← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 175

Sashe 94

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ki na yi muku lamani ku zauna ammh kuyi adalci ku biya da zarar kun samu" Da sauri nace"Wlh zamu biya.In sha Allahu" Daga haka ya gyad'a kai ya yi ma samarin mgana suka fita tare ajiyar zuciya na sauke, na koma kan kofa na zauna ina kuka ahaka Yaya Ishaq ya shigo futu futu kafafunsa, dani ya fara cin karo ina kuka cikin tashin Hankali yace"Kuka Fa'iza me ke faruwa..? Ya fad'a yana zama kusa da ni da Sauri na Share hawayena ina kallonsa Daga sama har kasa ganin yadda yayi Futu futu kamar wanda yayi tafiyar kasa cikin mamaki nace"A kasa ka tako..? Bai bani amsa ba ya kara fadin"Me ya faru ne..? Sai nayi masa shuru yana shirin kara mgana ba sai ga Badariya ta fito ita ya tambaya ta maida masa yadda akayi har yadda na duka ina rokon su sannan ya amince ya d'aga mana kafa cikin d'aga murya ya kalleni yana fad'amin"kika duka mai Fa'iza..?kika dukamai fa..? Saboda wani dalili..? Yafad'a cikin bacin rai sai kawai na mike ina fadin"Ba dukawa bace roko ne da neman alfarma, in ban duka ba da yanzu kazo ka ganmu a kofar gida an fara yi mana watsi da kaya" Daga haka na shige daki sai kawai ya bini da kallo ga takaicin yaje bai samu Anty Binta ba, sun fita da mijinta a kasa ya tako tunda batagwarawa har Ajiwa,sai kuma yazo ya iske wannan tashin Hankali D'akin mama ya shiga ya isketa tana kuka dakyar ya Lallasheta tayi shuru tana fadi'n wai mai gidan ya zageta yasan halin Mama shiyasa ya kalleta yana fad'in"Mama bafa kowa ya ke da ragowa ga manya irin ku ba. Sannan kema Mama me ya kaiki sa'in sa da shi.?mu ne fa bamu da gaskiya hakkinsu ne a kanmu bamu biya ba kuma sun yi mana Hallaci bai kamata ki nemi zaginsa ba" Ganin ya rufeta da fad'a yasa ta sauya mganar da cewa"Ka samu Bintan? ya kuka yi..? Kai tsaye yace"Bata nan sun fita da megidanta a kasa na dawo duk nagaji" Mama ta yi tagumi kafin tace"Allah ya warware mana ko zakayi ma Zainab mganar ne..? Da Sauri yace"Aa Mama Allah zai kawo wata hanyar" Sai bata kara mganar ba,sanin halinsa Tunda yace a'a to bazai kara bi ta kanta ba,Batare da sanin kowa ba, ta Kira Zainab ta fada mata komai ita Zainab d'in ne ta kirani tana fadin"Haba Maman Amir sai ki boyemin wannan abu haka..? Sai nayi mamakin a ina taji nadai san bashi ya fad'a mata ba,sai da naji tana fadin Mama ta kirata ta fad'amata sannan nayi mata bayani sai tace bari ta kirasa to bansan ya suka kaya tsakanin su ba, ta dai turo masa kudin kuma ya biya mana kudin Hayan ranar da ya Tura ma mutumin kudin har sai da yace mai"Gaskiya kayi sa'an mata mai hankali da iya mgana." Da ko ya dawo gida tasani yayi agaba da masifa da fad'a wai na fito ina ma wani gardi magiya kallonsa kawai nayi kafin nace"Yaushe ka fara kishin Fa'iza..? Kai tsaye yace"Ke Fa'iza ki fita daga idona. ko a baya bana barin ki sakakaka.nasan abunda nake yi kada ki kara batamin rai da mganganun ki na banza" Daga haka ya barmin wajen yana ta masifa a raina nace topah Sabon Salo Tusa a lasifika. Hankalin mu ya kwanta tunda Allah ya