Sashe 98
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba,Duk ya'yana ne ku ku shigo nan ai duk mun zama Daya" Sai ga su Yaya ishaq sun shigo da mijin Yaya mariya da na Yaya Asiya sai Yaya Salisu waje aka basu suka zazzauna aka shiga gaisawa da tambayan Hanya,sannan muka tashi dukkammu muka durkushe a gabansa muna gaisheshi ya amsa bakinsa har kunne ya saka hannuwansa Biyu ya Dagomu yana fadin"Ku tashi ku zauna ya'yan Abba" Gabadayamu muka zauna a gabansa yabi mu da kallo kafin ya yi mgana Yaya Asiya ganin yana kallonta yasa tayi Saurin cewa"Asiya ce Abba' Gabadaya sai da akayi dariya shima Dariyan yayi yana fadin"Zan kama sunan sai kika rigani Ase ase ya gida da yaran..?kanta na kasa ta amsa mai sai ya fara waige yana fadin"To ni jikokin nawa yawa ne dasu kai yara maza kowa yaazo wajen mamansa mu gani"Kamar suna jira kowannen yazo ya rabe jikin uwarsa Anum har da kwantomin saman wuya rad'a take so tamin a kunne ban jita ba. Abba ya kallemu ya kara kallonmu sai ya juya yana kallon Inno Lokaci d'aya yana fadin"Alhandulillah yar'uwata ta bar min zuru'a inno" Inno ta gyad'a kai tana fadin"Ba shakka nima ai duk ta kara min yawan magidanta da kishiyoyi" Abba na Dariya yace"Inno Maman Nana sai dai tayi hakuri Kishiyoyo gareta Rututu ba adadi" Maman Nana ta washe bakinta fararan Hakoranta suka bayyana Lokaci daya tana fadin"Bakomai ban damu ba dad'in abun ma duk na Roba ce nice dai uwar Nana ta karfen" Gabadaya dariya akayi daga ganinta itama akwai barkwanci su Mama na gefe suna Dariya Saurayin ya dago ya kallah yana fadin"Babban yaya ta kanka zan fara fa" Mirmishi yayi mai kayatarwa kafin yace"Girman ka ne Abba" Badariya ta kara kallonsa ita tun shigowarsa taga kamar ta san shi, sai dai ta kasa tuna a ina shi kuma bai ma Lura da ita ba D'aya bayan d'aya ya fara Gabatar da mu kafin ya karishe da fadin"Duka wad'anan kannenka ne nauyi ya kara hawa kanka Babban yaya.kamar yadda kake tafiyar su da Nana Fadila haka zaka tafiyar da su ya'yan yar'uwata da na baku Labarin bamu had'u ba har Allah ya Dauki ranta wad'anan sune iyalan data bari" Cikin gamsuwa yace"In sha Allahu zaka sameni mai kulawa da kannena kamar ko yaushe" Jinjina kai yayi kafin ya Kallemu yana fadin"Fa'iza Asiya,Mariya da Auta ga yayan ku nan sunan sa Abdul'Ahad zai yi muku Jagoranci kamar yadda zan jagorance ku, ku gaisa da shi" Daya bayan d'aya muka rika gaishe shi yana amsaawa cikin Sakewa kafin Abba ya yafito Nana Fadila ta matso kusa da shi Tana fadin"Na'am Abba." Cikin Dattakonsa ya nuna mu yana fadin"Ga yan'uwanki nan.Kinga Asiya itace kamar age mate din ki to ki riketa Amana ku zama kamar yadda kike da Nana Fatima" Cikin gamsuwa tace"In sha Allahu Abba"Nan itama muka gaisa ya yafito Nana fatima ya gabatar mana da ita yana fadin"Ga age mate din ki nan Fa'iza ki kula da ita kamar yadda zaki kula da Nana khadija tana da raunin ji Hallita ne haka aka haifeta ki kula da ita"Da sauri ta rike Hannuna tana fadin"Ni daman Abba ina ganinta naji ina sonta"gabadaya sai akayi Dariya Abba ya Kira Nana khadija da Hafsah ta Dawo rakata Tiolet ya had'a su da Hafsah sai Yaya mariya taga an wareta Cikin damuwa tace"Abba ni wa zaka