Sashe 155
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sona ba,ba abunda zai iya sauya wannan abun kawai dai akwai wani gibi ko bangaran da ni zan cike masa ne shiyasa yaso komawata garesa. Ammh daga yanzu na fahimci komai kuma bazan kara bari rayuwata ta kara shiga wani hali ba,ya'yana na wa ne har kuma gaban Abada ba su da uwar da ta fini a wajen su,ko da sun Raunana na dan Lokaci ne zasu dawo daidai da yardan Allah. Da wayar Yaya Salisu nayi amfani na kira Abba ina kuka daman na Haddace lambarsa sai da na saka naga shima ashe yana da lambarsa. Jina cikin kuka da Damuwa yasa Abba yace na zauna a inda nake ga su nan zuwa shi da mallam bayan na fad'a musu ina gidan su Yaya isa. Sai da naji muryan Abba na bude kofa ina kuka gabansu na zube na had'a Hannayena Biyu ina fadin"Abba in nace na fasa komawa gidan Ishaq ran ka zai baci..?ba zaka kalleni a wacce ta maida kai karamin mutum ba..? Sai Abba ya saka Hannu ya Dago ni Cikin wani yanayi muka isa har falo kan Daya daga cikin kujerun falon ya zaunar dani su ma duka suka samu gefena suka zauna cikin Tausasawa Abba yace"Bazan taba cewa ba Fa'iza daman ai zabin naki ne ba namu ba ko ba haka ba Mallam..? Sai ya jinjina kai yana fadin"kwarai da gaske" Cikin kuka na zayyane ma Abba komai da ya faru tsakanina da Ishaq na karishe da fadin"Abba ko waye ka auramin shi ni dai ka taimaka kada ka auramin Ishaq Saboda yace ni Datti ce bazan je ce na gurbata masa Tarbiyan ya'ya ba' Na karishe fad'a cikin gunjin kuka Abba ya yi shuru ransa ya baci ya kasa mgana Mallam ne yace"Subhanallah shi kuma ya zai yi haka..?Ana mganar aure kuma zargi na shigowa ciki" Abba ya yi huci kafin yace"Ai shikenan bakomai daman zabin na baki da kaina ban miki katsalandan ba ne, saboda watarana ko bani ki iya sanin abunda ya dace dake. tunda yace haka ya gama mgana ba kwantai kika yi ba Fa'iza ke yar baiwa ce in yace ke Datti ce wani a Dattin zan bashi auranki kuma ya karba tashi ki je ki wanke Fuskarki ki kwantar da Hankalin ki insha Allahu bazaki ji kunya ba Allah zai nuna miki Ribar Hakurin ki tun a duniya." Kalaman Abba suka sanyayamin rai duk da ban kawo ma Engr a lokacin ba, na riga na yanke hukunci gwara na auri koma waye da na koma ma Waye da auran Ishaq,bayan tafiyar su Abba ba jimawa sai ga Ammi ashe Abba ya yi mata waya yace tazo ta zauna dani. Alokacin su kan su su Goggo ba su san abunda ya faru ba, ita kanta Abba bai yi mata bayani ba yace dai ina gidan su Isa taje ta zauna dani bayan tazo ne na zayyane mata komai.. Kyafci ta fara kafin tace"Uhm komai akayi da jaki daman sai ya ci kara mutum mai kima irin Engr ya yi ma wannan cin zarafin..? Ina hawaye na kasa mgana saboda ni kaina kunyar kaina da abunda Ishaq ya yi ma Engr duk ya kamani,Ammi ta rika fada kamar zata ari baki tana fadin"Daman wata Daraja naki ya sani..?dan renin wayau ne fa Jaka ya maidake wacce bata da yanci ki koma ki cigaba da gadin gida da kula da mahaifiyarsa da ya'yansa da