Sashe 43
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
min in kuma ba alheri aciki Allah ya kawo min wata mafitar ta alheri Ameen. Kafin kayan abincin da Sa'adatu ta kawo mana ya kare ta kawo min Dankali hausa da yawa tace itama daga gida aka aiko mata dashi,Babansu ne ya noma na karb'a na saka albarka shi nakan soya ma yara da Safe su tafi makaranta,Wata rana ma har da rana ina soya mana muci mu sha ruwa,kuma dayake na koyama yarana cin komai duk abunda suka samu zasu ci basa zabar abinci shiyasa sai rayuwar tazo min da Sauki. An yi wata da cike Form din da mukayi ni da Badariya tazo sau d'aya mukayi mgana tace Raliya tace an Tura Tarkadun namu chan kaduna inda Babbar Jibiyar kungiyar take da su zabi wad'anda zasu dauka za'a turo ma kowa ta sakon waya da lambar da ya saka Badariya ta tabbatar min da Hajiyar su Raliya tace ba matsala sai na saka raina asalama araina nace bakin Da Allah ya tsaga bazai taba hanasa abinci ba. Ana haka kwatsam sai ga Ya Ishaq ya Dawo ranar wata asabar da azahar Lokacin bana gida na shiga wajen sa'adatu muna hira to yara in sun tafi makaranta sai ni kadai kamar mayya na da zauna tunani ya kasheni sai nake shiga muna hira tana Debemin kewa rashin dangina akusa dani. Get din a bude na barsa saboda ban yi nisa ba yagaji da Hon ya fita ya Bude ma kansa ya shigar da Motarsa sai da ya shiga gidan ya tabbatar da ba na gidan mamaki ya kamasa ya D'aga waya ya Kira Mama ko nazo Mama tace tafi wata biyu ban zo inda take ba. Ransa ya baci nan da nan ya fara Tunanin haka nake fita ina barin masa gida a bude ina tafiyata gantalin da baisan yaushe na iya ba,Ni kuma ban san ya dawo ba sai biyu da rabi na Dawo gida domin yi ma yara girki,sannan nazo da Guzurin Dambun Dankalin da Sa'adatu ta zubamin mafarin zamana ma yau saboda na koya ne ina so nima watarana nayi lokacin da na shigo Haraban gidan naga Motarsa ban ji tsoro ko fargaba ba Allah na Tuba in da sabo ai yaci na saba da Tozarcin sa a gareni. Kaina Tsaye na shiga cikin gida kamar daman yana jira na ne sai yau ya gwada kiran wayata a kashe duk tsawon Lokacin da ta lalace bai sani ba. Yana ta Safa da marwa a falon ya kasa zama na shigo bayana goye da Ahmad Hannuna Dauke da kwanon Silba da Sa'adatu ta zubomin dambun aciki. 1do hudu muka had'a dashi Sanda na shigo yana bi na da wani kallo na raini kamar yadda ya saba ni kuwa sai na Dauke kaina ina fadin"Sannu da zuwa.." Nafada ina nufar Hanyar Kitchen nasan yayi mamakin yadda nayi mai shiyasa ko taku uku ban yi ba yasha gabana cikin bacin rai yana fadin"Ni kika gani kika dauke kai kamar kin ga Dan'iska Fa"iza? A gajiye na kallesa cikin yanayina nace"Nayi maka sannu da zuwa..ina so na shiga kitchen na sauke abun hanuna ne" Kallo hannuna nawa ya shiga yi Lokaci daya yana fadin"Miye wannan kuma..? Sai na Bude masa ina fadin"Dambun Dankalin Hausa ne na shiga ta koyamin ne saboda ina so nima nayi ma yara" Yamutsa fuska yake yi kamar yaga kashi kafin yace"Wannan bakin abun ne zaki yi ma yarana su ci..?Shiyasa kika bar min gida a bude kika fita yawonki me na sha fada miki..? Ban ce ban amince ki rika fita ko na nan da chan ba indai ba gidan Mama ba..?shine kike so ki nuna min kin isa har kina shigowa kina ganina kika Dauke kai kamar kin ga sa'an ki ko..? Na kallesa da Idanuwana da suka yi ciki ciki ban iya rashin kunya ba Saboda ba Halina ba ne ammh dai naji Tsoro nan nasa da nake ji a baya ya gushe araina na kasa ce mai komai kawai sai na rabasa na wuce kitchen na sauke kayan hannuna a zafafe ya biyo ni yana fadin"Fa'iza ina miki mgana kina wucewa yaushe kika raina ni haka ban sani ba..? Ko tankasa ban yi na sauke kwanon Hannuna ya shigo Kitchen din yana Fadin"Daga gidan uban wa kike..?rokon abinci kika fara na salon zubar min.." Bai karisa mganarsa ba yayi shuru ganin Dankalin hausa zube a kitchen din sannan na bude karamar kular dake saman wajen wanda na soya ma su da Safe ne na rage ma Ahmad in ya tashi daga barci yaci,na dauko na barsa akitchen din yana Dube dube cike da mamaki.. Afalo na zauna akasa na kwanto Ahmad daga bayana da naji motsin tashin sa kamar walkiya sai ga shi a gabana yana fadin"Fa'iza wannan dankalin fa..?sannan naga store ba komai wannan watan mama bata aiko da kayan abincin ku ba ne..? Ahmad na kallonsa ammh sai ya lafe ajikina ba irin zumudin daya saba yi mai a baya ni kuma ban kallesa ba nace"Wannan dankalin shi kad'ai garemu shima daga gidan haruna aka bani kyautarsa kayan abinci kuma ba'a kawo ba" Daga haka na tsuke bakina daga alamu jikinsa yayi sanyi sai ya fara Fadan meyasa ban kirasa na gayamai ba cikin gajiya da korafinsa