damka ma Amanata? Yana dariya yace"Amanarki tana hannu nagari D'iyata. Maman Nana ga wata amanar na kara miki Dukkansu ya'yanki ne kamar su Nana fadila ki zama uwa tagari garesu kamar yadda na sanki kada ki kara bari suyi kukan maraicin rasa uwa" Da Sauri ta Gyada kai Lokaci d'aya tana jawo Yaya mariya ta Rumgume tana fadin"In sha Allahu Baban Nana,Mari babban kifi rabu da wad'anan yaran ke da uwa kika samu sukutum ga Abdul'Ahad da zan saka yafi shagwabaki" Yana dannan wayar sa yace"Itace fv sister di'na ma daga yau Ammi" Nana Khadija ta shagwabe fuska tana fadin"Kai yaya ni din fa..?. Yana tabe baki yace"Kin zama tsohon yayi"Sai dariya gabadayanmu Farinciki ya samu muhalli a zukatanmu Abba ya gabatar da su Baba ati ne a matsayin Goggon su kad'ai data rage mu su sannan ya gabatar da Maman Nana a matsayin matarsa uwar su Fadila sai su Goggo a matsayin Dangin mahaifin mu. Badariya ya gani ya nunata yana fadin"Wannan fa ban ganeta ba..? Da Sauri nace"Kanwar mijina ne Badariya Abba" Cikin gamsuwa yace"Itama ya'ta ce sannu Badariya"kanta na kasa ta amsa tana gaishesa sai lokacin Abdul'ahad ya lura da ita ammh shi karon farko ya gane ta,har Hoton wayarsa ya Dauko yana gani to ai dolensa ya ganeta duk kan Hoton Raly dake wayarsa rabin sa tare da wannan kawar nan tata take yi, in bai manta ba sunan kamar Badar sunan ta, in suna tare wani Lokacin har gaisawa suna yi ta kalleshi shima ya kalleta ammh ganin kamar bata ganesa ba sai shima ya basar. Yaran duka Abba yasa muka yi masa bayaninsu,muma muka tara su wajen shi muna fada musu Abba ne su gaisheshi Amir ya karisa ya gaishe shi ya Dagosa yana fadin"An ya Fa'iza bazaki bani abokin nan nawa ba yaron ya burgeni akwai natsuwa sosai' Ina dariya ban yi mgana ba Da Sauri yace"Kada ki damu in dai bangaran megidan ne ke da shi Duka ya'ya ne ina da iko a kanku da ya'yan ku gabadaya"Nana Fatima na gefe tace"Allah ya bar mana Abba" Nana Fadila da Inno na tayata Dariya shi bai ma jinsu ba Hankalinsa na wajen Anum kuke tana faman tambayansa"Kai ne Abban Umman mu.?ya gyad'a mata kawai sai ta kalleni tana fadin"Umma ba kin ce Baban ki ya rasu ba har muna addu"a ba? kafin na samu amsar bata ya amsata da cewa"Wani Sabon Abba ta samu ke kuma kin samu sabon megida ko bakya so na..?.sai su Anum aka noke kai ana dariya kafin tace"Ina sonka mana ammh sai na girma zamu yi aurre"Gabadayanmu muka saka Dariya Ammi tace"Kaji min yarinya Daga haduwa sai fashin miji"Abba ya Dora t saman cinya yana fadin"Maman Nana dai ana ta kishi"Sai dariyan barkwancin su muke yi, Sai yarinyar da suka fara shigowa naji Nana Fadila na kiranta Falaq,ita tayi ma mamanta Rad'a a,kunne sai ta Dago tana kallon Anum kafin ta kalli Ammi tana fadin"Ammi Kin ji Falaq tace Anum tazo bikin uncle Junaid ta ganta a gidan Anty Laila" Sai kallo ya koma kan Anum tana jin haka jikinta na rawa tace"Nima na ganta"Sai mamaki ya kamani Ammi tace"Haba ni fa ina ta yi ma yarinyar nan kallon Sani sai da Falaq ta fad'a na tuna kunga yara da rashin mantuwa ko..? Nana Fadila tace"Ko ita ce Anum d'in da kika Dameni da zencenta da kika koma gida.?sai yarinyar ta Daga kai sai mamaki gabadaya ya kamamu Abba