Sashe 132
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kira shema'u D'akinta ta na matsa mata kafafunta da sunan sun kumbura. sannan bayan ta gama ta saka ta Had'a mata ruwan wanka ta shiga ta gasa jikinta, basu hadu ba sai wajen takwas da Rabi na Dare ya dawo daga sallar Isha'i ya iske yaran na kallon Cartoon a Falo Farhan ne yazo wajensa yana Fadin"Daada yunwa nake ji" Anum ya kallah Dake zane a Takarda ya Kira sunanta ta taso fuskarsa ba Annuri yace"baku ci wani abu ba ne..? Anum tace"Eh Daada naso na Dafa mana Indomie Yaya, yace ka hana mu kunna gas" Yaya suna nufin Amir tunda shine Babban su,Ba shi ma a Falon yana Dakinsu yana karatu yana kaunar yaron Sanyin Halinsa kamar na Fa'iza ne Ya sani shi ya hana su kunna gas a farko dawowar su Anum na karambani Tunda duk ta iya wasu ayyukan wajen Fa'iza kai ya kad'a kafin yace"Ina Antyn ku..? Anum tace"Tana Dakinta tun dazu" Tsaki yaja a fili Zainab bata da wani amfani ko zama da yaran fa batayi taji matsalan su,Bai ga shema'u ba ya tabbata ita ta sakata wani aikin illai Anum tace wanki take yi ma Anty a bayan Compound ko Tsayawa bai yi ba ya Sauke Farhan Jamal ya kwalama kira ya fito da jallabiya a jikinsa shuru dai har yanzu sunansa bai Fito har yan Batch b sun tafi camp. Kudi ya basa yace ya yo takeaway din abinci yadda zai isa duka gidan Jamal ya karba yana jin Tausayin ya'yansa da kuma kara kyamatar aure irin auran yayan nasa ta wani Bangare bai jin Hauahi Anty Fa'iza ba. yasan hakan ma wani Darasi ne Allah ya fara nuna ma yayan nasa Key din motar daman na Hannunsa daganan ya fice sauran yaran su Ahmad Hankalin su na wajen kallo basu bi ta kansa ba,sai yace Anum ta kula da su ya shige Dakinsa shima wanka yayi ya watsa ruwa ya saka Gajerun wando ya kwanta Ruf da Cikin kansa ke saramai sannan makogaransa ya Bushe ammh kuma bai jin shan komai. ko cin wani abu shi dai ga shi nan yana jinsa kamar wanda ya Tafka wata mumnunan asara. Zainab bata nemesa ba shima yaki nemanta ta kansa yake yi,Bayan jamal ya Dawo ne ya shigo Dakinsa ya kawo masa key din mota da chanji yana daga kwance ya ce ya ijiye key din saman dirowa kudin kuma ya rike ya yi masa godiya ya fice. Shi da yaran suka rika Budurin abincin Jamal ya kira Anum yace ta samu Filet da Ruwa da lemu ta kai ma Daada nasa tunda Zainab bata fito ba. Nata ma A kitchen suka barta mata basu san tayo takeway a Hanya ba taci ta koshi abunta. Yana kwance Anum ta shigo da abinci Farar shinkafa Miyar kaza sai maltina da ruwa. Ijiye wa tayi a saman Cafet tana Fadin"Daada ka tashi kaci abinci" Yana daga kwancen ya Dago yana kallon Diyar tasa kwallah ta cika masa ido Fa'iza da ya'yanta sune sanyin Idanuwansa ko yaki ko ya so. Saurin daidaita yanayinsa yayi da Fadin"Anun maida abincin nan ban ji Dadi. bazan iya ci ba" Sai ta Rude ta fara fadin"Meke damun ka Daada..?in kawo maka panadol..? Da Sauri yace"Ina da shi in na tashi zan sha ki barmin ruwa ki je ki kula da kannen ki,ku kashe kallo ku yi karatu Gobe akwai karatu a gidan Anty Fadila" Da toh ta amsa mai ta fice da abinci