← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 175

Sashe 30

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dauke da Ahmad inaga Hannun Badariya ya karbesa. Fuskarsa a gintse ganin Ya mariya Ita bata ma san yanayi ba Anty Mahma ce ke mai mgana ya fita ganin ina Sallah ba jimawa ya sake dawowa lokacin na Idar ina zaune ina azkar Tun zuwan su bai neme ni ba sai yanzu na zata ma Ahmad ke rigima ashe wai Girki zan yi amaryansa tace Faten dankalina kadai zata iya ci.,batare da nuna Damuwa ba na amsa masa ya fice Ya mariya ta hade rai ganin ina Ninke Hijabin da nayi salla a harzuke tace"Au ke ce ma baiwar Amaryan tasa kenan..? Nayi shuru na kasa mgana Anty Mahma tace"Tunda umarnin mijinta ne ki barta taje tayi..Tashi kije Fa'iza" Da Sauri na kama Hanya zan fice sai Naji Hafsah na fadin"Tab to ai ko achan gidan in yazo da ita..Itace komai nasu abincin su har da gyaran makwancin su" Ya mariya ta gwalalo ido ni kuma sai na kasa fita na juya ina Harran Hafsah Saboda na jita ina kusa da ita Sanda ta fadi mganar..Anty mahma tace"Kin so ne Fa'iza gaskiya wannan karon ban goyi bayan ki ba..Har da gyaran inda kishiya ta kwanta da Mijina kayyasa.." Ko da yake naga bakaramin so Ishaq ke mata ba..Ciki gareta naji Anty Binta na fadin shike wahalar da ita mama ai naji da wannan jikan nata Tun kafin ya Fito duniya.." Ciki..!na nanata acikin raina kafin na girgiza kaina kawai na Fice Daga Dakin ina ji Ya mariya ta fara bala"i ban tsaya jinta ba Domin bazasu taba Sauya ma Tuwo suna ba har Abada yana nan a tuwonsa.. Adaran nan na tike nayi Faten Dankalin Turawa da Hanta,na kuma kai mata da kaina har Bedroom din Hajiyar Dala da ire iren mu bamu da Ikon shigansa. Ita da kanwarta ne Zuzu,Na ganta duk tayi wani irin fari kamar zabiya tana kwance,Na gaisheta ta amsa tana Dagamin hannu ina ji suna mgana da kanwarta da wani yare shi dai ba Turanci ba kila bayanina take mata naga ta juyo tana min wani kallo ni dai na Fice ban kara kallon inda suke ba. To bikin ma bai musu dadi ba washegari ya kwasheta suka koma Mama ke yawon fadin Laulayi ne ya sakata gaba mai wahalarwa yace ma ta bar zuwa bikin tace sai tazo Hajiyar Dala kanta ya kara fashewa ballatana da ta kawo kudi masu nauyi ta bata gummuwar Bikin ni duk sai Daga baya nake jin ma sun tafi ban ci Daraja ko arzikin ko sallama ya yi dani ba. yaya Asiya bata mgana,yaya mariya ne bata iya shuru,Goggo kuma ke Tausanta to ba'a ma yi rabuwar arziki da Goggo karofi da Hajiyar Dala ba Ranar Litini suka koma karofi rayuka ba Dadi,Ba'a san me yahad'asu ba sun dai yi Hayaniya,Mu kuma sai ranar Talata muka koma katsina tsinke na abun Biki ba wanda ya bani ni kuma ban saka rai ba ammh su Mama sun yi guzarin Kayan fulawa da kalanda da jakunkunan rabo kaya dai niki niko ni ko Cincin kad'ai Ya Asiya ta bani na Riko ma su Amir.' *ASSALAMU ALAIKUM* *KAYA SUN SAKE SAUKA*. *INGANTATTUN SAIWOWI DA SASSAKE NE DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZA DA SU*. *ABIN BIRGEWA BA SAU DAYA AKE AMFANI DA SHI BA*. *KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR KO KUWA KE DA KANKI ZAKI YI GYARA?