Sashe 13
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rigima da karfi suke mganar Shiyasa nake jiyo su sama sama Tunda Baba ya fita sallar asuba bai Dawo ba Mama ta rude ta shiga tashin Hankali Saboda rashin Sanin inda Ya Ishaq ya shiga Tunda yaji mganar auran mu Ni dai ban san ya akayi ba ina kwance sai ji nayi an rufeni da duka kota ko'ina,ina kuka ina ihu ammh Mama bata Tausayamin ba kuka take yi tana Dukana fadi take yi"Dangin jaraba dangin masifa Saboda ke Abban Ishaq yace zai iya rabuwa dani...?Saboda ke Ishaq ya bar gida ban san ina ya shiga ba..? Kuma ahaka zan amince na hada Zuru'a dake..?wlh sai dai ki mutu ammh ni Saudatu bazan taba Hada zuru'ata da b'ara gurbi irin ki ba Shegiya ya'yan shegu dangin maciya amana Mummuna dake D'ana yafi karfin ki" Da karfi take mgana shiyasa na ke jinta ina ta bata Hakuri bata jini ba Badariya na gefe tana kuka tana rokon Mama ta kyaleni ammh bata tanka ta ba Jamal kuwa yana Tsaye shima Fadi yake yi"Mama duka wayoyin ya Ishaq suna kashe ne sannan na kira abokan sa na kusa sun sanar dani bai zo ba kuma bai kira su ba..Gaskiya Baba shima bai yi Tunani ba Ta ina Ya Ishaq ya Dace da Fa'iza..? Ina ji Mama ta wurgoni Falo tana Fadin"Ai yadda ta saka ya bar gidan nan nayi Rantsuwa bazan yi kaffara ba itama ta gama zama a wannan gidan yau ba sai gobe ba sai ta bar min gidana" Da duka da gori da Tsinuwa Mama ta rakani waje ta maida kofa ta Rufe,Dagani sai rigar jikina ta atamfa sai dankwali shima tana Dukana na Rarumeshi na rike a hannuna kafata ba Takalmi Mama ta koreni nan na rakube jikin gidan ina ta kuka na Duba gabas da yammah kudu da arewa bani da wani gata a garin katsina kuma Mama Tunda tayi Rantsuwa to da gaske take Dankwalina na warware na yane kaina Dashi gidan Anty Mamah ya fadomin tana da Sauki Sauki kila ita zata iya taimakamin da kudin motan da zan koma karofi domin chan ne gata na anan duniya.. Da kafata Tun daga Kofar soro har Cikin asibitin kashi,A kafata ina tafe ina kuka kamar zararriya,ban gaji ba Domin halin da nike ciki gajiya bata da Muhalli a wajena Sai dai Anty Mahma ta ganni kwatsam kamar Daga sama tayi matukar kad'uwa da na zube ina bata labarin korar da Mama tayi min Kai ta girgiza kafin tace"Kai Mama meyasa bata bin abu a Hankali ne..? Bari na kirata.." Da Sauri na rike mata Hannu naji tana mgana ban ji me tace ba sai dai Yanayin mganarta da wayarta data Dauka sai Tunani na ya bani Mama zata kira ko Anty Binta ni kuma na shiga Tsaka mai wuya acikin wannan Halin Karofi nake son zuwa na Durkushe gaban Hajiya na Roketa ta janye wannan mganar in tana so na cigaba da Rayuwata yadda Allah ya Tsaramin in bata so ta kara jefa Rayuwata cikin wani Sabon kangi. Dakyar Anty Mamah ta amince da Rokona ta bani kudin mota ta Daukeni a motar ta da kanta ta kaini Tasha ta sakani a motar Karofi ina ta kuka ta Tausayamin ta Dafa kaina Dake cikin Sabon Hijabin data bani da Takalmi tace"Ki daina kuka Fa'iza ba matsala in sha Allahu Mama zata Sauko" Har na kai karofi kuka nake yi sai da Muryata ta