Sashe 2
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Center Table din dake falon na Sauke Farantin Hannuna kafin na karisa D'aya daga cikin Bedroom din Dake bangaran inda na san Ishaq din yana ciki. Da sallama na Tura kofar na shiga yana Tsaye gaban madubi ya gama saka kayan barcinsa masu Taushi Farare,riga da wando,waya ce a Hannunsa yana mgana cikin Sanyi da Tattausawa. Ganin haka yasa Fa'iza ta juya zata fita har ta kai jikin kofa Hannunta kan marikin kofar ba zato taji muryansa Cikin Kaushinsa akoda yaushe ya Kirata. "FA'IZA.." dayake da karfi yayi mganar na jisa Da Sauri nq juyo inaa gyara wuyar riga ta kallon da yake min ne ya sanyaya min Jiki D'aya sa na kariso gabansa Jikina na rawa ko kafin nq samu Zarafin mgana ya D'aga min hannu Cikin Fushi yana Fadin"Je ki ma kawai domin ganin ki karin Takaici ne a wajena.." Yafada kai tsaye Lokaci D'aya yana kauda kai Dauke da matsanancin Takaicin daya Dade yana cinsa tun shekaru Takwas da suka gabata. Duk da ba duka tna jisa ba nasan ransa ya baci sai na Durkusa kan gwiwiyoyina Cikin yanayina nace"Ka..kayi hakuri.." Kamar na watsa ma Fushinsa Fetir haka ya taso min yana Fadin"An ki ayi Hakurin..? Nace bazan hakuran ba..? Aikin banza ni zaki raina haka Fa'iza..?In shigo gidan nan tund'azu kiyi banza Dani kamar wani kashi sannan kin ga Dama kin shigo bangarena kuma kin gan ina waya ki Tsaya in gama ki gaisheni ne ki ke ke jin asara ko..? Har da juyawa ko kunya zaki Fice ga Dan iska ko..? To tashi ki Ficemin Daga Daki bana son ganinki..Domin ganinki ba komai Cikin sa sai karin Takaici da bakinciki..wlh har gobe bazan Daina cewa Hajiyar Karofi da Baba sun cutar dani ba..Cuta ta har Abada da suka Hada aure na Dake FA'IZA.." Ya karishe Fad'a yana nuna min babban yatsansa Lokaci Da'ya da wani banzan kallo dayake bina dashi kaina na kasa ko motsin kirkin na kasa yi daga inda nake durkushe Domin indai ana Sabo da Tozarci da Mganangun Cin mutimci to ni na gama Sabo indai Daga bangaran Yaya Ishaq ne. Baya ya juya min yana Faman kokuwa da bacin ransa yana jina Cikin yanayin mganata ina kara Fadin. "Kaayi hakuri don Allah..Ban ji shigowarka bane ina chan ina ma su Anum shirin barci sai yanzu Hafsatu ke shaidamin dawowarka..! Sannu da zuwa.." Kyaci yayi kamar wani maciji shifa ba Domin Ya Binta ta Kira sa akan yazo yaga kayan lefensa da ya bata kwangilar hadawa ba,da babu abunda zai kawosa katsina cikin wannan Satin ballatana har yazo ya shaki wannan Bakinciki. Juyowa yayi yana kallona Lokaci d'aya kawai ya tsaya yana kara kare ma Fa'iza kallo akasan ransa yana kara Tambayan kansa da gaske FA'IZA matar sace? Fuskarta ya kara kalla yana jin Shima Tunda yake bai taba ganin mai baki,bakin Fuska irin Fa'iza ba, zai iya Rantsuwa ga Allah kaf ajikinta banda Hakoranta ba inda yake da Haske bakace ta kwantance irin bakin nan mai Duhu da Dususu,Sannan mummuna ce bata da kyau a ganinsa sannan bata da Tsaho wanda Hausawa suke cewa mai cike Girman kyan y'a mace Gajera ce,da Fadin Fuskarta kamar Fanteka,Da guntun Hancinta da bakinta mai Fadi shima,Abu daya ne zai ce mai kyau a wajen Fa'iza shine tana da Kirar mata Wannan kam masha Allah Dirarriyace Kirjinta da kugunta suna cike