Sashe 118
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar wacce aka bugi kaina,cikin kiftawan ido na dawo cikin hayyacina na fahimci shirmen da na kusa yi ma kaina da rayuwata,kamar yadda na saba a baya. Da sauri nace"Direba. Direba juya mu koma,Mu koma kawai" Na fada ina kokarin danne kukana,cikin mamaki Direba yaja ya tsaya sannan ya juyo yana kallona Cikin wani yanayi ganin yadda nake kuka,sai kawai ya koma ya gyara zama yana fadin"Hajiya ki tsaida Shawara d'aya in tafiya tafiyar in kuma komawa to komawar" Sai kawai na shiga Sharan kwallah da Bayan hannuna cikin Dashewar murya nace"Muje kawai.." Cikin jadaddawa yace"kin tabbata Hajiya? Cikin Tabbatarwa na gyad'a masa kaina lokaci d'aya ina kokarin bama kaina karfin gwiwa. Acikin zuciyata kuma ina maimaita Hasbunallahu wani'imal wakeel domin samun karfin gwiwa,Nan take Direba ya juya muka koma. Ban kara yadda na zauna haka ba saboda kada zuciyata ta kara raunana muna tafe ina salati da Hailala acikin raina,sai dai kuma kukana ya kasa tsayawa ina na zucci sannan hawaye sun kasa daina ambaliya a saman fuskata muna tafe ina yi ina saka hannu ina sharewa sannan ina faman jan Hanci da majina. Wlh bansan mun iso Karofi ba sai da naji yana tambayana inda zamu je sannan na daga ido na ga inda muke,sannan nayi masa kwatance,Ina jin wayata acikin jaka tana zuzu alamun ana kira ammh bana cikin yanayin da zan iya duba wayar ma. Bamu jima ba sai gamu a kofar gidan Goggo,muna isowa na bude mota na fito karamar pos din dake hannuna na Laluba dubu hudu ne yan Dubu Dubu Sabbi na cire na bama Direba ya karba yana godiya Yaran da basa rabo da kofar gidan Goggo,su suka yayyameni ana fara sauke kayan suka rika jida suna shiga cikin gidan Goggo da shi,Nima bayansu nabi cikin wani yanayi har ga Allah ko gani bana yi jiri ke dibana ga ciwon kai mai Tsanani,ina ji muryan Direban na fadin"Allah ya kawo miki mafita" Ko amsa shi ban yi ba. na shige gidan goggo,a tsakar gida na isketa tana tambayan yara kayan waye ?ina Sawo kaina Tsakar gidan nace"Nawa ne Goggo" Muryata a shake,na bata amsa baki sake Goggo ke kallona cikin mamakin ganina bata rufe baki ba. taga ana shigowa da freezer,suna kiciniyar inda za'a sauke Goggo ta nuna musu dakin da ta ke sauke karikitaanta suka shiga da su,sallaman ma Goggo ce ta sallame su ni ko ban iya tsayawa a ko'ina ba sai akan Daya daga cikin kujerun falon Goggo na zauna Dabas ina Numfarfashi kamar wacce tayi gudun Tsere,Goggo ta shigo ta tsaya a saman kaina,Hijabin jikina na cire kan kujeran ma sai naji sama sama nake jin kaina. kasa na koma na zauna,ina Kokarin tare kukan dake neman tasomin. Cikin mamaki da al'ajabi Goggo tace"Fa'iza daga ina?kun fasa tafiyar ne..?yanzu nan su Nasara suka fita suna shirin tafiya tace kin kira kince su Dakata ga kinan zuwa lafiya.?ina yaran ina shi Megidan naki..? A jere Goggo ta rika jefomin Tambayoyin,ammh na kasa amsamata ko d'aya daga ciki sai na koma na Dafe kaina ina kokarin daidaita yanayina,Goggo bata hakura ba ta cigaba da kallona tana Nazari na sai ta Fahimci na fita daga hayyacina Idanuwana sun kumbura alamun nasha kuka sai ta Firgita cikin jimami da