← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 175

Sashe 121

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba, Sannan ba a kaina aka fara zama zawarci ba kuma ba kaina za'a kareta ba,sai dai nayi alkwarin zawarcina ba irin na kowa ba ne. ban rabu da Ishaq Saboda na koma makaranta domin na samu Ilimin da yake min gori ba a'a na yanke rabuwa da shi ne,saboda baya sona sannan yana zama dani ne Saboda Kalaman Baba da kuma alfarma. tunda ya auri zabinsa sannan ya Jingine aurena da shi addini ya bani Damar iyayena ko shari'a ta shiga ciki ta raba auranmu. Ranar kamar an yi min fami Yini nayi ina kuka,ni ko sai na nuna ma masu Tunanin Ishaq rufin asiri na ne da cewa ba shi ya Rufamin asiri ba. Allah ne sannan shi ke rufama bayinsa asirin su na Duniya har da na Lahira. naji kwata kwata ko ina da burin komawa Saboda ya'yana na cire wannan Tunanin ina da yakinin tunda ga Zainab ga Anty Fadila yarana baza su yi maraici a Lagos ba. ***** Ina da Kwana ashirin da Biyu da jinya a asibiti ranar wata asabar Nana Fatima ta Diro,bata zo da yaram ba. daga ita sai Direba tace kuma zata kwana min Daya sannan ta koma,tazo min da katan katan din lemuka da kayan karin jini,sai pepe Chicken da yawan shi,gefe daya ga Yam ball,sai Faten wake da yaji hanta da allayahu,Naji dadin zuwanta sosai daman kuma ni na fada mata bakina bayamin dad'i sosai ba kasafai nake son cin abinci ba,kuma naci Faten waken sosai ya kuma saka bakina yayi dadi. Mun kule a daki muna ta Hira na saki jiki da ita saboda Nana Fatima ta Dabam ce gaskiya ina kaunarta don Alah kamar yadda take kaunata,Ba ta sako min mganar Ishaq ba kwata kwata. sai dai tana ja na da Labaran da suka saka na saki jiki muna ta Hira kowa yazo dubani Ranar sai yayi mganar sakin jikina sai an ga Nana Fatima sai ace Lalle jinina ya hadu da ita. Mun tsinke da hira ko kiran wayata ban ji ba,muna ta hiran ginin Abba da aka gama komai Fenti kadai ya rage Nana fatima ke cemin"Kila har da Inno zata dawo nan" Ni kuma sai nace mata"Anya..?Abba ban ji yana mganar ba" Sai tace min"To ai naga Inno ta saba da Baba Ati ne dakyar ta yarda Abba ya Dauketa zuwa nan sai dai su dawo tare"Kai tsaye nace"Ita kuma Ammi ai bazata ji dadi ba in dai Inno ta dawo nan da zama" Muna cikin Hiran ne Abba ya kira wayar Nana Fatima bayan ta Dauka sun gaisa tace gata ta ga Fa'inzan sa Cikin Dariya yace"Au madallah ashe ke Fa'iza ta samu yau ba'a ji kiran Abba ba"Dayake ta saka ta a amsa kuwwa ina ji. Cikin Dariya na karbi wayar ina gaisheshi ya amsa yana fadin"Fa'in Fatima shikenan yau ina ta kira baki Dauka ba ashe Fati ce tazo ta sha gaban Abba"bakina na rufe da Hannuwana ina yar Dariya nace"Abba wayar na nesa ne ban ji kiran ka ba kayi hakuri" Da Sauri yace"Bakomai Fa'iza daman naji ya jikin ki ne..?na kuma jiki Lafiya lau ga Nana nan ta wakileni ki kula da shan mganin ki kin ji ko..? Na gyada mai kai Lokaci daya ina fadin"Toh Abba" Sallama muka yi gabadaya ya kashe wayarsa bayan yace min zai zo da zaran aiki yayi masa sauki. Mun cigaba da Hirarmu da Nana