← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 170 OF 175

Sashe 170

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ma Badariya Labarin Halisa ba Dad'in ji Yaya Asiya ta fad'amin miji duk ya saida kayan dakin Halisa tunda Dila me na yan kwaya yana sha kuma yana Saida ita. An taba ma kamasa dakyar aka sake shi Fad'a kuma ya kacame tsakanin Anty Binta da ya'yan Hajiyan Dala akan tace ai susan halinsa suka yi shuru ya auri yarta,Fada har da Gore gore,A raina nace Dara taci gida. Kafin Engr yazo ya Daukeni sai da Yaya Asiya ta rakani gidan Halisa ya ma saida wannan gidan sun koma gidan Haya,wajen su goma agidan daki Ciki daya Halisa har sai nayi mata kwallah Rayuwa kenan,da zamu tafi Dubu biyar na bata ta amsa tana ta min godiya muka fita muna Tausayamata. Ranar yawo muka sha agari mune har Shoprite ba inda bai kaini ba sai Dare muka dawo,washegari muka tafi Dutse gidan Nana Fatima,mun ko ga Tarba Nana Fatima tayi zencen sauyawata har sai da nagaji har addu'a ta rika yi Allah yasa ciki gareni. ni kuma in mata Dariya Engr ma ya hade da mijinta suna ta shan Hira abun su agidan muka kwana Barayin megidan suka barmana mu da zamu yi kwana daya sai gamu mun yi biyu. Ranar yawo muka fita cin abinci mu da su da yaran sai dare muka Dawo sai washegari muka koma kano a ranar muka bi Jirgin Dare zuwa kaduna. Gidammu muka sauka bamu kira kowa ba,Saboda muna cikin gajiya sai da muka yini muka kwana sannan mukaje gida. Sai dai su Abba suka ganmu kamar Daga sama,Ammi sai da ta Rumgumeni ita da su Hafsatu suna ta min Ihun wai na zama kamar black american. Nan Engr ya barni sai Dare yazo ya Daukeni tunda sun ma fita tare da Abba ne,da zamu tafi Abba nata sakamin albarka ko bai Fada ba nasan yaji Dadin ganina ahaka. Engr hutunsa ya kare zai koma bakin aikinsa sai yace zamu je Karofi mu gaida su Goggo,daganan Abuja zamu tafi chan zai barni ya koma Edo in ya Sake dawowa sai mu koma tare. Haka ko akayi sati daya muka yi muna Hutawa a kaduna na sake Dibar wasu kaya tare da Hafsatu da Nana Khadija muka tafi sun gama jarabawa har sun samu hutu. Arana daya mukaje karofi muka Dawo,Inno daman tana Karofi cham muka sameta,mun je har gidan Yaya Mariya sannan mun shiga Dutsemah gidan da Tamadina tayi aure Engr ya yi musu Kyauta,daganan mun shiga katsina har gidan Hajiya na kai mata Engr ta gansa tana ta Saka albarka,ban manta da makotana ba Sa'adatu da Habiba na kuma saka Engr yayi musu alheri suma suna ta Mgaanan na sauya na zama kamar bani ba. A katsinan muka kwana Hotel ya kama mana washegari muka Dauki Hanyar Abuja a mota,daga ma'aikatansu na kaduna aka bamu mota da Direba,gidan su Papa muka Fara sauka sai Dare muka karisa gidanmu su Hafsah ganin su kafaya suka ce nan zasu kwana Maa tace a barsu muka rabu suna ta godiya da Tsaraba. Engr yaji dadin zaman su gidan su Papa yace gwara su bar shi yayi kara'in bankwana aivko ya yi. kwana Biyun nan mun yi soyayya kamar bazamu kara had'uwa ba. Ranar lahadi ya Hau jirgi zuwa Benin,ya barni cike da kewarsa ba domin Su Hafsah ba da na sha kewa ko da yake ga su Kafayatu. Sai da gajiya ta sakeni na samu sararin kiran mutane muna gaisawa. *Janafty* [8/2, 7:21 PM] Hauwa Galadima: *KNKB3020* *Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.