Fargaba tace"Fa'iza ki yi min mgana mana naganki da uban kaya sannan ke kadai kika zo ina su Amir..?ina shi Ishaq din..? Ambaton su Amir yasa na fashe da wani marayan kuka zargin Goggo sai ya tabbata ta ji jikinta yayi sanyi sai ta koma ta Durkushe a gefe na tana fadin"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un Fa'iza ba dai Ishaq din ne ya sake ki ba? Ban bata amsa ba na cigaba da Dirzan kukana Goggo na tayani da Sallalami fadi take"Haka Allah ya kaddara. Fa'iza ki yi hakuri" Ta kasa zama ma mikewa tayi tana fita tana Dawowa cikin wani yanayin da na kasa Fassarawa,sai da nayi kukana ya isheni sannan na lallashi kaina Lokacin Goggo ta kawo min Ruwa da abinci tana fadin"Wannan wata irin kaddara ne..?bai rabu dake tun kuna samun matsala ba sai yanzu da kowa ke ganin abubuwa sun daidaita? Sai da na sha ruwa naji na samu natsuwa sannan na Dago jajayen Idanuwana na sauke a kan Goggo ganin yadda ta rud'e ne hankalinta a tashe yasa na bude baki nace"Ba sakina ya yi ba Goggo.." Sai da naji ajiyar ran Goggo na samun Salama. cikin mganarta tace"Har na samu salama Fa'iza to me ya faru.?na ganki da uban kaya ko kun fasa tafiya Lagos din ne" Kai tsaye nace"Aa ni ce dai na fasa binsu chan ne,ammh su inaga suna Hanya ma Goggo" Cikin mamaki Goggo tace"To saboda mene Fa'iza..? Kaina na kasa ina kokarin Danne abunda ya tasomin nace"Na GAMA AURAN ne Goggo." Cikin Razana Goggo tace"Wata irin mgana ce wannan Fa'iza.?Daman ana gama ibadar Ubangiji ne ko a gaji da ita..? Ina tsiyayan hawaye na dago ina fadin"Wlh Goggo na gama aure tsakanina da Ishaq. Bama shi ba na gama auren ko wani Namiji a duniyan nan,ba komai acikin aure sai kaskanci da zalunci da Tozarci Goggo" Na karishe fad'a cikin Kuka mai Tsanani,sai Goggo ta saka salati Tana fadin"Haba Fa'iza wannan wata irin mgana ne..?aure fa Ibada ne mai yinsa bai taba Tabewa ba. Me akayi miki Fa'iza?meyasa tun a baya baki yi wannan Borin ba sai yanzu da naga komai ya daidaita har ita Saudatun kuna zaune lafiya da ita.?shi kan shi Ishaq din ya sauko Fa'iza sannan Meyasa kika yanke hukunci batare da kin tuna da ya'yanki ba.?wazai rike miki su Fa'iza? Cikin Kuka da karfi nace"Zainab da Mama zasu rike su Goggo. bazasu mutu ba..chan ne dolen su tunda gidan Ubansu ne,ni kuma ba gidanmu ba ne nan ne Dole na Goggo" Goggo ta tsorata da yanayina da bata taba gani ba cikin wata irin murya tace"Fa'iza bautar auran kika gaji da shi?Saki kika nema? Kin san yadda al'arshin Allah ke girgiza saboda Sakin aure..? Nima cikin kuka na bata amsa da cewa"To Goggo ibadan aure ai ba Bauta mutum ba ne..?sannan ba laifi ba ne in nace na gaji da auran ina da Dalili na Goggo" Sai Goggo ta fara fad'a tana fadin"Dalilin menene..?wani Dalilin ne zai sa ki bar auran ki da ya'yanki Fa'iza abunda baki yi ba a baya ba sai yanzu..?anya kin yi tunani kuwa..? Mikewa nayi ina ganin jiri na Dafe kujera ina fadin"Bazan fadi Dalilin ba Goggo ,ammh shi ya sani in ya fada muku zan kara muku bayani in kuma bai fada muku ba shikenan domin alkwari ne nayi masa baza'a ji wannan mganar a bakina ba" Hijabina na kwasa da Karamar jakana na wuce dakin Goggo ina jinta tana