← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 163 OF 175

Sashe 163

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai daga baya su Ammi suka zo dakin suka sameni Anty Nasara na juya baki tana fadin"Jama'a kun ji yadda yare ke tashi.? Yaya Mariya tace"Komai sai da sanadi ga shi Sanadin Fa'iza nazo tsakiyar abun naci kuma amala kamar cikina zai fashe" Dariya aka saka mata Anty Fadila tace"Kai dangin sun burgeni. komai tsab gasu wayayyi kamar ba yarbawa ba." Hajiyar Dala tace"Uhm ai naga abun mamaki ayi ta cewa yarbawa kazamai masu kashi a leda kaza kaza ni ko da muka zo ban ga haka ba ga su nan Tsab da su kamar ma mu hausawan" Ammi tace"Ai in kin lura sun surka kowani yare a cikin su, ba kabilanci ko jin kyamar wani yaren". Haka dai suka yi ta hira suna Tattaunawa ni dai bana saka musu bayan la'asar Maa tace daman za'a fara tarom muna idar da sallah Wata yar matashiya tazo shiryani Wanka ma sake na fesa turaruka sannan aka bani wani less baki da Fari na saka Riga da zani ciki da alaku har Daurin zanin matar ta dauramin ta min Daurin Kallabi irin na su,sai dan kunne da sarka ga murjani da ya saukomin har Cikina hannayena ma ta sakamin su da yawa,Takami baki ta bani mai tsini yana da igiya sai karamar Jaka pos ligth makeup tayi min sai nayi kyau kamar bani ce uwar yara Hud'u ba. Suma su Anty Nasara sun shirya,abun dariya har da ciki da alakun suma suka yi suna fadin suma fa duk an zama daya,Har su Anum suma an shirya su da kayan yarbawa su kafayane da wannan aikin yara sai suka saje kamar anan muka same su. Sai biyar akace su Ammi su fito dani Ita da Hajiyar Dala a haraban gidan an shirya kujeru da kuma in da zamu Zauna sai da muka fito naga ashe Engr ya iso ban sani ba,domin bai kirani ba shima irin less din jikina ne da shi yaci hulansu na ashoke har da karyata gefe sai alokacin na hango kamarsa da yarbawan gefensa aka zaunar dani ina zama ya ramkwafo yana Fadin"Eh Tife..Tife.." Idanuwana na kan mu shiyasa na kasa juyawa sai dai mirmishi masu Hotuna nata aikin su,sai gani na fito ba mayafi Cikin mutane sai faman kunya nake ji na kasa sakewa shima daya Fahinci haka sai yace"Ki yi hakuri yanzu za'a gama Nima fa ina jin kishin yadda wasu mazan ke kallemin halalina" Tokarinsa nayi da gwiwan hannu na ya koma gefe yana dariya, an yi jawabi Maa ita ta gabatar dani ga Hajiya Kudirat itace head of the family,sai kuma suma suka min jawabin maraba da Yarbanci da Turanci Engr yace a fasaara da Hausa,dole a ka samu wani ya yi mgana da Hausa kuma nasan saboda ni ya yi sai naji na kara son shi. haka aka rika min layi ana gabatar min da su Daya bayan d'aya Engr ya koyamin irin gaisuwan su kamar na indiyawa kayi kamar zaka Duka sai a dafa kanka a saka maka albarka sunaye ko wlh na kasa rikewa ga sunan birjit suna da yawa sosai wlh kamar tsaki. An ci an sha kuma an yi rawa Engr yaso yajani muyi rawa naki sai yaja su Anum da daman suna tare da shi. suna ta rawa an zubda kudi kamar ba'a son ranar su ba Anty Nasara da su Nana Fatima sun shiga sun sha rawan su,ko ajikinsu ina gefe ina Dariya,sai mangriba aka tashi na samu kudi tunda duk wanda za'a gayamin sunan shi in na gaishe shi sai ya bani kudi sakamakon gajiya yasa ina sallar isha'i sai barci ko Engr ban nema ba,su Anum ko na Tare da shi bama Daki daya muka kwana da su ba Wajen Maa suka kwana. Da safe kuma akayi walima,gabadaya aka taru afalon gidan manya da yara aka yi karatun Qur'ani izifi Ashirin,naga ranar ilimi naga kuma gidan ilimi ni na fara Bude karatun Daga suratul Muhammad muka fara,Engr kuma shi ya Rufe karatun ashe shima haka yake da kira'a an rarraba charbi da Dardumai sai da yammah kuma akayi party shi a Hall akayi na cikin gari shima an ci an sha kuma an chase,sai washegari ni da Engr zamu wuce Edo su kuma su Ammi zasu koma kaduna. Mu muka fara tafiya gabadaya kaya na daman suna hade ne waje d'aya. Ammi ta yi ta jadaddamin na rike kamshi da Tsabta biyayya da sanin kan miji sannan bata jina ta bangaran girki,Mun rumgumeni ni da Anum har sai da nayi kwallah tace zata bini nace zan je da ita Engr ma yace da ita zamu tafi Ammi ce tace ba inda zataje. Sai da naga rabuwan da gaske na fara kuka suna ta min nasiha na rumgume yaya mariya da Yaya Asiya suna ta fadin Fatan alheri Fa'iza. Haka ni da Badariya kamar wasu yara A babbar Prad o din Engr fara zamu tafi dagani sai shi sai Direba. An kai ni wajen Hajiya kudirat ta sakamana albarka sannan ta bani kyautan warwaro da ashoben su da murjanai,sai duka kannen Papa da yayyensa suma na samu kyatuttukan na kudi da kaya tare da addu'a daga garesu. Gabadaya kuma suka rakomu