← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 175

Sashe 4

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kusa ni na sani Tazaran Dake tsakanina da Ya Ishaq kamar Tazaran kasa da Sama ne ko abaya ban taba mafarkim auran miji kamarsa ba Domin ba Tsarana ba ne, sannan ba kuma Had'i shi kanshi na san ni ba irin wacce ta Dace dashi bane Mama kofar soro kullum tana Fada min hakama Anty Binta batagarawa,To ammh Ba kai kake Tsarama kanka Rayuwa ba Allah ne Kana naka ne yana nashi kuma Tsarinsa ne akan gaba. Na tabbata ba Domin kakkausan Bakin Baba kan Ya Ishaq ba, da Tuni bayan kasa ta shafe idonsa ya rabu dani ya samu salama kamar yadda yake Fadi sai dai ina Ya Ishaq bazai iya Tsallaken mganar Baba ba Shiyasa har yanzu muke tare ina D'aukan dukkan cin kashi da Tozarcinsa Bani da wani gata nan Duniya sai Ishaq shine uwaa na shine Ubana da Duniya ta Tamadina ga yanayin yadda Rayuwa tazo mata sauran yan'uwanna ba waje daya muka tashi ba Bayan Rasuwar mahaifinmu Raba mu akayi ni a karofi na fara Rayuwata Kafin dalili ya yanke zamanna achan Baba Kabiru ya maido ni katsina ya Damkani Hannun Mama. Hawaye na haka suke faman zuba ban iya saka Hannuna domin na tare su ba Saboda ko na goge su wasu ne zasu kara fitowa a irin wannam Lokacin nake samun Fitar da abunda ya dade yana Damuna,Ba bakinciki nake yi Saboda Ishaq zai kara aure ba,A'a ai daman na sani yafi shekaru yana ikararin zai auri Zab'insa Daidai da Ra'ayinsa tun kafin ma yakai haka zama a rayuwa ballatana yanzu dayake jin kansa ashi wani ne. Sai dai abu D'aya na sani zuwan Amarya nan tozarcin danake sha sai ya Ninka wanda nake sha abaya abu daya ne naake gudu wulakanci ina tsoro da firgicin Amaryan tazo tasan duka labarina tazo tana ganina a wulakance ta goraanta min Kamar yadda Shima yasha Fadi Fa'iza ba kyau ba Turanci komai nata Total zer0 ne. ammh a raina bana mai Bakinciki don zai kara aure ai yayi ma kokari da muka kwarari wad'anan shekaru bai kara ba,sai yanzu na kuma ji Dadi da matar zatayi nesa damu ko Bakomai kazantar da baka gani ba Tsabtace akasan chan raina kuma ina da kishi Domin ina son mijina so irin wanda Duk Macetagari zata nuna ma uban ya'yanta,duk da tarin Nakasun da auran mu ya kunsa, duk da ko shi din' bai taba sona ba. sai dai bazan barsa yayi wani Tasiri a kaina ba tunda inda Son ke da muhalli baza'a martabasa ba, zan iya Rantsuwa ko Kaffara bazan yi baa Ya Ishaq baya sona karfin Biyayyar Baba ce take Rike da igiyar auranmu. Naso na sauya Rigar Jikina kamar yadda yace sai dai kuma Tunda yace na bar shi nasan ko da na bisa Shashensa sai ya koreni shiyasa ban bata ma kaina Lokaci ba na Haura kan gadona naa jawo Ahmad jiki na,na Rumgume sa A bu D'aya ke sanyayamin Rai ya'ya na Domin duk duniya bayan Ishaq bani da kamarsu basa san iya adadin Lokacin Dana Dauka inaa kuka ba ammh nasan Har barci ya kwasheni kukana bai Tsaya ba. Kiran Sallar Farko na tashi kamar yadda ya zame min Jiki Fa'iza bata barcin Rana sannan karfe Hudun Asuba take tashi sai kuma wani Dare. Fita nayi naje Dakin yaran na Tashi Amir da Mustapha zasu bi Babansu masallaci Bayan sun