Sashe 145
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
baki albishir din" Cikin mamaki na kalleta zan yi mgana ta dora yatsa a bakina tana fadin"Ba yanzu ba sai kin dawo" Da kanta ta mike ta zabo min wani hijabi sea green cikin kayana Sabo ne ban ko taba sakashi ba. Ta bani na cire na jikina na saka bayan ta sakani na sauya kayan barcin jikina na saka wata bakar Abaya,ta kuma saka na goga Turaren Humra cikin mamaki nace"Ammi bana son kamshin turare,kuma fita zan yi fa" Ammi tamin dakuwa tana Fadin"Kuma kike had'awa kina Saida mana amnh ke kice baki so..?ai ko baki isa ba yarinya ba turare yanzu kika fara son shi da saka shi" Dariya nayi ban yi mgana ba,haka ta sakani gaba muka fita ina tafiya ta shiga gabana tana nuna min wai irin Salon Tafiyar da zan yi in na Shiga Falon Abba baki na bude kafin nace"Ammi waye ya zo wajena..? Ko baki Abba ya yi.? Fadin haka yasa sai da gabana ya amsa ko dai ko dai Engr ne..? Na juya nayi ma Ammi mgana naga Tuni ma ashe ta koma Shashenta ta barni nan tsaye sai na fara waige ina jin wani yam acikin jikina. Kamar najuya zuwa shahshen Inno daman ban shiga mun gaisa ba da Safe,Sai kuma na kasa bazan iya komawa ba tunda Ammi ce da kanta ammah jikina ya bani wani abu. To ko dai ishaq ne..?in shi ne kuma da Anun ta fad'amin.." Ni dai kafafuwana suke ja na zuwa Falon Abba ga yanayin mganata ga Sanyin murya shiyasa da nayi sallama ban sani ba ko yaji,ni kuma sai naji kamar gyaran murya shiyasa na shiga falon kaina na kasa. Kafafunsa na fara gani zuwa kansa yana tsaye ya juyamin baya yana waya ammh kuma abun mamaki wani yare yake yi kamar yarbanci yarbanci na kasa dai ganewa saboda ina Rude ne. Dagowa nayi in kallesa dakyau karaf ko kamar juyin waina naga ya juyo muka hada ido hud'u da shi jiri ne yaso ya kwasheni na kame kaina da jikina ammh a wannan karon ma jikina da gabana sai da suka amsa wannan kamilaliyar Fuskar da wannan mirmishin da yaki b'acemin yau ma da su ya jefeni kafin ya yi mgana ashe wayar na makale a kunnensa bai kashe ba naji yana Fadin"Is ok Papa i will call u later" Daga haka ya katse kiran kacokan kuma ya maida Hankalinsa kaina ni ko ban saba ganin irin wannan kallon ba, kaina na kasa ina rawan jiki Lokaci daya ina faman cikwikwiye hijabina ta gaba. Ina ga fahintar haka ya yi yasa ya yi mirmishin sa dake dimautani kafin ya matsa yana nuna min saman d'aya daga cikin kujerun falon Abba yana fadin"Barka da shigowa sarauniyar mata Hv a sit.." Sai kuma daya fada haka yayi yayi sauri gyarawa da fad'in"Ki zauna bismillah" Yafad'a duka a tare ai da sauri na samu gefen kujera na zauna ina kara Dukar da kaina sai kawai naji yace"Kada mu fara haka dake Fa'izaa kan kujera zaki hau a matsayin ki na Sarauniyar mata,ni kuma na zauna a kasa a gabanki tunda nine zan mika kokon barata." Da sauri na dago muka hada ido sai na Dirirince zan yi mgana ya yi saurin cewa"Kada ki fara da min gaddama Faa'izaa ni mutun mai son ya yi mgana Daya ajisa. kuma a Sauraresa" Yafada kai Tsaye cikin taushin murya mamakin kalamansa yasa na dago