har bakin mota,Abaya na saka maroon mai zanen baki sai Nana Fatima tamin nadin mayafin baki nayi kyau sosai duk da ina kin sakawa sai gashi na saka takalmin kafata ma baki ne,mai Tudu duka kayan jikina ba na kudi kad'an cikin ma wanda muka siyo ne da Ammi ne. Ina ji ina gani Ammi ta sakani a mota suna d'agamin hannu Engr ma ya shigo Direba ya rufe shi ya tsayama Lallashin Anum ammh tana ta kukan sai ta bimu a raina nace Anum ta girma bazata daina shagwaba ba. Mun dauki hanyar Edo cike da kewa na tuna Maa yadda ta rika sakamana albarka da fatan zaman lafiya itama tace duk abunda nake so na kirata ita uwa take gareni. Hawaye haka suke bulbulomin Duk Dauriyan Engr haka ya rumgumoni yana Lallashina kamar karamar yarinya fad'i yake"Shii..am sorry matata..Ko mu koma ne kawai mayi shagalin mu achan..? Wata uwar harara na Dago ina hawaye na makamai sai ya yi Dariya yana Fadin"To ba ke bace kina ta kuka ina kike so na saka raina don Allah..? Hawayen ya fara sharemin yana Fadin"Kin yi bamkwana da kuka har Abada sai dai na farinciki. Ki bari kawai mu sha kara'in mu ba gani ba..?ko ni ne baki son gani kike kuka saboda mun baro su..? Sai na kasa mgana na sunne kaina a saman kirjisa ina mirmishi kamar yadda na yace bayason kuka dole na shanye hawayena ina ji ya saka hannayensa duka biyu ya rumgumoni. Kaina na saman kirjinsa yana lallashina kamar wata karamar yarinya ni ko na lafe ina samun natsuwa Lokaci d'aya da natsuwar zuciya. Sai kuma na fara tunani had'e da kuma Fargaban wata irin kuma rayuwa zan fara gudanawar tare da Engr..? Shin wani irin bambamci zan samu a zaman aure na da shi..? Fatan farinciki nake yi ma kaina ko ya ya ne. Fargabata har da yadda nayi aure abunda ban taba tunanin yinsa nan kusa ba. *Janafty* [8/1, 5:16 PM] Hauwa Galadima: *KNKB3018* *TASTED & TRUSTED* *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*. *AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*. *ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWOWINRL ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.* *AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*. *SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.* *DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*. *SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*. *KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.* *AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.* *AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*. *SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH* *DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*. *TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU* *08032773332* *DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*. *NATION WIDE DELIVERY* *Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.* *09069067488* Sai Dare muka isa garin Edo,gidan Engr na garin karamin gida ne gaskiya. Saboda Falo d'aya ne sai bedroom guda biyu sai Kitchen haraban gidan ma karami ne bai wuce wajen ajiyan motoci biyu ba. Sai Dakin megadi sai daga ciki kad'an D'akin waje muhallin da Direba kan kwana in suna gari. Mun iso da daddare sannan ga gajiya a tare damu tunda tun da muka zo Benue ban yi wani barcin kirki ba,Shi ya sake fita ya siyo mana abincin kayana ma duka shiya shigomin da shi,ni ko sallalolin dake kaina na fara saukewa bayan ya nuna min Tiolet shi kuma da ya fita ina ga ya yi nasa a chan. Koda ya dawo har na fara barci shi ya tasheni muka ci abinci rabin ma abincin a baki ya bani,muna gama ci na bingire sai barci ko kayan jikina na kasa ragewa shi ya kwashe sauran abincin yakai kitchen ya dawo ina jinsa yana tashina, na bude ido a kasalance ina kallonsa cikin yanayin mganarsa yace"Ki tashi ki yi wanka ko zaki ji dad'in jikin ki" Luu nayi da ido na zan koma saboda na jini ne gabadaya gabbaina sun saki kamar wacce akayi ma dukan tsiya. Ganin na sake komawa yasa ya kyaleni ya shiga tiolet din ya yi wanka Saboda baya so ya takuramin. Nidai bansan yadda akayi ba naji ya gyaramin kwanciya sannan ya yi ta matsamin kafa alamun Tausa naji yana mgana ammh barci yaci idona, bansan me yake fad'i ba ammh dai nasan ya jima ya na min Tausa da ya yi sanadiyar sawa na kara lafewa samman makeken gadonsa ina kara jin Dadin barcina. Hankalina kwance Allah sarki bawan Allah shima fa a gajiyan yake ammh bai duba kansa ba yafi ji dani tukunnah Ckin Dare na farka na ganni nannade acikin kirjinsa ba haske acikin Dakin ammh ta window labulen na dagawa Hasken wata daran goma sha Biyar ya haskemin Fuskar sa. ko yana barci Mirmishinsa bai barin Fuskarsa yana Sanye
Chapter 163 · 0% Book details