← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 175

Sashe 55

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya bada Lada A nan suka yi sallar La'asar sannan suka yi shirin tafiya sai nace su jirani mu wuce tare Lokacin Yaya Isa ya iso ya tafi masallaci ne,na mike na shiga uwar Dakin Tamadina na Dauko jakar kayan mu da Hijabina.da Yaya Asiya ta wankemim Goggo ta matsamin nayi wanka da Safe na fito falo na ce Hafsatu tazo ta sakamin Ahmad a bayana na goyasa ta sakamin shi har na saka zani na goyasa irin na D'ago kaina sai Duhu ya mamaye ganina na fara Laluban bangon gabana na rasa sai nayi luu ta baya zan fad'i sai naji an tareni ana salati kuma hannuwana ne da yawa suka rikeni,Sama sama nake jinsu jiri ya rikeni da kaina da ya dauki wani irin azaban ciwo,Kamani sukayi na zauna Yaya mariya ta kwanto goyon Bayana Goggo fad'i take"Daman ni nasan yarinyar nan bata da lafiya, shigen zurfin cikinta yasa taki mgana" Asiya kira min Isa yayi maza yazo in asibiti zai kaita ya kaita kada ta yi ma kanta Lahani bamu sani ba" Ina nan zaune Dafe da kaina ina jin Sannu sannu na tashi Daga bangarori Dadama, chan jimawa na zame na kwanta naji shigowar Yaya Isa da Bayanin da Goggo take yi masa,sai yace a kamo ni muje asibiti a dubani. Yaya mariya ta kamani muka fita mutan gidan na tambayan lafiya tace jiri ne ya kwasheni Maman isuhu tace"Daman daga ganinta bata cika lafiya ba itama" Ni dai ina jinsu har muka fice muka shiga mota wani asibitin kud'i acikin gari ya kaimu shi ya shiga ya fita muka ga likita akan Lokaci gwajin Farko sai ga jini na ya yi sama Dari Biyu da Doriya sai ucler likitan nata fada ina so na kashe kaina da na fadi zan iya kamuwa da Ciwon barin jiki, ko jini ya haye yayi sama na mutu mgunguna ya bani bayan yayi min alluran jijiya ta ucler sannan yace na rika cin abinci sosai saboda kiyaye lafiyata. Muna hanyar Dawowa Yaya Isa sai fad'a yake yi,Yaya mariya bata mgana sai dai kawai ta sauke numfashi tace"Uhm" abun yafi karfin ta wannan karon ko da muka koma makotana sun tafi sun so su jira dawowarmu Goggo tace su tafi Saboda Dare sannan sun bar iyalansu agida to sanadin haka komawa Katsina bata yuyu ba da Goggo ta kawo mganar Yaya isa ya maidani sai yace"Haba Goggo kalli Halin da take ciki fa..?,jininta yafi dari biyu a yadda take nan ko kanta bazata iya mora ba ballatana ga yara tare da ita,kawai mu wuce da ita gida in taji sauki sai ta koma" Sai Goggo ta kasa musamai saboda taga Halin da nake ciki,Ni a motar Yaya isa muka tafi ni da Goggo da Baba Ati da yara su Yaya mariya da yaya Asiya da itama tafiya kano tasha ruwa suka hau ta haya mun yi sallama da mutanen gida muka rabu suna Hawaye muma muna yi. Sai dare muka isa karofi ni dai abinci suka matsamin naci, nasha mgani na kwanta barci. Salolli na ma sai da asuba na rama su na ji saukin Jirin sai dai ciwon kan ne,Washegari Yaya Asiya ta koma kano Yaya mariya daman muna isowa ta wuce gidanta Wasa wasa jikina ya ki dad'i har sai da na kara Sati a karofi Goggo na kula da ni,tare da su Amir kamar kada na koma inda na fito sai dai ba Dama ranar da nake da kwana bakwai a karofi Goggo ta