ina kallonsa kwarjinsa yasa na kasa mai gaddama sanda ya sake nuna min kujera yana fadin"Ga inda ya dace dake nan" A kunyace na mike na zauna kamar zan yi kashi,saboda yanayin zaman nawa sai ya yi dariya kafin na ankara sai ganinsa nayi a gabana ya zauna har da tankwashe kafa baki na bude ina kallonsa da Sauri yace"To Rufe bakin mana kada ya makale a haka na shiga uku" Mganarsa ta bani Dariya har sai da na kannen fuskata cikin Hijabi Saboda kunya shima yar Dariyan ya yi kafin kuma yadan ci Serious yace"Da farko dai ni sunana Abdulbasit Abdulghaffar Alowatosin.." Da sauri na d'ago ina kallonsa in naji dakyau sunan yarbawa naji ya fad'a shi kan shi yasan yanayin kallon nawa kenan yasa yayi dariya kafin yace"Yes ni bayarbe ne mahaifina Haifaffan garin Beneu ne,mahaifiya ce Bahaus hiya haifaffiyar garin kano ni ruwa Biyu ne Hausa_Yoruba" Yafada kai tsaye bai kuma bani Damar mgana ba ya cigaba da fadin"Ni Engr ne ina aiki da matatan mai na Edo state,ni ba yaro ba ne ba Wasa ko bata Lokaci ko Doguwar mgana yasa nace ayi miki mgana ba. jiya ne da kika zo gaisheni na ganki to mganar gaskiya tun daga jiya zuwa yau baki bari zuciyata ta Huta ba Faa'izaa.." Ya fad'a yana kallona nima abun mamaki shi nake kallo ina auna daman akwai yarbawa masu kyau haka..?Na san maza masu kyau da gayu tunda na zauna da Ishaq ammh sai naga kamar wannan na gabana ya hada wasu abubuwa masu tarin yawan da Ishaq bai da su. Sai dai tunanani ya tsinke ne da nganarsa na karshe gabana ya fad'i kada dai shima jiya tunani ne ya kamasa kamar yadda ya kamani..? Sai dai ganin yadda na bada Hankalina a kansa ne ina jin yadda yake kiran sunana na shiga duka sassan jikina FAA'IZAA..! Gyara zama ya yi yana fadin"Kai tsaye ba tare da kwana kwana ko zagaye zagayen samarin zamani ba, na ganki kuma naji ina son ki Faa'iza kuma so irin na aure" Ido na waro a firgice kafin nace"Ni..? Sai ya gyadamin kai kafin yace"Yes..Ko ban kai ki soni ba ne..?nayi miki tsufa ko..?Shekarata arba"in da Biyar kiyi hakuri ban fara Furfura ba, a kai ne kuma bata wuce guda Biyar in baki so sai na aske su Faa'iza.." Dariya ce take neman kamani sai na kanne na juyar da kaina ganin yadda ya marairaicemin a gabana cikin yanayin muryata nace"A'a ko d'aya ai kai ba tsoho ba ne" Ajiyar rai yayi har ina jin saukanta kafin yace"To mene laifina ne..?ko so na ne kawai ba'ayi..? Kai na girgiza kafin nace"Ba haka ba ne" Da Sauri ya katse ni da fadin"To ya ya ne Faa"izaa..? Yadda ya kiran sunana sai da tsikar jikina ya tashi kai na girgizamai kafin nayi mgana yayi saurin fadin"Bana son mgana da kai. Ina son ko da wani Lokaci na rika jin muryan ki mai Dadi" Sai na saki hanci kawai ina jin abunda ban taba ji ba,ni daman ashe muryata na da dadi...?muryan da Yaya ishq yace yana jin haushi ina mgana ina rabeta kamar yar koyo. Sai idanuwana suka ciko kwallah kaina na kasa nace"Ni ba ajinka ba ce kafi karfina bani da dukkan abunda mata masu kyau da wayewa suke da shi..ni bazawara ce" "Ya'yan ki kuma hud'u ko..? Yafad'a da sauri bayan katseni cikin mamaki