Sashe 70
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ne ake cewa in ya zauna anan me zai yi..?ayi dai mu gani in tusa zata Hura wuta. Bai wani jima ba yayi ma su mama sallama da cewa gobe zai je kano ya bi jirgi zuwa Abuja.Yaya ishaq da zainab din suka fita rakasa jikokinsa na Hannunsa,ya dade yana Tattaunawa da yarsa kafin ta Dawo cikin gida har ga Allah naso mu koma gida sai naga ko shi kan shi Gogan bai yi mgana ba, kada nazo nayi mgana cibi ya zama kari sai nayi shuru da bakina ammh har ga Allah ina cikin Takura. Sai da muka shafe kwana Hudu a gidan mama yayi mganar komawar mu Gida Mama tace mutane na zuwa Jaje da murna ya zauna,Zainab kuma aranar Direba yazo ya Dauketa ita da ya'yanta ta koma Abuja saboda aiki a gabana a gaban su Mama tace ma Yaya Ishaq yaushe zai zo..?ina kallonsa ya gimtse fuska kafin yace bai sani ba sai ta wuce tana fadin zasu yo mgana ta waya Mama har bakin mota ta rakata kamar zata goyata saboda kauna. Mu kuwa sai da mukayi kwana Biyar naga zaman dai yaki ya kare na Tattara yara na nace zan koma gida,Sai yace mu tafi shi sai anjuma da Daddare jamal zai rakosa zasu karisawa Tattauna mganar da suka fara da Mama,naji dadi da bai hanani ba sannan itama Maman yan mutumcin na kusa batace komai ba ko da yake mai zugatan bata kusa Anty Binta kenan. Ina komawa gida duk yayi kura na zage na gyara ko'ina Amir na tayani shida Anum saboda na koya ma yara na aiyukan da basu da wahala saboda gaba,bayan mun gama muka yi sallar la'asar sannan na Dora girki Sa'adatu da Habiba sun shigomin daman sun je har chan gidan Maman sun min barka da arziki da su mukayi ta Hira sai yammah suka tafi,girki daman farar shinkafa ne Amir ke dubamin ya iya hae dafa indomie da, taliya kadan bamai yawa ba,Da miya nayi mana ina da komai na kayan cefane na saboda tunda na fara samun gumina na daina jiran ayi min komai,tsaye nake a kaina kuma na tsaya akan ya'yana, ko yanzu din ma nace su kimtsa gobe sai makaranta fashin ya isa haka duk da sun koma karatun zango na farko akwai Laluran biyan kudin makaranta ga kuma abubuwa duk sun Chude ni dai na gama lissafina ko zan yini ina aikin sana'ata ne bazan gaji ba,Saboda ina so yarana su samu Ilimi bana fatan su rasa damar su kamar yadda na sara. Ina da Aiki da yawa na Hada Turaran wuta da Humra,sannan akwai masu Dilka wasu har kudin su sun turomin rashin natsuwa ne yasa ban ce musu komai ba sannan ga yan sarin Zobo da kunin Aya suna jirana,So nake sai hankula sun kwanta na Dawo da sana'ata kafin komai ya daidaita naga kuma inda Rayuwata zata kara Cillamu tunda sun bamu Notice nan da wasu kwanaki zamu tashi ashe da gaske zan tashi daga wannan Muhallin sai dai ba irin wanda na Kudiri niyya ba. Yaya Ishaq bai dawo ba sai washegari da Daddare muna zaune da yaran suna duba aikin da aka basu a makaranta,Ni kuma ina ta lissafin kudaden mutanen dake kaina acikin wani Littafi inda ban gane ba na Kira Amir ya dubamun suka shigo shi da Jamal,ya rakosa yaran suka mike suna Ihun ga Daada nima mikewa nayi ina musu maraba dukkansu nan falon suka yada Zango na shiga kitchen na kawo musu ruwa muka gaisa da Jamal shima na gaishesa ya amsa hankalinsa na wajen yaran. Jamal nayi ma mganar abinci yace sun ci abinci a gidan Mama sai dai ko In Yaya ishaq zai ci shi kuma sai yace sai dai zuwa anjuma, jamal bai Dade ba yayi mana sallama shi kuma ya nufi bangaransa yaran suka bisa yanzu har Ahmad ya Daina barci da wuri. Ni yaran suka bari da tattara musu littafan da suka watsar na kai musu Dakin su na adana musu nima na shige dakina, ina cigaba da lissafin abubuwa bani da wasu kayan Hadin sai na siyo sannan Kudina na Hannun Hafsah nake bama ajiya basa Hannuna. Ina so na kirata sai na Duburce na rasa ta inda zan latsa na nemo lambarta,Daman sun koyamin ba duka na iya komai a wayar ba,Sai na mike na leka shashen shi na gansu a falo suna da Budirin su na kira Amir sai dai ban ga baban nasu ba,Anum tace ya shiga wanka Amir na ba ma wayar shi ya nemo min Lambar Hafsah ya kiramin nayi mgana da ita tace min tunda na dawo gida gobe zata dawo nace yauwa gwara ta dawo din. Ina cikin Gyaran gado na Anum ta shigo da gudu tana fadin"Umma Daada yace ki hado masa Tea" Sai na amsa mata da Toh sai da na gama gyara gado sannan na fita na Dora ruwan zafi na saka mai citta da kanunfari,da Top tea suka Dahu tare na tace sannan na juye mai cikin karamin Fulas din da na siya,Tunda na siya sabbin kayan aikin Kitchen,su dai da suke nawa