saka Yaya isa ya maidani da Yammah bayan taga naji sauki,Tare da sha tara na arziki komai ta had'amin su garin kunu,garin Danwake,Wake,Tsaki,rama bushasshiya da Zogale sai Taliya yar Hausa da yara suke so sai ta saka aka Murzamin ta samin a kwali saboda kada ta karye hatta kayan maggi sai ta siyamin,da kayan miya mai yawa sannan ta saka Yaya isa ya kaini har gida ni da yara ina ta masa godiya shima da ya saukeni ya bani dubi biyar yace na rike sannan ya Jadaddamin naa kula da lafiyata na amsa mai da in sha Allahu. Gyaran gidan na fara ko'ina duk yayi kura,Amir na tayani da kwashe kaya su Anum kuma sai dai su kara batawa,Adaran Taliya yar murji na Dafa mana na manja mai ruwa ruwa muka ci tare a faranti daya muma Santi muna gamawa bayan mun yi sallah na saka suka kwaso littafan makarantansu nace su duba tunda gobe zasu koma makaranta. Wasahegari Laraba da wuri na shiryasu na kuma fita da su da kaina,Haruna da Sa'adatu da na leka gidan suka karamin gaisuwa da tambayan ya karfin jikina..?nace naji sauki sai hamdalar ubangiji. Makota na dake kusa dani wad'anda ban taba ma shiga gidajen su ba sun shigo sun min gaisuwa daga suce Sa'adatu ta fad'a musu ko Habiba naji Dadi Sosai domin ba karamin masoyin ka ba ne zakayi rashin uwa yazo yace maka Allah ya kara hakuri kuma bazaka manta da wannan mutumin ba, wanda kuma bai ce maka Allah ya kara Hakuri ba,shima girman abunda ya aikata yana nan acikin ranka bazaka taba mantawa dashi ba. Na dawo da kwana Biyu Anty Mamah tazo min gaisuwa tace ta zo sau biyu bana nan,nace mata eh nayi rashin lafiya ne tayi min gaisuwa ta kuma bani Hakurin sun yi tafiya ne chan dangin megidanta Kumo dake jahar Gombe ta jima muna ta Hira sai la'asar tatafi bayan nayi mana Danwake da manja da yaji taci ta koshi,sannan mukayi sallama washegari kuma daga makaranta Sai ga Badariya tazo min gaisuwa itama da ban hakura Mama bata nan bikin D'iyar Hajiya Barira k'awarta tatafi wajen satin ta daya Abuja aka kai Amarya, dagachan ta biya gidan su Zainab ta kwana biyu. Sai kawai na samu kaina da cema Badariya"Sun dawo ne..?ya mai jiki..? Badariya tace"Basu dawo ba suna chan jikin Farhan da sauki sun dai Tsaya Hutawar su kawai" A fili nace"Allah ya dawo da su lafiya" Daganan ban kara tofawa ba,Bata jima ba ta tafi tace saboda Mama yanzu in taga ta Dad'e sai ta fara fada, nace gaskiya kam ya kamata ta tafin kada dare yayi mata. Mutuwar Tamadina ta Dakeni matuka,sai dai na zauna nayi Tagumi ina sharan kwallah in Amir yaga nayi Tagumi sai ya cire tagumin yana fadin"Umma ki daina tagumi ummanki zata dawo" Sai ya bani dariya na jawosa jikina ina fadin"Aa bazata dawo ba Amir..Ai kasan mutuwa ko.?kuma a makaranta an fad'a muku duk wanda ya mutu ai baya Dawowa a rami za'a ha'ka a binnesa shikenan bazamu kara ganinsa ba" Cikin yanayin mganar sa yace"Ita Umman ki a rami aka sakata..? Sai na gyad'a mai kai Lokaci d'aya ina fadin"Eh mana..kowa zai mutu muma watarana zamu mutu a hak'a rami a binne mu baza'a sake ganinmu.Mu yi ma wadan'da suka rigamu mutuwa addu'a muma in mun mutu sai mu samu masu yi mana addu'a" Ya gyad'a min kai kafin yace"To Umma zan rika yi