Sashe 81
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yayi da hayaniyar iyayan.Ni kaina barci nake yi sai da na tashi a firgice" Kamar zan tambayeta sai kuma na fasa,Daman nasan zata koramin yadda akayi Kitchen na shiga na Dauko Purewater nazo na zauna ina basa yana karba da sauri alamun kishi yake ji cikin alamun Tausayi nace"Allah sarki bawan Allah kishi yake ji" Badariya tace"Komai ma zai ji tun safe an fara fada,Daman ni nasan sai haka ya faru yadda Yaya Ishaq ya gina auransa ba kan turba mai kyau ba ne Anty Fa'iza" Sai na kalleta ina fadin"Hala me ya ke faruwa..?. Sai ta gyara zama tana fadin"Nima ban san kan mganan ba ina dai jin Kan tafiyar Anty zeey ne.Babanta ya Turo mata Mota tuni Direban ma ya iso zata koma Abuja to ina ga shine Yaya yace wlh bazata tafi ba sai dai in ta tafin ta fara shirin dawowa nan gabadaya ku zauna tare. shi bazai rika binta ba tunda baya aiki achan yanzu ita kuma ta Daka Tsalle tace bai isa ba sai ta tafi kuma bai isa ta ijiye aikinta ta Sauya rayuwarta Saboda shi ba,in bazai Bita ba sai dai ya bar shi" Sai na jinjina kai jikina duk yayi sanyi Badariya tace"Ta wani fanni fa tana da gaskiya abunda ya zaba mata ne Tun farko rana tsaka ba shi da Hujjan da zai ce a'a duk wanda ya siya rariya yasan zata zubda ruwa" Kafin nayi mgana Zainab ta shigo Dakin tana kiran Badariya ta kawo mata Fadil na mike na mika mata shi ta fita dashi nima sai na bita Daidai Zainab din ta fito da karamar akwatinta ta kalli Badariya tana fadin"muje mota da shi" Taci gayunta ta yafa mayafinta abun nasa ya shafeni ko sallama batamin ba ta juya ta fara tafiya kenan Ya fito Daga Daki cikin Daga murya yace"Wlh Zainab in kika saka kafa kika fita daga gidan nan batare da izinina ba kin tafi kenan" Dam!naji mganar nasa na d'ago ina kallonsa ita ma sai ta tsaya cak kafin ta juyo tana kallonsa Mama ta fito daga Daki hannunta a saman kai tana fadin"Na shiga uku ni Saudatu me zan ji haka..?Don Uban ka ka janye kalaman ka ko ranka ya baci" Idanuwansa sun sauya launi yace"Bazan janye ba Mama haka nace.Wlh bazan zama jani talau ba..Ni ke auranta ko ita ke aurena..? Mama ki duba fa wannan mgana taya za'a kafa min sharadin zuwa Abuja ina naga ko kudin mota.?zirga zirgan kansa ina naga kudin yinsa..?in a baya ina da aikin yi na dauki wannan Dawainiyar yanzu ta sani bani da shi To meyasa bazata zo ta zauna da ni a inda nake da shi ba in dai har da gaske tana so na? Yafad'a cikin bayyana bacin ransa,Mama kuwa ta kasa mgana Ni kaina ban ce komai ba ni da Badariya muna tsaye cirko cirko,kamar wasu zakaru,ita ko Zainab sai batayi mgana ba ta jawo akwatinta ta shige Falona ta fito da waya tayi kira sai ta sauya Harshe turanci da Fillanci. Shi kuma Mama ta shigar da shi Daki bansan me take fadamai ba,chan kuma sai ga Anty Binta suka sake kulewa Daki itako Zainab tana falo na kafa d'aya kan daya tana girgizawa karamar akwatinta na gefe sai hura Hanci take yi bini bini ana kiranta a waya tana mgana yadda batamin mgana ba nima sai na kama kaina na fito ina harkan gabana. Zuwa azahar ina waje ina