Rufa mana asirin duka,Badariya Sunanta ya fito a Bach B, an tura ta Camp yola Raliya kuma Abuja suka barta,Hajiyar su Raliya ta bata kudin mota da kudin kashewa na har ta dawo,Hajiya ta Dauke mana wannan nauyin ta tafi da tarin nasihan yayanta da mama akan ta kula da kanta,Sati uku tayi ta dawo gida,Sai kuma cuku cukun yadda zata dawo kusa gida tayi bautar kasarta. Haka muka cigaba da Rayuwa yau fari gobe Tsumma Goggo na lekomu ita da su Anty Nasara nima nakan lekasu,Makota na su Sa'adatu basu manta dani ba,Nima ban manta da su ba, ina leka su wani Lokacin sana'ata ne baya barina fita har kuma yau Yaya mariya bata kara takowa gidana ba.sai dai mu yi mgana da ita ta waya. Hajiyar Dala ko ba wanda ya kara jinta ko garin ta shigo bata zuwa Anty Binta kuma ta maida hankalinta wajen Shirin Bikin Halisa daya rage Saura wattani bata cika zuwa ba ma. Ina zuwa gidan Hajiya gaisheta Lokaci bayan Lokaci anan ne har tace Yaya Ishaq ya kawo takardunsa daga barayinta tagani ko za'a dace da murnanta nazo nayi mai magana sai kawai ya kalleni kafin yace"Ina fatan ba zuwa kika yi kikace kina so ta nema min aiki ba..?. Wani Haushi ya bani, ba ka da ko sisi sai shegen girman kai hararansa nayi ina fadi'n"Sanarwa na bada a masallaci baka ji ba..? Sai ya maida abun wasa ya taso zai rikeni na matsa baya kafin nayi mgana yayi saurin tareni da fadin"Kai na bisa wuya afuwan na manta ne" Sai kuma ya bani Tausayi yadda yayi mganar,ni da kaina naje na kai ma Hajiya Takardunsa,a amsa da yakinin acigaba da addu'a za'a dace. Ana cikin haka Badariya ta samu aka ijiyeta kano inda zatayi bautar kasarsta sai Mama tace ta zauna gidan Hajiyar Dala Badariya tace bata son zama,Maman ta had'a ta da Yayan nata yayi mata fad'a Nima nayi mata nasiha sosai ina fadin"Kiyi hakuri kije ki zauna ke mace ce yafi ki zauna a inda baki sani ba,duk tsiya ke yarta ce bazata ce zata kore ki ba" Da haka Badariya ta amince ta tattara kayanta ta tafi kano Bayan,Maman ta samu tayi mgana da Hajiyar Dala Anty Binta dai sama sama take da Badariyan acewarta ta mata rashin kirki,tunda abun da ya faru tsakaninta da Halisa da har yanzu ita da Badariyan basu koma Daidai ba, ba sa gaba suna mgana da juna,ammh sama sama. Raliya kuma kaduna aka ijiyeta,Sai ta zauna gida kawar Hajiya gidan su Laila kenan. Tafiyar Badariya ba jimawa sai ga waya daga Abuja akan wani kamfanin Sarrafa fattu da Mahaifin zainab ya taba kai takardunsa sun nemesa,Dole ni nayi murd'a murd'a na basa kudin mota ya tafi,bayan tafiyar sa mun yi mgana da shi sau d'aya ya samu sun yi interviuw sai jiran kiran su bai dawo ba ne saboda baya so bayan ya koma su sake kiransa,To yana zaman jiran kiran nasu ne,Zainab ta fara rashin Lafiya har da kwanciya a asibiti,Ashe ciki gareta da sauran rabo a Tsakaninsu. Daya kirani ya fad'amin ne bayan suna asibitin da ita nace in ta farka ya bata waya na gaisheta sai dare ya samu ya Had'amu na gaisheta bai fadaminciki gareta ba, ita ce tace min"Maman Amir bakin ki dai ya amsu,zai zo miki da Farhan ki yaye min shi tunda Honey yaki bari na huta hakanan" Daganan sai na d'ago