Sashe 150
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nana Khadija ta lekoni tace Inno na Cigiyata,sai nace tace mata bana jin Dadi ne zan shigo da Daddare. Bayan sallar mangriba Abba ya Dawo gidan tare da Ammi kila sun biya ne sun D'auketa,ina daki Hafsatu tazo ta kirani In ji Abba sai da gabana ya fadi amnh sai ban razana ba na riga na yi zabi kuma bazan sauya ra'ayi na ba. Cike da kwarin gwiwa na tafi falon Abba ammh duk wanda ya ganni yasan bana cikin natsuwata. Suna tare da Ammi Lokaci duka na duka na gaishesu. Ammi ta kalleni idanuwana sun kumbura tace"lafiya naga idon ki sun tasa..? Cikin Dishewar muryata da yanayina nace"Lafiya kalau Ammi inaga ciwo suke" Sai ta faramin fad'an meyasa ban yi mgana ba da sai aje asibiti Abba na gefe yana jin mu bai ce komai ba. Ni nace ma Ammi idon fa ba sosai ba ne duk Abba na jin mu bai yi mgana ba sai da aka kira wayarsa bai Dauka ba Ammi ta kallesa tana fadin"Ba kiran ka ake yi ba Baban Naana..? Kai tsaye ni ya kallah kafin yace"Engr ne yau ban san adadin sau nawa ya kirani akan Fa'iza ba" Ammi sai ta zaro ido kafin tace"Topha lafiya ba su yi waya da Fa'in ba ne..? Abba yace"Gata nan kiran da nayi mata kenan ya kirani a rude baki ji sa ba, yace tun safe bata daukan wayansa kuma ya tura mata sakonni bata bude ko Daya ba,yanzu ma kiran da kika ga ya yi min nace mai ne ina Office ya bari na koma gida" Ammi mamaki ya kamata ni ko sai sharan kwallah Abba ta kallah kafin tace"To me ya faru.? Ke Fa'i meyasa baki daukan wayansa kada fa ki rikita bawan Allah kinga yana son ki" Sai kawai na Fashe da kuka Abba Da Ammi suka tasani suna kallona cikin mamaki yi nake yi harda shessheka daganan Ammi tasan akwai matsala. Cikin Sausauta Murya tace"Fa'iza bar kukan nan fadamin meke faruwa..? Ko kun samu Sabani ne..? Abba na gefe yaki cewa komai ammh Tabbas ya fahimci wani abu. Fa'iza na son Engr ammh Ishaq ya sakata cikin Tsaka mai wuya. Wayar Abba aka sake kira sai ya Turo wayar gabana yana fadin"Ina jin nauyin Engr Fa'iza ki dauka ku yi mgana kada yaga kamar ina masa yawo da Hankali ne" Kaina na kara shigarwa cikin Hijabi ina kuka Abba bai nuna ya damu da kukana ba,ya cigaba da fad'in"Dauki mana Fa'iza" Sai na dago kaina cikin kuka nace"Abba bazan iya ba. Bazan iya mgana da shi ba" Na fada ina rufe bakina saboda ji nayi zuciyata na wani harbawa saboda yanayin da nake ciki. Ammi ta kalleni a tsorace kafin tace"Wai ban gane ba..? Mgana da Engr ne bazaki iya ba ko mene..? Abba kuma shuru yayi bai yi mgana ba ammh kukan fa'iza ya gama tadamai Hankali Cikin kukan na cigaba da fadin"Abba ka bama Engr Hakuri.." Gabadaya da shi da Ammi suka kafeni da ido shi yana min kallon Tausayi ita kuma Ammi na Rudani da mamaki. Kafin tayi mgana Abba ya rigata da fadin"Hakurin me..? Kai tsaye ina kokuwa da Numfashina nace"Na zabi Ishaq. Zan koma gidansa Saboda ya'yana Abba ka tayani ba ma Engr hakuri wlh ba da son raina ba ne Bansan haka zai faru ba Wlh bansani ba" Na karishe fad'a cikin gunjin kuka Abba yaji