← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 162 OF 175

Sashe 162

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tayi mgana Hajiyar Dala tayi karaf tace"Eh ita ce ma ta biyu. ai akwai ma yayanta da kannensu biyu,Kunsan ai auran zumunci ne da shi tsohon mijin nata" Ammi sai hararanta take yi fadi ba'a tambayeta ba sai Hajiya Shukra ta bata mamaki da cewa"Ai Babatunde ya fad'amin Allah Sarki ya sunanki..? Ta tambayi Anun ni kuma ina jin tace Babatunde nasan Engr take nufi tunda shi ya fad'amin sunan datake kiransa. Anum da Falaq suka fada mata sunanyensu cikin Mirmishin ta tace zasu zo mata hutu sai suka juya suna kallon mu tayi dariya kafin tace"Suna tambayan ku ne ku ce eh" Gababaya sai akayi dariya,ni kuma har inda nake ta kariso ta dagoni ta Rumgumeni kafin ta dago kaina Tana Fadin"'Sannu da zuwa Faa'iza.." Allah ya sanya alheri ya baku zaman lafiya" Gabadaya aka amsa da Ameen cikin yanayin fara'arta tace"Papa din su na hanya. bari ya kariso ku gaisa sai muje chan gidan ko..? Kaina na kasa na kasa mgana sai ta Dafa kaina tana fadin"ki saki jikin ki kin ji ko..?nan din ma duk gidan ki ne kina jina ko.? Sai na daga mata kai sakin Hannuna tayi kafin tace"Baku yi mgana Da Babatunde ba ko..? Meeting garesu nima tun safe da mukayi mgana ban kara jinsa ba" Sai naji Hankalina ya kwanta jin yana Lafiya sauran yan'uwanta ma suna ta saka albarka kamar zasu lasheni. Bayan fitan su su Kafaya suka shigo dukkansu kaya iri da'ya suka saka Atamfa riga da sikat har da Murjanin su,Rumgumeni suma suka yi suna murnan ganina Yan biyu ne masu kama daya baka iya bambamce su. Harda Mirmishin su iri daya ne. Suna kallo na suna min mirmishi sai na Tsargu naga kamar sun ganni ba yadda suka yi Tsammani ba ammh basu nuna ba. Kafaya tafi yawan mgana ita tace min"Anty Fa'iza u are welcome..'" Ita kuma Sharifa ce min tayi"Bro Tosin na son ki sosai ya bamu Amanarki yace mu kula dake sosai kiji abinci kada ki zauna da yunwa" Dariya kawai nayi nasan zai aika su Ammi na gefen mu suna ta kallon mu gwanin ban sha'awa zama suka yi dani suna min hiran Engr ina dariya ashe har a gida haka yake na Dauka yana rage wasu abubuwan ashe ma ni banga komai ba. Sai da akayi la'sar suka fita suka barmu muma muka yi sallah Ammi da su Anty Nasara sai fad'i suke nayi dacen suruka da dangin miji Hajiyar Dala dai ba baki sai dai nazarin abubuwa da take gani,sai bayan mun yi sallah ne aka aiko cewa mu shirya zamu tafi chan gidan daman bamu fito da kayan mu ba,sai muka natsa sannan Maa tazo ta tafi dani wajen Paapa dake falonsa. Dattijon ne mai kamala,yana zaune yana karatun Jarida da siririn gilashinsa mai karamai karfin gani,har kusa da kafafunsa Maa ta kaini ta zaunar tana fad'amai ga ni nan ya sakamin albarka. Ba ruwan shi kaina ya dafa yana ta sakamin albarka daga karshe yace"Allah ya sa ku zauna lafiya ki yi hakuri kin ji ko..?Oluwatosin God Boy ne ammh in bai yi miki daidai ba. juzt call me nima papa din ki ne kin ji ko? Sai na gyada mai kai ina Godiya ya bani kyautar kudi cheque Maa ta amsamin,nayi masa sallama muka fice bayan yace bazai samu zuwa Beneu