← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 175

Sashe 16

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

GIMBIYAR KAZA DA SU*. *ABIN BIRGEWA BA SAU DAYA AKE AMFANI DA SHI BA*. *KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR KO KUWA KE DA KANKI ZAKI YI GYARA?* *INA SAKE YIN ALBISHIR DIN GARIN DAKA MAI KYAU DAN CHADI, SHA DA MADARA KO NONO DA KUMA TSUMIN GAMGAM*. *GADALIN MATA AKWAI*. *INA DA TABBACIN INGANCINSU*. *SANNAN WACCE TAKE SON A DAFA MATA KAZAR, ZA'A DAFA*. *TUARAREN WUTA NA ASALIN CHADI AKWIA SU AVAILABLE, SAI KIN GWADA ZAKI BADA LABARINSU* *TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU DOMIN KARIN BAYANI* *08032773332*. *NATION WIDE DELIVERY*. *SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE* Filon da nake kwance akai sai da ya jike saboda hawayena,na kara birginawa ta b'arayin hannun haguna domin hannuna na dama yayi min Tsami sai naji kamar na Danne Gefen Kafafun Ahmad dake kwace gefena da Sauri na mike ina kara gyara mai kwanciyarsa barci yake yi hankalinsa kwance domin akwai haske acikin dakin ban riga na kashe ba ina kallonsa ne ammh a kasan zuciyata fad'i nake shi kam ya huta bai san duk wasu walhalhalun duniya da tashin Hankalin dake cikinta ba. Hawayena har suna d'iga saman cikinsa nayi saurin matsawa ina sharesu da duka hannayena kafafuwna na zuro kasa kafin na dukar da kai na haka kurun nake jin kamar na yi ta rusa kuka da dukkan karfi na,na Dad'e ina so nayi kuka da karfi ammh bansan Kafad'an da kirjin da zan kwanta na rera kuka a lallasheni ba kawai sai na durkushe saman Dadad'den Cafet din dake cikin bedroom dina na fashe da wani marayan kuka hannayena duka biyu na tallafe fuskata da su wani irin kuka ne dake fitar da karar sauti cikin Yanayin da ni ke ciki. Meyasa zan damu don Ya Ishaq yace zai jingine aure na dashi..? Na dauki tsawon Lokaci daman ina jiran ranar da zai auro zab'insa na yi tunanin zan fuskanci tozarci ninki ba ninkin wanda nake karba a wajensa da wajen su Mama ammh bantab'a Tunanin zan fuskancin irin wannan cin Fuskar ba duk da nasan kalaman Baba sune suka yi ma wannan auran nawa tsakani da Ishaq sarka ba domin haka ba Tuni ban kawo lokacin nan acikin gidan sa ba. Menene laifina domin na kasance a yadda Allah yake fatan ya ganni..? Nayi kuka,kukan da ban taba irin sa ba Tun bayan da abubuwan suka fara zame min jiki sai dai wannan kukan nawa ya sha bambam da na kowani Lokaci na yau ina kukan yadda Rayuwata zata kare ne ni da ya'yana. Kwarin gwiwa naji yana shigana irin wanda ban taba ji ba alokacin da wata zuciya ta tunasar dani ni uwace ina da ya'ya bai kamata na zama mai Rauni ba in na Raunana ya'yana suma zasu Raunana in na karfafa nima watarana ya'yana zasu zama karfafa. Nasan Rad'ad'in maraici daga na uba har na uwa Tamadina tana raye ammh ban san Dad'inta ba,bayan Laluranta kaddara tazo ta raba tsakanimu da ita gwara ko wa dani Domin ni kam Ya ishaq ya rabani da kowa nawa ciki da har da uwar data Haifeni. In ni nayi maraici ya'yana bazan bari su yi wannan maraicin ba, zan zame musu komai a wannan rayuwar zan zauna na basu tarbiya sannan na zama Tsani wajen inganta rayuwarsu domin sune Duniyata a yanzu