Sashe 83
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta zauna da shi ba sai dai shi ya bita,ta nuna mai daman ba sonsa take yi ba. Ta aure sa ne saboda kyansa da wani kyalkyalin duniya kamar yadda shima ya gina nasa auran ashe ba'ayi ma Allah Wayau..? Ishaq yana da taurin zuciyar da ko abu ya damesa ba dai kaga kukan sa ba.ko mutuwa akayi sai dai yayi kukansa a boye ammh sai ga shi kwance Hawaye suna sauka ta gefen kunnuwansa duka biyu,suna jika zanin gadon dake jikin katifarsa zuciyarsa ta yi wani irin nauyi kamar ana yi mai wahayi haka abubuwan daya aikata suka rika dawomai Daki daki acikin kasan ransa fad'i yake yi"Allah na tuba. Allah na tuba ka yafemin" Kansa yake girgizawa yana ji a ransa in ma Fa'iza bata yafe masa ba, bazai ga laifinta ba ammh baya raba d'ayan Biyu duk bala'in dake bibiyansa akwai Hakkinta,ya tuna sanda ya wulakan ta Mariya da kalaman data furta masa alokacin, ya tuna ta fadamai ko ba Hakkin Fa'iza ba,sai hakkin Zumunci ya tambayesa watarana. Ga shi tun ba'aje ko'ina ba ya fara gani rana tsaka aka samu saka Hannun Fidda makudan kudad'e bai san hawa ba bai san sauka ba,ya shiga matsala karshe bayan ya rasa aikinsa sai da ya rasa duk abunda ya mallaka Allah ya barsa da ransa ne saboda ya gane kuskusransa in da yaso gidan yari za'a kaisa ya kare rayuwarsa a banza. Sai hankalinsa ya dawo jikinsa ya tuna ko abokansa yanzu da suka san ba shi da aiki sun gujesa tunda bai da shi bazai iya ma kansa komai ba ballatana su.hatta abokan aikinsa nachan Abuja bamai kiransa sun ma fara mantawa da shi, daman haka Duniya ta gada in yau mune to gobe fa wasun mu ne. Bai taba daukan furucin Baba a matsayin wani bakar sarka mai wuyar warwaruwa a garesa ba,ya dauka tunda bai saki Fa'iza ba ya fita daga Furucin sa abunda bai sani ba Shi Furucin iyaye kan ya'yan su yana tasiri har mutuwar su Baba ya bashi Amanar Fa'iza sannan ya kakkausa mgana kan in ya wulakantata bai yafe masa ba shi ko adadin sau nawa ya wulakanta Fa'iza bazai iya sani ba..? Zumbur ya mike kamar an tsikare shi da ya Tuna da shirmen da ya tafka na Jingine auran sa da Fa'iza tun kafin ya auri Zainab bazai manta ba tun a wannan Lokaci wani abu na auratayya bai kara shiga tsakanin su ba,Shekaru Biyar kenan Innalillahi ina zai kai girman hakkin Fa'iza daya Dauka..?bai taba Tunanin ita ma Mutum bace mai lafiya..?bai taba Tunanin zata shiga masifa da bala'i saboda jinginarsa ba..? Ya tuna Zainab macece mai yawan bukata har tama fisa shi wani lokacin,yana da Hakuri wani Lokaci ammh ita bata da Hakuri ta wannan Fanni shiyasa bazata yarda ya yi wata D'aya bai je ya ganta ba. Mahaifinta yasan zata cutu shiyasa ya Tsaya mata Ita Fa'iza wa take da shi da zata kai masa kukan ta ya tsaya mata..? Sai kamar ana gayamasa da kansa yace"Allah.." Shi ya tsaya mata" Hannayensa duka biyu ya saka ya Tallafe fuskarsa yana jin kamar ya fashe da kuka,Sai dai duk abunda ya faru da gudummuwar Mama yasan ita din uwa ce garesa da bai da kamarta ammh ta bada gudummuwa wajen kara karkatar