Sashe 8
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
aurensa da Haihuwarsa da Mutuwarsa'" In yace mata haka sai dai ta kallesa ta Harareshi kafin tayi kyafci Sai tace"Ai daman haka zakace Yaron nan Sidi ya gama dakai kai da Aisha Fati ce kadai tasan ciwo na" Sun riga sun Saba da Halinta shiyasa suke Lallabata su rabu lafiya,yana katsina sai sati sati yake zuwa ganin gida Tun auran su daman Hajiya ta gama karanta ma Saudatu kaf Waye Sidi da auran cin amanan da Asiya tayi da mijinta,Sannan ta fadamata Sidi ba dan sunna ba ne An haifesa da cin Amana ne,shi yasa ta tsane shi duk da ta Lura Kabiru na bala'in ji da kaunar Sidi shiyasa ranar da ya fara kawo mata shi kadahan kadahan ta karbesu sai faman tab'e baki take yi Sidi na lura da ita bai yi mamaki ba Daman yasan za'a rina shiyasa baya fatan in yayi aure ya kawo matarsa wannan gidan yasan ta zama Nama. Sai da Kabiru da Saudatu suka Haifi Diyar su ta farko Fatima suna kiran ta Binta sunan Hajiyar Dala taci. Ashekaran Sidi yayi aure auran da Hajiya taji dadinsa tunda ba auran kece sa'a ba ne,Sidi yar'uwansa ya aura da kakansa na wurin uwa da kuma kakan TAMADINA na wajen Uwa itama sun hada iyaye daya,su biyu kadai mahaifinsu ya haifa kafin ya rasu Tamadina da Usman kuma ba uwarsu daya ba kowanne da Tsatson sa Ita ta Madina mahaifiyarta haifaffiyar karofi ce ita kuma mahaifiyar Usman yar karaye ne dake kano Lokacin data gama Takaba ta roki alfarman Tafiya da Usman garinsu aka bata Tun yana da Shekaru goma aduniya ya bar Karofi. Hafsatu(Tamadina) shine ainihin sunanta,kuma ta samo sunan ne tun tana karama tun da bakinta ya bude duk wanda yayi mata mgana sai tace madina zata tafi shikenan Hafsatu ya bace sai dai tamadina,sannan Tamadina Bebiya ce kuma ba Ciwo bane da shi aka Haifeta mganar ta baya fita Sosai sannan bata ji sosai,ahaka taso cikin rashin gata tunda kaf zuru'ar su Asiya ba wani mai arziki sai Buga buga kawai. Tamadina baka ce kuma gajera shiyasa duk wanda yasan Tamadina ya ganni ni Fa'iza zai san kammaninta da suffanta duka na Dauko sakamakon su ya Asiya sun Dauko Tsawon babbanmu da Hasken Fatarsa ni kuma hatta bakin Tamadina ni na Dauko shi har da gadon Rashin ji, na duk daga wajenta na gaje shi. Ba auran Tausayi Sidi yayi da tamadina ba shi ya ganta yaji yana sonta kuma manya suka shiga ciki,Musamman Alhaji Sulaiman da ya shige ma Sidi gaba,har akayi auran da farko yaso ya tafi da ita Katsina ne sai Alhaji Sulaiman ya hana yace ya barta agida kamar yadda Dan'uwansa yayi shi kuma bazai iya yi mai gaddama ba sai ya bar Tamadina a gidan karkashin Hajiyar Karofi da Saudatu(Mama kofar soro) Ba iya ni na wahala da Mama ba Mahaifiyata ma taci wuyarta ita da Hajiya suka maidata kamar jaka gashi Tana da lalura sai su yi ta zaginta bataji,Gashi ba daman tayi mgana sai Hajiya ta hantareta tana fadin"Ta fi chan Dangin maciya Amana..Dangin bakake munana kawai masu bakincikin munafunci" Kalaman tun tamadina bata gane su har ta fara ganesu ta kuma Haddace su,In Sidi na nan ne take samun salama sannan tana jin dadin zama da Uban mijinta Alhaji Sulaiman. Da kuma Hajiya Aisha(Goggon karofi),Sai Kabiru wanda shima ba ruwan shi ammh Hajiyar Dala sai abunda