dishe kukan rashin gata da kuma Tunanin yadda yanayin Rayuwata ya fara na fara jin kamshin gaskiya kila bani da sa'a ne komai nawa ba mai kyau ba ne irin na kowa rayuwata ba Daidai take da Sauran mata ba. Sai dai Goggon Karofi ta ganni yarkace yarkace kafin na fadamata abunda ya faru sai ta nemi dukana sannan na Zayyane mata komai bazan manta ba sai da ta share kwallah ta kamani ta Rumgume tana Fadin"Abunda Saudatu ta aikata miki kenan..? Daina kuka Fa'iza watarana sai Saudatu tayi kuka idanuwanta akan abunda ta aika miki akwai Allah" Araina ban taba Hango hakan ba ni kuwa wani matsayi zan taka da Mama zatayi kuka Saboda ni..? A daran ta Kira Baban katsina ta fadamai Halin da ake ciki yace da Safe zai shigo garin ni kuwa Lallashina Goggo ta dinga yi Hatta Hafsatu dake da karancin shekaru ta shiga Damuwa ganina cikin wannan Halin Hajiyar karofi kuwa tana kwance sai bina da kallo take na kasa na mata wata mgana domin sai naji bakina yayi nauyi ganin yanayin datake ciki Goggo tace tun ranar da Baba ya bar nan jikin Hajiya ya kara rikicewa. Washegari Baba yazo sun kai ta ba dadi da goggo ta nuna mai ya janye mganar auran nan ita zata rikeni Allah ya bani wani mai sona in yi aurena ammh ba Ishaq d'an Saudatu ba shi kuma Baba yace indai yana Raye sannan shi ne Uba ga Ishaq kamar ya aureni ya gama ina Durkushe gabansu suka rika wannan Hayaniyar ad'akin da Hajiya take jinya itama tana kwance bata iya mgana ba sai gyad'a kai hawaye na bin gefe da gefen Fuskarta. Baban katsina ya tafi ko sallama bai yi ma goggo ba Allahu akbar adaran Hajiya ta amsa kiran Mahallacinta,Tun daga Lokacin da naji goggon na Salatun mutuwar HaJiya da kaina ya amsa Dum! Har gobe in na Tuna da mutuwar Hajiya sai yanayin ya Dawomin da gaske ne ni Fa'iza bani da Sa'a? Meyasa duk wad'anda suka Tsayamin suke tafiya su barni Farko Babanmu Sannan ga Hajiya itama har aka kai Hajiya kushewarta bana cikin Hayyacina gida ya cika Har Hajiyar Dala da duka zuru'arta suna nan Hadda Mama da su Anty Binta su Ya Asiya sun Dauka mutuwar Hajiya ce ta tab'ani basu san abunda ke Faruwa ba har kuma lokacin ba'a san ina ya Ishaq ya shiga ba. Ranar da bazan manta ba,Itace Ranar da aure ya kulli tsakani da Wanda bai Taba sona ba har ko yau da muka Tara zuru'a dashi aurena da Ya Ishaq wanda yau har gobe Mama bata daina aibatani da zuru'aar maciya Amana Dangin Tsiya ba,Ranar addu'ar bakwai din Hajiyar Karofi Baba ya tara Mutane ya Biya Sadaki aka Daura aure na ba wanda ya sani sai da aka Daura Gidan mutuwa sai ya koma Gidan Fad'a da Hayaniya domin Mama kaina tayi tana fadin sai taga bayana Goggon Karofi ta shiga Tsakani Ranar ba iya ni kad'ai ba hadda Mahaifin mu dake kasa yasha zagi Taamadina na gidan sulalewa tayi ta koma gidansu tana kuka,kukan maraici da Tausayin ya'yanta. Sai alokacin kowa yasan Halin da ake ciki Goggon Karofi ce kad'ai da ya'yanta ke tare dani ban da Hajiyar Dala data mara ma Mama baya,Aranar Mama ta koma katsina ta sha alwashin sai taga yadda auran nan zai Tabbata shi kuma Baba yace sai dai