na kallesa shi kuma cikin kwarin gwiwa yace"Nasan ke bazawara ce na kuma san muna da ya'ya yaushe kika shirya kaini na gan su? ko kuma ki bani lambobin su New papa din su zai kira su ya gaishe su" Sai na kasa mgana kiris ya rage in yi kuka kai tsaye yace"Sai kuma me ma kika ce..? Yauwa ke ba ajina ba ce sannan baki da abunda da mata masu kyau da wayewa suke da shi ko..? Yafada cikin sigar tambaya sai na kasa bashi amsa yanayin Fuskarsa sai ta sauya cikin Sautin maza jarumai yace"Kafin na baki amsar ki meyasa kika yi min wannan mganar..? A ransa yana tunanin meyasa suke da wannan tunanin Baban Nana ma ya fad'a masa Ni ko kaina na kasa nace"Saboda mazan wannan mazanin basa auran mace in bata da abubuwan kamar kyau,nasaba,gata,karatun boko wayewa,in kuma suka samu akasin haka sai kuke ganin kamar ba ku auri macen da ta dace da su ba kuma haka naga kuna yi shiyasa" Katsaneni ya yi da fadin"Kika ga suna yi dai Fa'azza..! Ni ba haka nake ba ni Abdulbasit kyan mace bai taba Damuna ba" Wlh tallahi billahil azim in kyau nake nema ba a Nageria zan yi aure ba akwai kasashen larabawa,ina ne bamu shiga ba wasu matane bamu gani ba..? Ammh ba wacce ta kwantamin arai sai ke Faa'iza ina sonki da zuciya d'aya ba domin wani abu naki ba ke din kawai nake so.." Yafad'a yana bina da wani kallo kaina na kasa sai hawaye cikin Tagumi yace"Ya illahi ni Tosin saboda rashin so na har da kuka Faa'izaa..? Sunan da ya fad'a yasa bansan sanda na kwashe da Dariya ba ina Tare bakina kallona yayi yana mirmishi kafin ya cire tagumin yana Fadin"Eh Alowatosin Yoruba name dina ne shine a gida su papa ke kirana Tosin in ba a bangaran aiki ba, achan Benue Da tosin suka sanni ammh yanzu a gabanki Abdulbasit ne" Ina dariya nace"Ko dai Tosin..? Sai kawai ya sake tagumi yana kallon bakina kafin yace"Tosin din FAA'IZAA ammh" Dariya ta shakeni na fara tari da sauri ya mike ya isa frige din Abba ya Daukomin ruwa jiki na rawa ya budemin ya mikamin na karba na sha kadan na mika masa ya karba yana min Sannu sai da yaga tarin ya Tsaya sannan yace"Oh ni Tosin zan ma kaina Tsiya tun kafin na gama na kafa gwamnatina.." Dariya naji ta kara kamani sai da ya sauke ruwan hannunsa sannan ya zauna yana fadin"Ni dai ki bar Dariyan nan ki fara ji da Tosin bawan Allah" Ya fad'a kamar ya yi kuka ni yanayin yadda yake fadin Tosin din ne yasa Naji na kasa daina Dariya ai sai ya Hade rai yana Fadin"Kin san Allah? kika kara shakewa ko ruwa bazan miko miki ba" Sai na natsu ina Sadda kai na kasa mgana sai dai ina ta mirmishi leken Fuskata yake yi yana Fadin"Cute" Nasan ma'anar cute da Sauri nace"Nasan zagina ka yi" Ido ya waro kafin yace"Ni tosin yaushe..? Kai tsaye nace"kace cute ni nasan ba Cute ba ce..Nasan ni mummuna ce sannan ana yawan fad'amin ni mummuna ne" Rai ya hade kafin yace"su waye..? Gaskiya ba gaskiya suke fad'a ba..To ni dai koma menene haka naji kuma nagani" Kai tsaye nace"Baka ce ni. ga shi ban da ilimin boko ban iya turanci ba" Shima kai tsayen yace"Ni bakin ki ya yi min daidai ma,nima baki ga bakin ba ne, mu