← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 175

Sashe 29

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wayau da sanin me ake ciki,gabadaya na rasa mafita Kwana takwas da Faruwar haka Ranar da yammah sai ga Jamal yazo shima k'wallo suka zo yi anguwan ya shigo gidan ya iske su a bakin Anum yaji basa zuwa makaranta da ya ce meyasa yau basu je ba..?Shine daya tambayeni nace an koresu ne basu biyu kudin makaranta ba yana ta mamaki ya tambayeni ko na fadama Ya Ishaq sai nace mai A'a. A gabana ya Daga waya ya Kirasa yana fadamai abunda ke faruwa duk da bana jin me yake fada nasan Fada yake yi kuma duk a kaina,Sai da suka gama mgana yace min Ya Ishaq yayi fada kan meyasa ban kirasa na fadamai ba..? Har Jamal din na fadin"Anty Fa'iza kema da kin kirasa kin fadamai Halin da ake ciki.." Kallonsa kawai nayi ban yi mgana me zan ce..?ko na fadamai ba ganewa zai yi ba shurun yafi alheri. Labari har kunnen Mama da Anty Binta na kuma san nasha Zagi da cin mutumci washegari Jamal din yazo ya Dauke su ya kaisu makarantar ya biya komai,Sannan da yammah ya kawo min 20k a bama Haruna kafin ya Dawo na karba nayi godiya da Safe kuma da kaina na shiga na kai mai yana ta godiya nima inayi sai naga ai ni ce da Godiya domin ni yake yi ma alfarma. Haka rayuwar ta cigaba da gangarawa masu jin dadi suna ji masu jin akasin haka ma sun cigaba da ji,Har azumi ya karato Ya Ishaq bai waiwayo mu ba abun na bani mamaki ace in shi ya manta damu su Mama ai basu manta yana da mata da ya'ya ba ammh sai naga suma basu damu ba kamar hakan ma yafi ye musu,Kayan abinci ko wani sako sai dai ta Hannun Mama ko Anty Binta batagwara,Ni bani da wata Daraja ko kima sai ta zaman ya'yansa kamar yadda yace din. Tuni yara har sun saba tafiya makaranta ba biskit ba Lemo saboda babu Daga shinkafa sai taliya ake kawo min sai man girki da kayan maggi,duk abunda bazai zama Dole ba ba'a kawo mana shi,Nama ko mun manta rabon mu da shi,ni bana ma jin kaina yaran nake ji sun gaji da Rigima sun Hakura tunda babu sannan Tun suna Zencen Daada har suka hakura suka Dangana ni ce karfin gwiwan su shiyasa bana yarda na Sare ko Raunina ya bayyana agabansu Ahaka muka fara azumin watan Ramadana,Har kuma muka fara shi muka sauke Ya ishaq bai zo ba,kuma bai taba nema na ba,Ni ma sai na kama kaina sai dai da watan nan mai albarka ban yi barci ba nayi addu'an Allah ya sama min mafita domin ya'yana domin goben su,Kayan sallar yara Sai ana gobe sallah Jamal ya kawo musu Amir da Musty shadda guda biyu sai yan kanti kowanne D'aya d'aya Ahmad ma shadda guda daya sai sauran yan kanti Anum kuma Atamfa da leshi dinkakku sai Doguwar riga guda daya,sai takalma su sai nawa kala daya jal na wata Bakar atamfa,ko araina ban ji zan sakaba sai dai in na zauna ba kaya ammh in dai suturan Ya ishaq ne na hakura da su har abada Tsoffin dai zan cigaba da sawa Tunda bani da zabi ammh bayan ya jingine aure na dashi na cire ma raina kara Daura wani abu daya fito daga Hannunsa.. Ganin yadda ya kwarari wata Hudu bai zo ya ganmu