matarsa. to ai kuma yaci taliyar karshe ya'ya in bazai rike ba ya baki zaki hada ki rike abinku kuma na tabbatar da Engr wlh ko duka duniya kika haifa bazai gaza ba wajen rike miki su ba' Ina tsiyayan hawaye nace"Ammi ni fa ban ce Abba ya auramin Engr ba. Cewa nayi ya bani duk wanda yaga Dama" Ammi ta min dakuwa kafin tace"Kaji min sakarci in ya je ya aura miki wanda baki sani ba fa..?an rabu da bukar kuma sai a haifi Habu" Ina kuka ne ammh sai da nayi dariya a raina nasan Abba uba ne na gari bazai taba min zabin da zai zama Cutarwa gareni ba, shiyasa ma ban damu ba ni dai tunda na sahale ma kaina Ishaq sai naji kamar an saukemin wani katon dutse mai nauyi daya tokaremin zuciya. Cigiyata suka fara yi dagachan Gidan Goggo,tunda an ce ina ko tare da Abba ne sai aka kira Ammi tace tana tare dani,Yaya Salisu kuma na tare da Amir yana lallashinsa Domin yaga yaron ya shiga damuwa shi ko Amir kalaman Daada ne ke masa yawo a kwakwalwa tare da Kukan Umma sai yaji ya tsani Daada ta ya zai kira Umma da wannan sunan mara kyau..? Kuma ya sakata kuka.? Kawai don yana Da dauriya ne yasa bai yi kuka ba ammh duk yayi zuru zuru. Abba da Mallam suka tattauna mafita batare da sun yi zencen da kowa ba. Engr na gidan inda Ishaq ya Fice ya barsa cikin kogin nadama,Hankalinsa ya tashi Tunanin abunda ya aikata kuskure ne bai zo mai ba sai da ya aikata wani kishin Fa'iza ne ya taso masa da yasa ya kasa iya Sarrafa kansa. kishin ta samu wanda ya fisa komai yace yana sonta shi ya Dauka bayan shi ba kuma wani namijin da Fa'iza zata Burgesa,yana da yakinin in ba shi ba,Fa'iza ba ta da kowa kuma yana takamar cewa shi da ta gujen ma wa bata da kamarsa sai ga shi Allah ya nuna masa Isharan sa da cewa ita Daukakan Allah ba ta zaba ba ne, Daukakarsa ta kowa da kowa ne koda kai ba kowan kowa ba ne in ya tashi zai Daukaka domin nuna izina ga maza ire iren su ishaq masu Tunani irin nasa. Har ga Allah shi kan shi Engr bai san da Sauyin mganar ba sai da suka shiga masallaci Abba ya karkata ya ce masa ya kawo sadakin Fa'iza ya bashi auranta Engr sai yaji kamar bai ji da kyau ba, sai da Abba ya maimaita masa bashi da Cash sai cheque ya rubuta ya bada sannan ya kira Sister dinsa kafayatu Vedio call Papa na gida tunda Weekend ne ya bama Direbansa ya Daukan musu Daurin auran Live suka kallah duka duka Lamarin ya faru gaza da mintina talatin ne. sai akalan Fatan alherin ya koma ga Engr a madadin Ishaq da aka barsa baki Bude. Engr bakinsa kamar zai Tsage daman ga shi ma'aboci mirmishi da Fara'a haka jama'a ke ta ba shi Hannu cikin masu hannu da shi har da Dr.Lawal bako. yazo Daurin auran Abba ya fad'amai Ishaq ma haka shi kan shi da yaga Engr sai da ya rankwafa Aiko a gidan giya akwai babba shi kan shi yasan yanzu ko yarsa zainab bata isa ta Dagama Fa'za kai ba,Tafita komai na Duniya Tunda ta samu miji a gefenta kamar Engr da ya taka matakan Rayuwa masu girma. ******* Tsakanin Mama ko Anty Binta an rasa mai iya mgana