Sashe 116
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hijabina Lokaci d'aya yana fadin"Ki yi ma girman Allah Fa'iza ki yi hakiri ki bar mganar nan. Hankalina tashi yake yi in naji kina fadin saki da kuma cewa bazaki bimu ba.?Ta yaya kike so na fara rayuwa a in da baki..? Bansan Lokacin da na juyo,har ina bangajesa cikin daga muryan da bansan ina da shi ba nace"Zaka iya. Nace Ishaq zaka iya.." A baya ka zauna da wata macen inda bani kuma baka mutu ba. Na fuskanci Kaskantattaciyar rayuwa a gidan auranka,na fuskanci tozarci a wajen ka da wajen dangin ka a karkashin auran ka,ka rabani da kowa nawa ciki har da mahaifiyata ka rabani da yan'uwana duk wani mai so na baka kaunarsa,baka son ganin Dariyata sai kuka na Ba a macen aure ka Daukeni ba,ka Daukeni a baiwa,mara gata,jahila wacce bata da ilimin zamani,sannan mummuna baka wacce ka ke zaune da ita Saboda alfarma,wacce tayi ma rayuwarka karan Tsaye Fa'izar dai da tayi ma mafarkin ka kutse, Fa'izar da ka zaunar da ita kana rokonta da ta taimaka tayi maka adalci ka zama na mace Daya,Matar da ka fifita a kan Amaryan ka,Fa'izar da baka san ciwon ta ba,baka san cikin ta ba,baka san zafin nagudar haihuwar ya'yanka da ta dinga yi ba, itace dai wacce ahaka ake kiranta kamar akuya ta cika Haihuwa Fa'izar da ka nemi datse mata Haihuwa saboda baka kara kaunar Zuru'a da ita,Ni ce dai Fa'izan da kasa nuna ma duniya ni matsayin matarka kana jin kunya,Nice Fa'izan da ka ke barina wata da wattani Saboda wata mace ni ce Fa'izan da na dauki dukkan Tozarcin yan'uwan ka har da na Dangin matarka saboda Fa'iza bata da gata,Fa'iza ba kyakyawa bace. Sannan bata da ilimin zamani ba wayayyiya bace ba kuma yar gayu ba ce,sannan ita ba fara bace bata kuma iya haihuwan Fararan ya'ya ba,ni ce Fa'izan da kake kirana mara amfani Fa'izan da auran ta bai amfana maka komai ba ni ce dai Fa'iza nan wannan mai raunin jin,wacce ka ce ka tsani mgana da ita saboda tana saka ka ihu ko ka manta ne..? nice fa nice fa kake kiran bazaka iya Rayuwa a inda bani ba..?karya ka ke yi..Wlh karya ka ke yi.." Na karishe fad'a cikin Tsawa Lokaci daya da kuka sai kawai na zube saman Cafet din ina wani irin kuka mai cin rai ban sani ba ihu na da mganata yasa su Mama rugowa Dakin,duk a gabansu na rika amayar da abunda ke cikina. Su kansu jikinsu yayi sanyi sannan sun kasa gane wasu abubuwan Shi bai ma gansu ba sai ya rarrafa cikin Fitan hayyaci ya na kokarin rikoni nayi maza nayi baya da jajayen idanuwana ina fad'in"Kar ka kara tabani. Kar ka kara in ba haka ba wlh zan sharara maka mari" Na fad'a ina nuna sa da yatsa cikin bacin rai da bai taba ganina aciki ba Sai ya kasa karisowa gabana,cikin rawan baki da na murya yace"Fa'iza ba kin ce kin yafemin ba..? Me ya sa..? Kai Tsaye nace"Eh da gaske na yafe maka,.ammh ba shi zai goge tabon da kayi ma rayuwata ba. Dalilinka aure ya fita kaina na Tsani duka maza sannan nake Tausaya mata ire ire na da Tunanin wata irin Rayuwa su kuma suke fuskanta a gidan nasu auran..?ka taba Tunanin ko sau d'aya kayi min adalci? Nace ka taba wannan tunanin.? Sai