tashi na fita zuwa Dakin Hafsatu na isketa ta tashi har ta Shiga Tiolet sai na Fice su Amir ta Tsaya akansu sukayi alwala Daidai Sanda Ishaq ya fito Daga bangaransa Sanye da Jallabiya baka da Carbi Kofar Dakin yaran ya Coge duk Fadan sa bai isa yayi ma Fa'iza Fadan rashin Tarbiya da kula da yaransa ba wannan in bai Gode mata ba ai bazai Zageta ba. Amir ne ya karisa ga Baban yana Fadin"Oyoyo Daada sannu da zuwa.." Yafada yana rumgumesa rike sa yayi yana Shafa kansa kafin yace"Jiya na dawo lokacin kun yi barci.." Ina musty..? Yafada yana kallonsa Fa'iza na kiciniyar saka mai wata riga bayan ta cire mai na barci sai faman mutsike ido yake yi alamun barcin bai sake sa ba. Dariya yayi yana kallonsa kafin ya Bude Hannunsa yana Fadin"Oya come Here..!" Da gudu yaron ya nufessa ya Fada jikinsa yana Fadin"Daada.." Shafa kansa yake yana jin Farimciki acikin ransa Fa'iza ya kalla Dake tashin Anum da dan karfi yace"Kyaleta mana.." Fa'iza ta Dago tana Fadin"Suna da Hadda yau." Yana rike hannun su Amir yace"Ai da Sauran lokaci ke komai naki na Hanzari ne karfe Biyar din Asuban ne zasu tafi Haddar..? Bada karfi yayi mganar ba saboda Haka ban ma jisa ba nadai san yayi mgana kuma nasan bai wuce Fada ne irin nasa Daya saba ba, shiyasa har yaja su Amir suka fice ban kara mgana ba.. Suna Fitan nayi kokarin tashin Anum Saboda tayi sallah ta wartsake kafin su Dawo Daki na muka koma Tare nima na Dauro alwala mukayi sallah Tare da Anum muna idarwa Ahmad ya tashi na Daukesa naga ya bata pampers dinsa,sai na mike na Goyasa na shiga Kitchen bayan na gargadi Anum kada ta koma barci ta zauna tayi azkar din Safe wanda yaran duk sun Haddace.. Ruwan Zafi na fara sakawa saboda nayi ma Ahmad wanka kafin sauran yaran su Dawo Sai kuma na fara kokarin Fere Doya saboda na soya musu na Tafiya dashi makaranta sai ga Hafsah ta shigo Kitchen din da Hijabinta. Fa'iza Hankalinta na wajen aiki bata san Hafsatun ta shigo ba sai da ta tabata sannan ta dago tana kallonta kafin tace"Kin fito Hafsah..? Da yanayin mganarta Hafsah tace"Eh Ina kwana.." Da dan daga Sauti Saboda Fa"izan ta jita sosai. Ta amsa mata Cikin Sakewarta Hafsah tace"Bari na amshe ki." Fa"iza tace"A"a barin min wanan aiki..Ga dai ruwa nan na saka in ya Tafasa ki juyo ki yima Ahmad da Anum wanka kafin su Amir su dawo." Tafada cikin yanayin Raba mganarta Hafsah ta amsa mata da Toh,ba Dadewa ruwan ya Tafasa ta Dauko wani Karamin baho ta juyo ruwan ta kai Tiolet din Dakin Fa'iza da suna da Shower na wanka ya lalace kuma ya Ishaq yace da gan gane saboda haka bazai gyara ba. Dawowa tayi ta karbi Ahmad ta je ta fara mai wanka ta shiryasa sannan tayi ma Anum nata wanka alokacin har su Amir sun Dawo masallaci suna Falo Tare da Ya Ishaq Sanda Hafsat ta fito Dauke da Ahmad daya fara Rigima ne Fa'iza ta fito Daga Kitchen din tana gaida Ishaq ya amsa mata bai ko kalleta ba Hankalinsa na wajen Amir Dake bashi Labarin abunda ya Faru a makarantasu jiya shi kuma Musty bai da Hayaniya yana Lafe jikin Uban.. Hafsah ma tabi ayarin yar'uwanta ta gaisheshi ya amsa yana Dubanta ganinta Dauke da Ahmad yasa yace"Ina zaki kaishi..? Hafsah