ballatana su fahimci yadda aka samu wannan Sauyin haka bangaran su Goggo ma suna ta jimamin garin yaya aka samu Sauyi ba tare da kowa ya sani ba..?Sai dai ba amsa tunda mazan duk ba su dawo ba,ni kuma ina gidan su Yaya isa Nana Fatima ta kira Ammi tana fad'a mata Halin da ake ciki da sauyin da aka samu. Ammi ta rangada guda ta yi rawa tayi juyi ina zaune ina kallonta Sai da ta katse wayar Fatima sannan ta kalleni tana fadin"Aure ya Dauru murna muke ta yi. Kin Zama Amaryan Engr igiya uku har Abada" Kamar an zaremin wani mutuwar jiki haka naji,sannan na ji gabbaina da suka yi sanyi sun tashi daga suman da suka yi,Naji dai yanayina ya sauya kadan ammh kuma bana bakincikin sai ma wani boyayen ajiyan zuciya da na saki batare da na sani ba,Ina da yakinin zan samu farinciki ko ba duka ba ammh zan samu ko da kad'an Daga cikin farincikin da Sauran mata suke samu a gidan auran su. Sai da mukayi sallar Azahar Ammi ta sani gaba muka koma gidan Goggo ba wasu jama'a sosai sai na gida,Muna shigowa Yaya Mariya ta saka gud'a tana fadin"Shi daman alkawarin Allah baya tashi" Daman ita bata wani so Yaya ishaq ba,tun da farko da bata yi da shi yasa har yanzu sama sama sama ne,ni dai daki na wuce,Su Mama na falo duk jiki ba Dadi,Badariya ce kadai ta biyo su Nana Fatima zuwa dakin wajena ita kuma Ammi ta tafi wajen Goggo Abba ya kirata suna bukatar abinci da abun sha. Duk da Jikin Badariya ya yi sanyi bayan Nana Fatima ta rumgumo ni tana fadin"Ina tayaki murna yar'uwata. Allah ya sanya alheri" Na amsa mata da Ameen kasa kasa Sai Badariya itama ta kariso tana Fadin"Ina murna Anty Fa'iza Allah yasa gwara da akayi" Na amsa mata ina kallonta tana so mu yi mgana ammh sai taga idanuwan mutane shiyasa ta juya ta fice Su Raliya ne da su Yaya Asiya tare dani suna ta tattauna yadda lamarin ya sauya ni dai ina jin su ban ce komai ba zan yi mgana ammh ba yanzu ba. Abinci su Abba Nana khadija da Hafsatu suka kai musu,Sai wajen uku na rana muka samu kebewa da Badariya shima din tazo fad'amin su Mama na shirin zasu koma katsina ne.. Cikin mamaki nace"Yau kuma..?Na sha sai gobe..? Cikin damuwa tace"Mama tace kunyarku take ji bazata iya zama ba. taji abunda yaya ishaq ya aikata Jamal ya kirani a waya duk ya fad'amin yace Yaya ishaq nata kuka yana bama Abba hakuri, shi kuma yace bakomai tunda dai kin auri wani shi ba da shi za ayi masa rufa rufa akai masa Datti ba.." Kai na sadda kasa ban yi mgana ba sai ta Dafani tana fadin"Don Allah ki yi hakuri Anty Fa'iza" Ina kokarin maida hawayen da suka kawomin nace"Bakomai rayuwa ce Badariya" Nama kasa mgana sai kawai na saka kuka,sai ta rumgumeni tana Lallashina itama tana cikin damuwa ammh kuma bazata iya gayamin ba ganin yanayin da nake ciki. Tare da ita mukaje wajen su Mama,Anty Binta dai ta kasa mgana Mama ce ke ta bani Hakuri nace bakomai Anty mahma tace"Shi ma dai Ishaq kamar wani yaro..? Ai ba haka ake nuna kishi ba" Yake kawai nayi ban yi mgana ba Halisa nake kallo duk