da Fasali ya mace ko ayanzu Data Haifi ya'ya Hudu bata Sauya ba Ta na nan da Jikinta mai Fasali daidai misali bata da kiba sai dai Haihuwa ta d'an Budata. Sai kuma bangaran Ni'imar jikinta ta wannan bangaran bai da ta cewa ya san Fa'iza fiye da yadda ya san kanshi Fa'iza bata shan kayan mata ko wani abun da zai kara mata Ni'ima duk abunda yaji in yazo tarayya da ita shine Hallitarta wanda Ubangiji ya yi mata,bazai kusheta ta wannan bangaran ba,abu daya ne ke masa cikas baya sonta sannan tun farko komai nata a wajensa bamai kyau ba ne shiyasa ta wannan bangaran ya gaza sakin jikinsa to ya saki jiki a wajen Fa'iza yaji me..?Matar da bata iya komai ba,Shiyasa ba kasafai ya cika Raba'arta ba. Kayan jikinta ya kara bi da kallo,sai da Ransa ya baci har gobe yana jin Mamakin yadda Fa'iza bata taba saka kayan da yayi mata Daidai ba ko Rigar da hannu yayi yawa ko Sikat kagansa kamar Buhu in yayi mata mgana sai tace itake son haka kada watarana su mata Kad'an,Yau ma din riga da Zani ne ajikinta Rigar Hannun dai bai zama ya na yi ya na Sabule mata Jan Bra dinta Data sanya tana bayyana Saman kafad'anta. Wani mololoon abu ya tsaya mai yaki wucewa a makogwaronsa Saboda Bakinciki kamar shi ISHAQ KABIR KAROFI kamar shi Ace wannan abar ce Matarsa Uwar ya'yansa..? In ya kalli FA'IZA sai yaji Fiye da madaukacin Takaicin daya ke ji in ya tuna itace yau MATAR SA..Fa"iza ba mafarkin sa bace a irin Rayuwar ISHAQ KABIR KARAFI..Sam Fa'iza bata dace ko kadan da Tsarin Rayuwarsa ba kowa yasan Ishaq dan gayu ne mai ilimi ne,kyakyawa ne dan Fafane d'an Alfahari ne Duniya tasan da zamansa mai Burin Auran mace FARA mai kyau mai Tarin kwalayen matakan karatun Zamani SAI DAI KASH" Hakan bai samu ba..Sakamakon kutse da Fa'iza tayi cikin Rayuwarsa ta Ruguza Mafarkinsa har Abada bazai daina Hango FA'IZA a matsayin Nakasun Mafarkinsa ba. Sannan karin bakin cikinsa yana da Burin kullum in ya Dawo aiki kyakyawan matarsa ta tarbesa ita da yan Gudi gudin ya'yansu Farare masu kyau kamar ya'yan Turaawa tun yana yaronsa yasha yin wannan mafarkin sai dai ina Hajiyar Karofi da Baba sun Saka almakashi sun Datse wannan Mafarkin nashi,Gabadaya ya'yan da suka Haifa da Fa'iza Shekara Takwas da auransu duka ita suka Biyo acikin su ba wanda ya Dauko ko da Hasken Fatansa ne sai Baki irin na uwarsu,Yana Tsananin kaunar yaransa ammh wani Lokacin yana kunyar nuna su ga Duniya Saboda a yanayin Tsarin Rayuwarsa bai kamata Tsarin Iyalansa su zama haka ba. Duk da irin barnan kudin dayake yi a kansu Fa'iza bata da wannan Tattalin komai sai ta barshi su lalata shiyasa ya gaji ya barta ta karaci muguntarta sai dai yaci ta ita kadai. Gefen gadon Dake Dakin nasa ya koma ya zauna yana Kad'a Fararan kafafunsa masu cike da gargasa yana kara kallon Fa'iza Dake duke har Lokacin kanta na kasa kamar tamai Sujjada,Kai ya girgiza yana Tunanin yadda yaso ya Dakile ma Fa'iza Haihuwa sai dai ina kana naka ne Allah na nashi,Kowani Tsarin iyali bai karbeta ba,da an saka mata lokaci kadan' sai ya bata matsala na karshe ma da aka saka mata yar Ashanan da jini ya Tsinke mata Dakyar ta sha Ashe Rabon Ahmad ne,Haihuwa take yi akai akai ita ko gajiya batayi da Hidiman yara da Haihuwa kamar