bani da kowa daga Allah sai su sai yan'uwana. Kamar kiftawan ido naji kukana ya Dauke na kurama Bangon Dakina ido ina Lissafin yadda zan fara gudanar da Sabuwar rayuwar da kaddara ta kara Budemin. Abaya komai lalacewar aure na da Ya Ishaq bai furta zai jingine ni ba ammh ayau ya furta kuma alama ce ta angaji dakai ana neman maraba dakai,ni ba jahila bace ta bangaran addini nasan menene ma'anar Jingina amusulunci,Nasan zai kula da ya'yansa Saboda Dolensa ammh a yanzu ni ban zama Dolensa ba ya zama Dole na sama ma kaina mafita mafitar rike kaina tsayawa ga kafafuwa na ba saboda kaina ba sai Saboda in inganta rayuwar ya'yana anan gaba. Ji nayi wani irin karsashin gwarin gwiwa na kara shiga har cikin Tsokar jikina,Hawayena na share kafin na yunkura na mike,Fuskata nake ta faman gogewa araina ina nanata sunan Allah,Afili na furta"Tunda ka bukaci hakan ya ishaq zan yi maka hakan kamar yadda ka fad'a domin rama alheri da Baba yayi min..Sannan kamar yadda nayi maka alkawari babu wanda zai ji wannan mganar indai daga bakina ne sai dai daga bakin ka da ikon Allah zan zama Jajirtattaciya uwa ba domin na karfafa kaina ba sai domin na inganta Rayuwar ya'yana anan gaba" Daga haka na fara laluban wayata dake saman madubin Dakin,Na dannata naga 1pm na dare ta wuce biyu saura,sauke wayar nayi nan saman madubin dakin nawa na Tura kofar Tiolet na shiga na dauro alwala nafito nazo na shimfida Darduma na Fara Nafilar da tazame min jiki duk daare na saka yakinin araina Bayan kowani Tsanani Allah na samar ma da bayin sa masu hakuri Sauka'kawa Abaya in nayi sallolina na cikin Dare ina addu'ar Allah ya shiryamin yarana,ya saka musu tausayin junansu aransu,ya inganta goben su ya saka musu albarka acikin karatun su,Sannan na kan roki Allah ya sausauta zuciyar Ya Ishaq a kaina Ya sa ka Mama tasoni ta kaunaceni,ammh daga daran yau sai na sauya alakar addu'ata na roki Allah ya bani karfin gwiwa ya ciremin rauni da karaya yasa na tsaya nayi tsawon rai da zan zama Bango abun jigina wajen ya'yana na roki Allah da kyawawan sunayensa Chasa'in da tara akan ya tayani Tarbiyan y'ayana ya kular min da su ya zama gatansu ya tausaya musu ya shiryamin su duniya da Lahira yasa su zama abun alfaharin al'umma da musulaimai gabadaya. Ban kwamta ba sai wajajen karfe uku na Dare,shima Ahmad ne ya farka da kuka na isa garesa na Daukesa na Fara Lallashinsa ganin yaki daina kuka sai na bashi Nono yana kamawa sai shuru ashe yunwa ce yana koshi sai barci,Garin nima na shimfid'ar da shi sai barci ya kwasheni sai jin Mganar Hafsatu nayi a kaina tana ta kiran sunana Lokaci d'aya tana Buga kafafuwana.. Firgigit din da nayi na farka sai da Ahmad dake rumgume dani ya farka shima a tsorace sai ya fashe da kuka mikewa nayi ina mika Sosai Hafsatu kuma na Tsaye a kaina ita ta D'auki Ahmad tana fadin"Kai sarkin kuka ai garin ka ya waye" Sama sama na jita mikewa nayi a kasalance,na sauko daga kan gadon cikin yanayin mganata nace"Lokacin sallah ya yi ne..? Tana zama gefen gadon da Ahmad a Hannunta tace"Eh har su Ya Ishaq sun tafi masallaci da su Amir yau kin makara" Da karfi tayi mganar shiyasa na jita idanuwana na mutsike bina da kallo tayi lokaci d'aya