ba. saboda aiki sai dai akwai brothers dinsa da Danginsa yasan i will Enjoy it. Bayan ni ma har su Ammi sun je sun gaisa sannan muka tafi gidan Engr Dake Apo,a motar Papa direba ya tukamu ni da Maa da Ammi sauran kuma suka Biyomu daga baya,su da yake basu da wani al'adu kamar namu na Hausawa Nakiya kawai da alkaki Ammi tayi musu aka raba biyu aka bamasu Maa sauran kuma Ammi tace sun munje Benue tunda iya abunda muke da shi zamu yi. Gidan Engr dake Apo Abuja karamin gidane ammh ya hadu falo biyu Bedroom hudu sai compaund akwai kitchen da bayika sai ta chan baya akwai tsakar gida da Famfo. Ammh gidan ya had'u yaji kayan alatun rayuwa har da wajen shakawatawa da wajen lilo,Akwai megadin dake tsaren gidan,Kowa sai santin gidan yake masha Allah. Hajiyar Dala fad'i take yi"Allah mai kyauta da kari yanzu Fa'iza ne a wannan gidsn..? Tana tunanin ko yayanta da suka auri masu da shi ba wacce ta samu gida kamar nawa,daganan ta sare tasan na riga na sha kwana daman ai abunda ya baka dariya watarana shi zai baka Tsoro. A babban bedroom din gidan Maa ta saukeni tana min addu'a su kafaya ne suka rika zagayawa da mutane suna ganin gidan da suka dawo suka baje suna labarin gidan Yaya Mariya tace"Faa'iza mutumin nan kudi garesa kenan" Ashe bamu ga kudi ba sai da Maa ta saka aka bude dayan bedroom d'in shake da akwatina bakwai babu abunda babu aciki harda zinare sai makulin mota kamfanin Peageua,ashe itace muka gani a haraban gidan,tab ashe kudin da yabani na kayan cin bikin ya hada lefensa ba tare da ya gayamin ba. Kayan ciki kuma masu tsada ne da yarari,bakin dangina ya kasa rufuwa dai masha Allah ke tashi,Hajiyar Dala da Anty Nasara ke fadin darajan kayan da Tsadan su, tuni ta saki ta san duk hassadann mai hassada Faa'iza dai ta dace da gidan kima da arziki. Yaya mariya da Yaya Asiya fadi suke"Fa'iza. yanzu ke ce da wannan kayan alfarman harda mota..? Allah mai hikima in yaso sai ya fidda matacce acikin rayayye in kuma ya so sai ya fidda rayayye acikin mattacce" Daman haka Allah yake lamarinsa ga Faa'iza ta hau wani mataki na rayuwa,ahalin kuma bata da ilimin boko kuma bata da kyau sannan ba fara bace sannan ita ba kowan kowa ba. Allah ta rike shi kuma ya bata Engr a matsayin miji domin ribar Hakurinta. Ni ko ina gefe bana mgana sai mirmishi zuciyata da gangan jikina sun cika da kewar Engr da Tunaninsa na kara gwada kiransa ban samu ba. kamar ya kashe wayarsa ni duk wannan kayan basa gabana na samu kwanciyar Hankali da salama shine abunda nafi kwad'ayi. Ammi bakinta har kunne itace kiran Abba tana fad'a mishi har Goggo sai da ta kira Badariya ko Fadi take"Masha Allah Anty Fa'iza ta tako wlh.." Nana Fatima sai faman daukan Video take saboda su Hafsah daman sun ce ta Dauki musu duk abunda ya wakana su Anun ko tuni sun fice suna chan wajen Lilo suna wasa Sai yammah su Maa suka koma gida da Daddare Direba da su kafaya suka kawomana abinci kala kala da ababen sha,Daman Maa ta fad'ama Ammi karfe takwas zamu tafi tunda tafiyar Mota ce in muka isa za'ayi taron gabatarwa bayan la'asar na chan garin haka suke yi in bako ya shigo cikin su,anayi masa