Dafa zobo na sai ga Mahaifin Zainab ya fad'o gidan kamar daga sama ashe jirgi ya shigo ya iso kano,Direban da yazo daukan Zainab yaje ya Daukosa Kai tsaye ya shigo cikin Hanzari ina gaishesa ko amsani bai yi ba cikin Kaushi da Dagawar murya yace"Ina Ishaq din..? Muryansa ya fito da Zainab Daga dakina tana ganinsa ta nufesa da Sauri ta fada jikinsa ta fashe da kuka tana Fadin"Daddy wai ni Ishaq zai ce in na fita a bakin aure na..?ni Daddy Ishaq fa..? Sai ta kara saka kuka,Cikin Kakkausan murya yace"Shi..Am here bai isa ya fad'a miki wannan mganar ba,Who is he.? Mganarsa da kukan Zainab ya fito da Ishaq da Mama da Anty Binta suna ganinsa suka fara kame kame Mama ke fadin"Alhaji sai da ta taso ka? Kallonta kawai yake yi bai yi mgana ba Ishaq ne ya nufesa yana fadin"Daddy k.." Hannu ya d'agamin cikin tsawa kafin yace"Kayi min shuru Butulu kawai." Sai ya tsaya ya kasa gaba ballatana baya Su Mama sai ido yayi kasa,Hannun Zainab ya kama kafin yace"Ina son mgana da kai domin ba zama nazo yi ba" Da Sauri Mama tace"Mu shiga daga ciki Mana Alhaji" Wani kallo ya watsa mata Lokaci d'aya yana fadin"Ba ni da wannan lokacin.Nazo ne Ishaq ya maimaita abunda zeey tace ya gayamata.." Yafada yana bin su da wani kallo ni dai ina gefe ina kallon ikon Allah. Ishaq ya sausauta murya yana fadin"Daddy da ka shigo ciki don Allah" Cikin Tsawa yace"Ina da Lokacin shiga ciki ne ballatana naji shirmenka?nace ka maimaita abunda ka fad'amata so nake naji da kunnena" Ishaq sai ya gyara Tsayuwa yana fadin"Daddy gaskiya na fada mata nace baan iya juran binta Abuja ba sai dai ta dawo nan mu zauna tare" A wulakance yake kallonsa kafin ya nuna gidan cikin Yatsina yace" A wannan kejin gidan zata zo ku gamutsu da iyayanka da matarka..? Yafad'a yana masa wani kallo lokaci daya yana kare ma gidan kallo a wulakance,Gabadaya su Mama sun daskare sun kasa mgana Yaya ishaq kuma sai ya sunkuyar dakai ya kasa mgana cikin kakkausan murya ya cigaba da fadin"Na ce a wannan a kurkin gidan kake tunanin y'ata ta bar komai nata ta dawo ta zauna dakai saboda kai ne autan maza ko? Yaya Ishaq ya dago yana fadin"ammah Daddy.." "Dakata min shashasha butulu a irin wannan gidan ka ganta ka aureta..? Nace a irin wannan gidan ka ganta ka aureta da zakace hakkun Dole sai tazo ta zauna da kai a haka..? Ya fada bayan ya katsesa,cikin Fusata da Bacin rai. Ya nuna Zainab cikin Daga murya yana fadin"Lokacin da ka y'ta kace kana sonta acikin rayuwar hutu da jin Dadi ka ganta.cikin iliminta da tarin gata ka ganta kaji sha'awanta ka nemi auranta na aura maka ba domin ka chanchanta ba, sai domin nayi maka alfarma ina kallon ka kamar D'ana ashe baka da mutumci ban sani ba..?yar tawa kake so ka saka ka maidamin ita bazawara..? Yaya Ishaq yace"ni ban ce zan saketa ba"Ya taresa da fadin"Ba ka ce ba kalaman ka me suke nuni..?kace in ta fita kada ta dawo..?so kake ta ijiye rayuwarta da Aikinta da komai nata tazo ta tare a wajen ka, to ka ba ta mene..?Kada kaa manta ko da ka ganta chan ta fara gudanar da rayuwarta bazata iya zama a ko'ina sai a inda ta saba.Bazan