← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 175

Sashe 140

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da aljannah kamin godiya sosai Abba" Abba yace'In sha Allahu" Ammi na daukan bandir daya na kudin take fadin"Kowanne goma ya bata kenan..? Abba yace"Ban sani ba fa. ni naga dai suna tarawa waje d'aya" Ammi tace"Tab..don ma ba babban Gwaska kenan Engr da kila sai a takarda check" Abba na Dariya yace"Maman Nana ke dai kina kaunar Engr din nan" Ammi tace"To dole na kaunaci Engr da zuru'arsa mana Baban Nana suna da kirki da Dattako ga harkan girma. karon farko fa kyautar dubu Dari ya yi min Baban Nana ina zan manta da wannan kyautar,nayi takaicin rashin zuwansa jiyan nan wlh" Abba ya girgiza kai yana kallo na kafin yace"Fa'i kina jin maman ku ko..? Ni ma mirmishin nayi ban ce komai ba Ammi tace"Wlh da yazo da Fa'i taga kyautar girma" Abba yace"Kila yana da abu mai muhimmanci ne shiyasa. ni dai yace min ayi mai afuwa ammh na bisa bashi zai zo har gida ya gaida Maman nana da Diyarta da gajiya" Ammi tace"Allah yasa dai yazo rabonsa da gidan nan tun murnan auran Nana fatima da ya zo maka Bayan ya dawo kasar na Abdul'ahad a waya kuka yi abun ku bai zo ba" Abba yace"Yana da ayyuka da yawa ne kinsan Babban mutum irin haka Allah yasa kada tafiya kuma ta kamasa zuwa wani wajen" Ammi ta amsa da Ameen suna ta Tattaunawar su ni dai sallama nayi musu Abba yasa na kwashi kudina zuwa shashen Inno nan nake zuwa mu sha hirarmu in su Hafsah sun shiga makaranta. Na nuna mata kudin ta yi ta saka albarka da na matsa ta Dauka sai ta kalleni tana Fadin"Shikenan komai sai kin bani Fa'iza..? Ban ce komai ba ta saka Hannu ta dauki Dubu biyu tana fadin"Na dauka Allah yasa albarka ni da ba abunda na rasa baban ku da mamanku tun kafin nace ina bukatar abu suke min. kuma ga ku kuna iya bakin kokarin ku Allah yadda kuka ji kanmu Allah yasa kuma naku ya'yan su ji kan ku' Na amsa mata da Ameen Ameen muka ci gaba da Hira,ina jin dadin zaman kaduna alherin da na samu na kudi ban san iyaka ba sana'a nada dadi da amfami mu tashi mu nemi sana'a sannan mu kuma gayama Allah Cikin Hirar ne take tambaya na ya wajen yarana nace duk suna Lafiya cikin mganar su na manya tace"Fa'iza kina ganin bazaki ba ma baban yaran nan wata dama ba..?ya yi nadama zuwan sa gidan nan ba adadi yana zuwa gaishemu kuma cikin neman ki koma ne Fa'iza" Ina jin nauyin Inno sai na kasa mata musu,Ishaq ya riga ya samu kan Abba da Inno harda anty Fadila ko da yaushe muka yi waya sai ta fara korafin na dawo gidan mijina na zauna da ya'yana Abba dai bai taba min mgana ba sai dai a yanayinsa na Fahimta,ga Inno ma tagaji ta furta kaina na kasa na kasa mgana sai ta jinjina kai kafin tace"Ki yi Tunani ko Saboda yaran nan Fa"iza. ko wani aure da na shi kalubalen yanzu bama shi ba ko Ahalinsa bamai kara takaki kina da komai da bazai saka namiji ya rainaki ba. ga yaranki sun kawo girma ki yi tunani a matsayinki na uwa ko Saboda ya'yan ki" Tafada cikin wani yanayi na lallashi,kafin ta gama mganarta hawaye sun kawo ido na,Inno ta Cigaba da fadin"kuma in ki duba kina da kuruciyarki bai kamata ki kare rayuwarki ba aure ba, ko ki yi Tunanin koma ma uban ya'yanki ko kuma ki fitar da wani mijin ki aura ammh a shawarata da hangenmu na manya gwara ka koma inda ka saba ka kuma sani da ka koma inda baka sani ba Fa'iza, sannan ko bakomai akwai zumumci tsakaninku ko ba'a duba komai ba a duba zumumcin Tunda Allah ne ya Umarcemu da mu yi zumunci kuma mu rike zumunci wlh wutar Allah zataji wanda bai rike zumunci bai kuma taimaki zumunci ba" Ni dai na baro shashen Inno ina Hawaye yinin ranar a kwance na yi sa ya tadomin wani tsohon ciwo ne daga abunda ya shafi rayuwata ina neman in binne mganar Ishaq,ammh sainaga kamar yanzu ne ma suke neman tadomin da ita Tsausayi yake bama kowa yanzu har Yaya Mariya da a baya take adawa da shi yanzu ta dawo itama tana min mgana komawa gidansa,Harta ko Da goggo itama abunda take fadamin kenan,su Anty Binta da su badariya sun gaji da rokona na koma har sun gaji Zainab ma har gobe bata Hakura ba ni Uban gayyar bana jinsa sai dai gabada'ya ya Nannade dangina da Nadamarsa da kirkinsa,A satin kaf naji kaduna ta fita raina saboda matsawar Inno kan mganar Ishaq,Sai na dai zuwa na zauna a shashenta ita kuma in dai naje sai ta Tsaidani da nasiha da tunasarwanta. Ranar ma gaban Abba tamin mgana shima kuma ta kallesa tana fadin"Usman kada fa ka zama uban banza. Wajibinka ne ka shiga rayuwar yarinyar nan in bazata koma ma tsohon mijinta ba,to ka bata dama ta