj ba akan kafadarshi ya sargafo shi, Ya fito masu da kawunansu daga cikin ruwa, ya ɗaga murya yana fadin"Ta mutunce ba aljani ba," Gaba ɗaya suka zaro idanu waje suna lekensu kowa da abunda yake sakawa aranshi, Bayan sun fito dashi daga ruwanne suka kewaye shi suna kallon shi, anan suka ga alamar bai mutu ba, da ranshi, wani abu daya basu tausayi game da shi, mummunan raunin da suka gani akan tafin kafarsa ta dama, fatar wurin ya rarake yayi rami, ba tare da sun 6ata lokaci ba suka tafi da tajudden can rigarsu, a inda suka cigaba da bashi kyakkyawar kulawa suka ɗaure masa raunin kafarsa bayan sunyi mashi ƴan dabarun su na mutanan daji, tsawon kwanaki baya acikin hayyacinshi, ko bacci yake yi ya dinga farkawa kenan yanayi masu sambatu akan yarsa da ya baro cikin ruwa, sun rasa gane me yake nufi saboda basa jin harshen hausa, wani lokacin kamar zautacce yai ta kuka yana ambaton sunan Angel, a kalla taj ya shafe tsawon watanni ba tare da ya iya taka kafarsa ba, wannan dalilin ne yasa bai samu damar zuwa neman Angel ba, bayan haka ya yi loosing memory dinshi, sunanta ne kadai ya tsaya mashi aran shiyasa yake yawan ambatonshi....

Lokacin da ya fara samun sauki yaci gaba da rayuwa da su yana ta kokarin ya tuna miya faru dashi amma ya kasa saboda lalurar data sameshi a haka ya rayu a rigar su na tsawon shekara biyu cikin ikon Allah a daren wata rana yana tsaka da baccinsa yayi wani mummunan mafarki dangane da Angel dinsa wanda ya yi silar dawowar memory din shi, tun a cikin daren ya fara kokarin barin rigar don yaje nemanta gaba daya ya tada masu hankali duk wani mai bacci sai da ya farka yai ta ambaton sunan ƴarsa da ya jefa cikin ruwa yana ta kokarin kwatanta masu sai dai sun kasa gane me yake nufi, lallashin shi suka cigaba dayi suna kwantar masa da hankali, a dole ya hakura bai fita a daren ranar ba,

A Washe garin ranar da sassafe kakansu habu ya bashi kyautar sandar da zai yi amfani da ita wurin yin tafiya, saboda har time ɗin kafarsa bata dawo dai dai ba, lokacin da su habu zasu tafi kiwon shanu sai yabi bayan su don ya nemo Angel dinsa, sai dai kash ita kuma a lokaci har wannan tsautsayin ya fada da ita, tana acan gidan kurkukun kaddara, kuma bata jima da barin rigarsu Danejo ba, shi kuma yafara zuwa nemanta, tunda yaga kogon ruwan ya ƙafe babu ruwa acikinsa saboda damuna ta wuce, mutun na iya ganin komai dake a kasan ramin, yayi kuka na fitar hayyaci kamar ransa zai fita, har yunkurin fadawa yayi don ya kashe kanshi, da sauri su habu suka rirrike shi tare da jan shi suna lallashin shi, saidai sam baya fahimtar me suke cewa.
Chapter 38 · 0% Book details