← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 175

Sashe 22

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yammah muka koma gida bayan ni da Hafsah mun zage mun gyara gidan Mama tas sannan Anty Binta ta bani key din gidan na Tattara duka ya'yana muka koma gidana Hafsha kuma nace ta bari sai washegari sai ta tafi." *Littafin KANA NAKA book 2,3 paid book ne biya kudin karatun ki akan Naira N500 Regular posting sau d'aya a rana.* *Ko kuma tsarin VIP 1000 Posting sau biyu a rana akan wannan acct din 0552179550 Jamila Umar Gt bank,sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488 Wannan karon babu tsarin kati,kowani tsari zaka yi ka turo ta POS,Mutanen mu na Niger kuma zaku tuntubi Kausar Aglan Nissa ta wannan lambar +22796562223* *Janafty**KANA NAKA..!* *Wattpad:JamilaUmar315* *Mallakar:Janafty* *Arewa book:Jamilaumarjanafty* *Nagode sosai da addu'o'in ku ga kawu Madalla da ku naji dad'i Allah ya amsa, shi kuma kawu Allah ya jaddada rahma a kabarinsa Ameen summa Ameen.* MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT Y'A SKWATO__SAKINA HASSAN 08066726866 INA MATA Y'AN KWALISA MASU SON GYARAN JIKI MACCE DA TASAN KANTA KULLUM CIKIN GYARA TAKE INA MATA MASU FAMA DA RAMA KU KINSA KAYA BASU KAMA JIKIN KI INA MATAR DA ADDA JIKI BAKI DA HIP BAKIDA BAYA IN KINYI DRESS BAYANKI A SHAFE INA WADDA KE FAMA DA ZUBEWA NONO KU KE BAKI JIN DADIN GANIN SU KAMAR SILIFAS KINYI TA GYARAN BRST HAR KIN GAJI HJY TA GYARAN BRST WAHALA GARESHI DUK WADDA TACE MIKI GA MAGANIN BRST DA SHA ZAIYI TO KARYA TAFADA MIKI GYARAN BRST YANA SON JUREWA DA DAGEWA IN KIN FARA BA'A TSAYAWA INSHA ALLAH SAI KIGA SUN ZAMA NORMAL MUNA DA INGANTATA ZUMA BRST DA MUNKA SARRAFA DA KAYAN ORGANIC HERBAL SU MACA DASU AGUAJE WADDA INDAI KIN RIKE TA INSHA ALLAH ZAKI GA SUN CIKO SUNYI KOSHI RUBA 2 KU 3 SUN ISA YAZAMA MIKI YADDA KK SO 4K MUNA DA GARIN HIP DA BRST YAKE GYARA DA GYARAN JIKI DA KARIN NIIMA YAKE YI 4K MUNA DA INGANTATA ZUMA TA HIP ITA MA MUN SARRAFA TA DA KNGAN TATUN KAYAN ORGANIC HERBAL DA KE FIDDA MIKI HIP 6K MUNA DA ZUMA KIBA WADDA ZAKIYI FRESH DA BULBUL ITAMA RUBA 2 KU 3 ZATA YIMIKI YADDA KK SO 2K MUNA DA GARIN GYARAN BRST DA KARIN NIIMA SHIMA GUDA 2 KU 3 ZAKI SHA 2K GASKIYA DA AMANA ITACE NASARAR.MU MUNA AIKA KAYA KU INA CIKIN YARDA DA AMINCI MMN MUJAHID __SAKINA HASSAN MUNA SOKOTO DA KEBBI 08066726866 Da muka koma gida na zame jikina na shige daki nayi kuka na rarrashi kaina daga baya ranar ban yi moruwa ba ina kwance acikin d'aki ina Tunanin makomar rayuwata,Yaran suna tare da Hafsatu har ta ko da Ahmad Amir ne ya dame ta da Ina Umma sai tace na kwanta bana jin dad'i ne tunda taga yanayi na. Ita ta yi musu girki cikin sauran k'wayanim taliyan da suka rage mana ta dafa sai ta dib'i Tumatir din nan Tafashasshe tayi miya da shi suka ci ta zubomin nace ta dauke sa bazan iya saka wani abu aciki na ba. Tare da yaran suka yi ta burumtun su afalo ina jin su kafin ta yi musu shirin barci ta rakasu d'aki suka kwanta Ahmad kuma tayi mai wanka sannan ta