← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 175

Sashe 160

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mu kanmu bazamu so haka ba. zamu fi son ka ganta shar da ita ai mu a dad'in mu ne" Yana yar dariya yace"To ina godiya Anty daga gani kina so kanin naki ya zuba shagalin sa" Haka ya saki jiki suna ta Hira sai da suka yi sallama ta bani wayar kawai sai yace"Gaskiya Anty nasara dagani yar kara'i ce ita" Dariya na tsintsire masa sai kuma ya rage murya yana fadin"Ke kuma saura ki fad'amata sirri ne dai tsakanin amarya da ango" Aiko muna gama waya na gayamata ta sha dariya kafin tace''Ya ko fad'i gaskiya yar kara'i ce ni kuma zan mara masa baya ya yi kara'i" "Masha Allah Fa'iza Wlh nayi miki murna kin samu miji irin wanda kowacce ke fata,ina miki fatan wannan kaunar da yake miki har tsufan ku" Na amsa mata da Ameen ina bata labarin irin halin Engr da kuma inda yace zan zauna da garin su da zamu je su yi nasu shagalin. Cikin sanyi na nace"Ni fa ina so na zille wani irin shagali Anty nasara kamar wasu yara..? Anty nasara ta ballamin harara kafin tace"Ke dallah ja chan daman nasan sai kin taba halin wlh sai mun yi shagali zuwa Benue ba fashi muma mu ci zani da alaku mu saje cikin yarbawa sai kiji akaro na tashi bazaki ganemu ba" Tana dariya ina Dariya ta cigaba da fadin"Kuma wlh gyara zaki yi malama na jiki da chan kasa gwara dai a gyara mai yaji dadi.ttunda shima yace yana son ya yi shagalinsa" Ina rufe ido nace"Anty Nasara kada ki lalatani" Duka ta dakamin tana fadin"Shegiya ki gwale kafa ki haifi ya'ya har hudu kike kiran zan lalataki. ? Kaji min wani iskanci wajen Fa'iza..? Ina dariya ban ce komai ba nasan ko na bude baki na shekara ina mgana ba wanda zai yarda cewa ban san komai a harkan auratayya tsakanin miji da mata ba. shiyasa nake mamakin yadda su Anty Mariya suke rawan jikin gyara Saboda maza ina mamakin me suke ji..?domin mganar gaskiyan bansan dadin da suke mganar ana ji ba. Shiyasa ni wlh ban damu ba. shima Engr sai dai yayi mganar zai yi kara'i ammh wani mganar daya danganci haka bai taba hadamu ba. Anty Nasara tayi ta bani shawarwari tana ta nanata mganar gyara nace mata Ammi nachan na jira tayi dariya kafin tace"Shikenan ma nasan Ammi bata da wasa mu in kin raina mu ita kaniyarki zata ci" Kamar ko ta sani Ammi akwai wasa da Dariya ammh in taci Serious kowa shiga taitayinsa yake yi. Engr na da saura kwana goma ya Dawo Abba ya turo Direba ya Daukeni zuwa kaduna ina zuwa Ammi Daman na jira na turarukan wuta da Humra da kwallacha tace ni zan yi ma kaina Dilka da Halawa kuma tace na hada ruwan yin sa akwai wacce zata zo tamin har gida. Abba kuma mun zauna da shi kan mganar kayan daki nace Engr bai min mgana ba sai yace na tuntubesa saboda aje a jeramin komai a muhallinsa da na yi masa mgana sai yace"Matas rabu da Abban naki kawai duka gidajena ba abunda babu ina kuma zai yi tunanin saka wani kaya ban da rigima..? Alamun dai baya bukata ina fadama Abba yace"A'a kamar kowacce y'a kema haka zan yi miki ya ware cikin gidajensa ya fadi in za'ayi miki jere ni zan ma kirasa da kaina" Ai ko an sha muharawa kafin yace ayi amfani da gidansa na malali,duk da shima bangare daya akwai Furnutures,Bangare dayan ne ba komai aciki za'a gyaramim. Shima yana korafin wai Abba ya ki ya Fahimcesa ni dai na samu na lallashesa ya hakura. Kudin kayan lefe kuma 500k ya fara turomin tun yana chan ni da Ammi mukaje kano muka yo siyayya,kaya ba ni da kaya ba aakwatina biyar ta siyamin,muka siya kayan da zan fita tarewa da shi da duk abunda bukata Gidan su Ammi muka kwana washegari mukaje gidan Yaya Asiya muka gaisheta taga kayan tana ta saka albarka sannan muka dawo kaduna. Engr an ce yana da kudi ammh har ga Allah ni baya nuna min yana da shi,in zai min abu daidai misali yake yi min. Domin Ammi ma da nace mata Dubu Dari biyar ya turomin sai da tayi mamaki har tana fadin"Ko dai yace sai ya dawo zai cikamiki..?nace bansani ba,ni kuma ba kudinsa nake so ban damu ba wlh. Muna ta shirye shiryen mu Tunda su Goggo sun ce sun barma Abba azo nan a Dauke ni,Anty Fadila tace sai tazo itama sai na roketa akan ta yi ma Baban su Anum mgana ko zai barta ta tahomin da ita. Tace min zata tuntubesa taji a bakinta nake karajin yasha jinya kwanciyarsa asibiti biyu bayan wanda na sani,duk ya rame ya lalace a kaina tace min har ita yasha fad'amata cewa rashina gibi ne babban ne a rayuwarsa. Ni ko sai dai fatan Allah ya sauwake domin bani da abunda zan yi masa. Fatana Daya Allah yasa ya bar Anum din tazo domin zan ji dadin zuwanta. Kayan Furnitures kuma Abba