← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 175

Sashe 15

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yi sa..? Ka kiyayi ranar da Fa'iza da ya'yanta zasu zame maka inuwa wacce zaka iya rab'ar ta ina jiye maka watan watarana kada kayi nadamar abunda ka aikata" Wannan marin ya jamin abubuwa Dadama tsakani da Ya Ishaq,kamar ni na bama kaina cikin Dalilin Baba yasa Saudatu tazo duniya(Anum),Da kulawarsa na haifeta Lafiya ita ma kamar Amir ne Baka ce irina,Basu da yadda zasu yi su sauya wannan kaddaran tunda haka Allah ya Tsara Mama ta tsane ni ammh ta kasa Tsanar jokokinta Amir ma ita ta karbesa ta yayesa sai wahalan tamin Sauki,Goggon Karofi Sati daya tamin ta koma ni na mike na Rika kula da kaina har nayi arba'in din Anum. Ya Ishaq baya barina fita ko'ina Sai gidan Mama ko gidan Anty Binta Su kuma har naje na Dawo bana samun kallon arziki,Karofi kuwa Tun da nayi jego ban kara komawa ba Har Haihuwa Ya mariya tayi ya Ishaq yace gulma zai kaini bazani ba. Gidan Yaya Asiya kuwa tun bayan auranta kafata bai kara taka kano ba,Ya Ishaq ya rabani da kowa ciki har da mahaifiyata domin har Haihuwa tayi yaron bai zo da rai ba bai barni naje ba wai zan kwaso ma Anum Sanyi Baya sona ammh kuma yana kaunar ya'yan sosai yake kula dasu kamar yadda yake kula da kansa. Anum na da wata Hudu watarana Baba ya fara rashin Lafiya anje asibiti an yi gwaje gwaje sai aka gano Hantarsa ce ta tabu ba'a sani ba,Ya kwanta asibiti yafi sau hudu duk Hankalin su Mama ya tashi ni kaina Hankalina baya kwance domin Baba shi kad'ai ne ya ragemin Saura gata na,Kwanciyarsa asibiti na Karshe an sallamosa Da ya ishaq zai fita yace na shirya naje na Dubasa Amir daman yana chan tun yaye bai Dawo ba. Naje na dubasa yana kwance ne yana ganina sai da ya mike,Ya miko min Hannu na Kwanto Anum daga baya na mika masa ita yana ta mata wasa Baba yayi ta min Nasihan hakuri da kuma Umrtana da na zauna nayi Biyayyan aure zan rabauta Ranar gobe kiyama.. Ashe wasiyya yake barin mu yace na kula da ya'yana na basu tarbiya kada na Biye ma Ishaq,nayi hakuri dashi Sannan na kara hakuri da su Mama watarana dani da ya"yana duk sai mun zame musu Inuwar Rab'a,na dawo gida da Tunanin mganganun Baba ashe bazai kwana ba adaran Allah ya Dauki ransa. Alokacin mutuwar Baba na kara yarda Tabbas ban da sa'a domin duka wada'nda nake gani agata na sun kare bani da kowa anan duniya da zan kallah nace Gata na ne duka sun tafi Na tabbata ko Mama bata kaini kukan mutuwan Baba,na fade lokaci d'aya nayi zuru zuru tabbas Mutuwar Baba ya sanyaya ma Ishaq zuciya sannan ya sa ya rage wasu abubuwan. Rasuwar Baba ba'a rufe shekara ba Ya ishaq ya samu karin girma zuwa Abuja,chan ya koma aiki sai bayan Sati biyu yake zuwa katsina sai nauyin su Mama da su Jamal duk ya koma wuyansa abubuwa duk suka Tabarbare daman karfin zumumcin Baba ne to yana Rasuwa sai ahankali Hajiyar Dala ta matse kanta gefe itama Goggon Karofi sai ta kama kanta itama Daman basa shiri da Da Mama sai ta Dade bata zo katsina ba ba ita kadai ba Saboda Sanin Halin Ya Ishaq yasa ba mai son Rabata abu kadan