tana nazarina kofar Tiolet na Tura na shige na rufo alwala nayi a gurguje na fito na iske tana cire ma Ahmad Pampers naji tana fadin bai ma yi komai aciki ba. Ina kokarin Tada sallah domin har na sanya Hijabi na juya ina kallonta Lokaci daya ina fadin"Ha..Hafsatu..Kin yi sallar ne..? Kai tsaye tace"ina Hutu dame zan taimaka miki kafin ki idar da sallar..? Shuru nayi ina nazarin abunda zasu tafi da shi makaranta babu cefane komai ya kare hatta lemun yaran da Biskit sai kawai cikin yanayina nace mata"Babu indomie ta kare dafa musu farar shinkafa ki yi musu amfani da miyar nan" Da toh ta amsa min ta fice Dauke da Ahmad ni kuma na tada sallah sai da nayi raka'atul fijir sannan nayi sallar asuba ina cikin azkar sai ga Anum ta shigo da karamin hijabinta alamun itama tayi sallan ne bayana ta D'ane tana fadin"Umma ina kwana" Yaran sun san raunin jina in zasu yi min mgana sai sun daga murya musamman Anun da Amir. Mirmishi na saki na saka hannu na Jawota gabana, na zaunar da ita ina Fadin"Ina kwana Anum d'ita" Lokaci d'aya ina jan kumatun ta Anum irin yaran nan ne masu yawon tsiya in suna mgana sai ka zata ana gaya musu ne. Kuri tayi min da ido ni kuma hankalina na kan littafin azkar din dake Hannuna ina karantawa sai ji nayi kamar daga sama tace"Umma kuka kika yi ko..? Waya dake ki..? Ban ji mamakinta ba sanin Halinta da Sauri nace"A'a wani kwaro ne ya fadamin a ido Anum." Da Sauri ta bata rai kafin tace"ko Daada ne ya yi miki Fad'a? Shuru nayi ina bin ta da kallo yarinya ce yar shekara biyar da wannan mganar ina laluban amsan da zan bata sai ga su Amir sun shigo yana rike da Hannun Musty dukkan su jikina suka fada Amir dai gefe yayi agabana kusa da Anum yazauna Musty daman akwai son jiki shi ya lafeni sai na rike sa ina jin wani Farinciki in na Tuna nima uwace ina da iyalaina da zasu iya zama abun alfaharina watarana. Amir ne ya daga murya yana fadin"Ina kwana Umma" Na amsa masa ina shafa kansa Musty ma da gwarancinsa ya gaisheni na amsa ina Dariya zama na gyara ina Fadin"Kun yi azkar din Safe..? Amir yace"Umma Daada bai barmu mun yi a masallaci ba ana ta kiran sa a waya sai muka dawo gida" Amir da kasafai ya cika mgana ba, sai in yaga dama,ban ce komai ba sai na kauce mganar nace su karanta azkar din su na Safe kafin Lokacin wanka yayi. Nan suka zauna gabana suna karantawa in da suka yi kuskure sai na gyyara musu har Musty da bai gama iya mgana ba yana ta garancinsa. Muna cikin Hakane Hafsatu ta shigo tace ruwan wankan su yayi zafi sai nace ta bari zan yi musu wankan ita taji da abun karyawan su. Ko kafin bakwai na Safe gabadayan su sun shirya cikin Uniform din Tahfeeez din su,Babansu ban gan shi ba Domin tun jiyan nan bamu sake had'uwa ba. Farar taliyar Hafsatu ta dafa musu sukaci da Sauran miyan jajjagen da nakedashi,Sauran kuma nace ta saka musu a basket din su babu lemo ko Biskit sai kawai nace ta dura musu aruwa a gororin su. Suna zaune afalon suna cin abincin ni kuma ina gyara ma Anum littafanta da ta wargazasu,Ahmad na bayan Hafsatu yayi barci tun da yaji Ruwan zafi ni ban yi wanka ba Hijabin da nayi sallah ne dogo ajikina. Hafsah na Durkushe gaban Musty ta na bashi
Chapter 16 · 0% Book details