← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 175

Sashe 92

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nayi saurin kwace kaina cikin ihu nace"kada ka sake ka tab'ani..' Kada ka sake..". Na fad'a cikin ihu lokaci d'aya da kuka sai ya kasa kara tabanin ya koma gefe yana kallona,da kafarsa ya ja gajerun wandonsa ya saka kaina na maida kasa ina kuka,kamar ana dawomin da komai haka abubuwan da suka wuce suka rika dawomin na Dade bana fama da Kuncin zuciya tunda Allah ya samamin mafita ammh yau sai naji kamar komai anan yake faruwa kirjina yayi nauyi bakinciki ya cikani da na kasa sarrafa kaina agabana ya Durkusa kamar jaririn dake neman nono wajen uwarsa,yana shirin kara tabani nayi gefe da sauri ina kara rike zanin gadon dake hannuna gudun kada ya rabu da jikina,Sai ya Daga hannu cikin kasala da sanyin jiki,idanuwansa sun sauya Launi Jijiyoyin kansa sun mike gabad'aya cikin alamun Sararawa yace"Na bari naji bazan taba ki ba,ammh kiyi ma girman Allah ki bar kukan nan ki tsaya muyi mgana Fa'iza" Sai a lokacin na dawo hayyacina na Fahinmci gadar zare ya hadamin Allah na sona da Rahma da na Rufta acikin shirinsa da na shiga uku. Bani kuma da sauran mgana burina da na dad'e dashi acikin raina zai mutu batare da na cika sa ba. Rokona ya cigaba da yi ganin naki daina kuka ganin yana magiya kamar zai yi kuka yasa na saurara da kuka na, sai dai ban daina jan Numfashi ina Jan majina ba,zaman dirshan yayi a gabana cikin wata irin muryan da bazaka taba cewa Ishaq kabir karofi gaye dan kwalisa ne ya mallaketa ba murya ce da zata iya kasaara jikin ko wacce d'iya mace mai lafiya in dai ta jisa da muryan ya fara mgana cikin karyayan sautin da ni kadai zan jisa yace"Haba Fa'iza haba fa'iza meyasa..?kin san halin da kika sani Tsawon wannan lokacin..?ki dubeni kiga yadda na koma a gabanki don Allah ki kara bani dama na gyara kuskurena na yarda na amince ni mai laifi ne ammh kada ki horani ta wannan bangaran na amince ki min duk abunda kika ga dama,ammh ba ta wannan bangaran ba ki bari na samu natsuwa daga gareki koma menene sai ya biyo baya.." Sai da ya Dire mganarsa na Dago jajayen idanuwana na wurgasa masa wani harara da mamakin jin kalamansa na karshe,cikin karya wuya yace"Don Allah Fa'iza.." Har da kokarin sake rikoni na ko kara matsawa baya shima yana kara matsaoni da karfi nace"Ka na matsowa wlh zan yi maka ihun kwarto wlh" Cak ko ya tsaya yana kallona cikin mamaki yace"Kwarto fa,kwarto fa Fa'iza..? Kai tsaye ina kuka nace"Eh Kwarto nace. kuma ka kara matsowa kusa da ni kasha mamakina" Sai ya koma gefe na ya zauna yayi Tagumi kamar wani maraya Lokaci daya yana fadin"Ina cikin wani Hali don Allah Fa'iza ki bar ni na samu natsuwa daga wajen ki don Darajan don Allah Fa'iza ki ji tausayina" Banza nayi da shi ina ta sharan hawaye ya kara kwaso magiya har ya gama ban ce masa komai ba, sai ya matso kusa dani na zaro mai ido sai ya koma da baya hannunsa a sama yana fadin"Wlh bazan taba ki ba..ammh in kika min haka kin min adalci kenan Fa'iza.?zina kike so naje nayi ko kuma kina so na fad'a wata Halakan ne..? Idanuwana suna fitar da kwalla na Dago ina kallonsa cikin Muryata nace"Adalci ka ke mganar ban yi maka ba..?kai kasan