← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 175

Sashe 57

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dai a duba zumuncin da Allah ya riga ya had'a ,kuma shi sada zumunci Umarnin Ubangijine kuma shi Umarnin Ubangiji sab'a masa babban Laifi ne. Haka kurum naji ina sha'awar shan Faten Rama ina da sauran tsaki tun wanda na dawo dashi daga Karofi shi na Tankad'e na wanke na d'ora sannan na Jika bushasshiyar Rama nayi amfani Dashi bani da nama ko kifi sai nayi amfani da wake na watsa musu aciki,sai Faten yayi dad'i yana tashin kamshin kayan miya da Daddawa da su Citta,na juye a kula ni saboda bazan iya jiran yaran ba, sai da na Dib'i nawa muka sha ni da Ahmad sannan na sake yi mai wanka nima nayi muka sauya kaya shidda Saura yaran suka Dawo daga makaranta suka cire Kayan makaranta, suka sauya na gida sannan na zubo musu faten a faranti suka na suna santi,bayan sun gama Anum ta fara min labarin makaranta Musty kuma sai wasan zagayen falon yake yi Amir kuma kan kujera ya hau yana Duba Littafansa. Anum wasa da kaina take yi,kalaba ne daman har ya kusa warware kansa ma, domin ni nayi ma kaina.Ahmad kuma na daka Tsalle saman jikina Amir yace"Umma ki dubamin aikin nan ban gane ba..? Ya fad'a yana mikomin littafin rubutun sa na karb'a nayi gefe da kaina Ahmad nata mika hannu da Sauri Amir yace"Umma karki basa zai ya ga min" Cikin yanayi na nace"Bazan basa ba.Arabiya ne zan koya maka kabari ayi sallah mu natsa tukunna" Ya amsa min da Toh ya karb'i Littafinsa Kiran sallar mangariba ya tadamu mukaje mukayi alwala mukayi jam'i gabad'ayanmu afalo bayan mun idar na d'aga hannuwana Ina addu'a Sai suma suka d'aga sai da na shafa sannan suka shafa na kalle su ina Fadin"me kuka rokar mana acikin addu'an..? Amir ne yace"Umma a makaranta an ce mu rika ma iyayan mu addu'a" Kai na jinjina masa ina fadin"Yauwa to ina so in dai kuka yi sallah ku rika rokar ma Umma Sa'a da nasara a abunda zata yi kun ji ko..? Da Sauri Anum tace"Umma me zaki yi..? Kanta na shafa ina fadin"Ba'a fada ma yara sai abun ya tabbata ke dai ki rika yi ma Umma addu'a ai zaki yi ko..? Da Sauri ta d'agamin kai sai na Shafa kumatun ta ina saka musu albarkar acikin raina Musty da Anum har sun fara wasa na dakatar da su nace su karanta azkar din su,shiyasa suka natsu,Kiran sallar isha'i ya tadamu muka yi sallar tare sannan muka zauna mukayi addu'o'i Anum da karfi ta rika fadin"Allah ka bama Umma sa'a Allah ya bata gida da mota" Sai ta bani Dariya Amir ya kwab'e ta da Fadi'n"Aljannah ake cewa" Da sauri tace"Eh Allah ka ba ma Umma Aljannah " Ba zato kawai Musty yace"Allah ka sa Umma ya hau jigi" Gabad'ayanmu muka kwashe mai da Dariya idona ya ciko da kwallah na kama Musty na rumgume ina fadin"Ameen Ameen Allah yasa amsa bakin ku ya'yan albarka kuma Allah ya baku duk abunda kuke so duniya da lahira" Anum ce ke gyara ma Musty sunan Jirgin da bai iya fada ba sai nanata mai take yi yana fadin Jigi sai suka sanyani Nishadi ina ta Dariya Tuni na manta da duk wani bakincikin dake Damuna. zuciyata ta dawo fara tas kamar farar takardan da