* *09069067488* *Prologue* *Ina rubuta muku wannan shafin alhinin kewarku da zan yi*. Na gode wa Allah da ya haska mini wannan labarin*. *Na kuma gode muku. Dan haka wannan shafin kacokan sadaukar wa me ga duk wacce ta saka ku'dinta ta siya. Na gode, Allah ya saka da alheri*. *Sai mun sake haduwa a sabuwar tafiya nan ba da jimawa ba*. *Janafty tana muku albishiri din bayan Faiza ta kau ce, Yabi zata bakunce ku nan ba da jimawa ba, cikin littafin BAK'AR TA'ADAH*. *Son so fisabidillahi* Tafiyar Engr Edo ta dauke sa kimanin Sati uku da wasu kwanaki ne sannan ya dawo. lokacin su Hafsatu sun gama min Hutun su. Sati uku suka yi min sannan suka koma saboda an koma makaranta har ga Allah naji dadin Hutun su a wajena tun ballatana ga su Kafayatu da suka saba da su watarana duk gidana ma suke kwana, A taru ayi ta Hira ana dariya Su hafsa na son koyon yarbanci su kuma suna son iya Hausa sosai Diramansu ma abun dariya ne. Engr kudi ya turomin masu yawa tun yana chan muka je nayi musu shooping kamar yadda yace haka ma Papa ya bada kudad'e yace aje kasuwa su dauki duk abunda suke so. Maa ma ba'a barta a baya ba. dukkansu kowacce da akwatinta shake da Sabbin kaya da kayan amfani sai wanda ya gani. Sannan Direba ya kai su har gida sannan ya juyo Abba da Ammi sun kira suna ta fad'an Hidima tayi yawa nace ba ruwana Aikin Engr ne tunda nace haka sai na kashe bakin su. Sanda ya dawo na fad'amai abunda su Abba suka ce dariya kawai ya yi kafin yace"kyaleni da Rigimammen baban nan naki. ya kirani zai fara mganarsa nace ni sisters d'ina nayi ma alheri ko Haramin ne..? Ai daganan bai kara mgana ba nasan mganinsa" Tsungulinsa nayi ina fadin"Uban nawa..?sai da ya yi wata dariya kafin yace"Nima ai Ubana ne. Tunda ya bani ke ammh wani lokacin ki kauda idanuwan ki bayan Uba shi abokin aikina ne" Dariya kawai nayi ban ce masa komai ba tunda nasan gaskiya ya fada tare na gansu kuma ban isa nasan Tsakanin su ba. Sati Daya ya yi min ya koma,yaso ma mu koma tare zuwan Hajiya Kudirat Abuja yasa ya barni. bamu tafi tare ba yace sai in dan ya dawo. Shiyasa gudun zaman shuru na kan je gidan su Papa na yini watarana har kwana ma ina yi Hajiya Kudirat ne ta tsawatarmin akan na rika zama agidan mijina yau da gobe sai naga na Saba,jin haka yasa sai Papa yace su Kafayatu su bini in Oluwatosin ya dawo sai su dawo gida hakan sai ya ragemin zaman kadaici tunda muna tare da su basa dai yini a gida ne suna makaranta sai weekend wani Lokacin ma Ranar Lahadi ne kadai suke gida. ammh tunda muna kwana tare a kallah dai nasan akwai mutane a kusa dani,kuma a baya nasan na yi zaman kadaici ammh lokacin akwai yara suna Debemin kewa yanzu ko bayan kewar mijina har da ta yara ina yi kuma ko da yaushe cikin Tambayar Zainab nake yi yaushe zasu samu hutu Saboda ina so suzo su yi min Hutun su awajena. A na cikin haka sai ga wayar Badariya daman na jima bana