bayan ta ijiye mai ruwan har ta fice tana waigensa,Shifa sai da yaransa su kula da shi ban da Zainab,Musamman Amir da Anum suna da karancin shekaru ammh Tarbiyan da suka samu yasa suna abu kamar manya,Da farko in yaga Fa'iza na matsa musu kan karatu da sauran su,sai yayi ta ganin iyayin ta nw sai yanzu yaga amfanin shi,Ko da bata nan yaran basu yada Tarbiyanta ba. barin ma Amir yana kokarin taimaka ma kannensa kan karatu musamman ma Da yanzu yake ganin ba Umman su dukkan girman ya hau kanshi,sai ya kama kanshi yaran suna girmama shi ko mgana yayi yanzu zasu shiga taitayinsu,Shima ganin haka yasa in dai ya Dawo yana tare da su ga Jamal ma yana shiga cikin su shima yana kokari wajen nuna musu abunda basu gane ba. Zainab dai ya'yanta ma bata san yadda zata kula da su ba ballatana ya'yan wasu,Dalilin haka yasa yaso Fa'iza ta dawo lamarin fin karfinsa yayi. Anum na fitowa Daga Dakin Ishaq suka ci karo da Zainab da Cikinta a gaba tana tafiya Dakyar sannu Anum tayi mata ta amsa tana fadin"Ya kika Dawo da abincin Anum..? Anum tace"Anty Daada yace bayajin Dadi bazai ci ba" Bata yi mgana ba ta raba ta gefenta ta wuce Dakin yana kwance yadda Anum,ta barsa yaji shigowarta da mganarta"Honey whta wrong with u Anum tace kace a maida abinci baka da Lafiya..?. Tafada Lokaci d'aya tana zama wajen kafafunsa sai ya janye ya yunkura ya mike zaune ya Dafe kansa,matsowa kusa da shi tayi tana fadin"Honey..Honey..! Saurin Dagowa yayi ido jajir yace"Lafiya na kalau,na Rabu da Fa'iza yau na saketa" Zainab ta zaro ido kafin tace"Ka sake ta fa Honey..?Maman Amir din..? Da kai ya gyad'a mata yana jin wani Rauni na saukar masa. Zainab sai ta shiga Tafa Hannu kafin tace"Kayi wauta honey why..? Wani irin banzan kallo ya jefeta da shi,kamar ya daketa sai yaji duk Haushin Abba ya huce a kanta cikin Fad'a ya mike yana Fadin"Naji ni wawane ko Zainab?nasan haka dole zaki ce nayi wauta mana duk ba ke kika jamin ba. Sanadin auran ki yasa na jinginee aurena da Fa'iza na kuma zabe ki a kanta Dole yanzu kice na zama wawa mana" Ya karishe fad'a cikin bacin rai idonsa ya Rufe kamar ya kama Zainab da Duka haka yake ji kamar duk itace Silan komai,Zainab ta saki baki galala tana kallonsa ta mike dakyar da Cikinta a gaba tana Fadin"A'a Honey kada ka doramin Laifi what i do..? Abunda ka shuka ne kake girba ni ba ruwana" Tafad'a Lokaci daya tana dagamai kafad'a irin bata damu ba. ransa ya kara baci ya nuna kansa yana fadin"Ni ne kike fad'ama haka..? Zainab ta fara tafiya tana tura cikinta gaba tace"ban fad'i karya ba. Honey ka sani kaima abunda ka yi ma Maman Amir baka kyauta ba" Har ta fice ya kasa motsi,saboda kalamanta gaskiya ta fad'a duk abunda ya faru shine sila,ga shi yanzu abunda ya faru Allah ya barsa da zabinsa ya ga yadda zai yi kansa ya kara Dafewa kafin yace"Allah na Tuba. Allah ka dawo min da Fa'iza" Aransa yaji bazai karaya ba Kafin Fa'iza ta fita idda zai kara gwada sa'arsa. Ranar haka kowa ya kwana ad'akinsa yaran kawai ya fita ya Duba sai da ya Tabbatar sun kwanta da Safe kuma Shema'u ta dafa ruwan