Sashe 149
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya gano shi Ishaq bai yi mgana dani ba abaki yaran yaji mgana ya hau ya zauna kuma ya yad'a labarin batare da ni na sani ba lalle ko in hakane akwai kura ya zama Dole nasan Halin da ake ciki na kuma yi gaggawan fidda Guda daya in Engr na bama Dama z ai bama Ishaq hakuri in kuma Ishaq ne zai san yadda zai lallabi Engr yasan shi da Takwalli da yakana. Ni daman nazo sanar da Abba ranar asabar zan tafi Karofi ne saboda walimar mu,sai kuma naji yace yana son mgana dani ni yanzu nauyin Abba nake ji saboda Engr,naji Abba na mgana ammh har ga Allah ban ji da kyau ba ina chan ina tunanin hirarmu da Engr na rigiman sai yazo walimarmu har karofi daganan ma sai na nunasa wajen Dangi. Kamar daga sama naji Abba na ambaton Ishaq da mganar ya kirasa yana tambayansa Lokacin da da suka sanya na auran mu. Sai na kalli Abba cikin wani yanayi kamar ban ji da kyau ba nace"me kace Abba..? Sai da Abba ya kara maimaitamin sannan na gane in da aka dosa gabana ya fadi cikin rawan murya nace"Abba..Ni kuma..? Daman ka ba shi dama ne..? Abba ya girgiza kai kafin yace"Ke yace kin basa dama kin fad'ama yaran da Antynsu" Sai na tuna mganar muka yi da Anum,Da mganar mu da Zainab sai naji hankalina ya yi bala'n tashi cikin tashin hankali da rawan murya nace"Ni na fad'a ne wasa nake musu Abba.." Kai tsaye Abba yace"Zabi naki ne har yanzu Fa'iza ki yi tunani in Ishaq din kika zaba falillahil hamdu sai na sallami Engr, in kuma Engr kika zaba sai na bama Ishaq hakuri ki yanke hukunci daga yanzu zuwa ranar da zan zo Karofi yaushe ne Walimar taku..? Cikin rawan murya nace"Sati mai zuwa" Abba ya jinjina kai kafin yace"To kiyi tunani a tsanake kafin lokacin aranar zamu tsaida mgana in sha Allahu. Tashi ki je, jibin Direba zai kai ki zan barma mamanku Sako ta baki." Daga haka ya sallameni na mike jikina na wani girgiza zuciyata na rawa. Allah ne ya kaini d'aki lafiya ko gani bana yi,gabadaya idanuwana sun yi Duhu kamar yadda zuciyata ke cikin Duhu da Sarkakiya. *Janafty* [7/31, 6:37 AM] Hauwa Galadima: *KNKB3013* *Goron Tula* *Ingantaccen maganine dake saukarda niimar mace sannan dadin dadawa fruit ne ga dadi abaki zakine dashi chakwai sannan bashi da wata illa yadda kikasan fruit haka yake* *yana da matukar kyau da tasiri ga ma aurata daga mace harna mijin Kuma munada Syrup nasa da akataceshi sannan aka hada da ingantattun magunguna dasuke temakawa ma aurata kwarai don inganta lafiyarsu dakuma maganin matsalarsu ta auratayya yana saukar da niima sosai yana karawa mace dadi fiye dazatanku sai kingwada zak ibada labari insha Allah* *Sannan akwai zumar kiba* *Duk macen dake son ta murmure tayi kyau taciko tatada komad'a sosai shaf dinta yafito sosai da sosai to tasha wannan zumar insha Allah zaki gode min* *Zumar gyara nono* *Zasu yi kyau suciko ammanfa bawai su tsaya ba zadai suciko suyi kyau sosai insha Allah* *Zumar hips* *Indai kinsha zumar nan to hips dinki zai bude zasu yi kyau suciko sosai zaki godemin nina fadamiki insha Allah* *Note magungunan mu ingantattune basu da side effects kokad'an anyisu da ingantattun* *magunguna sosai* *Location Gombe munaturawa ko ina 08030861857* *Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.