yace munafunci ake yi shiyasa Dole dai su Mama ne bani da kowa a garin katsina sai su da ya'yana. Samun karin girman Ya Ishaq yasa sai ya samu rufn asiri fiye da baya ya gyara ma Mama gida ya koma Fasalin na zamani shi kuma ya siya Fili ya fara gini a Anguwan layout,Jamal kuma ya shiga jami'a sai Badariya da ta zama yammata yanzu sai ni da ya'yansa wanda Darajan su yasa yake Ragamin shima ba wai don ya daina Tozartani ba ne A'a har yau har gobe ni Fa"iza ba kowa bace a wajen Ishaq kabir Karofi Cikin mustapha ko ni bansan ina da shi ba sai da yakai wata Biyar Mama data ganni da ciki ta Dinga bala'in na zama kamar beran masar bani da aiki sai Haihuwa ta manta ba ni kad'ai nake samar da cikin ba har da Gudumuwar D'anta ammh bata ganin Laifinsa sai nawa,Na haifi Mustapah ba Dadewa muka tare a sabon gidan da Yaya Ishaq ya gina katon gida mai shashe biyu,Shashen farko mai 3Bedroom da Falo sai kichen,Nawa daya sai na yara sai guda d'aya na baki,Ya ishaq shi ya Zuba Sabbin kaya agidan komai bamu Dawo da Tsoho ba, Mama ta kwashe su ta kyautar ni ko da har nayi Tunanin na aika ma Tamadina da su Dakinta Sai leda ba kujeru ganin Mama tace akwai wacce zata bamawa ban yi mgana ba, Sanin Halinta. Haihuwar Mustapah yazo da Budi sosai Ya Ishaq har motar hawa ya mllaka ya siya mama nata,Budi ta ko'ona sai hamdala da Godiya yana Dinkamin suturu daidai gwargwardo sai dai na yaransa Dabam suke,Ni wani Lokacin ko yayi niyar yimin Rantsatsun kaya sai kalaman Mama su Dishe niyyarsa tunda tasha fadin siyamin kaya na alfarma barnan kudi ne, Tunda ba kyau zasu yi min ba sannan bansan yadda ma ake gayun ba kuma gaskiya suka fada ba karya sukayi ba ban san komai na gayu ba. Ni dai iyakata nayi wanka na shafa mai na saka kaya,Abaya telan su mama ke min dinki Mama ta koma ba wata mace saboda sai nace yana kamani ni kuma bana so kaya su kamani na fison a shatamin na rika yawo aciki,ya Mariya ko Ya Asiya ko da wani Lokaci suna kokarin gyarani ni ko bana jin su gani nake yi gyara da gayu na wajen mata masu kyau da gata ban da ni da bani da ko d'aya daga ciki Dalilin dayasa Ya Ishaq yake Biye ma Mama kenan in ta fadi mgana hakan take indai a kaina ne ballatana ba ran Baba ita ke tafiyar da komai. Mama ta bada shawaran nayi Tsarin iyali sai dai bai karbeni ba wannan yar ashanan aka sakamin ya sakarmin jini Dole aka ciremin ana ko Ciremin ko wata Biyar ban yi ba na Samu Cikin Ahmad,na haife su kusa da kusa domin a shekara ta takwas da auran mu da Ya Ishaq duka na Haifesu haihuwan gwarne na rika yi don ma Allah yasa ina da jarumta daukan duka kwarmiyan yaran Cikin ikon Allah cikin ya'yana ba wanda ya Dauko Lalurata sai na godema Allah Ammh wani ikon Allah susan Lalurata barin ma Anum da Amir susan bana ji sosai in zasu yi min mgana sai sun daga muryansu. Allah ya bani yara masu kirniya,musty Da Amun basa jin mgana komai suka gani sai sun taba abunga ga wanda bai da karfin ji ina chan ina aiki su kuma suna Falo suna barna bana sani kuma Duk abunda suka Lalata sai Ya Ishaq ya dora komai akaina,Shiyasa ya dinga masifan na bari duk sun bata gidan