ba nasan da gaske yake yi ya zabi Zainab a kaina sai ban ji komai ba sai dai naji Bakinciki har da ya'yan sa suma ya jingine su..? Ban damu ba ni kawai Fafutaka nake yi har akayi azumi akaga gama bamu ci ko tsokar nama ba ballatana su Dankali da kwai sai tsurar abinci kawai nice nake Sarrafa nau'in abincin Tunda Allah yasa na iya sai Wahalan bata mana yawa sosai ba. Naman Sa da naman kaza Jamal ya kawo min ranar idi da Safe na gyara na soya su Anum nata murna zasu ci Nama sai da nayi musu kwallah ina Tunanin tun yanzu kenan to nan gaba bansan wani Hali ni da ya'yana zamu shiga in dai na zauna ahaka ba, Allah Sarki Goggo washegarin Sallah sai ga Hafsatu ta aiko da sakon Nama da Cincin da Cake,Naman soyayye da Danye,Sann an da sakon Hijabi Sabo da Anty mariya ta dinkamin da takalmi na karba na rumgume kayan ina kwallah Allah Sarki yan'uwana basu manta dani ba duk da ni ma ban manta da su ba yanayi ne yasa nayi nesa da su ba acikin son raina ba Ta fadamin daga gidan Tamadina take jiya taje chan ta kwana ta kai mata kaya daga kano Anty Asiya ta aiko dashi sai naman sallah Daga Goggo sai na wajen Ya mariya naji dadin jin Tamadina tana lafiya,Naji takaici bani da abunda zan daga na bama mahaifiyata nima nema nake yi. Zuwan Hafsah ne ya Debemin kewa Dani da yara Ranar sallah ta uku gidan Mama muka yini sai Dare Ya Ishaq ya sauka shi da Zainab,Anty Binta da Mama suka rasa ina zasu saka su saboda murna mun gaisa da ita sai mamakin ganin chanzawarta nake yi ta zama wata katuwa ta kara gogewa shima gogan ya Sauya kamar ba shi ba har da Tumbi ya sauke. Darajan zainab yasa da ni da yara da Hafsah ya kwaso mu muka koma gida,Wannan karon ma Shashen sa ta sauka kuma ni na rika wahala da ita da shi,Dalilinta yasa yayo mana Cafane mai rai da lafiya Saboda sai abun take so ake ci acikin gidan,Da kuma zabinta ake amfani.. Hafsah ita kanta da take yarinya sai da ta ga abun bai dace ba ranar da zasu fita yace na shiga na gyara Bangaransa nasa,Suna fita ta kalleni kafin tace"Yanzu Anty Fa'iza bayan Girkin da kike musu har da gyaran inda suka kwana kamar wata yar aiki..? Ban ce mata komai ba sai ma Dariya kawai da nayi to ai batayi karya ba kamar yar aiki nake agidan nan,Sati Daya suka yi mana suka koma inda suka fito,Hafsah dai ana jibi Tafiyarsu ta koma Karofi Saboda an koma makaranta.. Bayan tafiyar su muka koma Gidan Jiya kamar yadda muka Saba dai,Allah ya taimake ni Matar Ya Isa wajen Goggo ta haihu,yan biyu Dalilin dayasa Mama tace na shirya aje suna Dani,Murna kamar an biyamun aikin Hajji,Dukkamu muka tafi har da Anty Mahma da Halisa da yara,Nima tare da su Amir muka tafi chan na hadu da Ya Mariya,Yaya asiya dai bata samu zuwa ba,naji dadin zuwana karofi Allah yasa kuma Lokacin Tamadina tazo gida na kai mata su Amir ta gansu sai mamakin girman su take yi shi da Anum,Koda wani Lokaci in naga Tamadina sai na tuna da Dan'uwan ta da akace sun hada Uba,Wanda tunda mahaifiyarsa da Danginsa suka tafi dashi ba"a kara jin Labarinsu ba sai ina Tunanin ko yana Raye..?ina