in ba shi ya Haifi Ishaq ba. Ya Asiya da Yaya Mariya sun koma Gidajen su da Tunanina aransu da Tausayina su kan su sun hango Yadda rayuwa da kaddara suka kara gangarawa dani. Kwana Ashirin da Rasuwar Hajiyar Karofi Sai ga Baba ya zo shi da Ya ishaaq,wanda ya gama gudun nasa ya Dawo jiya da Daddare ya samu labarin An daura masa aure dani Ya Ishaq ya kasa katabus domin Baba ya Daga mai murya yace in har yaki karb'ata a matsayin mata to sai dai ya chanza wani uban ba shi ba. Wannan mganar shine Sarka na Farko da ya fara kulle aurena da ya ishaq,Baba ya bama Goggo kudi ta yi min siyayya sannan ya kama mana Haya a katsina cikin gari in da zamu zauna ni da Ya Ishaq,har suka tafi ban gansa ba shima bai nemi ba,Tun kuma Daga Lokacin Baba ya fara shirin Tarewata Mama kuwa tayi Kukan har tagaji ta Saduda ganin Da gasken Baban bazai fasa ba. Kafin Ranar arba'in din Hajiya karofi hatta jere na Goggon Karofi da ya'yanta da Yan'uwana sun gama min komai Domin Baba yace ranar addu'ar arba'in Zan tare agidana Yaya Mariya ita takaini gidanta ta tsifemin kai ta wanke ta kaini akayi min kitso da Kunshi Ina ta ce mata ta barshi kunshi da gyaran jiki sai Mata masu kyau ba irina ba ban taba manta kalamanta alokacin Kaina ta Dafa kafin tace"Kema kina da kyan ki Fa'iza sai dai in ba'a gansa yanzu ba ne..Ammh na tabbatar miki nan gaba zasu ga abunda nake gayamiki" Alokacin mirmishi nayi mata Domin nasan ta fada ne ni kaina nasan bani da kyau sannan ina da nakasu ta bangaran Ji na da mganata Aranar da Hajiya ta cika kwana arba'in a kushewarta ranar na Tare agidan Ya ishaq aurena ba irin na mata masu kyau da gata ba ne,Daga ni sai kayana da Goggo ta d'inkamin Sabbi ita da Baba domin da Goggo Taso su yi min Rakiya sai ya Ishaq yace baya Bukata dagani sai shi a mota sai Baba da Direbansa. Daga Mama har ya'yanta ba wanda ya Leko karofi,Baba da kansa ya shiga Dani karamin flat din da ya kama mana mai Falo da Dakuna Biyu sai kitchen da Tsakar gida,Shi ya damka Amanata Hannun ya Ishaq da karin wasu manya manya sarkunan da Tun abaya na fada muku su suke rike da wannan auran namu yau har da nike baku wannan Labarin,Domin cikin kaukkausan murya yace mai"Ishaq ga Fa'iza nan na baka auranta ba Domin ta rasa me son ta ba sai domin cika Muradin mahaifiyata..Wlh tallahi ko da Rana daya in ka zalunce ta ban yafe maka ba Ishaq..Kuma ko da rana d'aya kabi Hudubar mahaifiyarka ka Tozarta Fa'iza shima nace ban yafe ba..Daga karshe matarka ce ta sunna ka Kula da ita kuma in ka Danne mata Hakki Allah na kallon ka sannan nima bazan yafe maka ba Sannan kasani Ranar gobe kiyama bazaka Rabauta ba Ishaq in dai ka saba ma Umarnina.." Kafin ya tafi sai da ya kara Jadaddamai in ya danne min hakkina na aure ko guda d'aya ya sani bazai kara samun albarkarsa ba,ya tafi bayan yayi min nasiha hakuri sannan ya sanar dani na zauna nayi ma aure Biyayya bazan taba Tabewa ba Duniya da Lahira Tabbas wannan Biyayyar da Baba ya Rokeni har bayan mutuwarsa ban sauka daga kanta ba,nima ita ke rike dani acikin rayuwar aure