ta manta cin mutumci in tazo gidan nan Tamadina sai tayi kuka Taruwa suke yi su yi ta cin mata Mutumci wani Lokacin batama jinsu har Jin dadi take yi da Allah yasa bebiyace ita da ta kunshi bakinciki. Bayan Haihuwar Saudatu in da ta Haifi ISHAQ Bayan Haihuwar Saudatu,Tamadina ta haifi yarta mace Aka saka mata suna Asiya sunan mahaifiyar Sidi taci,Shekara shida tsakaninsu an yi sunanta ba jimawa Alhaji Sulaiman ya kwanta jinya ciwon sugar da bai tashi ba Gabadaya duk abunda ya tara sai da ya kare wajen neman mgani daga karshe bai tashi ba ya koma ga Allah. Rasuwar sa itace silar Wargajewar komai an yi ta rigima wajen raban gado,Domin Hajiya ta yi tsaye tace Sidi bai da gadon Alhaji Saboda shi din d'an cin Amana ne ganin rigiman tayi girma sidi ya tattara matarsa suka koma katsina ya kama Hayar Daki biyu da Tsarkar gida sai kitchen,Ya kuma ce ya yafe gadon har Abada aka rasa rai ma aka Hakura ballatana Duniya tun faruwar lamarin yasan Hajiya bazata taba kaunarsa ba kawai sai ya Hakura wanda ya hada ya raba,Tundaga Lokacin sai ya Dade bai je karofi ba Sai dai suna mgana ta waya da Kabiru da Aisha tunda su kam basu yar da Zumunci ba.. Ko shekara basu shafe a katsina ba ya samu aiki a wani kamfanin Sarrafa leda dake malunfashi sun basa matsayi mai girma da gidan zama ya tattara tamadina suka koma malumfashi da zama Acikin shekarun da suka gabata abubuwa dadama sun faru ciki har da Sauyin rayuwar da kowa ya samu Sannan da Nadamar Hajiya,Rana daya ta rika kuka tana a kira mata Sidi ta nemi afuwarsa dayake ita kadai ce agidan yanzu Kabiru shima ya Tattara sun koma cikin katsina da zama Tunda ya zama principal bayan yaje ya karo karatunsa Sidi yayi matukar mamakin nadamar Hajiya daman bai taba riketa ba ya riketa yana share mata hawaye tare da Fadin bai taba riketa acikin Ransa ba kowa yaji dadin wannan al'amarin ban da Hajiyar Dala domin har Abada bazata kaunaci Sidi da zuru'arsa ba. Hakama Saudatu(Mama kofar soro) itama ta tsani Sidi da zuru"arsa ganin tafi TaMadina komai na bangaran kyau da Nasaba ammh a bangaran jin dadin gidan miji,Sai dai su goga domin bata fita komai na inganta Rayuwa ba, Sidi na yima Iyalansa komai sun gado Halin Dattako wajen mahaifin su Alhaji Sulaiman ***** Shekaru goma da suka gabata. A cikin wad'anan shekarun goman,komai ya faru kuma ya kare,mun fara samun ingantattaciyar Rayuwa a malunfashi,Bayan haihuwar Ya Asiya sai Yaya mariya sai ni Fa'iza da aka Haifeni da Laluran Raunin ji sai autarmu dataci sunan Tamadina Hafsatu ita an haifeta ma ne Babanmu na cikin Tsananin jinya shima Ciwon sugar yayi gado wajen mahaifin su Alhaji Sulaiman shima kamar shi din sai da komai ya kare tas wajen neman mgani kafin rasuwarsa sai da aka yanke mai kafa Da Hannu bazan taba mantawa ba ina Aji hudu na matakin primary a asibitin gwammatin garin Malunfashi Babanmu ya rasu a hannun Alhaji Kabiru(Baban katsina) da Tamadina Mutuwar da Sanadinta ta gama gigita Rayuwarmu gabadaya sanadinta muka san halin Rayuwa muka san maraici da rashin gata. Da gidan da muke ciki kadai muka Tsira shima da aka saida shi duk a bashi ya tafi tunda jinya yayi kusan shekara uku sai da komai ya kare aka koma cin bashi duk da