Sashe 130
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a Abuja sai dai ban sani ba ko zai samu zuwa" Ammi tace"To kila in yana gari" Abba yace"Ba lalle ba gaskiya" Da haka suka rufe wannan Hiran suka Fara shirin kwanciyaa ******* Tunda ga ranar da Abba ya bar Karofi, Rana bazata tab'a fitowa ta fad'i Abba bai kirani mun gaisa yaji Lafiyata ba. sannan ya turamin 100k na bunkasa kasuwancina mganar makaranta kuma Mallam yace a jira sakin ya tabbata nayi iddata in nagama ina da Damar fita duk inda naga Dama,Da haka sai na Dakata ammh na samu natsuwa da kwanciyar Hankali,sannan na fara maida jikina,Goggo na da almajirai masu Dibo ruwa da sharan Tsakar gida gyaran Daki kawai nake yi sai Girki,Yarana kuma muna mgana da su ta wayar Zainab ammh ba ko da yaushe ba,Goggo da kanta ta shiga kasuwa ta min siyayyan kayan zobo da Kunin Aya,aka sauke a dayan Dakin inda na saka Freezer dina sana'ata zata dawo gadan gadan tunda zaman bazai min Dadi ba. Goggo ta aikamin makota yaya mariya ma haka tunda nan kusa da su suna siya Lokacin da ta kan sara a wajena shiyasa da na fara Zobo ba laifi ana samun ciniki matsala D'aya na samu Rashin wuta in nayi kunin aya sai ya fara Lalacewa kafin ya kare Tunda ba ciniki ba kamar Lokacin ina katsina ba. Da na fad'ama Abba ana matsalan wuta batare da sanina ba Sai ga Yaya Isa da katon Generator in ji Abba sai dai na kira nayi Godiya Baba Ati na nan bata koma ba,Inno dai Abba ya Turo Direba ya Dauketa zataje ganin Likitan ido. Gida kuma Tuni ma'aikata sun zo sun kawata gidan da kayan Furnitures masu kyau muma mun je mun gani mun kara gyara gidan nan Su Abba zasu rika sauka Tunda Baba Ati tace bazata iya zama ita kadai ba. Muna waya da Anty Fadila kuma tana zuwa duk weekend tana Duba su Amir suma Baban nasu na kawo su Tunda yaga sun shaku da yaranta. Mama bata koma Lagos ba tana katsina wajen Anty Binta sai dai Badariya da Jamal suna chan Zainab ga Tsohon ciki ammh haka ta fara zuwa aikin da Mahaifinta ya samar mata sannan kuma ya siya mata Motar da zata rika zirga zirga aciki ta Riga ta sadakar maman Amir bazata Dawo ba. Shi kan shi Uban gayyar tun bayan Tafiyarsa sai kirana yake yi ban taba Dauka ba,in dai naga shine ammh ina Daukan kiran Zainab Saboda nasan ko ita ko yara ko kuma Badariya,Har Jamal ma yana kirana duk korafin su Daya na dawo sai dai na bisu da toh ammh su kan su sun tabbatar da bazan Dawo ba. Dad'ina Daya da su Amir suka fadamin sai la'asar suke tashi daga makarantar Boko,gidan Anty Fadila suke zama saboda yaranta suna da Malamin islamiya in suka yi karatun Tare babansu in ya tashi aiki sai ya Biya ya Dauke su,Zaman su sai asabar da Lahadi shima gidan Anty Fadila suke yin shi Zainab fama take da kanta Ko nata ya'yan su Amir ke kula da su sai mai renon da ta zo da'ita. Ashe bani kadai Ishaq ke kira ba Harda Abba shima bai kara Saurarensa ba domin yace in yana son mgana da shi ya rubutamin Takardan Sakina,Tun bayan Lokacin Abba bai zo Karofi ba sai dai Hafsah da Nana Khadija sun zo sun yi Sati Daya suka koma Hafsah ta zama katuwa tayi jajir da ita ta samu Waddatccen hutu da jin Dadi. Ba Laifi sana'ata ta Dawo kuma Tunda aka ganeni ana ciniki sannan Goggo tasan almajiranta na Dauka su tafin da shi wata makarantar maza ta secondary sai kudina suma da suka gane har gida suke zuwa siya in ba Wuta sai na Tada in ji na,Ganin aikin namin yawa yasa Goggo ta ce na Dauki wacce zata rika taimakamin nan makotan su Goggo na samu wata Jummala Mijinta ya rasu tana da marayin ya'ya ita mukayi ciniki da ita zan rika bata 5k duk wata ta amince da Murnan ita ke Dafamin zobo ta kuma wanke aya ta kai nika nawa kawai Dubawa da zaman Had'awa sai aikin ya Ragemin Kuma Alhamudulillah sai Hankalina ya Dauke Damuwa ta rage samun Muhalli a zuciyata,Saboda ayyukan dake gabana. Yaya Asiya duk abunda ya Faru Labari taji mun yi mgana ta waya abu daya tace min"Fa'iza ki zauna ki yi Tunanin makomar rayuwarki in rabuwa da Ishaq mafita ce gareki zamu baki Goyon baya,in kuma komawarki itace Mafita Fa'iza ki koma Dakin ki ki Rumgumi ya'yan ki'' Da toh kawai na amsa mata Saboda bani da abun ce mata komai zan Fad'a bazata gane ba Makotana ma muna waya da su barin ma Sa'adatu sai dai ban taba Fada musu ina Karofi ba na barsu a ina Lagos ne Haka ma Hajiya sai dai ita nasan Kila Raliya zata Fadamata ammh har Lokacin batamin mgana ba,Sai nima na share ban mata ba,na maida jikina duk da ramar kasusuwan wuyana basu shige ba,Sai dai sun fara shigewa din Koda yaushe Nasiha ne tsakanina da yan'uwa suna Lallab'ani Saboda na samu kwanciyar Hankali kuma na samu matuka. Anty Binta ta kirani sau