* *09069067488* Ko gani bana yi haka na fad'a kan gado yaraf kamar kayan wanki. tunanina ba shi a tare dani ya tafi wani waje mai nisa na tunanin yadda zan iya kara zaman aure da Ishaq..?tuna Engr kawai in nayi sai naji gabana ya amsa kaina da zuciyata suna amsa kuwwar Rugugi a lokaci daya. Tsakani ga Allah ina son Engr a lokacin da ban sani ba,na fara son shi batare da na sani ba,Sai dai na amince da kyawawan hallayarsa da barkwancinsa da kuma yadda yake sona batare da shi ya yi tunanin alfarma ya yi min ba,shiyasa na ba shi amanar duka rayuwata gabadaya. Saboda Tsabar Rudanin da na shiga har bansan ana ta kiran wayata ba sai da Hafsatu ta shigo ta kawo min nata wayar tana fadin"Yaya Asiya ce tace tana ta kiran wayarki baki dauka ba" Idanuwana har sun yi ciki ciki Tsabar Tashin Hankali na mike a kasalance zaune kan gado ko Hijabin jikina ban nemi cirewa ba, na karbi wayar ina gani tana kallo na kasa kasa nazarina take yi ganin yanayina,ammh bata ce komai ba ta juya ta fice ta bar min Daki. A amsa kuwwa na saka wayar kamar yadda na saba,Sallama nayi Yaya Asiya ta amsa muka gaisa kamar yadda muka saba jin muryata a chunkushe yasa tace"Ya na ji muryan ki ta yi ciki ne ko Mura kike yi..? Na rasa amsar da zan bata sai nace"Uhm' Sai ta min fatan samun sauki kafin ta zarce da fadin"Ashe kuma zaki koma gidan mijin ki Fa'iza naji dad'i wlh. Gwara ki koma ko Saboda yaranki" Wani irin Dum!naji a tsakar kaina nama kasa mgana saboda bakina ya yi nauyi sosai kamar ma miyau ya kasa tsirgamin saboda yadda naji harshe na ya nad'e waje daya. Ina jinta tacigaba da fad'in"Gwara da kika yi wannan tunanin Fa'i komai lalacewar Ishaq dan'uwanki ne kuma akwai zuru'a a tsakanin ku,tunda kuma yayi nadama kema ai kin kwatarma kanki yanci na tabbata kika koma kina da Darajan ki" Ni da yake ma ko Goggo bata fadamin ba Gidan Halisa naje jiya kinsan ta kara samun bari Anty Binta ta kirani tace naje na dubata, ita ke min zencen daga gani suma sun ji dadin komawar da zaki yi,Da farko mamaki nayi tunda ban san mganar ba sai da na Kira Mariya tace itama haka taji baku yi mgana a waya ba dai gaskiya" "Uhm" kawai na samu kaina da Fadi Saboda yadda harshe na ya Nad'e waje daya,mgana ta cigaba yi tana tunamin manufa da alherin komawa gidan Ishaq jin yanayina yasa bata neme ni da wata mgana ba. muka yi sallama na rude zufa kawai nake yi kenan mgana ma ta shiga bakin yan'uwa ban sani ba..? Zufa ya jikamin jiki tunda ga Hijabi na har jikina, Tsabar shiga wani yanayi,kenan har su Goggo suma sun ji labari ni ina nan bansani ba..? Dole na zare Hijabin jikina ina Fifita da shi zufa har kasan wuyana,sai lokacin na tashi na Dauko wayata kira ne ba adadi kuma nasan duk na Engr ne domin tun safe da shi nake fara mgana. Wayar na hannuna ina Tunanin kiransa ammh kuma kamar an hanani saboda ina ganin ban kyauta ba in na cigaba da yaudaransa,kila ni tawa kaddaran kenan yin