kawo min shi ya fara rigima na bashi Nono sai yayi barci ni kuma na Rarrafa na tashi na yi alwala nayi Sallar mangariba da isha'in da kasalan Rayuwa ya danne ni na kasa tashi. Washegari tun safe Hafsah ta shirya bayan su Amir sun tafi makaranta Haruna mai adaidaita na roka ya kaita inda ta hau motar Karofi,ta barni Dagani sai halina acikin gidan da bansan makomata ba. Tun kuma bayan tafiyarta ban karaji Daga kowa ba hatta Yaya Asiya bata kirani ba Daman goggo nasam tayi Fushi ga abunda kuma daman ya sake Faruwa nasan tun kafin su Anty Nasara su koma Yaya mariya taje mata da Labarin komai. Harta bangaran su Maman ba wanda ya kara nema na ballatana ace bari a kaga Halin da nake ciki ni da ya'ya to wanda ma Hakkinsa ke kan mu ai bai Damu damu ba ballatana wani ya nuna Damuwarsa a kanmu. Tunda bayan auran Ya ishaq da Abar kaunarsa ban kara jinsa ba bai kirani ba kuma bai min sakon kudi ba an wayi gari bani da ko sisi a hannuna. Na shiga damuwa ga shi kayan abinci duk sun kare daga shinkafa sai sauran Taliya ta ragemin Indomie ta kare saboda ina dafa musu sau biyu a sati suna tafiya da shi a makaranta sau ukun kuma na dafa musu taliya Ranakun Hadda kuma sai na Dafa musu shinkafa,Doya da Dankali Sun kare kwai daman kires daya yake siya nama daman ba Cefanen sa ba ne sai in yana gari ne yakan siya in baya gari kuma sai abunda ya zama Dole a garesa. Lemun yara na makaranta ya kare harda kayan Tea komai ya kare, sauran maltinan da ya siya tun wanchan dawowar na rika basu suna tafiya itama tazo ta kare na koma Hada musu biskit guda biyu suna tafiya da shi Saboda makaranta sai uku ake tashi ana kuma tashi akwai islamiya ana shiga,asabar da Lahadi kuma Tahfez duk makaranta D'ayace sai biyar suke shigowa gida akwai yunwa da gajiya ga yara kanana tunda su basu wayon su fahimci babu ba ballatana su yi hakuri. Sati biyu da auran Ya Ishaq Dubarata gabad'aya ya kare na zauna nayi lissafin zama a haka bazai haifarmin da D'a mai ido ba dole na mike na nemi sana'a ba domin ni kaina ba sai Domin Ya'yana su Dogara dani. Na fara Tunanin sana'ar da zan yi sai komai ya kwancemin me na iya..? Babu abunda na iya sai girke girke shi kuma in ba aikatau zani nayi ko agidajen mutane ko gidajen masu abinci na kan hanya bansan ina zani ba Kuma in wannan ne Ya Ishaq bazai taba barina ba ko ma ya barni Mama sai ta Dakile duk wani abu indai na Cigaba ne Daga bangarena. Nagama Tunanin ko na samu sana'ar da zan yi ai bani da jari shima din wata mganace mai zaman kanta sai na Saki wannan Tunanin na fara Tunanin yadda zamu kwashe da Anum gobe litini in zasu tafi makaranta bana jin Amir shi ya fi Anum natsuwa ita kam sai a hankali ita da Mutsy tunda yara ne kanana a kan Amir din. Tun da na tashi a sukuku na dinga yin musu komai inda Allah ya taimakeni tun wannan kayan miyan da su Yaya Asiya suka zo min dashi nayi miya dashi sauran kuma na sakashi cikin karamin Fridge d'ina shi nake diba kad'an kada'n ina amfani dashi Taliya ta kare itama sai na Dafa musu farar shinkafa da