jikinsa ya yi sanyi Tausayin Fa'iza da Engr ya gama kassara Sauran kuzarinsa kaunar da Engr ke yi ma Fa'iza daga Allah ne, Ubangijine ya hada wannan soyayyar ba ta mutum ba ce. Ya tuna kalamansa dazu da ya kirasa kan bata amsa wayarsa fad'i yake yi"Baban Nana ina son Fa'iza ina jin ta a raina yadda ban taba jin wata y'a mace ba, ka fad'amata tayi hakuri in Laifi nayi mata ta bari in nazo sai ta Hukuntani ammh ta yi ma Girman Allah kada ta hanani jin muryanta" A yanayin yadda yake mganar zaka Fahimcin yanayin da yake ciki sannan zaka san mganar daga karkashin zuciyarsa suke fitowa. Ammi kuwa mgana ma kasawa tayi baki ta bude kafin tace"Bangane ba..? Baban Nana meke faruwa ne..? Ta fada tana kallon Abba na neman karin bayani. Shi ko Abba ni ya ke kallo na wani Lokaci kafin yace"Kin tabbata..? Bana so ki yanke hukunci cikin gaggawa kina da Sauran Lokaci" Kai Tsaye nace"Ban yi gaggawa ba Abba. Na yanke shawaran zan koma gidan Yaya ishaq" Na fada ina kokarin danne yanayina ammh fa hawaye bai bar idanuwana ba. Ammi fadi take yi"Ke baki da Hankali ne..?Engr din fa..? Ina Abba bai bi ta kanta ba zama ya gyara yana fadin"To Alhamdulillah. Allah yasa hakan shine mafi alheri zan yi mgana da Engr zan basa hakuri goben zaki tafi karofin.?. Ina kokarin Dauke hawayena na daga mai kai sai yace"Allah ya kaimu lafiya tashi kije kin ji ko..?Allah na tare da ke Fa'iza" Jikina na rawa na mike na fice ina Kare Fuskata Saboda kukan daya tasomin,haka na koma Daki na kulle kaina ina ta kuka wayata ma kasheta nayi gabadaya.. Sai bayan fitar Fa'iza Abba ya yi ma Ammi bayani ashar ta zuba kafin tace"Wlh wannan mugunta ce ya za'ayi bai yi mgana da Fa'iza ba sai ya kama yad'a mgana haka ake yi baban Nana..?Saboda yasan Fa'iza kan ya'yanta shiyasa yayi mata haka Engr fa ya zaka yi da shi..? Abba ya lumshe ido kafin ya bude yace"Muna namu ne Allah na nashi kuma na Allah shine Daidai. Komawarta gidan Ishaq ba laifi ba ne Aziza,Duk kyan Sabon gini gwara Tsohon yabe" Ammi ta karkace kai kafin tace"Wlh da Tsohon yaben nan na Ishaq gwara Sabon gini irin na Engr ko baka lura itama Fa'izan na son shi ba..?Fin karfi yayi mata kuma kana gani kai bazaka yi mgana ba" Abba ya girgiza kai kafin yace"Ai zabi na bata kuma ta zaba ni bani da wani abu zan yi mata. Ba Hurumina ba ne" Ammi ranta ya baci tace"Sai kayi shuru yarinya ta cutu Baban Nana..? Wannan ba zalunci ba ne" Abba yace"Komama Uban ya'yan nata ne Zalunci..? Ammi ta mike ranta ya gana baci kafin tace"Eh Saboda bai dace da Fa'iza ba" Fuu kamar iska haka ta bar masa Falon kai tsaye shashen Inno ta wuce su Hafsah na wajenta idanuwanta sun rufe ta shiga karanta ma Inno Abunda ke faruwa sai Inno tayi shuru kafin tace"Kin san shi aure rai garesa Azizatu..Gwara da Usman bai saka baki ba,in har Fa'iza ta amince da komawa gidan Uban ya'yanta shikenan Aziza abu ne mai kyau hakan suna da ya'ya a tsakani,sannan ga zumunci kuma ko Allah ma muna masa laifi ya yafe mana ballatana mu d'an adam..?mganar wannan bawan Allah