aure har Abada batare da naji dadin auran ba. Zama nayi na tasa wayar a gabana ina gani Engr na kira ammh na kasa Dauka Idanuwana suka cika da kwallah Hirarmu na dawomin a cikin kaina bansan Lokacin da naji hawaye sun cikamin ido ba a fili na Furta"Allah Sarki Tosin" Kiransa na katsewa sai ga kiran Badariya sai da gabana ya fadi daman mun kwana Biyu bamu yi mgana ba. kamar bazan dauka ba saboda nima bana cikin yanayi mai Dad'i sai dai na Daga kiran Tuna fa Badariya ce. Ina Dauka sai jin guda nayi a cikin kunnuwana sai da na matsar da wayar Cikin Ihun murna tace"Lalle Anty Fa'iza irin wannan kome na ban mamaki ba Labari.? Wayata ta lalace tun last week Mama ta fad'amin da muka yi waya sai yanzu nan Yusuf ya kawo min sabuwa ina saka layi ke na fara kira. Ina murna Anty Fa'iza yayan dai nawa In sha Allahu" Salati na saki a raina kafin naji na tsinke da al'amarin itama kenan taji Labari,ni dai bayan Badariya na amsa wayoyin mutane da dama ciki har da Anty Fadila a bakinta nake jin har kayan dakina da ita akaje aka siyo an gama shiri dawowata kawai ake jira naji ina kuka ne batare da nasan hawaye na fitomin ba Anty Fadila na fad'amin irin murnan da su Anum suke yi zan dawo har a makaranta sun gayama yan ajinsu, suma Umman su zata dawo hatta da Zainab da Mama suna farinciki da dawowata,har muka gama waya hawaye nake ina sharewa a matsayina na uwa ban isa na Karya ma ya'yana zuciya ba. Zan koma ma Yaya Ishaq ba domin ina son shi ba sai domin Ya'yana da Farincikin su,bazan iya karya musu zuciya a karo na biyu ba,barin ma da Na kira jamal saboda shima naga kiransa shima zencen yake yi min,jikina bai kara saki ba sai da yace a wayar wani dan ajin su Amir shi Amir din ya ara ya kirasa ya fad'amai haka na zauna na hada kai da gwiwa ina ta kuka kamar raina zai fita,kukan rasa wani abu da nake so kuma ya yi min nisa. Kamar kuma yan gidan sun sani ba wanda ya nemeni da Hafsatu tazo karban wayata baya na juya bata ma ga Halin da nake ciki ba,bakin kowa sai dai yace na koma ma Ishaq Saboda yarana ba wanda ke tunanin shin in na koma zan samu Farinciki ko bazan samu ba..?meyasa mata da dama ake kokarin Danne musu hakki Saboda yara da an yi mgana sai ace ki koma Saboda yaran ki babu wanda ke tunanin ya mace zata yi in ta koma..?Shin zata yi farinciki..?ko zata Dauwama cikin kunci Allah Sarki Uwa uwa itace wacce zata Sadaukar da Duka Farincikinta Saboda Farincikin ya'yanta. in dai ko hakane naji zan Sadaukar da farincikina saboda Farincikin ya'yana na. Na Tsaida mgana zan koma gidan Yaya Ishaq saboda yarana Engr kuma bansan ya zan yi da shi ba,Sai dai ko sunan shi na tuna sai naji kuka yazo min na san yana sona ya zai yi in nace na fasa auran sa..?wlh da nasan hakane da tun farko ban basa Dama ba da tun farko ban karya masa zuciya ba. Ammi bata a gida diyar kawarta ta haihu sun je barka,shiyasa na yini a Daki ina kuka Engr ya kira har ya gaji yayi sakonnin ammh saboda na riga na yanke hukunci yasa ban bude Sakon ba,Ina son na bama kaina karfun gwiwa abincin ranar bai shiga Cikina ba sai ruwan Tea sai yammah