Sashe 95
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sauri ake yi Fa'iza" Jikina na rawa na ruga daki na Dauko Hijabi na fito ina fad'in"Mama su Amir" Da mamakina sai kawai tace"kuje ko taliya zan dafa musu,tunda akwai komai kafin ki dawo" Sai kawai nabi bayan Yaya isa da gudu daya riga ya fice gabana na fad'i jikina na rawa a raina nace kodai Goggo ce..?da sauri nace"Aa ba haka ba ne" A mota na same shi na bud'e gidan gaba na zauna cikin Sauri yace"na kira hafsa tana makaranta zamu biyu mu dauketa" Sai kawai na Sadakar Mun rasa goggo,kawai sai ji yayi na fashe da kuka cikin kukan nake fadin"Allah Sarki Goggo" Tsawa ya dakamin yana fadin"Wayace miki wani abu ya samu Goggon.? Cikin hawaye nace"To me zai saka kazo da gaggawa ka daukemu zuwa karofi..? Hankalinsa na wajen tuki yace"To ba mutuwa ba ne abun farinciki ne, Dan'uwan mahaifiyarku ce ya bayyana, shi da mahaifiyarsa yau a karofi" Na ji dai kalmar dan'uwan mahaifiyarku a kunnena sai na Dafe kirji ina fadin"Ta madina..? Kai ya gyad'amin yana fadin"Shifa..Sauri suke yi shiyasa Goggo ta tasoni daga gun aiki tace na dauko ki keda Hafsah" Daganan ban kara bi ta kansa ba farinciki da wani irin zumud'i ya sarkeni hannuwana na da'ga sama ina fadin"Alhamdulillah..Allah abun godiya" Har muka isa makarantan su Hafsah bakina yaki rufuwa a waya ya kirata ta fito a gaggauce itama kamar ni duk ta Rud'e sai da yayi mata bayanin da yayi min sannan itama ta rud'e da Murna tana fad'in"Yaya Isa ya ka gansa? yana kama da Tamadina..? Mirmishi yayi yana fadin"Tsammanin abunda baku yi tsammanin ba. muje dai zaku gansa labari bazai gamsheku ba." *Janafty* [7/17, 7:32 PM] +234 703 465 7829: *KNKB2012* *Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.* *09069067488* Har muka isa karofi ban sani ba, na lula cikin wani irin farinciki da zakwad'i abun da ka dade kana hasashensa bai faru da wuri ba sai yanzu. Wani irin farinciki ne ace yau ga wani naka daka jima kana jin labarinsa baka taba ganinsa ba, kafin isar mu gidan Goggo a cikin zuciyata na wasaafa yadda zan ga Dan'uwan Tamadina bansan iyaka ba nadai san bakina yaki zama waje d'aya na kasa natsuwa har Hafsah tafini mallakan kanta. Tunda Muka iso kofar gidan Goggo sai kuma jikina yayi sanyi maimakon na zama ta farkon shiga gidan sai na kasance ni ce ta karshe na koma na rab'e bayan Hafsah kamar wacce tayi karya, gabad'aya sai naji gabbaina sun saki na fara tunanin wani irin tarba ko maraba zai yi damu alhalin bai taba ganin mu ba? sannan meyasa ya kai wad'anan shekarun batare da ya waiwayemu ba?har sai da Allah ya Dauki ran Tamadina basu gana ba? Ya ya zamu gansa..?mu ma ya ya zai gan mu..?yadda ya zata ko ba yadda yayi tsammani ba? Duk wad'anan tunanin suka taimaka wajen da dakushe murnanta a fili har Yaya Isa yayi sallama kofar falon Goggo Ya shige Hafsah tabi bayansa nice karshen shiga falon, sannan sallamata ma a saman bakina ta makale idanuwana suka fara wurgawa cikin falon ina neman bakon fuska naga Goggo da megidanta,Sai Baba Ati da wasu Tsofaffi maza daga gidan su Tamadina ne,Sai wata Dattijuwa mai natsuwa da Haiba zaune kan kujera cikin shigar alfarma kallo d'aya zaka yi mata kasan ta samu dukkan gatan duniyan