zafi suka sha Tea,wanka kuma Anum da Amir ke yi musu suna taya kananan shiryawa. Jamal ya kwashesu zuwa gidan Anty Fadila dayake bai da Fita Office sai ya koma Daki yayi kwanciyarsa yana jinyar zuciyarsa Zainab bata kara nemansa ba shima bai nemeta bala'in Haushin ta yake ji. Ita kuma aranta tana fadin meye nata da zai zargeta..?tun adaran ta kira Daddy ta sanar da shi abunda Ya faru Tsakaninta da Ishaq,Dr.Lawal ya yi Tsaki kafin yace"Ki kyalesa dota in ya matsa miki ki biyo jirgi ki Dawo gida. ni ina sonki na kuma san Darajan y'ata.." Aransa daman yasan Engr Usman bazai kyale Ishaq ba. su ina ruwan su basu sukace yak'i Daraja matarsa ba. Wannan shine in da ka raina inda zaka na ran maka" ******* Bayan Sati biyu. Kimanin Sati biyu ina cikin Iddata zuwa Lokacin tuni Labari ya bazu a ko'ina wanda ma ba'ayi Tunani ba duk sun samu Labari,su Nana Fatima bakin Ammi sukaji duka sun kirani suna min nasiha sai na nuna musu ba komai,Anty Binta ko kunya kirana tayi a waya tana cemin yanzu sai da na kashe wannan auran..?ni kuma sai na bata amsa da cewa daman Tuntuni ya kamata ya mutu Bai mutu bane Daganan bata kara mgana ba Yaya Asiya kuma duk sai jikinta ya yi sanyi tace"Fa'iza zawarci ba Dadi" Kai Tsaye nace"Ni ba zawarci zan yi ba makaranta zan koma, na karo ilimi sannan zan bunkasa kasuwancina ke dai kiyi min fatan alheri" Jin haka yasa sai ta bini da addu'a kawai ganin Nima ban damu ba. Hankalina kwance abuna har yar kiba nayi ina mgana da su Anum ta wayar Zainab tunda itama ta kirani tana Fadin"Yanzu shikenan mamam Amir..?ina mirmishi nace"Ba shikenan ba Maman Fadil zumunci Allah ne ya had'a sannan akwai ya'ya tsakani ke ce kuma uwar su ko Auran su ya tashi ni yar kallo ce" Ban bata Damar da zata rokeni ba na cikata da mgana sai ta kasa mgana Sannan yaran kuma ko da yaushe sukace Umma yaushe zaki zo..?Sai nace ina nan zuwa to sun ma Fahimci ina Fade ne kawai sun daina Damuna ammh ban yi wasa ba duk sanda mukayi waya zan ce su kula da salla da Azkar ban da kawayen banza su taimaki kannensu sannan na roki Anty Fadila dom Allah ga amanar ya'ya na nan ne tace Haba kada na Damu kamar suna gidanta ne tunda nan suke weekend. Har Badariya sai da ta kirani tana jimami nace mata tayi min Fatan alheri a bakinta nake jin Hajiyar Dala nata Fad'an wai da na kashe aurena ina da wanda yafi Ishaq din ne.?taga mai kwasata wato ina Takama muna da Uba mai arziki. Ban ce komai ba sai mirmishi kawai da nayi, na jima da sanin Hajiyar Dala bata kaunarmu kuma bazata taba ba shiyasa nima na shata mata Layi,ranar da Badariya ta Fad'amin ta kira Goggo tana fad'a ta kuma ce a bani waya ta maimaita min abunda Badariya tafad'amin ni ko ban yi mata shuru ba nace"Bani da shi Goggo,kuma bana Fatan samu ma. saboda sha'awan aure da Namiji dalilin ishaq yasa ya fita a raina" Sai mgana ta yasa jikinta yayi sanyi bata kara mgana ba sai cewa tayi"To su yaran fa wa kika bar ma su.? Nace Mata Allah sai ta kashe wayarta a raina naji Fes,duk da Ishaq din na Damuna da kira ban taba Dauka ba. Text din ban hakuri safe