fatan yana Raye domin shi kadai ne shakikin Mahaifiyarmu. Hajiyar Dala tazo anan take kara Fadin Bikin Diyarta Suwaiba nan da wata Daya,ban saka raina ba Saboda nasan ba barina ma za'ayi naje ba. Kwananmu biyu muka Dawo gida Mama kuma Yamai tatafi kanwarta Hure mijinta ya rasu ta tafi gaisuwa ta jima tafi Sati biyu Sai Badariya ta Dawo gidana tana kwana in gari ya waye tayi wanka ta shiga makaranta in kuma tana gida mu shiga kitchen tare tana ganin girki Saboda bata iya Sosai ba Tunda bata zaman gidan. Ita kanta sai da tayi mgana ganin Daga Shinkafa sai Taliya kawai muke da shi tace ban gayama Ya ishaq cefane ya kare ba ne. ?Sai nace ban fada masa ba ashe da ta koma gida Mama ta dawo sai ta fada mata shikenan Cibi ya zama kari wai ina yawo ina fadin Ishaq ya barni da yunwa Mama musamman tazo gidan Har Store ta shiga taga shinkafa ta fara Masifa tana zagina wai wannan abincin dake gidan gidan uban wa zan kai da zan ce ba kayan abinci..? Har tana fadin nama samu ne mata dadama suna neman irin Damata basu samu ba,Har jamin kunnen tayi kan wai ina albuzuranci da kayan abinci,bai isa ace sun kare ba ko dai ina Saidawa ko kuma ina kyauta dashi Ina mata rantsuwa da abunda zai kasheni ban taba Saida abinci ko nayi kyauta da shi ba,Tace bata yarda dani ba ni bakar Munafukace ni. Haka tatafi ta barni ina kuka kamar raina zai fita abun ya koma har da kazafin Satan abinci wlh ban taba ba,Ba Halina ba ne sai dai nasan ko zan shekara ina Rantsuwa Mama bazata yarda dani ba. Sai nayi kuka na ni kad'ai na Share hawayena na riga na yardan ma kaina Allah kadai ke da mafita sannan garesa nake neman mafitana,Acikin wannan tsukin Bikin Diyar Hajiyar Dala ya taso har ga Allah ban sa araina zan je ba sai ga Mama ta aiko Badariya akan na shirya dani za'a tafi kano yara kuna gidan Anty Binta zasu zauna tare da Halisa suna Exams bazata samu zuwa ba. Ashe ashe da walakin goro a miya,Hajiyar Dala tace azo dani Saboda aikin abinci Shiyasa Mama ta ce na shirya ana gobe biki muka tafi dani da Mama da Anty Binta da Badariya,Su Amir kuma na bar su wajen Halinsa. Chan muka iske Goggo da Anty Nasara Da Hafsatu Yaya mariya sai adaran da muka isa ta iso,Yaya Asiya kuma ace ciki gareta har ya fito sai korafin na Rame na lalace suke yi sannan na kara baki na zama kamar tsohuwa ni dai bana cewa komai Saboda bani da tacewa,Tunda muka isa Hajiyar Dala ta Turani Dakin girki,Da Goggo tayi mgana sai Mama tace Saboda na iya ne,kuma don na rika nuna ma ma'aikatan girkin yadda komai zai tafi ni ban damu ba Saboda ai wahala aikina ne. Ranar Daurin aure da Safe Bak'in Abuja suka Diro Ishaq da Zainab da kanwarta Zuzu wacce bata jin Hausa,ire iren kawayen Suwaibar Hajiyar Dala Hafsah dai da Badariya suna tare,Bamu hadu ba Saboda ina kitchen muna ta aikan abincin yan Daurin aure da ma'ikata,sai Dare na samu kaina ina Dakin da muka sauka nayi wanka kenan,na tada Sallar mangariba su Ya mariya suna Dakin ita da Anty Mahma da ta iso da Safe sai Hafsah,Sai ga Ya Ishaq ya shigo
Chapter 29 · 0% Book details