da Rayuwarsa zuwa hawa kan keken bera in da tana ankar da shi ko in yayi ba daidai ba ta yi masa Fad'a da bai kai haka Lalacewa ba.Sai ya tuna Baba lokacin yana gabda rasuwa yake mai fad'an ya zama adali sannan magidanci mai kyautata ma iyalansa,Kada ya biye ma Mahaifiyarsa wajen kuntata ma Fa'iza kada ya manta marainiya ce bata da kowa kada ya wulakantata domin mace ce tagari ce in ya rasata ba lalle ya samu mace kamarta ba. Kamar karamin yaro haka ya dinga rera kuka yana fadin"Ka yafe min Baba..Ka yafe min Baba na Tafka kuskure ka yafe min" Shi kad'ai haka ya dinga sambatu Daran nan barcin sa rabi da Rabi ne da asuba Dakyar ya iya tashi fuska da Idanuwansa sun kumbura saboda Damuwa da suka dawo masallaci sai da Jamal ya tambayesa ko zazzabin ne.? yace ya warware saboda Mama ta sanar da shi lokacin da yayi rashin lafiya. Daki ya sake komawa ya kwanta yana Sake saken yadda zai fara gyara mu'amalan sa da Fa'iza sai dai ba shi da wannan kwarin gwiwa yana tunanin bama ita ba ko waye yaji abunda ya faru zai yi tunanin Saboda yanzu ba shi da shi ne yaga amfani Fa'iza ammh har ga Allah daga daran jiya zuwa wayewar gari zuciyarsa ta cika da Fa'iza sunanta alherinta,Sanyin ta,Ladabinta da Hakurinta kaunar ta Kunyar ta,had'e da nauyinta sun hade masa waje d'aya sun ki barinsa yayi wani sukuni tunda ya dawo masallaci bai bari sun hadu ba ya shigo Daki,Wajen Mama kadai ya leka suka gaisa. Gani yayi har bakwai ta gota kuma yaji hayaniyar yara afalo suna ta shirin Tafiya Makaranta,Sai ya mike Dakyar yana rawan jiki ya kwashi kular abincin jiya da ta kawo mai da Kofin ruwa,ya fito falo ya iskeni ina Ta fama da Musty wajen saka masa Rigar makaranta Hafsah Lahadi ne tana gida ita ke Kitchen ta na yi musu abun kari Amir ya shirya tuni shi yake taimaka wajen shirya Ahmad Anum kuma ta shiga Daki neman Hijabinta bata gani ba ,Dagani har yaran Hankalin mu yayi gaba bamu san fitowarsa ba sai da Anum ta fito daga Dakin su tana ganinsa ta bude murya tana fadin"Daada ina kwana" Muryanta yasa duk muka Dago muna kallonsa Amir ma ya saki Ahmad yana gaida shi ya amsa yana ta sakin fuska kamar an saka shi Dole sau daya na kallesa na kauda kai na,Musty na saki ina fadin"kullum kai ne rigimamme ko Ahmad ya daina rigima ammh kai babban kwabo baka daina ba" Ina shirin nace Amir ya karbi kayan hannunsa sai naga yaje ya karba ya wuce kitchen shi kuma ya kariso falon yana fadin"Musty na ne Umma ke ce ma Babban kwabo..? Ya fada yana daukan sa,Ahmad na ganin haka shima ya fara zillo sai ya koma ya zauna yana fadin"To karfin Daada kuma ya kare" Duka suka hayesa ya dauke su yana Nishi suna Dariya ni kuma sai na Duka ina kwashe kayan da suka cire ina shirin gaishe shi Saboda na Dauka zan gansa cikin wani yanayi sai naga ya ware kamar jiya baya cikin Damuwa ba zato kawai naji muryansa yana fadin"Ina kwana Fa'iza.." Dankari makari mamaki ya cikani sai naji kamar ban ji daidai ba,na juyo ina kallonsa kai tsaye ya sake fadin"mun tashi lafiya ya kwanan yara..? Yadda ya kafeni da