Sashe 20
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ganin ban taimake ki ba meyasa sanda Baba ya nuna zai Aura min ke bata famsheni ta aura miki Isa ba..?karewar tana kaunarki da Tausayin ba..bana son Rainin wayau kada ki sake naji kin taka Karofi in kuma naji wlh tallahi kin ji Rantsuwan musulmi Fa'iza zaki ga Other side of me da baki Taba gani ba.." Hawaye wani na koran wani suke zuban min cikin wani yanayi nace"Ko gidan Ya..ya mariya..? Dogon Tsaki yaja kafin yace"Ita kuma wannan na yi miki iyaka da ki kara Takawa gidanta tunda bata da mutumci bata da,kunya har ni nan zata rika gani na, tana min kallon banza kamar taga kashi..?,Sannan naji Labarin ta raina Mama ta kuma raina Anty Binta har sa'insa tana yi da ita in dai ni ke auran ki kin bar kara taka gidan da ake cin zarafin Uwa ta da yayata sannan itama ki gayamata kada ta kuskura na kara ganin kafarta agida na in kuma ta bari muka Hadu sai na Koreta wlh" Daga haka kit ya kashe wayar sai nayi sororo da waya a Hannuna Hawayena suna D'iga a saman wayar gefen gado na koma na zauna kukana ya kasa Fitowa sai dai Hawayen kawai ina Tuna mganganunsa in ya zagi Yaya mariya bazan damu ba Tunda har Goggo bata tsira ba awajensa ni Ya ishaq daman ya saba kirana da duk sunan da yaga Dama,na yarda yace ban da amfani sannan bana Kiransa sai in ina da Bukata Saboda tun farkon fara aikinsa a abuja ina kiransa Ranar ya Dauka ya yi min fata fata yana min ihu akan me zan rika Damunsa na D'auka Abuja irin katsina ne..? Abuja yana harka da Mutane Dabam Dabam bazai zo cikin jama'a yana wage baki da murya Saboda mgana dani ba kada na kara kiransa kada na kunyatasa watarana cikin jama'a Tunda ga ranar ban kara gigin kara kiransa ba kada na kunyatasa kamar yadda yace d'in sannan Halin ko in kula da ya nuna kan Tamadina bai Dameni ba Domin bashi ba ne na farko ba kuma Kila bazai zama na karshe ba. Tunda ya ke aure na bai Taba taka gidan da Tamadina ke aure da,Niyyar gaida mahaifiyata ba akwai wani zuwan da mukayi karofi bayan Haihuwar Anum ne da Mama da shi a motar abokinsa Dakyar ya aminnce ya biya dani zan kai mata Anum saboda sanda aka haifeta bata zo ba Shima din Sai da na roki Mama ta saka baki ya Biya dani ammh K'iri k'iri yaki bari na shiga da Amir sannan Daga shi har Mama suka ki' shiga Gidan suka tsaya a mota ni kuma ya bani Minti goma. Ina shiga ko zama ban yi da kyau ba ya fara Hon ta na rike da Anum a hannunta ni na fad'amata tare da su Mama muke bata damu ba tayi Lullubi ta fito har kofar gida suka gaisa Ya ishaq kuma ki'ri kiri yak'i fitowa Daga mota Mama ce ma ta fito suka gaisa duk yadda Tamadina taso ta Dauki Amir ya ishaq ya ki fitowa da shi yana rike dashi,Sannan ya hanani komawa cikin gidan ko cikakken gaisuwa bamu yi da ita ba yace na shigo mota mu tafi da nace bamu gaisa ba sai yace sai dai ko na san yadda zan yi na Dawo gida wlh in ya tafi bazai dawo ya Daukeni ba. Ina ji ina gani na shiga mota bayan Tamadina ta bani Anum,Tana d'agamin hannun idanuwanta sun cika da kwallah,ni kaina kwallar ta kawo cikin Idanuwana da Dubara na share mun D'auki Hanya Ya Ishaq ya juyo yana fadin"Tab Mama ashe kice Allah ya Dubi Fa'iza da idon Rahma ana jin mganarta har ana gane me take fad'i naji Babarsu ba'a ko jin abunda take fadi sai uban Ihu kawai ake ji tana yi" Da Dauri na Dago ina kallonsa shi kuma ko ajikinsa maimakon Mama ta kwab'amai a'a sai cewa ma tayi"Eh mana ai uwar su ce ainihin Bebiyan Sai dai kaji tashin Ihu nan kuma wai mgana take yi" Ya Ishaq yayi dariya yana kallona kafin yace"Allah ya taimake ki Fa'iza da yanzu kema ihun kawai zamu rika ji" Daga shi har Mama Dariya suka saka har muka iso gida ina kuka Tozarcin ya tashi daga kaina da yan'uwa ya koma Har kan mahaifiyata shiyasa abunda yayi yau ba zame min Sabo ba sai dai shi Tozarci baka Sabo da shi ko yau aka yi maka shi sai kaji ba Dad'i. Ban karaya ba sannan na yi kudurin sai naje shiyasa da wuri na tashi na shirya yara suka tafi Hadda sannan na yi wanka na shirya Ahmad Na fara Tunanin me zan kai mata bani da komai ban ijiye ba sannan ban bama wani ajiya ba ina bakincikin wannan Rayuwar da nike ciki ko da bani da shi akwai Hakkin uwata a kaina sannan wazai amince bani da shi Tunda kowa yasan Ya Ishaq nada Rufin asiri sanna ba kowa yasan yanayin Rariyar ba ballatana yasan yanayin zubar ruwanta ba Nasan Su Yaya mariya suna iya bakin kokarin su ammh suma ai ya'yanta ne kamar yadda nake yarta akwai Hakkin kyautata mata a wuyana. Da