taron Introduction kowa ya san shi,shima yasan kowa. Sai dare Engr ya kirani ina Dauka sai na sakamai shagwaban da bansan na iya ba ina fad'in"Tosin yau ka sakani cikin Damuwa.." Duk yau fa ban ji muryan ka ba.? Shima cikin damuwa yace"Tife na Meeting muka yini yi fa. kema kinsan ban samu dama ba ne da sai na kiraki..To yaya..?kun isa tun dazu ko..?kuna gidan Papa ko gidan ki.? Kinsan fa Saboda zumudin nafara jin muryan ki ko naji sanyi yasa ko Sweethear ban kira ba" Ni na zayyane masa abunda ya faru sai naji ya sauke ajiyar zuciya kafin yace"Alhandulillah. Gobe sai da rana zan kariso benue lokacin kun iso kuma ko..? Sai na dagamai kai kafin nace"Maa ta karbeni sosai ita da su kafaya harda Paapa shima yana yi ma addu'a" Cikin jin dadi yace"Haka suke ba su da damuwa ballatana su san ina son ki, so suna Daraja duk abunda nake so ne" Na aminta da mganarsa cikin gamsuwa nace"Naga wasu kayan kuma har da mota fa?ka manta ka bani kudi na siya wasu a kaduna..? Kai tsaye yace"me kika gani..? wai wad'anan yan kayan..?me kika sani akan Abdulbasit Faa'iza..? Ai baki san komai ba sai zama yayi zama sannan kila zaki kara sanina sai kuma in nayi wani abun zaki ce daman Haka kake Tosin" Sai da dai ya sakani Dariya mun jima muna hira kafin yace naje na kwanta Saboda tafiyan gobe. Ai ban kwanta ba na Dauro alwala na fara jera salollin godiya ga Allah har sai da na gaji. washegari ma Daga gidan su Engr aka kawo mana abinci Direba ne ya kawo mana wannan karon da wuri muka shirya Maa da su kafayat suka Biyo ma Dauke da katuwar BMW din Papa da Direba aciki aka sakani sai Ammi ta dawo nan su kafayatu kuma suka koma wacce muka zo da ita. Tun safe daman mukayi waya da Engr yace shi sai 12pm zai baro Edo zamu hadu achan to muna Hanya sai yayi ta kirana kunyar Maa yasa ba na Dauka sai ya koma yana kiranta bini bini sai yace"How is Faa'iza? Is she ok.? Ita bata damu ba sanin Halinsa da naci kan abunda yake so. Tafiya tsakanin Abuja zuwa Benue akwai nisa,mun ma yi gudu sai 2pm na rana muka isa asalin Babban gidansu muka sauka wato gidan Sheik Abdulbasit Abdulfattah. Ya'ya da jikoki cike da gida gabadaya kannen Paapa da yayyensa sun zo da iyalansu,gida ya cika da mutane gasu nan kowannen kalansa Dabam Dabam sai dai sun yi shigan su na yaren su musamman ma mazan. Dakin Hajiya Kudirat aka saukeni su Ammi kuma sauran dakunan haka ta rikeni tana yaren su ni ba ji nake yi ba. tsohuwa ce fa ta tsufa gaskiya sai dai Hutu da jin dadi. Daman Hijabi na saka har kasa,sai wata farar amtafa super mai baki da Fari shiyasa ma Hijabin jikina Fari ne,sauran matan kannen Papa da yayyensa ma suka yayyemeni suna ta yare hatta Maa naji itama ta juya yare su kafayatu ko muna zuwa sun shige cikin Dangi. Ankawo abinci su amala da miyar kuka taji ganda da nama sai jallop d'in shinkafa da kaza abinci dai cima kala kala suma su Ammi suna chan ana karrama su. Bayan mun yi sallah ne muka natsa ni daman ina tare da Anum da Falaq ne. Maa tayi musu bayanin yanayin taron kayan da zan saka tace matar Uncle din Engr Tobi. Bimpo kenan zata kawo nawa kayan,ni kuma
Chapter 162 · 0% Book details