fitar da wani mijin zama haka ba shi da wata Fa'ida" Abba sai yaji nauyi na har ya kasa mgana ni kuma ganin haka sai na tashi na fita sai da na ficen sannan yace"Inno Fa'iza tayi girman da ta san daidai da akasa sin sa. Bazawar ce sharia'ta bata damar ta zaba ma kanta mijin aure, bazan mata Dole ba Inno ta sha wahalan rayuwa in ta nuna tana son komawar shikenan muna son hakan ammh in bata so Inno bazan iya mata Dole ba" Inno ta kasa mgana sai ma kai data jinjina kai tana fadin"Duk da haka dai mace ce tana karkacewa. ka tunasar da ita tare da nuniya" Sai ya tabbatar mata da cewa in sha Allahu zai yi min mgana da haka suka rabu shi kuma bai min mganar ba. balle Ammi da yasan bata son ma mganar Ishaq sai ya bar abun a ransa ammh har ga Allah mganganun Inno sun sakashi Tunani da Ganin cewa abunda ta fada din gaskiya ne. Ni ko na tsorata bana so Abba yace na koma domin bazan iya masa musu ba sai dai har a cikin raina bana sha'awan aure a wannan Lokacin. ballatana koma ma wanda ya taimaka wajen fitar da aure da jin dadinsa a raina. shiyasa ko Abba ya kirani nake jin Fargaban mganarsa a kaina ammh har lokaci ya tafi Abba bai ce min komai ba sai nima Hankalina ya kwanta sai dai duk wanda yamin mganar komawa gidan Ishaq cewa nake yi ba shi ba auran ma gabadaya bazan yi ba kasuwancina zan cigaba da yi. sai bakin su ya mutu basu kara mgana ba,Inno kuma da ta lura ina gudunta sai tace min"dai na guduna Fa'iza in dai mganar aure ne nayi shuru bazan kara mgana ba,ki rika zuwa muna Hira kina Debemin kewa" Sai naji kunya ashe har ta gane ina Gudunta,jin haka yasa sai na saki jikina Tunda itama ta daina Damuna da wata mganar aure ***** Sati uku da gama warkshop din su Abba ranar tun Safe cikin wani yanayi na tashi gabana haka kurum yake ta fadi ranar litini ne ina azumin Lada,har kuma da su Anum mun yi mgana suna Lafiya ba abunda ya same su sai na rika addu'a ina fatan koma me zai sameni ya zama na alheri. Azumin da nayi ya bani wahala saboda na kwanta ban ci abincin dare ba,sannan ban yi sahur ba kuma ranar na hada Turaren Humra na Laila,aikinta ya jima a Hannuna ban hada mata ba,Girki ma na kasa yi. Kunin tsamiya kawai na Dama nayi mana yam ball,Dakyar na iya yin wanka na sauka wata doguwar riga ta Roba mai ruwan kasa kunin kawai na sha na kasa cin komai haka kawai nake jin bakina ba Dadi da yanayin gabadaya sai na kwashi yam ball din da Pepe chicken din da tun jiya na yisa yau dumamasa kawai nayi zuwa Shashen Inno,tamin barka da shan ruwa muna taba Hira sama sama. Ina Shashenta har akayi isha'i sai nayi salla na anan kawai na kwanta saman Dardumanta sai ga Ammi ta shigo ta yi ma Inno sannu da gidana tana kallo na kafin tace"Inno fa'i ta fara barci ne..? Inno tace"anya..?naganta dai yau duk ba kamar yadda na saba ganinta ba. abinci ma bata wani ci ba.Ke Fa'iza Fa'iza." Sama sama na jita na mike ina Hamma Naci karo da Ammi da sauri nace"Ammi yaushe kika shigo..? Ammi tace"Yanzu mana. Daman babanku ne ya yo waya Megidansa Engr din nan Inno shi ya kirasa yace ya shigo kaduna yau kuma yana azumi zai samu abincin shan ruwa ya shigo an juma..?sai nace bari na Duba Fa'iza nagani" Inno tace"To ke Fa'iza kin ji babban bako ne wajem babanki in zaki iya tashi ki sama masa wani abun" Daman tuni na mike jin wanda ke tafe Engr fa mai girma ne a wajen Abba da su Ammi duk da yanayin jikina,Ammi ta kalleni tana fadin"Naga kin sha wahalan azunin nan Fa'i in bazaki iya ba bari na saka su Hafsah" Da sauri nace"laa zan iya fa Ammi. gajiyan azumi ne,kawai zai sakeni in na kwanta" Sai ta jinjina kai tare muka fita da ita,ina tambayanta me zan dafa masa sai tace nayi mai sauki suna tafe yanzu kila shi da Abba ko kuma shi Abba ya rigasa zuwa. jin haka yasa sai na bar masa sauran kunin Tsamiyar da na Dama da Ragowar yam ball,akwai nama sai na yi masa Ferfesun naman,sai jallop din shikafa colour da kayan lambu ban ko gama ba Abba ya dawo naji yana fad'ama Ammi a falo Engr na hanya zai kariso yanzu sai nayi hanzarin karisawa na had'a komai zuwa falon Abba yana ta sakamin albarka. Falon Ammi na koma wajen su Hafsatu suna ta aikin makaranta suna Hira sai na koma na lafe kan kujera muna zaune da yake falon Ammi na ta wajen Haraban parking space ne. sai muka ji karan shigowar mota Nana Khadija,ta mike ta Daga labulen Window ina daga kwancen nima sai da na mike na leka kamar an tadani Tsaye wata bakar BMW,ta shigo cikin parking space din gidan Abba. An dad'e kafin Abba ya fito daga cikin gida ya bude kofar baya kafa ce
Chapter 140 · 0% Book details