akuya..? Tsakani ga Allah ya'ya indai ta Bangaran Fa'iza ne shifa ya kai makuran Hakura da hakan. Shi kadai kawai ya saki Tsaki"Mtsewww.." Kallonta ya sake yi kai Tsaye kafin yace"Where is my Childreen.? Yafada da dan karfi ta Dago tana Kallonsa Kafin tace"Eh me kace..? Wani Tsakin yaja Kafin yace"Na manta ba Turanci..Ina yarana na nace..? Mutum yayi ta wage baki yana mgana har sai makota sun gama jinsa ke ko Sirri ne bamai yi Dake domin kafin ki gama gane abunda mutum ke nufi Duniya ta gama jin Halin Dayake ciki..Mtswwwsss.." Yana gama Fadin haka ya mike ya Tsallaketa ya fice Daga Dakin,Kaina na kasa na saka hannuna na share guntun Hawayena kafin na mike Salau Salau nabi bayansa saman D'aya Daga Cikin kujerun falon na samesa ya kunna kallo remot a Hannunsa yana Sarrafawa. Jikina na rawa na karisa inda na ijiye Farantin dana shigo dashi na Tsiyaya mai ruwa mai sanyi nataso nazo gabansa na Duka ina Fadin"Kayi hakuri..Ga ruwa kasha.." Sai da ya ga Dama sannan ya kalleni kafin ya amshi ruwan kadan yasha ya maida mata yana Fadin"Da ruwa kadai kika iya tarban mijin ki da yayi kwana Goma baya nan..? Ya fada yana mai Tsurata mata ido Fa"iza bata ji farkon mganarsa ba sai karshe yasa tace"Kwana goma..? Tafada Cikin alamun Tambaya kai kawai ya Dafe kafin yace"Innalillahi..Gaskiya an gama Dani..Ishaq ka gama aiki kawai.." Yafada kamar yayi kuka kafin ya kalleta yana Fadin"Ahmad yayi barci ne..? Tana kallonsa ya kara ware murya yana Fadin"Eh nace Ahmad yayi barci ne..? Da Sauri tace"Dukaa sun yi barci.." Kai ya girgiza kafin yace"Ruwa k'adai ne kuke dashi agidan..? Yafada muryansa asama kusan fa Fa'iza ta fara maida shi Sama sama ko ba da ita yake mgana ba ya yi mugun Sabon da sai ya Daga murya. Cikin Ladabina nace"Taliya Hafsatu ta Dafa ma su Amir ina jin ta kare ma..Sai dai bari da sauri nayi maka ko Faten Dankali ne.. Dayake bansan kana Hanya ba." Komawa yayi ya jingina jikin kujeran dayake kai yana maida Hankalinsa kan Tashar Mbc action din Daya sanya Reastling din da ake yi ya Fara Daukan Hankalinsa ganin haka yasa na Mike jikina na rawa na kwashi Farantin Dana shigo dashi na Fice ya Bita da kallo kamar ya saka kuka ai bazai ce A'a ba inda kuma bazai Zagi Fa'iza ba kenan ta iya girki,girkinta ba inda baza'a Kaisa ba,Shi kadai ne abu mai kyau a rayuwar Fa'iza ban dashi shi dai bai gani ba ya Dade yana ganin mutane marasa sa'a a rayuwarsa ammh Rashin Sa'ar Fa'iza na musamman ne ta rasa wasu abubuwa masu Muhimmanci a Rayuwarta Rashin Sa'arta ne ma ya shafesa shima Gabadaya Rayuwarsa na neman komawa irin tata ba Domin Mama na Tsaye kansa ba, da Shima ya koma Dangin KURAME kamar yadda Zama da Kaddara ya Hadasa da Fa'iza. Minti Talatin da wani abu na Sake Dawowa Dauke da Voul cike da Faten Dankali da Hanta sai maltina mai Sanyi Dana Hado mai dashi bai yi Tsaya mgana ba Domin yunwa yake ji Gidan Mama Tuwo sukayi shi kuma na Cimarsa bane abaya dai yaci banda yanzu Dayake cin guminsa. Kasa ya Sauko ya tankwashe kafa ya sha Fantansa sosai,ya Dora da ruwa Maltina,Yayi gyatsa Lokaci D'aya da Hamdala Duk Fa'iza na gefensa yana Gamawa Jikina har rawa yake yi wajen kwashe kayan daya yayi amfani da su, na maida Kitchen adaran nan