fadin"Fa'iza zo ki bi mijinki..Bazan zama goggon banza ba" Da karfi nace"Wlh tallahi ba inda zani Goggo. In kuma kika matsamin na fita Daga gidan nan to ba lalle ki kara ganina ba" Jin abunda nace ne yasa Goggo ta saka Salati tana fadin"Ai shikenan tunda kin raina ni kina da uba,Bari Isa ko Salisu su shigo zan sa su kirasa,shi in yazo zaki fadamai Dalili sannan in yace ki koma gidan mijinki shi bazaki yi mai gaddama ba" Ina jin haka na shige Dakin Goggo na Rufo kofar na fada kan gadonta na saki kuka,tun ina yi a Hankali har na fara yi da karfi,da dukkan zuciyata ya'yana nake tunawa ina tuna tun Tsawon Rayuwata in ba makaranta sukaje ba bamu taba awa daya bama tare da juna ba,sai yau da nake jin Nisa zasu yi dani na har abada,ina kwance ina tuna zama da nasu da yanayin yadda rayuwata da yarana ta kasance wlh sune duniyata ni ce tasu duniyar ina Tausayinsu na yadda Rayuwarsu zata kasance a bakon waje batare da ni ba,basu saba da kowa ba sai ni,nima ban saba da kowa ba,sai ya'yana bansan nima ta yadda Rayuwata zata fara tafiya daidai ba batare da su ba. Tuna hakan yasa nake ta rafzan kuka,kukan da ya rikitani yasa naji zazzabi na rufeni,daman na shigo da jiri da ciwon kaina sai kuma abun ya yi min yawa,ina jin hayaniyar su Goggo a falo da mganganun mata da maza ban iya motsi ba,har ta kai ga suna ta buga kofar dakin Goggo Lokaci daya da kiran sunana ba amsa ba. Naji muryan Yaya Mariya,naji na Hafsah da ta Yaya Isa ammh na kasa budewa saboda bazan karbi kalmar hakuri ba wannan karon sannan bazan yi mgana ba kuma bazan iya gaddama da su ba. gwara nayi nesa da Tambayoyinsu a wannan Lokacin,ni abu daya nake son ji ko gani ya',yana ina so naji Halin da suke ciki,ina cikin Dakin nan har Dare sai da aka kira mangariba na iya jan kafana na shiga Toilet nayi alwala na fito na rama Salollin dake kaina duka a zaune nayi su,wayata na ciro daga cikin pos dina,da naji ana kira Anty Fadila ce ina gani har ta gama ringing ban dauka ba kawai na ijiye wayar a gabana ana cigaba da Kira. Ba wanda bai kirani ba acikin su har da Yaya Abdul'Ahad,Abba ne ya kirani a karshe sai naji kuka ya kara kwace min Cikin kukan nake fadin"Kayi hakuri Abba..Kayi hakuri" Domin bansan me zan ce mai ba in na Daga wayarsa ina da Tabbacin Tuni Labari ya kai musu shiyasa suke ta kirana ni kuma bani da amsar Tambobyinsu a lokacinm Kaina na Hada da gwiwa na cigaba da Kuka,gabadaya duniyar tamun zafin da bata tabamin ba. Lokaci daya rayuwata ta baya na sake dawowamin kamar yanzu abun ke faruwa, an yi an gama. na gama Daukan Tozarcin da na Dauka baya ina Bukatar Rayuwar yanci nima. A chan Falo kowa Goggo ta kasa zama gabadaya Hankalinta a tashe yake,Har da su Yaya Isa ita kanta Yaya mariya ta kasa komawa gidanta Tunda Hafsah tazo ta gayamata Fa'iza tazo ammh ta rufe kanta adaki tana ta kuka. Goggo ita ta saka Yaya isa ya kira mata Abba tamai bayani yace yana warri baya gari ammh zai kirani a waya yaji meke faruwa? Ammh kafin nan bari ya kira Ishaq din yaji to yace yayi ta kiransa bai same shi ba,Zuwa yammah kuma Anty Fadila ta kira Abba tace Mijin Fa'iza da yaranta sun sauka a lagos ban da ita shi yake mata bayanin