lamunci wannan rainin da iskancin ba,in ba ma kana Butulu ba an dauke maka nauyin ya'yanka na Dauke ma nauyin gida da zirga zirgan ai duk hakkin ka ne sannan na Dauke maka nauyi ita kanta Zainab din hakan ma baka gode ba kawai naka ka shiga mota ka rika zuwa kana dubasu ne zai zame maka matsala..?batulci zakamin ko kuwa zafin Talaucin ne yasa ka fara Nuna min akan ya'ta..? Ya fad'a yana kallonsa cikin fusata,Sai wajen ya Dau shuru Mama bakinta yayi nauyi sai Anty Binta ta rika ma alama da tayi mgana itace tayi karfin Halin cewa"Alhaji ayi hakuri duk mganar bata kai haka ba a zauna a warwareta" Ko kallo bata ishesa ba yace"Zan iya warware mganar ko wata iri ne ba sai na zauna ba,Kan ya'yana zan iya shari'a da ko waye na lura D'anku baisan mutumci da Hallaci ba,duka abunda nayi mai bai gani ba in na barsa da Dawainiyar Zainab din zai iya Dauka ne..?to bai isa ba ku fadamasa bai isa ba.ba haka na aura masa yata ba kuma bai isa ya dawo min da ita haka ba, zan tafi da ya'ta kuma ya zama Wajibi ya janye kalamansa a kanta,Domin shima yasan hakan bazai taba yuyu ba ni ba sakaran Uba ba ne kan ya'yana sai nayi shari'a dakai wlh." Abun mamaki Yaya Ishaq sai gashi ya kasa mgana Har da mama,Anty Binta ne ke bada Hakuri yace sai Ishaq ya janye kalamansa,Mama ta kallesa tana fadin"Kana ji ana mgana kana banza da mutane shashasha kawai" Ransa bace yace"Na janye kalamai na" Da sauri Mama tace"Ya janye Alhaji don Allah kayi hakuri Zainab kema ki yi hakuri don Allah" Bai ko saurare su ba ya kalli yarsa yana fadin"Ina fadil.? Sai ta juya tana neman Badariya ita ko daman tana dakin Mama tana ji ta fito da Sauri yako karbesa ko kunya yaja hannunsa yarsa ya dago yana kallon su Mama da suka yi Tsumu tsumu,Lokaci daya yana fadin"Zan tafi da y'ata zata kuma zauna ta jiraka.Hajiya ki gayamsaa duk bayan Sati biyu zai rika zuwa yana ganin matarsa da yarsa in kuma yaki jin mganata wlh tallahi zan saka Hukuma aciki saboda tun farko yasan Da Tsarin ya amince da haka sai yanzu zai sauya mganaa..?ina ruwan aikin Zainab da rashin aikinsa..?da zai wuce a kanta..?to zan kai kararsa bai isa ya tozartamin ya' ya zauna lafiya ba.in kuma bai ji mgana ba zan nuna masa waye lawal bako dan mutanen Adamawa" Daga haka yaja hannun yarsa ita kuma ta dauki Jakarta suka fice Daga gidan,Sai aka rasa tsakanin Mama da Anty Binta ko Yaya Ishaq wanda zai motsa ni ko Allah ya kyauta nace araina na cigaba da duba dahuwar zobo na,Mama da ranta ya gama baci da Ishaq ta kallesa tana fadin"Ka kyauta ga abunda taurin kanka ya jawo ma ka nan, kaje in ya cire hannunsa a kanka sai ka duka ka Dauka." Anty Binta tayi tsaki kafin tace"To me ma ya kawo mganar ta ijiye aikinta ta dawo nan ta zauna..?in ta Dawo kana da wajen da zaka ijiyeta ne..? Sakarci kawai achan ya baku gida ya Dauki dawainiyar su Farhan da komai nasu ammh baka gode ba sai ka Tsiro da wata mgana Saboda kada a zauna lafiya.? Idanuwansa jajir ya dago yana fadin"Don Allah ya isa.Ya isa nace.." Mama ta saki baki tana kallonsa Anty Binta tace"To dake ni don na fada maka gaskiya Ishaq dake