ba'a taba yi mata wani Dameji ba. Falo na tattara su muka koma na hana wasan nace mza a dauko Littafan makaranta a duba sukaje suka Dauko na shiga Tsakiyar su,su kuma sun Zagaye Ahmad ne ya fara kiriniya zai yaga musu littafai sai na Daukesa na goya a baya na ammh duk da haka sai uban zillo yake yi shi sai ya sauka naki ko sauke sa. Na Amir guda biyu ne Arabiya da na English na Arabiyan na koya masa,Sai na Anum littafin koyon bakake ne da aka saka su,siya itama na nuna mata yadda zata yi na Musty kuma na turanci ne sai Littafin da na saka ya Rubuta Huruful Hija'iya na Damki hannunsa ina koya mai rubutawa da Fadin su a baki, muna rubutawa muna fad'in su d'aya bayan da'ya sauran na turancin da ban iya ba nace Amir ya taimaka musu tunda shi yana primary 3 ne zai je hud'u Anum na 2, Musty kuma 1,Ahmad ne ya rage shima in da ina da kud'i saka shi zan yi, bakinsa ya bude achan kamar yadda Babansu yayi ma Anum da Musty. Sai da suka gama duka aikin makarantan nasaka suka kwashe Littafan suka maida jaka suka maida su dakin su,sannan na zubo mana Faten nan a katon faranti muka Had'u muna ta sha Ahmad na kan jikina ina basa a baki Musty ma yasa ka rigima sai na rika basa Anum na ganin haka ta kwabe fuska zatayi kuka tace"Ni fa Umma" Sai itama na riga bata a baki Amir ne kad'ai ke shan abunsa da kansa muna cikin haka sai ga Yaya ishaq ya shigo da Leda sai dai yaran suka juya suka gansa kwatsam ni nama manta ko alama ban ce musu Daada ya dawo ba. Haka suka tsallakeni suka nufesa Har da Ahmad,Amir ne kawai ya tsaya a tsaye sauran kuma jikinsa suka fad'a ya tarbesu yana fadin"Oyoyo ya'yan Daada"Anum sarkin Karad'i ta ce"Daada yaushe ka dawo..?mun daina ganinka ko da yaushe muna tambayan Umma sai tace baka nan". Ina jinsu sai ya kasa bata amsa sai da ya kai ga zaune sannan ya Dauketa ita da Musty da Ahmad ya Dora zaman jikinsa Amir ya zauna agefensa yana fadin"Umman ku bata gaya muku nayi tafiya ba ne..?Kanin ku bai da lafiya jaririn Antynku muka kai Asibiti" Da Sauri Anum tace"Jaririn Anty mai kyau"? Sai ya gyad'a mata kai,sai suka nuna tausayawar su Ledar hannunsa ya warware ya fito musu da Minti da Biskit wajen rabasu musu ne yaga Hannun Anum duk maiko ya shinshina sai yaji warin Daddawa da Sauri ya Dago kansa yana kallona ni kuma shan Fate na, na cigaba da yi kallo basu isheni ba. Sai ya kalli Anum yana fadin"Me ye a Hannun ki Mamana..? Da Sauri ta ce"Daada Fatee ne Umma tayi mana dad'i" Sai ya k'ara kallona ya kuma kalli Farantin gabana cikin yamutsa Fuaka yace"Fa'iza meye wannan..? Naji sa ammh sai nayi kamar ban jiba. sai da ya kara Daga murya yana fadin"Nace meye wannan kika bama ya'yana Fa'iza..? Na dago kaina ido cikin ido nace"Fate ne" Saboda naga abun na sa kuma ya fara zama renin wayau faten ne bai sani ba..? Ya maimaita sunan fate a ransa da Fili kafin yace"Me kenan..?ina mikewa nace"Abinci ne shima.." Su Anum na kallah ina fadin"Kun koshi ne..?dukkan su suka d'agamin kai sai na nufi kitchen da shi nasan ya bini da kallo ammh ban ko waigo ba sai da na shiga na sauke abun hannuna na wanke