ya ba ma Ammi kudi anan kaduna ta siyamin komai da komai,masu kayan sukaje har gidan suka shirya komai Tare da Raliya da su Nana khadija ni dai ban je ba ina gida an faramin Dilkar matar na zuwa tamin na rana ni na goga ma kaina na Dare. Kayan mata kuwa musamman Ammi ta saka aka kawomin kayan sokkoto na tsumi na tsugunne ga gumba ga garin aya da ake sha da madara. Sannan ga saiwar Gudayo ta hannun Surayya marubuciyar Halin yau. Ina ta sha wani yana da dadi wani kuma daci sai na Daure nake iya shansu. Sun dawo suna santin gidan mai kyau Falo biyu Bedroom hudu sai Kichen sannan kowani daki da Tiolet,kuma ko'ina yaji kaya Abba ya kashemin kudi domin kayan alfarma ya yi min kayan kitchen kuma Ammi ta siya sauran su zannuwan gado kuma Nana Fatima tayi su cafets kuma da sauran kayan kamshin girki abubuwa Anty Fadila zata yi. Hajiyar su Raliya ma ta aikomin da su Dinner sets masu kyau da kofunan shan Tea sai Kayan adon mata na kwalliya kala kala da kayan gyaran fata da na gashi. Ina da kudi ammh basu barni nayi amfani da kudina ba komai su suka yi min yan'uwana kuma kudi suka hada suka siyamin katon Showglss na Turare sannan suka siyamin Turaren da kwalaben batare da sun fadamin ba,bayan wanda ni na hada da kaina Har hawaye sai da nayi Goggo kuma kayan dake dake tayi min irin su Kuka,daddawa kubewa kayan kamshi,sai kuma suka yi min kayan gara ita da mallam hatta Yaya Abdul'ahad dake chan sai da ya Turo kudi Ammi ta siyamin Dan kunnayen zinare masu kyau aka yi ci ko da sadaki na aka siyamin masu sarka har da awarwaro. Badariya ma da mijinta ba'a bar su a baya Tv suka siyamin da Freezer babba,Sai frem masu kyau na kwaliyar Daki,Mama ma ni da kaina na kirata na fad'amata ta rika sakamin albarka da fatan zaman lafiya Anty Binta ma ta kirani tamin Fatan alheri har da Halisa rayuwa kenan. Jamal kuma har kaduna yazo ya yi min murna ya kuma bani Dubu ashirin gudumuwa yana ta bani hakuri nace masa bakomai nagode da farko kin amsa nayi sai da ya nuna bacin ransa sannan na amsa. Engr na da wata daya da kwana Biyu ya sauka Nageria ta lagos dagachan ya hayo jirgin Abuja. Kwana daya yayi yazo kaduna ganina Karo na farko da jikin mu ya hadu waje daya domin ina shigowa falon Abba a bazata ya tashi ya Rumgumeni wata irin Rumgumar da ban taba sanin ana yin ta ba. Rumgumar da har ya tafi ban daina jinta ajikina ba. Mun fi minti goma ahaka kafin ya sakeni ya dago kaina yayi min kiss a saman goshi kafin yace"Kin yi kyau'" Kuma ba kwalliya nayi ba,Nadai sha gyaran fata da jiki nayi walwal ina tahin kamshi. Bai jima ba daman tsaraban America ya kawomin sai mganar wad'anda zasu bi ni zuwa Benue daganan su rakani Abuja,Sai nace zan musu mgana abincin ma da nayi masa kadan yaci kamar yana sauri ashe kada ya yi kara'i ne tun agidan Abba sai da ya tafi ne ya kirani yana Fadin"Kamshin ki ya yi min Dadi Faa'iza. na kusa na turmusheki a falon babanki wlh" Kunya duk ta kamani bai damu ba ya cigaba da fadin"Wlh na kosa na ganki gani ga ki, na kosa Tife na" Ni kaina na kosan duk da bansan yanayin abun ba ammh ina son sani ko ba duka ba sai dai kunya yasa ban furtamai ba. Ammi na fada'ma yadda muka yi ita kuma ta kira su Goggo suka Tattauna an Tsara tafiya da Yaya mariya da Yaya Asiya tunda yace akwai motoci ba matsala,sai Ammi su Nana khadija na gida suna jarabawa Anty Fadila zata zo sai Nana Fatima,Anty Nasara,Anty Amina matar Yaya isa,Badariya sai Raliya da Hajiyar su itama tace har Benue zata rakani. sannan na kira Sa'adatu na fad'amata tace min zataje itama sai ni mu sha Biyu kenan Goggo tace ta wakilta Ammi itama ai uwace sai Halisa da itama Daga baya tace zataje har ma na fad'amasa yawan Mutanen sai kuma Goggo ta kira tace Hajiyar Dala zata je. ina ji nace gwara taje taga komai duk da nasan abunda zai kaita kenan. Kai duniyan nan akwai mutanen da duk Daukakan da zaka samu bazasu ji suna sonka ba. kuma bazasu bar adawa dakai ba, to irin su Hajiyar Dala ce. *Janafty* [8/1, 5:16 PM] Hauwa Galadima: *KNKB3017* *TASTED & TRUSTED* *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*. *AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*. *ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWOWINRL ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.* *AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*. *SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.* *DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*. *SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*. *KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN
Chapter 160 · 0% Book details