da suka Boye shekarunta. Gefenta a kasa wajen kafafunta wani kamilin megidanci ne baki sai dai bakinsa ya hade da hutu da jin dad'i da Fatarsa ta sauya,yana Sanye da Shadda Mai ruwan kasa har da babban Riga tana maiko kansa da Hula zanna na mutanen maiduguri,yana duke ne ammh ina iya ganin yadda yake saka karamin farin kyale yana Tsane ruwan Hawayensa,Yaya mariya na gabansa itama a duke kamar kukan take yi, Dattijuwan nan ta rike mata hannu alamun lallashi. Daga sama naji murya Goggo tana fadin"Alhamdulillah ga Fa'iza nan da Hafsatu nan sun iso.." Kamar an zabure sa haka ya mike cikin Haibarsa da muryansa da ta dakeni yace"Ku matso nan ya'ya na ku matso naji dumin ku..Ku zo ga Abban ku" Yake fad'a cikin nuna tsananin murnansa sai alokacin na kara kallonsa ba shakka jini ba karya ba ne ina ganin kama ta jini Tsakaninsa da Tamadina Hafsat ne ta nufesa zata duka ta gaishesa sai kawai ya Rumgumeta,hawayensa na zuba ni kuma ya miko min hannu sai na sulale kasa a gabansa idanuwana sun ciko da kwalla,Dattijuwan nan ta kallemu ta kara kallon mu musamman ma ni sai kawai ta fashe da kuka tana fadin"Allahu akbar daga ganin wannan na shaida jinin Lauratu ne" Sai kawai ta rikice tana rusa kuka Goggo ta matso tana fadin"Haba Hajiya zuwaira ashe kukan naki bazai isa hakan nan ba..?. Cikin kukan take fadin"Dole nayi kuka, Dole na koka na yi sanadiyar da na yanke ganawa Tsakanin yan'uwan juna.?kaico na.." Tafad'a cikin wani yanayi da sauri ya tareta da fadin"Inno ni ne kika yi ma wannan laifin kuma nace na yafe miki ba shikenan ba..? Ni dai naji ciwon rashin ganawa da yar'uwata guda d'aya da nake da shi,Ammh nayi murna daya kasance ta barmun zuru'an da bazan jima ina kuka ba, in na kallesa zan tuna yar'uwata ta bar min su ne domin kada in na zo nayi kukan rashinta" Gabad'aya kalamansa sai suka sakani rauni bansan Lokacin da na fashe da kuka ba ganin haka yasa sai Hafsah ta d'auka Yaya mariya ma daman mun sameta tana kukan ta ne.Wacce aka kira da Inno ta sauko kasa tana neman Durkusa mana cikin kuka tace"Ku yi hakuri ku yafe min ya'yan nan na zalunce ku na yanke ganawa tsakanin mahaifyarku da dan'uwanta" Da Sauri ya saki Hafsa bayan ya zaunar da ita ya karisa gareta ya rikota ya maida ta saman kujera yana fadin"Inno ki daina wannan kukan don girman Allah" Sai ta ji mganarsa ta koma tayi shuru tana sharan kwallah kasa ya zauna a gabanta yana kallonmu d'aya bayan d'aya kamar yadda muke kallonsa. Lokaci da'ya yana Dauke Hawayensa da Farin hanky din dake hannunsa. Cikin Kayattaciyar Muryansa ya dago yana kallon su Goggo kafin yace"Cikin su wacece tafi kama da yar'uwata..? Har Baba ati da goggo suna had'a bakin wajen fad'in"Gata nan a gabanka Fa'iza kamar Tamadina ta tsaga kara yadda ka ganta haka mahaifiyarta take. sai dai ita bambamcin Tamadina bebiya ce ita kuma Fa'iza jinta ne yake da rauni" Kawai sai ya kuramin ido Lokaci d'aya yana fadin"Naji dadi da akwai fuskar da zan rika ganin yar'uwata a ciki, baku da Hoton yar'uwata ku nuna min ya'yana..?. Ni dai na kasa mgana Hafsah ce tayi karfin Halin cewa"Yaya Asiya na da shi a wajenta"da alamun karin bayani ya ke kallon mu Yaya mariya ta jinjina kai tana fadin"Itace babbarmu wacce su