* *INA SAKE YIN ALBISHIR DIN GARIN DAKA MAI KYAU DAN CHADI, SHA DA MADARA KO NONO DA KUMA TSUMIN GAMGAM*. *GADALIN MATA AKWAI*. *INA DA TABBACIN INGANCINSU*. *SANNAN WACCE TAKE SON A DAFA MATA KAZAR, ZA'A DAFA*. *TUARAREN WUTA NA ASALIN CHADI AKWIA SU AVAILABLE, SAI KIN GWADA ZAKI BADA LABARINSU* *TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU DOMIN KARIN BAYANI* *08032773332*. *NATION WIDE DELIVERY*. *SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE* *Janafty**KANA NAKA..!* *Wattpad:JamilaUmar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT 08066726866 Ni MMN MUJAHID Ina da kayn gyara kala kala na kasa da sama Ina Saida supplement da kayan mata kala kala cikin sauki Mai kama da kyauta Hjy ta ki ajiye kunya kifitu kiyi bayani matsala ki abaki ABINDA yaddace Dake Ina matan da ke FAMA da bushewa gaba Ina maccen da take a bushe kamas ba niima miji sai yasa yawun sa ku BASILIN Ina matar da kishiya ta tayi mata zarra ga miji ke rasa Ina matsala take Ina wadda mijinta kamar kurma baya nuna ya gamsu Dake Dan ku ayi ku abari duk dai suke dashi Shin ke ku y'ar kuwa ga mijin ki baya Yi da sanbatu in kinji ana Fadi sai kece karya ce Nazo muku da hadin Zuma wadda duk zata magance way'anga matsalolin cikin ikon Allah wanna Zuma ta samu yabo ga duban mutane Sha yanzu magani yanzu ce Banda haufi akanta wanna Zuma tana ta yadda sha'awa Kai tsaye ruba babba 2500 karama 700 MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT MUNA SAKWATO DA KEBBI INA AIKAWA KU INA 08066726866 IN BAKI SHIRYA BA KIBARI HAR KI TASHI SAYE Ta gidan Anty Binta batagwarawa muka fara sauka saboda yara nan muka yi sallar mangariba da isha'i sannan nayi shirin tafiya ganin Mama bata da niyyar tafiya, ni kuma Saboda Dare sannan ga yara,Ganina cikin shirin tafiyasa yasa Mama tace na tsaya su Amir su ci abinci,kamar abun arziki na zauna suka ci abinci nima Halisa ta zubomin naci kad'an na kora da ruwa shuru shuru Mama taga na zauna ban tafi ba tagaji dai tamin mgana sai na fad'amata bani da kudi a hannuna ballatana mu yi na adaidaita zuwa gida. Shikenan Mama ta fara fad'a ta inda take shiga bata nan take fita ba, ta kalleni tana fad'in"Ke kan Fa'iza ban ga amfanin ki ba..Tun da Ishaq ya aure ki bai Huta da wahalhalun ki ba..da an tabaki sai kice baki da ko asi ke ko irin Dubaran matan wannan zamanin baki iya ba? sai dai komai ki kwanta miji yayi miki tunda ya zama bawan ki" Anty Binta na gefe ta karb'e da Fadi'n"Kuma Mama komai ne sai ka zauna miji ya baka..?,tsakani ga Allah yana ma kokari wlh,ammh duk da haka ba'a gani barin ma Yan'uwanta da Goggon Karofi,su yi ta korafi kuma in za'a duba tafi duka yan'uwanta jin Dadi ita Asiya ai malamin makaranta take aure ga abokiyar zama ita kuma Mariya d'an kasuwa ne mai karamin karfi ba wacce takai jin dad'in da Fa'iza take yi acikin su ammh kullum gani suke tana cikin Wahala'" Mama ta ja tsaki kafin tace"To ai duk laifinta ne ita ke fad'a musu haka..Shiyasa nace miki Har ga Allah ban so hada zuru'a da Dangin Asiya da Sidi ba, domin nasan