biyu tana min Daidaiciyar mgana na bita da Toh,ta kuma saka har Anty Mahma da Halisa suka kirani duka mganan su kan ya'ya ne na koma Saboda su,ni ko bana cewa komai sai dai toh, sai yanzu suka san da yaran..? Bazan kara bari Saboda ya'yana a cutar dani ba. Suna ta so na koma ne na cigaba da Bautar da na saba ina bakin Alkalami ya Riga ya bushe ba Ishaq ba gabad'aya maza ne da aure ya fita kaina kwata kwata. ******* Ranar litini da Safe mukayi mgana da Abba zai je Abuja suna da Seminar,kwata kwata Abba bai Fad'amin niyyarsa ta zuwa Lagos ba ashe haka ya kudurta a ransa,sun je sun yi seminar na kwana Hudu ma'aikatansu uku kaduna,Edo,da Warri suka hadu a wajen,Tattaunawa ta musamman kan bunkasa mai a Nageria,Engr bai zo ba yana London shiyasa ranar da suka gama Seminar din Washegari jirgin Safe yabi zuwa Lagos yana sauka a Tashar Saukan Jirage na Murtala muhammad ya samu Taxi har Headquater tattara Haraji na reshen jahar Lagos. Yana zuwa sunan Ishaq kadai ya Fad'a aka masa jagora har Office dinsa misalin karfe 11am na Safiyar Ranar jumma'a. Ishaq sai dai kawai yaga Abba cikin Shigar Suit bakake ya shigo office dinsa. Cikin Rawan jiki ya mike yana rawan bakin Fadin"Abba.." Abba bai damu ba shi da kansa ya samar ma kansa wajen zama Ishaq ya kasa zama Jikinsa ya fara rawa sai zufa Duk da sanyi A.c din dake Office d'in ya san mganar data kawo Abba. shi kuma Rabuwa da Fa'iza daidai yake da Lalacewar rayuwarsa gashi nan yanzu ko cikakken abinci baya ci,Badariya ta gama Hutunta ta koma kano,Zainab bata zaman gidan koma tana nan ba iya girki tayi ba Sai dai fa ya rika siya,me renon ne ma kan yi ma yara abinci da daddare in sun dawo makaranta shi kuma bazai iya cin abincinta ba,Kudinsu duk a Restaurant yake karewa wajen siyan abinci. Sanda ya dawo din nan dakyar ya Lallashi su Anum da karyan Umman su zata dawo in ta gama karatun data fara,rigima suka yi masa sosai sai da yakai su gidan Anty Fadila suka yi weekend yace ta lallashesu sannan suka Daina rigima Allah ya taimakesa makaranta ya Dauke musu Hankali da kiran Umma,ammh Tabbas yasan Fa'iza ce ginshikinsa yau in da ta nan da da shi da yaransa basu taggyara ba. Abba ya gaji da ganin Ishaq a tsaye sai ya karkace ya dauko karamar Jakar Briefcase dinsa ya zaro wata Farar Takarda, da Biro ya Sauke a gaban Ishaq Lokaci daya yana Fadin"Ka zauna mana" Ya fada yana nuna masa wajen zama Jiki ba kwari ya koma ya zauna a Dofane,Zufa har tana gangaro masa ta saman Goshinsa Abba ya Daure Fuska ya gyara zaman Tie dinsa cikin kaushin murya ya tura ma Ishaq Takardan zuwa gabansa yana Fadin"Ka da ka batamin Lokaci ina kan Hanya ne" Ishaq yaji kamar zuciyarsa zata bar Jikinsa Cikin rawan jiki yace"Abba.." Hannu Abba ya Dagamai murya a kausashe kafin yace"In har ka yi abunda nake so shine kake da Hurumin kirana Abba" Daga haka ya koma ya Hade ransa kamar bai taba Dariya ba Ishaq ya Kallesa Yaga ba wajen da zai yi wargi sai yaja Takardan ya Dauki Biron Jikinsa na rawa da Hannunsa ya kasa Rubutawa ya sake Dagowa yana kallon Abba kafin yace"Abba Baba ya ce min duk ranar da na saki Fa'iza bai yafemin ba.." Abba ya daga murya a Kausashe yace"Zai yafe maka mana aure ai rai garesa ya mutu ne, Kuma kada ka manta a jingine auran yake karisa ballasa kawai zakayi" Ishaq ya bude baki zai yi mgana Abba ya Dagamasa hannu yana fadin"Zaka rubuta ne ko sai kaji sammanci..? Yadda Abba yayi ne yasa Ishaq yasan bai da zabi. Sai ya sunkuyar da kansa kasa ya Fara Rubutu zufan goshin sa na Diga Bisa Farar Takardan gabansa. *Janafty* [7/26, 10:21 PM] Hauwa Galadima: *KNKB3006* *TASTED & TRUSTED* *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*. *AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*. *ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWOWINRL ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.* *AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*. *SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.* *DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*. *SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*. *KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.* *AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.* *AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*. *SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH* *DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*. *TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU* *08032773332* *DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*. *NATION WIDE DELIVERY* *Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.* *09069067488* Hannunsa na rawa zufan goshinsa