Goggo suka ce tana kano tana aure" Sai ya jinjina kai yana fad'in"Rashin sani ne ai kano gida ce a wajena chan na girma nayi karatuna kuma chan nayi aure,kafin chanjin aiki ya Dawo dani nan kaduna,yanzu komai ya kare tunda Allah yasa nazo kuma na ganku nayi alkwarin bazan kara sakacin da zaku rasani ba" Sai ya fara sharan kwallah ya cigaba da fadin"Yau yau din nan Inno ta fad'amin ina da yar'uwa bayan ta sanar dani inda dangin Babana suke,a gaggauce na taho ko iyalaina ban zo da su ba suna kano ana auran kanin Mai dakina,yaran duka suna chan,ni kaina Tafiya gareni zuwa porthercourt gobe akwai Taron da muke dashi daga wajen aikin mu aka turamu,ammh nace bazan zauna ba sai nazo na ga ahalina ina zuwa kuma sai na samu labarin dangi duk sun kare itama yar'uwan nawa Allah ya yanke ganawa tsakanin mu da ita" Inno na sharan kwallah tace"Allah ya jikan Hafsatu ina kallon fuskarta ranar da zan bar garin Lokacin bata wuce shekara Biyar ba" Aka amsa da Ameen Ameen mu dai sai kuka muke yi muna sharban hawaye Shi ma kukan yake tayamu ammh nasa bamai sauti ba ne,yana dai yi yana tsane hawayensa,da farin Hanky din dake Hannunsa.. Baba ati ta gyara zama tana fadin"Zuwaira wani dalili ne yasa tunda kika tafi baki kara waiwayomu ba sai yau.?Sannan wannan yaron baki taba sanar da shi komai game da mahaifinsa da Danginsa ba..? Inno ta fara kuka kasa kasa tana fadin"Ba laifin Usman duka acikin abun da ya faru kada ku manta na bar garin nan yana da kananun shekarun da bazai iya tuna komai ba! Duka abunda ya faru laifina ne shiyasa nace ku yafemin" Hannayenta ya rike cikin Lallashi yana fadin"Inno ashe kukan nan ban ce ya isa haka ba..? Da jajayen idanuwanta tace" USMAN rashin kuka na ba zai sa laifina yaki bayyana ba,da gaske na zalunceka na tafi dakai na raba ka da Dangin mahaifinka gashi karshen karshen sai da na kawo ka gare su" Sai ya kasa mgana Saboda bata kiran sunansa sai dai tace mai BABAN Nana kamar yadda matarsa ke kiransa. Gyara zama tayi tana kara gyara zaman mayafin dake kanta tace"Bani da wani kwakwaran Dalilin aikata abunda na aikata Sai dai nace rashin son da ban yi ma mahaifin Usman ba aka aura min shi,alokacin ina da wanda nake so ammh Mahaifina yayi min Dole,ya aura min shi aka kawo ni wannan garin kada ku manta tun Lokacin da aka kawo ni,ban yi zaman Dad'i da kowa hatta da kakarku da ta haifi mahaifiyarku Lauratu,Sannan ban saki jiki da kowa ba,bani da aiki sai kuka sai zama cikin Damuwa Ko Usman Rabo ne ya rantse tsakanina da mahaifinsa aka same shi,ko da zama ya kare tsakanimu da shi bayan rasuwarsu zuciyata bata Rusuna ba. gani nake yi in na barsa a wajen ku bazaku barsa ya zauna dani ba, shiyasa tunda kuka amince na tafi da shi a raina nakudiri niyyar zan Nisanta shi da abunda ya shafi wannan nahiyar,Tsakaninsa da mahaifiyarku bai fi shekaru uku ba yana gabanta domin neman irin haihuwan yakai mallam ga aurena sai bayan na haifi Usman sannan Lauratu ta Haifi Hafsatu tabbas nasan an haifeta da laluran rashin ji da mgana,Sai dai bamu zauna da lauratu ba,Duk da mun yi zaman kishi na mutanen na wanchan lokacin,Ni ba kishi nayi da ita ba, ni tsanar duk abunda ya shafi mallan nayi shiyasa itama ban yi mu'amala mai kyau