mganarta nayi murna sosai da Fatan alheri da ta basa wayan nayi masa murnan karuwa sai kawai sai yayi yar murya yana fad'in"Saura ke. kema na kusa har ba miki alluran.." Da Sauri na katse wayar ina mamakin a gaban matarsa yake fadin hakan?a fili na murmusa,sannan acikin raina nace haihuwa ai na bar ma, matan so ba irin mu da rabo kan rantse ba. Kamar cikin na bata wahala ne an dawo da ita gida kwana biyu jikin ya rikice sai da aka kara maidata ita asibitin shiyasa bai dawo ba,Kuma har yanzu basu kirasa ba kuma yace an kira Mutane biyun da suka je interview tare,ni dai na lallashe da cewa Allah ne mai yi kuma shi ke ba da aiki in alheri ne Allah ya basa in kuma ba alheri ba ne, Allah ya musanya masa da wanda yafi alheri. Ya shafe kusan wata a Abuja ba yara ba ni kaina ina kewarsa kaji Fa'iza da Samun waje wai ina kewar mijin aro.?da Sauri na cire tunaninsa a raina na cigaba da Sabgan gabana ni nake rike da karfin gidan duk da muna da sauran kayan abinci, sannan daga Gidan Hajiya ma ta aiko mana da shi,Sannan na samu aikin yin Humra da kwallacha da kudin nake ta riritawa muna cefane da Hidiman yara.. ****** Wata ranar asabar data kama kwanan Yaya Ishaq Talatin da hud'u da tafiya Abuja mun yi waya da shi a daran jiya har da yara suka gaishe da Antyn nasu tana gida an bata Bedrest,Da gaske yake da yace yayi kuskure kuma yayi nadama zai gyara kuskuransa,yana kokarin kirana in dai baya garin sannan zai ji ya gidan yake tafiya mganarsa kenan"Nagode Fa'iza Allah yayi miki albarka" Safiyar ranar sai da na zane Musty sannan yaje Tahfezz da shirin sa bazai je ba,ya zauna yana min rigima na shiga jikinsa da Bulala,Daman tun jiya nake jin jikina ba dadi,da Safe kuma sai fama da sanyin jiki Hafsah ta shiga makaranta zasu su yi wani aiki ita da Sauran yan ajinsu tunda ta fita ina kwance afalo ban yi komai ba sai dai in masu siyan kunin aya da zobo sun yi sallama na mike na basu, Tunda jiya nayi da yammah shiyasa yau da Safe nace bazan yi ba sai da yammah. Wayata na cikin Dakina na baro ta ana ta kirana ban ji ba,barci ne ya kwasheni nan saman kujera acikin barci sai na ganni a gari Dabam ba karofi ba kuma ba katsina ba,bakon wajen da mutanen da ban sani ba,Kamar kuma acikin barci naji ana kiran sunana a firgice na mike ina Salati sai naga Mama a saman kaina, na mike zaune ina raruman da'nkwalina da ya fad'i saboda barci lokaci d'aya ina fadin"Mama.." Kallona tayi cikin nazarina kafin tace"lafiyarki kuwa.?Isa tun dazu yazo yana ta sallama baki ji ba..? Sai gabana ya fad'i na zare ido ina fad'in"Wani Isan.?Yaya isa." Kafin na karisa ya d'ago labule ya shigo a gaggauce yana fad'in"Fa'iza maza dauko hijabin ki Karofi zamu tafi yanzu" Gabana ya fad'i ras! Cikin Dafe kirji nace"karofi..?me ya faru ne..? Na fad'a ina wuce Mama zuwa gaban Yaya Isa itama Mama sai tabi bayana tana fadin"Isa lafiya kuwa.? Cikin natsuwa yace"Lafiya lau kada ku damu.Goggo tace na dauko su ita da Hafsah akawai wanda zai gan su ne" Dagani har Mama sai muka bisa da kallo zan yi mgana da sauri ya tare ni da cewa"Ki sako hijabi muje
Chapter 94 · 0% Book details