yayi mirmishi kafin yace"To yara dai sun san juna sai aji ta ina aka haihu a ragaya" Ammi ta kalleni tana fadin"Fa'iza ko har dake aka zo bikin Lailan ne bamu hadu ba.?Laila ta kaduna..? Sai alokacin na tuna bayan Amir yayi zaraf yace"Umma Anty Laila da take zuwa ita da Anty Raliya" Da Sauri nace"Laila..Oh na tuna ta Aa Anum kad'ai taje bikin ita ta roki babanta ya barta suka tafi da ita"Sai da ake mgana Badariya ta tuna inda tasan Abdul'ahad da Sauri ta kallesa tana fadin"Abdul'Ahad right.? Sai ya jinjina mata kai yana fadin"Yes Badar ko..? Sai ta fara Dariya kallo ya koma kansu ta kalleni tana fadin"Anty Fa'iza kinsan waye..?wanda zai auri Raly ne fa."sai na bude baki ina fadin"Raliyar ki.?sai ta gyada min kai sai na kasa mgana Ammi tace"ikon Allah kusan Raliyar da Abdul'ahad zai aura kenan..?kusan Hajiya Aisha Saulawa kenan? Kai tsaye nace"Nasan ta sosai akwai zumunci a tsakanina da ita da ahalinta. Raliya kuma yar gidana ce Aminiyar badariya ce, kanwar mijina" Sai mamaki ya kama kowa,Ammi ta bude baki kafin tace"Ke Fa'iza ba dai ke bace mai Turaran kamshi na Katsina ba..? Sai ta bani dariya na gyad'a mata kai lokaci daya sai na Tuna da Sauri nace"Ba dai ke ce yayar mijin Laila da na hada turare humra da Kwallacha wajen ki ba..? Sai ta fara Dariya tana fadin"Baban Nana diyar taka fa sananniya ce. Ba shakka ina turaren da nace maka naga Amaryan junaid dasu masu kamshi na tambayi inda akayi mata tace Daga katsina kawar mamanta Hajiya Aisha ta bada akayi mata?ka manta har kana min tsiya shegen son kanshi bazan iya siya a kaduna ba sai na lula har katsina..? Sai ya daga mata kai yana fadin"Duk na tuna"Da sauri tace"To ai di'yar kace mai hadawan Allah mai iko sannu Fa'iza" Sai kallo ya koma kaina Nana Fatima tace"Ammi wai turaran da na sace din nan da nazo duba Inno..? Dakuwa tayi mata tana fadin"Asirin ki ya Tonu kaga barauniyar gidan ka Baban Naana ina fad'an an dauke min Turare kace baka da barawo a gidanka to wannan fa..? Gabadaya dariya muke cikin Had:e rai yace"Yayi mata kamshi ne ta ara ko Nana Fatima..? Da sauri ta daga kai Lokaci daya tana fadin"Fa'izata zata sake had'amin nawa Ammi na dibar miki" Dakuwa ta sake yi mata tana Dariya AbdulAhad na dariya nace"Nana Fatima kamar itace mujaheed d'an sandan farin kayan wajen Lauya mgana" Abba yace"To Za'ayi mata taron dangin abun kuma ma nasu ne.daman haka abun yake ba gashi da aka had'u ba yara suka fara shaida da juna ba" Nan fa falo ya ka ure da Hira suma basu da bakunta sun saki jiki suna ta Hira damu,Ammi ko ta shige cikin mu ba ruwanta Inno dai Goggo tajata Daki don ta Huta Mama ba baka sai ido ta zama kamar mujiya afalon da na gabatar da ita a matsayin uwar miji na, cikin girmamawa Abba ya gaisheta sau taga ba ma raina gorin asalin datake yi min sai da ta raina kanta da taga Abba da Ahalinsa. Abdul'Ahad kuma na gefe ya Kira Raliya sun yi mgana da yace ga wata su gaisa sai ya bata Badariya tayi matukar mamakin inda suka Hadu sai Badariya ta bata labari tuni ta bazama Dakin Hajiya tana gayamata yadda komai ya wakana Daman tun a satin Abdul ya gayamata zasu zo katsina wajen dangin mahaifinsa tana ta mamakin daman su ba yan kano