Baban katsina na Tallafa mana shi da Hajiyar Karofi. Mutuwar Babanmu shine Silar Barowarmu Malumfashi muka koma Karofi daga Lokacin kuma komai na Cigabaman mu ya tsaya,Tamadina tana gama Takaba gidan su ta koma,mu kuma ta barmu gaban Hajiya da Farko da nan aka barmu da mun samu Rayuwa mai inganci saboda Hajiya tana kaunarmu kwatankwacin kaunar da take yi ma Sauran jokokinta. Ammh sai hakan bai samu ba Baban katsina ya tara su Hajiyar Dala yace zasu rabamu a Tsakaninsu Saboda Rage ma Hajiya Dawainiya,Shi farko Yaya Asiya yace zai dauka Ita kuma Goggon Karofi tace zata Dauki Yaya mariya ta hadata cikin ya'yanta ta rike Tsakani ga Allah. Shi kuma Baban Katsina sai yace Hajiyar Dala ta Dauke ni Tunda Hajiya ta maida ma Tamadina Hafsatu tunda tana karama ne Lokacin sosai tace ta riketa tukunna har sai ta yi wayo sosai. Ai Hajiyar Dala agaban kowa da kowa ta Daka tsalle tace bazata Daukeni ba takai gidanta ban ko ji sosai ta Daukan ma kanta Lalura ita bazata iya ba har Hajiyar karofi sai da tayi mata mgana tace bazata Dauki kowa ba,Sai aka kyaleta Baban katsina da ya fara fada Hajiya ta hanasa tace ita zata rikeni shi ya tafi da Ya Asiyan kawai ita zata rikeni Hajiyar Dala najin haka sai tace sai dai ta Dauki Yaya Asiya tunda ita Lafiyarta kalau Baban katsina yaso ya hana sai Hajiya tace abata,wannan shine Dalilin Rarrabuwarmu Yaya Asiya a kano ta tashi Ta samu tayi karatunta har Sakandiri ita kuma Yaya mariya ta taso Hannun Goggon karofi itama tayo karatunta ita kam har matakin N.C.E,Sai Hafsatu wanda Baban katsina yace in ta kara girma shi zai Dauketa Tunda ni Hajiyar karofi zata rikeni ammh duka Dawaniyata Na hannunsu. Naji dadin barina a karofi da akayi Saboda Tamadina da Hafsatu sai kuma Yaya Mariya dake kusa Damu ko da yaushe suna gidan Hajiya tare damu Ni dai Dakyar Hajiyar Karofi ta bari na gama nakai aji Biyar na matakin primary domin na rubuta jarabawar fita ba sai fada take yi Me zan ji a makaranta ko me zan gane Tunda ba ji nake yi sosai ba,Baban Katsina ya so nayi karatu ammh sai yaga bayan Hajiya Nima bana so Saboda ina shan Dariya da Wulakanci a makaranta wajen Sa'annina Saboda yanayin mganata da raunin ji na sannan kuma ni bakace bani da kyau shiyasa sai karatun ya ficemin Daga raina na,na saka araina sai mai gata ko mara Lalura yake zama mai ilimi bani da na ke nakasashiya ba. Ammh Hajiyar karofi bata bari nayi Sakaci da na addina ba,Ta sakani Islamiya da Hadda da Makarantar allo ta Safe da Dare,Shi kam ban yi sakaci ba Kuma dayake karatun Qur'ani ne da Liffafan addini ina ganewa sannan Hajiya bata hanani ba shima na Bokon bazata iya juran dawowa da nike da kuka bane Saboda har waka ake yi min bebiya mamarta ma Bebiya sai nake jin guilt din abun acikin raina da yasa naji na Tsani bokon gabadaya sai Hajiyar Karofi ta maramin baya domin gatan Duniya ba wanda bata nuna min ba. Rikon Hafsa ya koma Hannun Goggon Karofi Saboda Tamadina tayi aure a Dutsenmah ta auri wani magini ne matan sa Biyu itace ta uku,Sai Baban katsina yaso ya karbi Hafsah Mama kofar soro ta daka tsalle tace bazata rike zuru'ar Tamadina ba dangin Maciya Amana da Bebaye ba Hajiya tayi kuka kamar ranta zai fita tasan duk abunda