samunta a way a tun sanda muka dawo in na kirata wayarta a kashe nayi ta Damuwa har sai da na fad'ama Engr sai yace mu mata mun cika raggon azanci meyasan bantaba karban lambar mijinta ba..?Da sai na kirasa naji ko lafiya sai da ya fad'a naga gaskiyansa kuma ban taba wannan tunanin ba shiyasa akace mu mata karkatattu ne duk ta inda aka gyaro mu sai mun sake karkacewa. Lokacin da naga kiranta da Zumudi'na na amsa kiran sai dai yanayin da na jita ya fad'armin da gaba cikin damuwa bata budemin komai ba kawai tambayata tayi ina ina..?Nace mata ina Abuja sai ta nemi da in turo mata address din ta manta Dakyar ta iya kawo kanta. Ban rike anguwan da kwatancen ba Sharifatu na bama ta rubuta mata duk sai jikina ya yi sanyi da na kara tambayan ta meke faruwa muryanta a matukar Shake tace min"Zamu yi mgana Anty Fa'iza in da na zo" Sai na kyaleta har tazo din,har ga Allah na zata ba ta saka ranar Tafiyar ba,ban dauka da wuri haka ba sai dai a daran da misalin Tara na Dare sai ga Badariya cikin wani yanayi mara Dadin ji da gani tazo a galabaice saboda Tafiyar mota tana ta faman amai ga jikinta da zazzabi. Na rude sosai da ganin yanayinta Fadi nake yi"Badariya lafiya..? Ko wani abu ne ya samu Yusuf din..? Duk bata bani amsa ba tana cikin wani yanayi,tsabar na rude ma na rasa taimakon da zan bata sai su kafaya ne sukace bari su kira Family Doctor din su yazo ya dubata jin haka yasa na samu Tunanin kaita Dakina na taimaka mata tayi wanka,sai rawan Sanyi take yi hakoranta na Haduwa waje daya ga shi ta rame ammh naga ta kara fari kumatunta sun cika sosai. Suna ko kiransa ba jimawa sai ga shi yazo ya dubata sai ya Dibi jininta yace da safe zai kawo Result bai bata mgani ba allura kadai ya yi mata Sai Drip da ya saka mata ta samu barci,haka na ta sata ina kallonta Lokaci daya na zabga tagumi. Engr ranar yasan ba na cikin sukuni Tunda ka'idan kafin na kwanta nakan kirasa,mu yi bamkwana yaga ban kirasa ba kuma ya kirani ban dauka ba Allah nagani ban ma ji kiran ba wayar na inda na idar da sallar Isha'i. Sai ya kira Sharifa itace ta fad'amai nayi bakuwa tazo ba lafiya. Sai yace ta kawomin wayar ta wayarta ne muka yi mgana na fadamasa Badariya ce ga kuma Halin da tazomin cikin damuwa. Sai ya shiga lallashina da irin tausasan kalamansa. Hankalina tashe nace"Abunda ke damuna ina mijinta yake da ya barta ta yi doguwar tafiya ita Kad'ai? Engr yace"Allah masani kuma ga shi ba lambar shi mijin ballatana akira aji ko lafiya" Kai tsaye nace"Sai dai in wayarta.Gata nan a hannuna" Engr ya yi shuru kafin yace"ko kuma ki bari ta farka sai ki fara jin ta bakinta kada mu yi gaggawa" Da haka ya samu ya lallasheni da zamu yi sallama yace"Kada ki damu zata farka cikin lafiya. In kika saka damuwa ina kike so ni kuma na saka kaina Babyna..? Sai ya bani dariya daman Burinsa kenan yaga Dariyata,Kuma daman yasan in yace Bby sai nayi dariya don in yace min haka sai nace"Wata Bby da ya'ya zarata har hudu..? Bby kamar wata Anum.? Shiyasa in ya tashi zolayansa haka yake kirana tun ina jin wani iri har nazo
Chapter 170 · 0% Book details