Sashe 34
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
itama ta taso da Sauri na shiga Tsakaninsu na rike Yaya mariya ina wani irin kuka kamar zan shide cikin Shakewar murya nace"Ki tafi..Ki tafi don Allah yaya mariya ki tafi.." Yaya mariya ta kalleni kafin tace"Zan tafi..ammh ba ni kadai ba tare da ke Fa'iza yau zaki bar ma wannan azzalumin gidansa in kina da amfani in kuma baki da shi zai sani" Sai na Rud'e na kasa mgana ta ja Hannuna keey kamar rakumi da alaqa zuwa Dakina ta fara Hadamin kayana tana yi tana fadin"Kin gama zaman aure in da ba'a san Darajan ki ba..da ikon Allah hakkin ki bazai barsa ba sai Allah ya saka miki" Ni dai na kasa mgana sai uban kuka nake yi,Ta gama had'a min kaya cikin karamar akwatin Amir itama ta Hada nata kayan ta zura hijabi,Nima tace na Dauko Hijabi na saka ganin na kasa tashi yasa ta dauko min ta sakamin tajani,har zuwa Falo yana Tsaye hannayensa goye a bayansa yana Safa da marwa acikin Falon. Yana ganin mu ya saki mirmishi kafin yace"Better..Ni bazan hanaki tafiya da yar'uwanki ba ni dai ban ce ta tafi ba in kuma tabiki wannan ra'ayinta ne sai dai ta sani in dai ta saka ta bar gidan nan to ta Rubuta ta barsa har abada" Yaya mariya tace"To sai me..?ai daman ta bar sa har abada kenan wannan bakin gidan da bakomai cikinsa sai zalunci da mugunta da ikon Allah sai Hakkin Fa'iza ya Bibiyeka" Ya ishaq yace"Sai dai hakkin kashe aure ya Bibiye ki dai..Sakarya wacce bata san inda ke mata ciwo ba..Na dai gama mganata ni dai in dai ta Fita to a bakin auranta sannan har Abada bazata Dawo ba" Yaya mariya ta fincikeni tana fadin"Zaka gani yau kam zaman Fa'iza da kadaddaran auran ku ya kare" Bai damu ba ya koma ya zauna ya Dora kafa d'aya kan d'aya ko ajikinsa,Yaya mariya ta rika jana har kofar Falo cikin Dashewar murya nace"Ban saka takalmi ba yaya mariya" Cikin Fada tace"in mun je tasha na siya miki" Na kara turjewa ina fadin"Yara na..Yaya mariya su Amir fa..?in na tafi wazai kula da su..? Ta juyo tana min wani kallo kafin tace"Ko mutuwa zasu yi sai dai su mutu nan d'in ne gidan Ubansu ke kuma ai ba gidan naki uban ba ne wuce muje.." Ta kara jana naki yarda na Bita na Turje ta juyo ta kara kallona afusace kafim tace"Fa'iza kada ki bari na saka miki Hannu" Na kasa mgana sai kuka ya'yana nake Tunani in na tafi basu da wani Sauran gata bani da mafita sai zabin Dawowa na cigaba da zama acikin yanayin da nake saboda ya'yana. Yaya mariya mamaki ya kara kamata lokacin da na kwace hannuna daga gareta na juya baya ina kuka nace"Ki yi hakuri..Kiyi hakuri..Ki tafi don Allah..BAzan iya tafiya na bar ya'ya na ba" Kiyi hakuri" Sai kawai na kwashi gudu zuwa Cikin D'akina ina kuka kamar raina zai fita kaina har wani bugawa yake yi Dif dif,Yaya mariya ta kasa motsi saboda abunda nayi Ya Ishaq kuma na zaune yana Dariya kasa kasa kafin ya mike yana kallon Yaya mariya cikin gadara yace"Fita ki bar min gida bakar munafuka..Kin dai ji kunya wlh kin kuma yi asara..Yar'uwan naki da kike Hakilo a kanta ta nuna miki baki da wata Daraja sama dani..Sai ki fice