kawai na kara fashewa da kuka ina fadin"A gabana ka kori yar'uwata uwa d'aya uba d'aya,Har kana ikirarin in ka kara ganinta a gidanka zaka had'a ta da Hukuma?ashe ko bata ci darajan aurena da kake yi ba, bazata ci Darajan zumunci ba Ishaq..? Mahaifiyata ta rasu bata san Dadina ba. Har ta koma ga Allah ban taba zama da ita na yini d'aya ba. Ranar da zata rasu ma baku barni na kwana da ita ba,ta rasu ban sani ba. Na rasa uwata ammh ko gaisuwa baka zo min ba, kana wajen wacce ta fini muhimmanci a wajenka.Sai da ka dawo baka iya ce min Fa'iza ya hakuri ba sai Duba na kayi kana ce min ashe wai kuma babarku ta rasu..? Wai ne ma baka Tabbatar ba.?shine kake so na manta..?ko kuwa yadda ka ware ni daga cikin sauran mata a dalilin auranka yasa nayi shekaru ina fama da Gulit din mata masu kyau da gata ne suka chanchanci ado da kwalliya,a gidan ka na fuskanci mata ire irena basu dace da samun soyayyar miji irin Ishaq kabir karofi ba. Shiyasa na yanke shawaran karshen zama na dakai yazo daga yau.Na rantse da Allah bazan bika ko'ina ba. Daganan karofi zan koma daman ranar da Baba yace zai had'a aurena dakai Mama ta koreni sannan tayi alkawarin bazan koma mata gida ba,Karofi na koma wajen Goggo kuma chan aka daukoni nan duniya bani da gatan da ya fi gaban Goggo gabanta zan koma na zauna Domin Fuskarta Sabuwar rayuwata" Na karishe Fad'a ina share hawayena lokaci Daya na mike da Sauri ina fadin"Zainab zata iya kula da kai. Yara kuma Amir da Anum sun yi girman da zasu iya kula da kansu. Ahmad da mutsy ba su da matsala zasu kula da su. Ba lalle ba ne don na faro rayuwata dasu na karishe ta da su ba..Haka Allah ya kaddara Labarin ya kare daga wannan Lokacin" Na fad'a Lokaci daya ina Daukan karamar jakata,Mama na gefe sai sharan kwallah take Anty Hure ta sha gabana tana fadin"Haba Fa'iza ku ba yara bane. yi hakuri mu tafi in mun je chan sai a zauna a fahimci juna' Kallonta nayi kafin nayi mirmishin takaici na tuna har da ita a masu biye ma Mama suna cin zarafina,sai kawai na kad'a kai ina fadin"Bakin alkalami ya riga ya bushe Anty Hure.." Na kad'a kai na zan fita waje,Ishaq ya yi kukan kuran shan gabana yana rike Hijabina na balla masa harara ina fadin"Cikani kafin raina ya baci" Yaki ko sakina fad'i yake yi"Fa'iza ina zaki.?Fa'iza kada ki yi min haka..?me zan ce ma yaran chan..? Fa'iza..Fa'iza" Sharr sai kuka abunda ban taba gani ba,kai na kauda abubuwan suna dawomin kamar yanzu komai ke faruwa,kwace hijabina nayi ina fadin"Na fada maka kuma zan kara fad'a maka na gama zaman aure da kai. Na tsani aure na tsani kowani zamantakewa,Ka sauwak'e min Ko kuma ka k'ara Turgud'e shi daman jinginanne ne" Na turesa zan wuce sai ya makale kafafuwana yana fad'in"Kada ki yi min haka Fa'iza,Kada ki yi min haka" Kasa kwace jikina nayi sai kawai na juya ga Mama tana kuka nima ina Hawaye nace"Mama ki fad'a masa ya cikani don Allah" Sai Mama ta sunkuyar dakai shi ko,sai alokacin yaga su Maman sai ya sakeni ya Rumtuma wajenta ni kuma sai na kwashi Sauri na fita Daga Falon ina Fitowa sai nayi Turus ganin yaran duk