tace"Kuka yake yi zan kai shi ta bashi Nono ne." Hannu ya mika mata yana Fadin"A kitchen din zaki kai mata shi..? Wato salon ta jefa shi Cikin wani abu kin santa bata da kula." Hafsah dai batace komai ba ta mikamai D'ansa ya Cafe shi yana Daga sa sama cikin Fara"a Hafsah bata damu ba ta karisa kitchen din Domin kama ma yayar nata aikin itama gobe zata koma Daman Hutun Midterm break Aka basu a makaranta yasa Goggo ta barta ta taho itama tana Karofi ne wajen Hajiya Indo da suke kira Goggon Karofi ita take rikonta tun bayan da ta karbota wajen mahaifiyarsu Ta madina. Suna Kitchen din suna aiki Hafsah taji Sanda Anum ta fito ganin babanta yasa ta nufesa cikin murna tana Fadin"Daada yaushe ka dawo..? Daman Anum akwai kirniya da Rashin jin mgana Yana ganinta itama ya Tarbeta yana Fadin"Anum dina jiya da Daddare na dawo kun yi barci." Kai Tsaye tace mai ina Tsarabanta yace sai an juma in ya sake fita Hafsah ce ke Sauraran Hiransa da ya"yansa banda Fa'iza da baji take yi Sosai ba sannan Hankalinta na wajen Soya Doya bata ma san Abunda suke ciki ba. Kafin bakwai na Safe tayi Fa'iza ta gama komai sai ta bar Hafsah a kitchen din tana karisawa,ni kuma sai naje na Shiryan yaran saboda suna da Hadda Tahfiz ne tun Safe sai shida suke Dawowa Allah ya taimake ni Ahmad na wajen Ya Ishaq ya shiga Dashi Shashensa. Koda bakwai da Rabi tayi sun karya sun shirya Tsab Cikin kayan makarantarsu Ga Basket din kowanne an shiryamai da soyayyar doya da miyar kwai,Sai lemu da ruwa Fa'iza na kokarin Tura Hafsah ta leka tayi ma wani wani makotanci Haruna mgana mai Tuka adaidaita shi ke kai yaran makaramtar Hadda da Boko a wata Ya Ishaq na Biyansa Saboda abaya motace har da Direba ya Daukan musu tunda Anum ta taba koke motar Mama ta sa ya bama Jamal kaninsa motar tana chan gidanta Kofar soro in ya Dawo Hutu Daga Kano inda yake karatunsa na Engeering yake amfani da ita su kuma Ishaq ya Daukam ma yaran mai adaidaita a cewarsa Tunda bata iya Tattali ba shi ba asararrre bane sannan kuma yace Mota bata Dace da ni ba,irin mu yawo acikin Adaidatan yafi Dacewa damu,ni Dayake ban Damu ba, ba fita take yi sosai ba Daga Gidan Mama sai gidan Anty Binta shima na da'n Rage zuwa tunda ba maraba suke da zuwana ba Karofi kuma sai dai in an yi Rasuwa muje Gabadaya ammh ni kad'ai Ya Ishaq cewa yake bai yarda da ni ba zanje ne na Had'u da yan'uwana azagesa shiyasa ban ma Damu da Fitan ba nima. Ina shirin aika Hafsah ne sai ga Ya Ishaq din ya fito yace shi zai kai su,jin Haka yaran suka fara Murna sosai,Tare da Ahmad suka tafi har Lokacin bai koma barci ba shima ai yasam Ishaq saboda gaskiya in yana Gida yana bama yaransa Lokacinsa nice dai bani da wannan matsayin. Har sun fita naa bisu Haraban gidan ina kwalama Amir kira ya juyo yana Fadin"Umma menene..? Ina Sosa gashin idona nace"Kada ku manta ku karanta addu'ar fita Daga gida." Da Karfi Anum ta fara karantawa Amir na Binta shi da mustpaha suna gamawa nabisu da mirmishi ina Daga musu Hannu Ishaq dai Tuni ya Shige mota yana Dauke da Ahmad irin wad'anan Hallayar na Fa'iza ba wani Burgesa suke yi
Chapter 4 · 0% Book details