min Daga gida kada na kara ganin siraran kafafunki acikin gidana.." Yafad'a yana nuna mata hannun alamun ta fice ta bar mai gida Takaici da bakinciki yasa Yaya mariya Zubar kwallah ta kalle shi ta kara kallonsa kafin tace"Naji kayi nasara a kaina zan tafi..kamar yadda ka bukata bazan kara zuwa gidan ka ba..Sannan mganar Fa'iza karyan ka ta sha karya ai jini yafi ruwa kauri sannan wata kusan tafi wata..Zan cigaba da zumumci da yar'uwata domin ba kai ka Had'amu ba..Mgana ta karshe shine akwai Allah kuma yana nan a madakata Duk abunda kake aikata ma Fa'iza na sharri da zalunci kai da Mahaifiyarka da yayarka,Da ikon Allah sai kunga sakkaya tun a duniya sai Allah ya jarabceka da iftila'in da sai ka rasa ina zaka saka kanka in sha Allahu sai Allah ya saukar da aya akan maza ire iren ka da basu darajan matan su sannan basa adalci ya yin zamantakewar su,Kuma kada ka manta akwai Hakkin zumunci shima sai Allah ya tambaye ka, sannan hakkin Fa'iza bazai barka kayi rayuwar da kake Buri ba Ishaq Kabir karofi." Tana gama fad'in haka ta Sauke karamin akwatin na data Dauka,ta juya ta fice tana zubar da hawayen bakinciki da takaici duk da kalamanta sun Dakesa ammh bai damu ba ya Bita har get yana gayamata bakaken mganganu sannan ya Dawo Cikin gida ya Iskoni har dak'i yana gayamin duk mganar da ta fito bakinsa har yana fadim Tunda ya aureni bai Huta ba yake cikin Matsala ni ba matar kirki bace ni matar Tsiya ce. Nayi kuka,kukan da ban taba yi ba,kukan yadda ya tozarta yar'uwata ni ban damu da kaina ba Daman ni bani da wata Daraja ammh Yaya mariya fa..?yar'uwata ce bata chanchanci cin zarafi da tozarci ba. In da nagode ma Allah Yaran basu dawo daga makaranta ba,da suna gidan nan ban san wani amsa zan basu ba ina kwance ina kuka suka Shigo,Ganin su yasa nayi saurin share hawayena kaina ciwo yake yi duk yadda yaran suka so su fahimci wani abu ban basu dama ba da Amir ya dameni da Umma baki da lafiya ne..?naga fuskarki ta kumbura ne" Sai nace masa wani abu ne ya fadamin a ido,Nasan inda Ya Ishaq ya mareni ne ya tasa sannan ga kuma kukan da na sha. Tuni Ya Ishaq ya fice daga gidan na rarrafa na shiga kitchen na Dafa ma su Amir Jallop din taliya,kunyar kaina nake ji da abunda ya faru ace mijina shi ya tozarta yar'uwata da muka fito ciki d'aya uwa daya uba daya,Abun sai ya tsayamin a cikin raina ya kasa wucewa su kansu yaran su san yanayina ya sauya,suna mgana sai dai na bisu da ido kawai da wuri nayi musu shirin kwanciya Saboda ban jin Dadin jikina,Kamar kazar da kwai ya fashe ma aciki haka jikina ya koma,Kayana da Yaya mariya ta hada ni na kwaso su na maida su muhallinsu araina ina Tunanin Lokaci bai yi ba.lokacin da zan bar Rayuwar Ishaq bai yi ba akwai sauran Lokaci. Ina D'akina zaune ina kuka ni kadai ina sharan hawaye na Ya Ishaq ya shigo Fuskarsa ba Fara'a,Ina ganinsa na Dago kawai ina kallonsa ina jiran naji dame kazo Saboda nasan wani Sabon Tozarci ne ilai cewa yayi gobe geben nan nasan yadda zan yi na karbo masa D'ansa kafin raina ya baci. Jikina na rawa cikin rawan murya