ido ne yasa bakina na rawa nace"la.lafiya ina kwana" Da Sauri na wuce dakin yaran har ina cin Tuntube wajen waigensu to Allah na Tuba abun ne naji sa wani bambaramkwai namiji da suna Hajara ban gama mamaki ba sai da naga Hafsah ta zubo musu taliyar data dafa musu ya zauna kasa a cikin su yana bama Ahmad da Musty a baki in Anum ta bude sai ya saka mata Amir kuma sai yace"Daada kai ma bude baki na baka" Sai ko ya bude baki ya basa,mamaki ya sandar dani wani abu ne da ban taba gani ba ko a baya,zai dai dauke su yayi musu wasa ammh wahalar su kan bai sani ai abun mamaki na gaba sai da suka gama,Shi ya tarkata su yace zai kai su har makaranta,Saboda Halin Rayuwa yaran ma sun koyi hakuri ba kullum suke tafiya da abinci ba watarana ruwa ne sai ranar da na samu ciniki sosai har da Lemu ina siyan musu, yau ma nayi niyya ganin shi zai kai su sai na bashi naira Dubu nace ya siya ma kowannen su Lemu da biskit. Bai yi min gaddama ba ya karba yana fadin"Ni kar na siya ma kaina Umma? Sabon salon nasa ne ya girmeni sai na wuce kitchen ina fadin"Kaima ka siya" To fadan da yafi karfinka ai sai ka maida shi wasa,ina cin abinci ya shigo nayi mai sannu da zuwa na bude baki na ce abincin nasa na Dakinsa sai kawai naga ya tankwashe kafa a gabana ya zauna ya tsoma min hannu acikin Farantin da muke ciki ni da Hafsah ta tashi taje ta Dauko mana Ruwa ne. Baki na saki hade da Hanci ina kallonsa shiko ko ajikinsa Hankalinsa kwance ya fara ci a baya nasan Halin Fafansa,Ko abinci ban taba gani yaci da Hannu ba, sai da cokali ammh yau da Hannu yake ci har yana sude hannu,ganin haka yasa na tsame hannuna zan yi mgana yayi saurin tare ni da fadin"ki ci mana Fa'iza. ko baki son ci da ni ne.? Kai na girgiza ina fadin"Aa tare da Hafsah muke ci" Kafin yayi mgana ta fito Dauke da Ruwa itama ina gani ta saki baki taga bakon abu,yana ganinta ya Dago yana fadin"kin ji Hafsah jeki zubo naki kici ki barni na samu Ladan cin abinci da Matata yau" Kalmar Matata din ne na rika nanatawa kaina ya yi wani dum sai ya kasa Dauka duk da yaso na sake naci abinci da shi,sai na kasa saboda abu ne da ban saba gani ba. Kai ranar naga abu ni Fa'iza Shigowar Jamal ya ceceni suka zauna afalo suna Hira ammh Fita goma shiga goma in na dago idonsa na kaina mamakinssa ya cikani kamar wamda yayi gamo..? Ashe wasa farin girki tundaga ranar Yaya Ishaq ya sauya daga Ishaq din da na sani ya koma wani mai sanyi mai kula mai tallali,yanzu ya daina zama in dai yana gidan komai zan yi sai ya taimakamin yara ko da nayi musu wanka shi zai shirya su ya basu abinci ya kuma kai su makaranta,Ko gyaran Daki nake yi sai yazo ya amsa ko ya fara tayani tun yana bani mamaki har yazo ya daina bani. Sai wani kafa kafa yake yi dani wanda sam wannan Sabon dabi'an nashi bai burgeni ba domin nafi sabawa da wanchan Ishaq din,Ranar kwana Biyu Tsakani na fito da wankin yara kawai shima ya fito yace zai tayani jikina ya fara rawa kada Mama ta fito ta gan shi na shiga uku.na fara Hada sa da Allah ya bari yace bazai bari ba, sai