ba Dangin Alheri ba ne na tsiya ne kawai" Ni dai ina zaune kaina a kasa na kanzil ban ce ba sai da suka gama cin zarafina sannan Mama ta zage jaka ta Dauko Dari biyar ta wurgomin tace sai na tashi na bar gabanta bata son ta kara ganina. Jiki ba Karfi na mike nayi musu sallama yaran suna D'akin Halisa na Bisu na taho da su ko Tausayi na Mama bata ji ba ga goyon Ahmad ga Amir ga Anum ga Musty kuma na Tabbata Direban gidan zai kai Mama gida ni kuma Saboda k'iyayya bazata iya had'a Hanya dani ba. Haka na fita ina Tare tare da su Allah ya taimake mu kafin mu isa Titi muka samu abun hawa zuwa gida. Tunda daman dukkan mu a koshe muke sai shirin kwanciya kawai nayi musu,Tundaga Lokacin kuma Rayuwar mu ta cigaba da gudana yadda take tun farko ba chanji. Ya Ishaq ko Labarin sa bana ji Wayar ma tawa ta Lalace inaga yara ne suka Y'ar min ita a kasa ta bare biyu da na Had'a kuma nayi nayi ta kawo bata kawo ba sai na Hakura na tattara ta na ijiye ba mai nema na ni kuma ina gida Dagani sai ya'yana tun had'uwar mu da shi a kano sai da ya shafe wata biyu sannan yazo ya ganmu shima kwana d'aya yayi ya koma ko da daman ya Dawo komai na Cefanan mu ya kare daran ranar ma da yunwa yaran suka kwanta da Rana na samu nayi musu danwake da sauran garin Danwaken daya rage Shima jikinsa yayi sanyi daya ga ko kwaran abinci bamu dashi ya kira Mama yana mata mgana ga dukkan alamu komai na mu yanzu ya koma wuyar Mama ne. Ya bani dubu biyar a hannu sannan ya Biya Haruna kudin watansa biyu ya tafi bayan ya fad'amin zai Dad'e bai zo ba zainab bata da lafiya Laulayi na Matsa mata shi ne ke kula da ita ban damu ba nayi mata fatan Allah yasa a rabu lafiya domin ni yanzu duniya baya gabana ballatana na Damu da abunda ke faruwa acikinsa ni dai kawai ya'yana sune nake ji sannan kuma zaman su nake yi,kuma Allah ne gata na garesa nake kai duka kukanaa.. Tun bayan da ya tafi ko gidan Mama da nake zuwa na Dauke kafata saboda sai in ina da kud'in zan je,kuma koma naje ba tarban arziki nake samu ba Shiyasa na kame kaina agefe Badariya ne ke d'an lekomu Lokaci bayan Lokaci sai Jamal in yazo gida Huta yakan zo Tunda suna yawan zuwa anguwan mu buga Kwallo. Mama da Anty Binta kuwa Daman indai ka gansu to tabbas ba alheri ba ne ya kawo su. Bangaran Karofi ma shuru ba wani Labari Hafsatun ma da kan lekoni kwana biyu ban jita ba tun rabuwar mu da ita a kano bana jin kowa nima bamai jina,Dani da yarana muka kulla kawance da juna in sun Dawo makaranta suna tare dani sai in barci yazo sun ma daina Damuwa da Zencem Daada Anum ce daman mai Rigima sai Mutsy to yanzu sun gaji sun Daina yawan damuna da Tambayansa sai nima hakan ya fiyemin saboda wani lokacin na kan rasa amsar da zan basu. Ahmad na da shekara Biyu,na fara Tunanin ciresa a nono na yayesa ammh bani da komai da zan rika basa Tuni daman acikin Cefanan mu aka daina kawo mana kayan Tea,kuma ba ni da wani garin kuni ballatana na rika Damawa sai na kasa ciresa a nono Saboda kada ya wahala ni kaina bani da Lafiya duk na kara ramewa sannan ina Faman da yawan ciwon kai da
Chapter 30 · 0% Book details