nace"Goggo ce ta karb'esa fa..?Sai naje nace ta dawo dashi..? Cikin Tsawa yace"Ina ruwana da wata Goggo..Mama ce..?nace Mama ce..? In ba munafunci kika so ba, meyasa baki aika ma Mama shi ta yayesa ba..? To wa ma yace ki yayesa batare da kin Fad'amin ba..? Kaina na kasa nace"Saboda bani da lafiya ne ina asibiti da kuma na Dawo sai yak'i karb'an Nono sai na yayesa kuma Goggo Saboda Tausayina yasa ta tafi dashi fa" Karamim Tsaki yaja yana fadin"Kedai kika sani na riga na gaama mgana wlh in gobe da yammah tayi Ahmad bai Dawo gida ba sai na Wulakantaki Fa'iza" Haka ya fice ya barni ina kuka,ina jin wani daci na tasomin a kasan raina ciwo nayi ba sannu ba Tausasawa ba Lallabawa sai tozarci da cin mutumci ya Allah ga baiwar ka Fa'iza ka bata mafita D'aya daga cikin mafitan da ka ke bama Bayinka salihai. Adaran nan barci sai dai barawo ya iya Sace ni da Safe kuma da zazzabi da ciwon kai na tashi su Amir na da Hadda Dakyar na iya musu shiri da abun karyawan su,To basu samu ma tafiya makarantar ba Haruna adaidatan sa ya samu matsala Babansu kuma ko motsinsa ban ji ba,Ballatana na saka ran zai kai su,Sai kawai nace su tube kaya su bari sai gobe sai fadi suke Daada bazai kai mu ba nayi musu shuru kawai ina ji Anum ta je tana ta Buga kofar Shashensa tana kiran sunansa Ammh har tagaji bai fito ba. Sai daga baya da Amir yaja su suka fara wasa ita da Musty sai ta manta ammh da farko har ta fara kukan ta na rigima.. Ni ko kwata kwata hankalina baya jikina Tunani nake yadda Ahmad zai Dawo kafin yammah tayi nasan duk abunda yace zai aikata ammh na gwammace ni na tozarta da na iya cema Goggo ta Dawomin da Ahmad bazan iya ba Har abada bazan iya ba. Ranar ko girkin rana ban yi ba gari na jika musu suka sha,Nima ba na wani jin Dadi sai da na sha Panadol cikin mganguna na hawan jini kuma yana da karfi sai Dare nake shan sa. Bani da masaniyar Ya Ishaq na gidan ko baya gidan,Bayan la'asar ina Dakina na idar da sallah su Amir suna Haraban gida suna wasa dakyar na saka su suka dawo cikin gida suka yi sallah wasa na ransu suka koma suka cigaba da yi. Tashin mgana na rika ji afalo lokaci d'aya da kiran sunana zubur na mike jin kiran sunana kuma Muryan Mama nake ji tana tsagamin kira da karfi kamar zata tsaga gidan. Na fito da Sauri muka kusa cin karo da Anty Binta ina shirin gaisheta ta bangaje ni ta shige Mama na Tsaye tana Karkad'a jiki kamar wata mazari Cikin Daga murya tace"Shiga ki fito mata da kayanta jiya bata bi Yar'uwanta ba yau kuma zata bita Daga baya fito mata da kayanta yau in dai ba gidan Sidi da tamadina bane sai Fa"iza ta barmin gidan D'ana" Hankalina ya tashi jikina ya fara rawa na karisa gaban Mama na zube ina gaisheta bata amsa ni ba ta fito da wayarta ta kira,naji dai tana fadin gasu sun kariso daganan ta kashe wayarta ta koma ta zauna tana kad'a kafa Anty Binta kuma ta rika kwasomin kayana ta na min watsi da su a tsakiyar falo na zama mutum mutum na kasa mgana har Ya Ishaq ya fito Daga bangaransa yana sanye da Jallabiya ko barayina bai kallah ba ya isa ga Mama suka gaisa.