sun bata kayan kallo sun bata in ji min wanki kuma Mama sai tace bazai kara siya ba, a kyaleni na wahala ai da gangan na bari suka bata komai. Ni kuma bana cewa komai,Saboda bani da wani zabi,Har zuwa yanzu da girma ya kamani da ya'yana ban daina samun tozarcin Wajen Mama da Anty binta ba tun ba'a sani ba har kowa ya sani,Goggo karofi dai hakuri take bani,in ta kirani a waya sai dai fa ta wayan ammh Sai na shekara kafata bata taka Karofi ba Tunda nayi aure Sau Daya naje naga Tamadina Shima Haihuwan Mustapah ne da naje karofi da Ya Ishaq yaji Labari masifa ya farayi wai baya son ya'yansa suna zuwa gidan wasu suna Rabe rabe. Haka nan nake daga ni sai ya'yana sai Danginsa alhalin yasan bana jin Dadin su ammh ni nawa yan'uwan sai dai zumunci ta waya ya rabani da kowa nawa.Hafsatu ce kawai tana ta da Kulafucin yan'uwana bai da yarda zai yi da ita in sun samu Hutu tana zuwa ta zauna dani hakan sai yasa na Shaku da ita fiye da su Yaya Asiya. Nasan Tabbas Ya Ishaq zai kara aure watarana ban daukesa alokacin da najisa ba Nima abakin Anty Binta na farajin mganar auran sannan Mama ta Fadamin nasan bani da wata Daraja a wajen ya Ishaq ammh na Dauka zan ci albarkacin ya'ya ashe bani da wannan alfarman na Kunshi Bakinciki Tundaga ranar farko da na wayi gari agidan Ya Ishaq a matsayin matarsa,Na kunshi takaici a matsayina na Uwar ya'yansa na fuskanci Tozarci a matsayina na kanwarsa tun a baya to wani tozarci ne ni Fa'iza da ya rage ban gani ba..? Nayi Rayuwar aure shekaru Takwas da wani abu ammh Daidai da Rana d'aya ban Taba Danda'na yadda Dadin aure yake ba na dai yi shekaru Takwas ina Sanin yaya matsayin Tozarci da Gori yake sannan na kara zama Guilt akan kushen Hallita da kuma aibata Nakasa ta nayi rayuwa cikin Guilt din jin ban da sa'a na rayu cikin Guilt din Sannin ni bani da gata na zauna cikin Tunanin Mata ire ire na basu dace da suyi Farinciki ba. Basu chanchanci miji mai kirki ba, basu chanchanci samun soyayyar ko wani Namiji ba,Sannan basu chanchanci Rayuwar Farimciki ba. Mata ire irena Rayuwar kaskanci da Torzarci da Bauta ya dace damu,Ba kokarin mu goga kafad'a da kafad'a da mata masu kyau da gata ba shi yasa na Rayu cikin Tunanin kayan alfarma da shigar alfaarma da Kwalliya basu dace da ni ba, sun fi dacewa da mata masu kyau da Nagarta kamar yadda Ya Ishaq da mama ko Anty Binta ke yawan fadi akaina. Tabbas na aminta da duka zencen su da Tunaninsu" *Littafin KANA NAKA book 1 free ne book 2,3 paid book ne biya kudin karatun ki akan Naira N500 Regular posting sau d'aya a rana.* *Ko kuma tsarin VIP 1000 Posting sau biyu a rana akan wannan acct din 0552179550 Jamila Umar Gt bank,sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488 Wannan karon babu tsarin kati,kowani tsari zaka yi ka turo ta POS,Mutanen mu na Niger kuma zaku tuntubi Kausar Aglan Nissa ta wannan lambar +22796562223* *Janafty**KANA NAKA..!* *Wattpad:JamilaUmar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* *Book 1* *ASSALAMU ALAIKUM* *KAYA SUN SAKE SAUKA*. *INGANTATTUN SAIWOWI DA SASSAKE NE DA AKE DAHUWAR
Chapter 15 · 0% Book details