menene adalci kuwa..?kuma da kake mganar ka da ka fad'a zina ko halaka, au sai yanzu kasan Ana iya fad'awa wannan halakar.?ammh baka taba Tunanin matar daka jingine Shekaru Biyar baka taba waiwayanta da sunan bata hakkinta na aure ba.Ita baka taba Tunanin wata Halaka zata fad'a ba..?ko ita ba Mutum bace..?ko ita bazata iya fadawa zinar ba ne..? Na fada cikin wani yanayi Lokaci kamar alokacin yake fadamin ya zabi Zainab sama dani sannan ya jingine aurena fiye da shekaru biyar ammh Saboda Namiji bai da kunya har zai iya nema na da wani abu..? Wani irin kallo nake bin sa da shi kallon tarin takaicinsa da bakincikin da yayi shekaru yana kunsamin Hawaye suna kwarnya a saman fuskata. Kansa ya dafe cikin wani yanayi lokaci d'aya yana fadin"Na sani..nasan ni me laifi ne Fa'iza kiyi hakuri ki yafemin nasan nayi miki tarin laifukan da bazasu yafu lokaci d'aya ba, ammh ki duba ki gani wlh nayi nadama nayi nadama ki bani dama na gyara kuskurena" Cikin kuka nace"Ina nadaman da kayi..?yaushe ka fahimci Fa'iza mutum ce kuma macece kamar zainab..? Sai ya kasa mgana ya fara mgana cikin kame kame yana fadin"Tun tuni Fa'iza,Wlh tuni na gane kuskurena. nayi nadama kema kin sani" Kai tsaye nace"Babu abunda na sani.Abu d'aya na sani cewa baka sona baka taba kaunata ba.ka zauna dani ne saboda Baba..ka ce bani da amfani kace ni ba matar kwarai bace, ni ba matar rufin asiri ba ce kace ni Fa'iza ban dace dakai ba,Alfarma kake yi min,ka manta ka sha fad'amin baka Daukeni a bakin komai ba..?ka manta da kanka ka kirani ka nemi alfarman na barka ka yi rayuwar aure da Zainab ni kuma ka jingine aurena ba.?ko ba kai ba ne ka zabi wata macen sama dani ba?meyasa sai yanzu kake tsammanin komai zai zo maka da sauki..?. Na karishe fad'a ina tsiyayan hawaye,wani Turiri da hayaki na fitowa daga kasan raina,Hannuwana ya riko jikinsa na rawa yace"Na sani ki bar tuna baya wlh a wanchan Lokacin bansa me ya shiga kaina ba ne,Ammh wlh na dawo hayyacina na gane kuskurena na fahimci sakacina da laifina na fahimci sakacin da nayi Wlh na tuba na tuba..nabi Allah na biki Fa'iza na dade da sanin kin fiyemin kowacce mace amfani a Rayuwata kuma na dade da sanin nayi kuskuran furta kalaman jingianan auran mu fa'iza,ki bani Dama mu sake gyara rayuwar auran mu a karo na biyu don Allah Fa'iza.." Yafad'a lokaci d'aya yana jimke hannuwana cikin nasa sai kawai nayi Dariya lokaci d'aya da kuka kamar Mahaukaciya kafin nace"Fa'iza ce fa,kurma diyar Bebiya,Baka mummuna,Mara ilimin boko,mara gata mara kyau da nasaba,macen da bata chanchanci namiji kamar Ishaq kabir karofi ya so ta ba.Ni ce fa Fa'iza yar gargajiya nan,ina nan ban sauya ba.Ni ce dai wacce ka ke ciyar dani Saboda ina zaman kula da ya'yan ka, Fa'izan ne da ka ke tafiya wajen wata macen kafi wata biyu baka kirata a waya kaji yaya lafiyanta ba, Fa'izan da da bata san komai ba, sai ibadar aure da kula da ya'yanta da aka bar mata amanar su Fa'izan da ka rabata da kowa nata ciki har da mahaifiyarta marainiya da bata dukan wani gata, bata da uba bata da wani babban yayan da zai Tsaya ma rayuwarta ita ce dai wannan Fa'izan da Mama da Anty Binta suka maida abar wulakantawan su da cin mutumcin su, wannan fa Fa'izan da baka san ganinta