ma umman ki addu'a" Daman kuma ina yawan fad'a musu in sukayi sallan su rika cewa Allah ya gafartama iyayanmu da magabatanmu da yan'uwanmu,kuma suna yi,Har su Anum haka na koya musu nima in dai na yi sallah sai na Roki Allah ya jikan dukkan yan'uwa musulmai da suka rigamu gidan gaskiya mu kuma Allah yasa in tamu tazo mu samu cikawa dakyau da imani. An yi addu'ar Arba'in Tamadina,Ni ban je ba Hakama Yaya Asiya su Goggo ne da Yaya mariya suka koma sai dai daga gida nayi mata addu'a da Sadakan Allah yakai haske kabarinta na Rokar mata salama da amimci a wajen Ubangiji a kabarinta,Ni tunda Tamadina ta rasu komai ya fita kaina naji bakowani wani abu ne zai rika batamin rai ba,Na riga nasan na rasa dukkan wani bangare na jin Dadi, Dariyata kadai ya'yana ke gan. sune kad'ai yasa har yau nake tsaye kan kafafuwana,Saboda hakane yasa na Dage da shan mgunguna saboda in nazo na kasa ko nayi Rauni ya'yana baza su iya d'aukan maraici tun suna da kananun shekaru ba. shiyasa karfina da Kuzarina duk Ta dalilinsu ne shiyasa ita uwa ya'yanta kan zama gwarin gwiwanta sau da dama. Kwata kwata nama manta da mganar Form din da na cike na koyan sana'o'i da bada tallafi,na mikama Allah duka al'amarina,sai kwatsam Badariya tazomin da labarin an Turo mata sako Daga Kungiyar Women charity Foundation kan zasu tantancemu ranar asabar karfe goma na Safe a wata makarantar yan mata Dake cikin gari sai na rud'e na fara rawan jiki ina fadin"Bada..riya..To ni ya zan yi..?bansan ko'ina ba fa..? Sai tayi Dariya tace"Sha kurum ki zan yi ma Mama karyan makaranta sai nazo na rakaki" Sai da ta fad'i haka sai hankalina ya kwanta, tun daga ranar ko dayaushe addu'ata d'ayane in da alheri acikin wannan mafitan. Allah ya tabbatar min in ba alheri Allah ya musanya min da mafi alheri. Sai naji zuciyata ta natsu da al'amarin,Ranar jumma'a Dakyar na iya barci Saboda Zullumin abunda zai faru gobe,Da sassaafe na shirya yara suka wuce Tahfeez nima ban zauna ba na shirya tara da wani abu Badariya tazo na goya Ahmad na saka Dogon hijiba na mai ruwan kasa duk yasha ruwa na rufe gida muka tafi,Ita ta biya kudin adaidaita gaskiya akwai tafiya ba kad'an ba tsakanin gidana da Makarantar mun isa goma saura Haraban makarantar cike da manyan motoci daga gani abun na manyan mata ne. A wani babban hall na makaranta ake taruwa kai tsaye muka nufi chan mun shiga mun tarar da mata da yawa duk sunzo,muka samu waje muka zauna ina ta raba ido sai da goman tayi sannan Manya mata masu nasaba da ilimi da zati suka rika shigowa suka tsaya a gabanmu, ina ji Badariya namin Rad'a mai bakin mayafi mai jikan nan Hajiyar su Raliya ce na jinjina kaina daga gani kudi da isa sun zauna ajikinsu A she mu Talatin suka Dauka,Bayan sun kira sunayen kowa da kowa muka mike gabad'ayamu akwai yan rakiya ire iren Badariya,Wata Hajiya ce mai glass take kiran sunaayenmu,na kasa Raunanun kunnuwa a ina jin sunana na mike bayan Badariya ta rike hannuna muka mike tare sannan ta koma ta zauna, ashe Wani kati zasu raba na na shedar Training d'in da zamu yi sannan da wasu bayanan da suka danganci abunda za'a koyar damu.
Chapter 55 · 0% Book details