nace"A ina zan ganka ballatana na fad'a maka..? Kai tsaye yace"Ina wayarki fa ?ko bata da amfani ne da bazaki kirani ba..? Ina bama Ahmad Dankali nace"Bani da waya ta lalace tuntuni" Sai kuma ya kasa mgana,Daganan ya shige bangaransa bansan ko ya kiran Maman ne me tace mai oho yadai fita sai chan kuma ga shi da Cefanen kayan abinci masu yawa wani Lokacin Ya Ishaq bai da matsala ta bangaran hakkin iyalansa da ya'yansa sai dai Mama itace tafi matssala ta wannan bangaran Daga karshe yace na kwashe Dankalin nan na fitar mai dashi nace tab wlh bazan kwashe ba,Kafin yazo ai shine ya Rufamana asiri sai ya kasa mgana nasan yana ta mamakin yadda wannan karon nake iya maida masa mganarsa kai tsaye ni ko gani nayi tunda alfarma yake min nima sai na fara mai alfarma saboda ya'yan da suka hadamu tsakanina da shi ba Domin zumunci da baisan Darajansa ba. Yaran ma da suka dawo ko da suka gansa ba su yi wani D'oki kamar baya ba, shine daya lura da haka ya rika jansu ajiki washegari kuma yace bazasu je hadda ba ya daukesu suka tafi yawo ya siyo musu kayan kwalama da duk abunda suke so,Daganan ya sauke su gidan Mama sai Dare suka dawo ashe sallama yazo yi ma su mama zasu tafi india inda Mahaifin zainab ya dauki nauyin su Saboda aduba lafiyar Farhan sai a daran da suka dawo ya fadamin ban san Dalili ba sai naji ban damu ba nayi masa fatan isa lafiya da kuma samun abunda akaje nema. Washegari Litini ya koma ban ma sani ba ashe ya biya Haruna kudadensa har da na wata biyu anan gaba yana ta basa Hakuri,Harunan ya ke shaidamin washegarin talata da na rako su Amir kofar gida araina sai naji sanyi,in zan fadi gaskiya Yaya Ishaq baya so na ammh kuma yana son ya'yansa kuma bai hadasu da komai ba, sai dai sabon iyalansa sun Dauke masa hankali har akan yara sannan da karin muguntar Mama acikin lamarin tunda ita ake barin ma komai. Ina nan bansan abunda ke faruwa ba Ba mai nema na kuma nima bani da Hanyar neman kowa ashe Tamadina bata da lafiya ta fito daga bandaki ta zame ta fad'i shikenan jikinta yayi nauyi tun tana gida har an kaita asibitin general na bakin asibiti,Har Yaya Asiya dake kano ta sani tazo ammh ni da nake kusa ban sani ba Goggo ganin ba'a samu inda zan ji ba sai ta Kira Mama a waya tace ta fadamin Lokacin Hafsatu suna Jarabawa,bata samun zama shiyasa ma Goggon tace bari ta kira Maman,Tunda Har Yaya mariya sai da tace tazo ta fad'amin tace ma Goggo sai dai tayi Hakuri bazata iya zuwa ba jin haka yasa Goggo bata matsa mata ba. Ita kuma Mama da aka fad'amata washegari yamai ta tafi, diyar Kanwarta ta haihu,kuma abun bai Dameta ba shiyasa sai ta sha'afa. Sai da jikin Tamadina ya kara rikicewa Goggo ta tada Ya Isa tace yazo ya fad'amin nazo in muna da Rabon ganawa da tamadi na tana asibiti bata da lafiya. *Littafin KANA NAKA book2,3.paid book ne biya kudin karatun ki akan Naira N500 Regular posting sau d'aya a rana.* *Ko kuma tsarin VIP 1000 Posting sau biyu a rana akan wannan acct din 0552179550 Jamila Umar Gt bank,sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488 Wannan karon babu tsarin kati,kowani tsari zaka yi ka turo ta POS,Mutanen mu na Niger kuma zaku tuntubi Kausar Aglan Nissa ta wannan lambar +22796562223* *Janafty**KANA NAKA..!* *Wattpad:JamilaUmar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* *TASTED & TRUSTED* *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*. *AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*. *ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWAR ZAKI YI AMFANI DA ITA SAMA DA SAU DAYA.* *AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*. *SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.* *DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*. *SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?* *TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU* *08032773332* *DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*.. Na gigice tare da Dimaucewa lokacin da Yaya Isa yake shaidamin Tamadina bata da lafiya ta kwana uku a asibiti bayan tayi sati a gida ba yadda take. Sai naji na rasa hankalina na wani lokaci, na koma nayi yaraf saman d'aya daga cikin tsofaffin kujerun falona kamar wata kayan wanki. Hawaye nan da nan suka fara sintiri a saman fuskana kamar an bud'e famfo sai yau na kara tabbatar da cewa Mama bata kauna ta kuma har abada baza ta taba so na ba,Uwa ai ta wuce wasa ace a fad'amata rashin lafiya ammh ta gagara aiko ko Badariya ta shaidamin sai da aka gaji da jirana akaji shuru Goggo ta tado mutum tun daga karofi akazo aka fad'amin, kawai tuna hakan da nayi sai naji raunina ya karu na Fashe da kuka Yaya Isa