Tsoffin na Sadakar ne ammh na falo kam suna cikin wani Daki dake haraba kwashewa kawai nayi na sauya sabbi,nasan Halin sa tsab in yaji tijaransa zai ce ina kayansa Tunda shi ya saka komai na gidan kafin mu dawo. Da kaina na shiga na kai mai yaran dai ke ta duduma afalon shi bai fito ba na sauke mai saman Karamin Center table din dake falon na kalle su ina fadin"Dare yayi aje a kwanta gobe akwai makaranta" Anum sai ta dira baki tana fadin"Umma mu wajen Daada zamu kwana."sai na rike baki kafin nace"Da wajen Daadan kika saba kwana..?zaki wuce ko sai na mangareki" Nayi kamar zan kai mata Hannu sai ta goce ba zato kawai naji tace"To Umma Anty in tazo tana kwana anan ke ko baki taba kwana a dakin Daada ba.." Ta fada daidai Lokacin da ya fito daga cikin Daki yana sanye da jallabiya yaji kuma abunda tace ni ma mamakinta ya sandar dani na shiga tafa hannu Cikin mamaki ya kalleni nima na kallesa sai kawai na kauda kai na sukunci Ahmad da ya barci ina Fadin"Sai da safe..Amir riko Musty kuje ku kwanta" Daga haka na fice sum sum suka bi bayana Mazan na fara kula har suka kwanta sannan na dawo Daki mamakin Anum ya gama kamani na tashe ta tayi fitsari sannan ta koma ta kwanta araina nace yara ma kada a raina su,su na ankare da motsin kowa Allah mai iko har nayi barci da Tunanin Anum a raina. Haka muka cigaba da gungura rayuwar mu,Yaya Ishaq sai zaman gida ba inda yake zuwa sai ya bani tausayi magidanci ne fa da ya saba fita aiki da Zirga zirga yanzu ya Dawo sai dai ya kwanta in ya gaji ya zauna,Mutane na zuwa masa jaje cikin mutanen Mama,ko jamal yazo su wuni yana tayasa Hira,Hafsat ta dawo ita na Tura ta shiga kasuwa ta siyo min kayan da bani da shi na kunin Aya da zobo sai na Hada Turaruka ina da nayin Dilka na Halawa ne ta siyomin. Yaya Ishaq na da sati biyu da Dawowa na Fara sana'ata,yana shashensa bai fito ba sai dai komai ina yi masa,fita ko sai dai yaje gidan mama da daddare ya Dawo,tun Safe da na tashi ban koma ba ranar sau biyu nayi zobo Safe da Yammah Saboda yan sari ko da ya fito da yammah ya ganni ina ta Jera Robobin a katon Frezer na bai min mgana ba,nima ban yi masa ba yadai ce zai shiga gidan mama nace a dawo lafiya. Ina matukar Tausayamai Saboda akwai Tausayi ga wanda ya samu karayan arziki da kuma rasa aiki,Tunanin inda zamu koma nake yi, saboda ina lissafin saura Kwana goma Wa'adin da suka bamu ya cika yadda bai min mgana ba nima na zura masa ido ranar da yadawo yake fadamin abokan aikinsa daga Abuja zasu zo su yi mai Jaje akawai abincin da zan iya Dafa musu? nace muna da Cefane sai ya kalleni cikin mamaki kafin yace"Wa yayi muku cefanan..? Kai tsaye nace"ni mana" Cikin karin mamaki yace"ina kika samu kudi..? Ina Yar dariya nace"Baka ga ina sana'a ba ne..? Sai kuma yayi shuru bai kara mgana ba,washegari suka zo sun kai su goma Hafsah bata shiga makaranta ba ranar ita ta tayani muka yi musu abinci mai rai da lafiya na hada musu da Kunin Aya da zobo na da ke saidawa. Suka ci suna ta santi,Daganan gidan Mama ya kaisu sai dare ya Dawo,kwana uku tsakani yace min Mama ta kirasa kan mganar gida zai je yaji,da zai tafi na basa dubu daya nace yayi na adaidata sai yaki karba wai yana dashi ni nasan bashi da shi,bazai karba ba ne sai na kyalesa na cigaba da Harkan gabana. Daya dawo daddare karo na farko Tun aure na da shi ya taba zama ya yi shawara dani,sai ranar wai mama nata saida kayan gidanta na wuta da kayan katako tana so ta had'a kudin gida ne muma tace abunda zamu Dauka mu fara hade su waje daya Sauran sai a saida su. Ni ko sai naga kamar tsarin bai yi ba na kallesa nace"Ni ko da zaka bada shawaran da kudin da za'a siya gidan da zamu zauna me zai hana mu kama Haya na shekara daya..?kada ka manta akwai Hidima fa gata abinci gata yau da kullum ga na Makaranta da Dawaniyar yara ga Jamal yanzu yake aji Hudu Badariya wannan Shekaran zata gama ga Laluran Mama duka suna kanka ne shine naga sauran kudin in aka kama Haya sai a toshe wasu ramukan da su ko ya kagani..? Sai yayi shuru yana kallona kafin yace"Kuma fa Hakane Fa'iza ni sam ban yi wannan tunanin ba" Har acikin raina ni na fadi ra'ayina ne ban dauka zai ji mgana ba ta sai ga shi har su Maman da ya kawo mganar sai suka aminta,Mun fara shiryen shiryen tashi,na hada kayan da zamu Dauka wadanda kuma za'a saida aka fitar har da Tsoffin wad'anda na fitar duk aka saida su gabad'aya. kayan bangaransa yace a saida su duka,Katifa kadai yace za'a bar masa ta ishesa ni dai na ware gadona