Fa'izan nan ce da kake jin kunyar nuna ta amatsayin matarka, ita ce wacce kake jin kunyar duniya taga ya'yan da kuka Haifa tare ita wannan Fa'izan bata d" Ban karisa ba ya rufemin baki da Hannunsa ina kuka,hawaye jage jage,da majina shima idanuwansa Jajir kamar zai yi kuka yace"Fa'iza ki bar tuna baya..Na rantse da zatin Allah na gane kuskure na,Wlh kin fiyemin kowacce mace a wajena yanzu.Ki yi min aikin gafara ki yafemin laifuka na nayi miki alkawarin zamowa mijin da baki taba jin Labarin kamarsa ba' Don Allah Fa'iza ki yi hakuri" Kauda kai nayi kada kalamansa su sakani rauni cikin shakewar murya nace"Saboda yanzu ka rasa komai yasa nake da amfani a wajen ka..? Da Sauri yace"Wlh Talllahi ba haka ba ne. Allah ne ya dubeni da idon Rahma..Ya ganar da ni da wuri ba sai na mutu kasa ta kasa karb'ana Saboda bazan zamo adali gareki ba,Wlh Fa'iza in baki yafe min ba to Baba ma dake chan kabarinsa bazai taba yafemin ba" Kiran sunan Baba da yayi sai rauni ya kamani cikin kuka nace"Allah sarki bawan Allah mai son zumunci da son ya'yan yan'uwa. Allah ya jikan baba da Rahma" Da rawan jiki ya amsa da ameen Lokaci d'aya yana fadin"Ki yafe min Fa'iza ko don darajan Baba.Ki yafemin ki kuma bama Rayuwar auran mu Dama ta biyu don Allah.." Sai kawai na kallesa ina fadin"Ta ya ya zaka Zauna da wacce baka taba so ba..? Da Sauri ya Rumgumeni yana fadin"Wlh INA SON KI FA'IZA..wlh ina sonki" *Janafty* [7/17, 7:32 PM] +234 703 465 7829: *KNKB2011* *Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.* *09069067488* Kalaman Ina sonki Fa'iza. Sun shiga jikina sun kusa kassarani sai nayi masa kuri da ido kawai,bawai don na yarda da mganarsa ba,Ba kuma don na taba rikesa a raina ba,so nake ya kyaleni yasa na yi saurin cewa"To ka sakeni mana"kara kamkameni yayi yana fad'in"Sai kin ce kin yafe min. kuma kin amince ki bama rayuwar auran mu Dama ta biyu" Cikin Sarkewan numfashi nace"Na yafe maka ban taba rike ka a raina ba Yaya Ishaq,a komai in kayi min bana ganin laifinka. alfarman da kayi min da kake zaune dani baka taba korana ba,shima wani abu ne,na yafe maka duniya da Lahira" Sai kawai ya kara kamkameni yana Dariya cikin farinciki yake fad'in"Thank you so much Fa'iza.Na gode nagode.." Lokaci d'aya yana sumbatar bakina nayi saurin kwace jikina ina fadin"Na yafe maka ammh kuma ina da Sharad'i na" Sai jikinsa yayi sanyi ya koma yayi min kuri,yana kallona bakin sa na rawa yace"Me ne sharad'in Fa'iza.? Yana bani mamaki sunan Fa'iza a bakinsa kamar shi ya rad'amin. Ina kallon cikin idanuwansa nace"Na yafe maka duka abubuwan da kayi min. Sai dai indan har kana so na kara bama auranmu wata Dama, sai dai kayi min alkwarin bani Lokaci har zuwa sanda naga dama sai nayi maka mgana" kamar ya had'iye wani abu sai da naji karan miyan da ya wuce ta makogwaronsa mukut. Ban damu ba, na cigaba da fadin"in kuma ka matsa min to zan fasa yafe maka.sannan kuma bazan iya cika muradinka na bama auran mu wata Damar ba" Da Sauri yace"Aa to to na amince.ammh Fa'iza har zuwa wani lokaci?kada ki dauki Lokaci kinga fa Halin da nake ciki..? Kai Tsaye nace"Ba ruwnka da Lokacin da zan d'auka alkawari shine kada ka takuramin in kuma ka takuramin zan fasa
Chapter 92 · 0% Book details