Tsaye suna jin abunda ke faruwa ga Anty Binta itama. Cikin mamaki tace"Fa'iza meke faruwa ne har kofar gida ana jin Hayaniyar ku..? Ban bata amsa ba Ishaq ya fito rike da Hannun Mama ya kawota gabana yana fadin"Mama ki gaya mata wlh nayi nadama.bKi gayamata abunda Baba ya sha fada'min,Yace in na rabu dake zan lalace Fa'iza ko so kike kada nayi albarka..? Komai ban ce ba kaina na kallon kasa ina Digar kwallah,Mama ma sai sharan hawaye take yi Anty Binta ta kalli Anty Hure tana fadin"Anty meke faruwa ne..? Anty Hure cikin Damuwa tace"Fa'iza ce tace bazata bisa lagos ba. Tana neman saki ne da wasu mganganun da ban gane ba.." Sai ta waro ido kamar yadda yaran suka yi cikin wani yanayi tace"Fa'iza yanzu kuma?kika ma zauna dashi a bai da shi sai kuma yanzu da Dadi yazo sai kice haka.?aa ku bari muje chan sai mu zauna mu tattauna kin ji ko..?tafad'a gabanta na fadi domin bata san ya wannan al'amarim zai kare ba. Jallonata nayi ina tuna Yadda tayi Tsawon shekaru tana Tozartani har da ita masu saka bakin na zauna sai kawai na share hawayena ina fadin"lokacin da bai da aiki wannan yanayin da mata ire iren Fa'iza ya Dace shiyasa ban tafi ba tun a wanchan Lokacin,sai yanzu kuma da komai nasa ya dawo sai nayi Tunanin Lokacina ya kare daman kema kin sha Fad'a jin dadi bai dace da mata ire irena b a,wahala ce da bauta ta Dace dani kamar yadda Mama ta sha fada. Shiyasa zan tafi zainab itace ta Chanchanci zama da shi Tunda ita ta tako kashin arziki sannan bata yi kama da matan bauta ko wahala ba.." Dukkansu Tsaye suka yi an kasa mai mgana ina gani Anty Binta na zaran ido sai kawai nayi Dariyan takaici kafin nace"Na kwashe fin shekara goma ina bautar aure kuna ganin komai ammh baku taba zaunar da shi kin fad'amasa bai kyauta ba..?sai ni yau don a shekaru goma sha Biyar da auran mu na yunkuro sai ku nemi Danne ni.?wannan karon ba wanda ya isa ya hana Fa'iza tafiya. Zan tafi kuma tafiya ta har abada" Ina gama fad'in haka na ratsa Mama zan wuce sai ta riko Hijabina tana kallona,yanayinta zai sakani rauni sai na daga kaina sama cikin wata murya tace"kiyi hakuri Fa'iza. Ba domin na isa ba..Ki yi hakuri ki Duba yara nan kada ki bar su yi maraicin uwa" Ta fad'a tana nuna su Amir,Anum har ta fara kuka da su Ahmad zuciyata ta karye ammh ban damu ba Hawayena na Shatata saman fuskata nace"Ke kan ki shaida ce Fa'iza bata dace da D'anki ba.,yaran nan kuma rabo ne Allah ya sa na same su,maraici kuma baza su yi maraici ba Mama kina nan ga Zainab,sannan shi ma babansa zai kula da su tunda ya'yansa ne sune Dolensu bazan ce a zama da shi bai Tabamin wani abun alheri ba,yayi min Tunda dalilin sa yasa yau nake amsan sunan uwa,ammh mganar na Duba yaran nan bai taso ba. Nima a lokacin da yake tozartani ko sau d'aya bai tab'a Duba darajan ya'yana ba.." Na fad'a ina kallon su, bana so na cigaba da mgana a gabansu kada su ji,kamar ma Amun da Amir tunda suna da wayan su. Na tuna Lokacin da Anty Binta tazo ita da Mama suna min watsi da kaya akan sai na bar gidan,meyasa yau don nace zan tafi sai su damu..? Wani tukuki ya taso min