hannuna na fito ina Fadin"kuje ku wanke hannuwan ku" Kamar suna jirana suka sauka da gudu zuwa Daki har da Ahmad shi kuma sai ya kalleni yana fadin"Ina miki mgana kina basar dani Fa'iza? A kaikace nace"na baka amsarka nace maka abinci ne" Sai ya kasa mgana sai chan yace"Baku da abinci ne a gidan sai kin basu wannan abun sun ci hannunsu sai wari yake yi" Sai ma ya bani Dariya na murmusa na gyara zama na akasan cafet din Falon ban yi mgana ba da kansa ya mike ya shiga kitchen din yaga bakomai Sai Dubaruna irin na mace mai ya'ya Shinkafa kad'ai ta rage mana itama ko Tiya bata kai ba,ba domin Goggo ta taimakeni ba da Tuni asirina ya Dad'e da Tonuwa a idon duniya domin tun da na dawo daga Rasuwar Tamadina k'waran abincin ban gani ba.tun Cefanen da yayi mana kafin ya tafi shima bamai yawa ba ne,ina jin ba shi da kudi a tare da shi ne lokacin. Ina ganinsa ya fito cikin wani yanayi ya kuma daga waya ya kira Mama naji yana mgana ammh Dayake ban maida Hankalina akansa ba ban ji me yake fad'i ba.tunanina na chan inda mafita ta take, da Tunanin yadda komai zai faru jibi,Har na kosa ma jibin yayi mu fara kamar na matso da jibin gobe haka nakeji zumud'i kawai nake ji akasan raina kamar nama iya komai haka nake ji. Sunana naji yana kira da karfi sannan na Dago ina kallonsa cikin Mganarsa yace"Wani banzar Dabi'a kika samu ina mgana kina ji na,kina yi min banza..? Kai tsaye nace"Kayi hakuri abun ka ga mara karjin ji sai hakuri" Sai ya kasa mgana,Bata rai yayi yana Hararata kafin yace"Na rasa wata irin mace ce ke Fa'iza..? Yanzu kayan abincin ku ya kare bazaki iya kiran Mama ki fad'a mata ba..?jamal baya gida yana makaranta ita nake turo ma kudin cefanan ku duk wata da kudin bukatun yara, ammh yanzu da nayi mata mgana tace bata zauna ba sannan bata san cefanen ya kare ba" Kallonsa kawai nayi na kasa mgana shi kuma sai ya cigaba da fad'a yana fadin"Badar na zuwa gidan nan fa ko ita bazaki aika wajen maman ba..?Ko ke bazaki shirya ki je ki gayamata ba..? Sai kawai nace"Kayi hakuri.." Saboda na datse mganar ganin yaran sun fito kowanne da Biskit da minti a Hannunsu,Shima jin abunda nace ne yasa sai ya kasa cigaba da tijararsa,Daganan sai hankalinsa ya koma kan yaran yana ta tambayan su abunda suke so suna fad'amai da labarin makaranta ni ko araina ina kara jinjina kaifin ikon Mama akan komai shi kayan abincin sai naje na Fad'amata ya kare kenan zata fidda kudin da ya turo mata ta siyan mana kenan..?kamar tana yi mana alfarma a raina daman na Guduri niyar ko zamu mutu da yunwa na gwammace duk mu mace da naje wajen Mama nace mata bamu da abinci. Tara nayi na tattara yaran suka je suka yi shirin barci suka kwanta Anum ma da Ahmad na kwantar da su akan gadona,Na fito falo zan d'an gyarasa tunda yaran duk sun zubar da Ledojin Biskit din a tsakar falon na iske sa Lafe kan kujera yana waya a hankali yake yi shiyasa ban jisa ba sai na shiga abunda ya fito dani bayan na gama zan koma Daki sai ya kwalamin kira na Dakata na juyo ina kallonsa a kishingid'e yake sai ya Dago yana fadin"Naga zaki
Chapter 57 · 0% Book details