na rasa abunda zan kai mata sai na D'ibar mata garin rogo wanda Ya Ishaq kan siya saboda yara in yaga Dama sannan shima yana son gari da siga,sabulin wankan mu ya kusa karewa sai na Dibar mata na wanki da na Klin,sai na Daukan mata Maltina guda hudu na kulle aleda ina da Burin ko kaya na bata ammh bani Dashi sannan bazan iya bama mahaifiyata tsohon kayana ba kamar na ci mata mutumci ne. Sai nayi Hakuri na Dauki iya abunda nake da shi koda goma tayi na isa Dutsemah sai dai Tamadina ta ganni kamar Daga sama Allah Sarki Uwa bakinta yaki Rufuwa ta rasa ina zata sakani Saboda Murna taji Sauki Sai dai kafafun sun kumbura abokan zamanta sun ce Daga dare zuwa Safe ta tashi da Kafafu a kumbure ana ta dai shafa mganin sanyi. Tunda muka zo ta kama Ahmad ta goya ram a bayanta sai kallonta nake yi farinciki ya cikani ta tambayi su Amir nace suna makaranta tace meyasa ban kawo su ta ga yadda suka kara girma ba..? Idona ya ciko da kwallah ya'ya na ne suma ammh bani da iko da su ballatana mahaifiyata tayi iko dasu suma dai ce mata kawai nayi zan kawo su watarana. Abokiyar zamanta Maman isuhu suke kiranta tayi danwake ta kawomin naci abuna muna ta Hira Da Tamadina duk da mganar nata sai a hankali ammh mu ya'yanta da ta zame mana Dole muna ganewa ni dai ban gayamata wani abu da zai tada mata Hankali ba ko mganar auran Ya ishaq ban mata karfe biyu nayi na tashi na fara shirin tafiya bayan nayi sallah na bata abunda nazo da shi ta Dafa kaina tana ta sakamin albarka. Ta bani Ahmad na goya a baya na,na saka Hijabina nayi ma mutan gidan Sallama ta rakani har zaure tana D'ingisawa ina ta koma sai tace sai ta Rakani mun yi sallama kamar kar mu rabu har zan tafi ta riko Hannuna na Juyo ina kallonta ta kuramin ido sai naji jikina yayi sanyi cikin mamaki nace"Manene ke faruwa Tamadina..? Kawai sai ta Dafa kaina ta jijjiga nata kafin tace"Kiii....yi....hakuri..Fa'iza..! Sai naji raunina ya bayyana da Sauri na kauda kaina ina Boye hawaye na kafin na gyada kai ina fadin"In sha Allahu..Allah ya baki lafiya" Daga haka muka yi sallama har na kule tana Dagamin Hannu. Tunda bai amince na biya karofi ba Daganan ma hau motar katsina,na koma gida hud'u saura sallah kawai nayi na fara kokarin dora girki Saboda yan makaranta ammh gabadaya sai ina jin jikina duk yayi wani irin sanyi komai nawa yayi sanyi kamar an zare ma jikina lakka. Ko su Amir da suka Dawo makaranta sai da suka ga yanayi na Amir mai wayon ciki ne ya dinga ce min"Baki da lafiya ne Umma..? Sai nace mai a'a saboda kada na tayar musu da hankali sai na warware na shiga cikin su mukaci abinci bayan sun gama mukayi sallar isha'i tare bayan mun idar nayi musu karatun Qur'ani na kara ma kowannen su inda ya ke sannan nace su yi na makarantan bokon su da aka basu amatsayin aikin gida. **** Tunda Ya ishaq ya tafi bai Dawo ba sai ana Saura kwana uku D'aurin auran sa,sannan ya Dawo shima din gidan Mama ya sauka sai Dare na gansa,gari kuma na wayewa ya kara fita Jamal ya Dawo tare naga suna ta zirga zirgan karbo dinkuna Gidan Mama kuma ya fara cika da baki Badariya ta fadamin Hajiyar Dala ta iso tun jiya sannan da yan'uwan Mama na yamai ni dai ta barayina bana wani shiri Saboda ban ga abunda zan shiryamawa ba. Ana jibi Daurin aure da yammah sai ga Anty Mamah da Halisa sun zo gida na karb'e su hannun Biyu Saboda suna da kirki Har Halisa ba ta Dauko Halin Anty Binta ba. Na kawo musu ruwa kenan na zauna muna gaisawa,ba islamiya Saboda alhamis ne Su Amir suna gidan Mama dazu da Jamal ya kawo wasu kayan Shahen Ya Ishaq ya tafi da su Ahmad ne kad'ai tare dani. Bayan mun gaisa Anty Mamah ta kalleni sama da kasa har sai na Tsargu ina sanye da Riga da zani na atamfa da dankwali kaina na maida kasa ga Ahmad bayana na goya shi. Anty mahma ta bude murya tana Fadin''Fa'iza ina kunshi ina gyaran kai..? Haka za'a dauko miki amaryan a ganki yarkace yarkace.? Ban ce komai ba saboda basan me zan ce musu ba halisa tace"Ko Saboda ba anan Amaryan zata zauna ba ne shiyasa kika zauna ba wani gyara..? Anty Mamah tace"Wannan ba Hujja ba ne..ya kamata ko kunshi tayi saboda gyaran kanta da kanta Halisa" Ni dai kaina na kasa ban ce komai ba kamar daga sama sai da ya Ishaq ya shigo Gidan yana waya kamar Sauri ma yake yi Anty Mahma ta tsaida shi ya katse wayar yana Fadin"Mahma jira na fa ake yi a waje" Da Sauri ta mike tana fadin"Ya ishaq me zan gani haka Uwargida ba kun shi ba gyaran kai anya zakayi adalci kuwa..? Kallona yayi sama da kasa ina ganinsa ta