kuma ai ba nisa yayi ba sai Usman ya bashi Hakuri haka Allah ya tsara kuma mu bamu isa muja da hukuncinsa ba" Sai bakin Ammi ya mutu ganin Inno ma bata goyo bayanta ba ammh tasan wannan komen na zalunci ne,Sai ta yi fushi da Abba ta shige dakinta tana kunci tasan da Baffa na da rai shi kadai ne zai gayama Abba yaji,Ga tafiyar Fa'iza ga abunda ya faru ko siyayyan komai ma bata samu yi ma Fa'izan ba. sai da Safe da ta shigo gaisheta ta bata kudin da Abba yace ta bata ita kuma ta hada mata kayan kwaliya da atamfa da less da Hijabai wadanda bata dinka ba. In ta tuna Fa'iza zata rasa mutun kamar Engr sai taji ma Fa'iza takaici har sai da ta mata mgana da cewa"Ke yanzu gidan wanda baisan Darajan ki ba zaki koma Fa'iza..?kada fa ki yi gaggawa kizo ki yi da kin sani" Sai na fashe mata da kuka shiyasa ta kyaleni tare da Nana khadija da Hafsatu zamu tafi zasu weekend achan Abba na gida bai fita da wuri ba Direban sa zai kai mu har karofi. Naje yi ma Inno Sallama ta rika yimin nasihan hakuri da rayuwa Daga karshe tace"Ki yi hakuri ki kuma barma Allah, Zabin nan da kika yi in sha Allahu Hairan ne" Mganganunta suka d'an sanyayamin rai ammh muna mota na makure kaina a gefe ina kuka Hafsah na gaba Nana khadija na baya sai na sanya Nikab ina ta kuka na ba wanda ya sani wayata ko tana kashe ban kunna ba na so ma Enge ya same ni. Nayi niyyar zuwa nayi ma Raliya sallama,ammh bana cikin yanayi mai Dadi shiyasa ma na sha'afa kwana nayi kuka saboda haka da ciwon kai na tashi da shi kuma na isa Karofi. Muna mota amai na dinga yi ni da bana amai a mota ammh Ranar nayi duk na bata jikina,Lagai lagai muka isa gidan Goggo sai ga shi nice kwance da Daddare har da karin ruwa Ulcer ta tashi sai jini da yayi sama Abba nata Fad'an nasan ban ji dadi na shirya Tafiya, ita kuma Ammi ta ce Wlh bana son komawa gidan baban su Amir ne, in aka kyaaleni zan cutar da kaina. Abba kuma yaki biye ma mganarta Domin ya kira Engr tun a daran jiya ya ba shi hakuri tare da yi mishi bayanin Halin da ake ciki ya yi shuru na wani Lokaci kafin yace"Ita Faa'izan ta ce ta zabi komawa gidan Uban ya'yanta..? Abba kunya da nauyi dakyar ya amsa masa sai yayi mirmishi kafin yace"Shikenan hakan nada kyau. Allah yasa hakan shine mafi alheri na so ni na sameta domin na cike mata wani gurbin da ta rasa, ammh ko a yanzu bazan cire rai ba sannan bazan mata bakinciki ba,ina yi mata fatan alheri Allah ya sa tayi farinciki fiye da in ni ta aura." Sai Abba yaji ya kara jin girma da wani Darajan Engr ya karu acikin Idanuwansa,abun mamaki kuma sai suka cigaba da mganar aikin su ko alama bai nuna masa wani Damuwa ba duk da yasan tabbas akwai damuwan. Shi kan shi abun ya kamasa ammh kuma Fa'iza yake so ta yi ma kanta da Rayuwarta zabi shiyasa bai shiga mganar ba kuma a ranar da Fa'iza ta koma karofi ya kira Ishaq yace sati mai zuwa za'a maida auran sa da Fa'iza ranar asabar kenan in an yi walima jumma'a asabar daurin aure. Ishaq farinciki kamar an yi masa Bushara da gidan aljannah,Haka ya Dawo gida