miya na zuba musu kowannen a basket din su bani da biskit ba lemu ballatana na Had'a musu da shi kamar yadda suka saba. Ni da kaina na zauna ina goye da Ahmad da yaki kwanciya sai rigima yake yi,kamar ya tashi da zawon hakori ne jikinsa duk ya saki,Haka na rika bama Anum da Musty abinci nan a baki Amir kuma yana ci da kansa bayan sun gama rigima bai tashi ba sai da Anum ta duba basket din ta ba Biskit ba lemu sai ta fasa kuka ina zaune ina kallonta baki na sake kawai ina kallonta a kasan raina naji bacin rai kawai yana taso min daman ina jin Haushi yadda Anum ta koyi shagwabar banza abu kadan za'ayi mata sai kawai ta fashe da kuka wani Lokacin har da birgima. Mikewa nayi dakyar bata sani ba sai dai kawai taji saukan mari sai tayi tsit na kalleta raina a bace cikin fada nace"Ki ka ka..ra..min kukan banza anan sai nayi miki dukan tsiya zan baki Babu ne Saudatu..?. Na kirata da ainihin sunanta sai ta kasa mgana ta koma ta zauna ana son kara fashewa da kuka tana jin tsoro Amir da Musty sai suka tsorata suka koma suka lafe a zaune idanuwansu ya ciko da kwallah ganin yanayin su sai Tausayin su da tausayin kaina ya kamani na koma na zauna na jawo Anum jikina na Rumgume ina share mata Hawaye. Ta lafe ajikina tana sauke numfashi sai na Fahimci yara irin su Anum basa bukatar tsawa ko fad'a ko Duka a jasu ajiki sannan a lallashe su cikin yanayin mganata na fara lallashin ta ina fadin"Anum biskit din ku ya kare da lemu kuma bani da kudi ki yi hakuri ku tafi in na samu zan siya muku." Ta dago idanuwanta da alamun kuka tace"Umma Daada fa ya na ina..? Sai na kasa bata amsa Amir ne yace"Daada na Abuja" Mamakin sa ya kamani a ina yaji Babansu na Abuja wata zuciyar ta fadamin zai iya sani ai baban nasu na zauna yayi hira da su kamar manyan yara. Ni dai na samu na Lallashe su suka tafi hakanan na dawo na zauna tayi Tagumi ina tunanin in yau sun hakura gobe fa..? Ko Badariya da kan lekomu lokaci bayan Lokaci itama shuru naji ta ni ba kudi a waya ba ballatana na kirata,Ina gane lambar kowa saboda da ajami na Rubuta na iya rubutu da Ajamin labarci tunda Hausan ban iya ta sosai ba, ba komai nake ganewa ba. Haka washegari ma Dakyar Anum da Musty suka yarda suka tafi a makaranta ba biskit ba Lemu,na rasa yadda zan yi da su,kuma ko giyan wake na sha bazan taba kiran ya Ishaq nasan sauran abunda zai biyo baya shi da ya ijiyemu bai Tuna damu ba sai nice zan neme sa,ai ko bai neme ni ba sai ya Tuna da ya'yansa ya Tuna da Hakkin kula da komai nasu yana wuyansa ne ammh bai iya tunawa da wannan ba Tunda ya samu Cikar Burinsa bai damu da komai da kowa ba ni tunda ya jingine ni sai ya tuna da ya'yansa tunda su bai jingine su ba. Hakanan na cigaba da lallab'a rayuwata yadda Allah ya tsaramin Tun su Anum na rigima har suka zo suka Hakura,Sai kuma suka fara Damuwa da ina Daada bai taba Sati Hudu bai zo gida ba sai wannan karon in suka tambayeni ina Daada kasa mgana nake yi in suka Dameni sai nace ya kusa dawowa aiki ne yayi masa yawa Ranar da
Chapter 22 · 0% Book details