Fatima sai taba kashin wuyana take yi tana Fadin"Haba Fa'in mu wad'anan kasusuwan fa..? Ina Dariya nace"Daman ina da kashin wuya. Bani da kiba tun asalina" Nana Fatima tace"Har da ta damuwa da kuma yanayin rayuwa Fa'i" Kai Tsaye nace mata"To bawa ai ba'a rabasa da Tunani ballatana mata ire irena da suka samu nakasu ta bangarori da dama" Sai a alokacin ta kalleni cikin wani yanayi kafin tace"Fa'iza daman fa zuwana ba na duba ki ba ne. Harda cire miki wannan tunanin a ranki" Sai nayi dariya ina kokarin mantar da ita mganar nace"Shine kika k'i zuwa da su Jalil.."? Hararata tayi kafin tayi mgana mukaji Goggo na faman maraba da bakuwa afalo,Muna dakin bamu fito ba Goggo ta lekomu tana fadin"Ke fa kin yi bakuwa. abokiyar zaman ki ce ta zo yanzu" Ido na zaro kafin nace"Zainab..? Ban gama rufe baki ba sai gata ta shigo,da cikinta na fara cin karo har ya Fito dayake mayafi ta sanya ta kara Kiba ta zama katuwa,cikin Mirmishinta na yan gayu tace"Ni ce Maman Amir kin yi mamaki ko..? Ni da Nana Fatima muka kalli juna kafin ni na yunkura na mike naje na Tarbota rumgumeni tayi tana fadin"Sannu Maman Amir kin sha jinya" Na amsa mata ina kokarin karban karamin akwatin hannunta da jaka na jata gefen gado ta zauna ina fadin"Sannu..ai sannu na wajen ki maman yan uku da nauyin jiki haka kika Dauko hanya..? Kai Tsaye tace"Ya zama Dole tunda kin Hana Honey sukuni dole nazo nayi masa biko" Ban ce mata komai ba na fita falo na barsu suna gaisawa da Nana Fatima Ruwa na Dauko mata da lemu na kawo mata,ruwan kawai tasha tace min tana so tayi wanka sai na nuna mata Tiolet ta shiga ni da Nana Fatima sai muka fita falo mu bata waje ta natsa kan kujerun falon Goggo muka yada zango nan Goggo ta same mu ta kallemu tana fadin"Daman kinsan zaki yi bakuwa baki yi mgana ba Fa'iza..? Cikin girgiza kai nace"Wlh ban sani ba Goggo ni bamu yi mgana da ita ba" Goggo ta kada kai tana fadin"To me za'a dafa mata..? Kai tsaye nace"Abunda ya sauwaka Goggo kada ki matsa ma kanki". Goggo ta wuce tana fadin"Ke dai bari. ai bakon ka Annabin ka Fa'iza" Sai da ta bar falon Nana Fatima ta kalleni tana fadin"Wannan ita ce abokiyar zaman naki..? Na gyada mata kai sai kawai itama ta tabemin baki tana fadin"Lalle to me tazo yi..?daga Lagos din take kenan..? Da sauri nace"A'a ita bata bisa ba..Tace sai ta gama kintsawa inajin bata riga ta tafin ba ne" Daganan Nana Fatima bata kara mgana ba,sai muka sauya hirar muka Shiga wata mganan muna nan zaune sai ga Anty Nasara tazo sai muka hade muna Hirar gabadaya,Abinci da tazo da shi aka dibar ma zainab Farar shinkafa da miyar allayahu,da Nama taci kadan sai ta kishigida hutawa sai da aka kira mangariba na tada ita tayi sallah muma muka yi. Sai bayan mun idar muka zauna muna kara gaisawa ina tambayanta yara tace suna gida wahala ce tazo dasu tana fama da kanta. Na gabatar mata da Nana Fatima sai ta kalleni kafin tace"Ok..nagane Daddy ya bani Labarin Kanin mamanku friend dinsa ne yarsa ce ko..? Sai na gyada mata kai itama Nana Fatima na gabatar mata da Zainab suka gaisa sama sama na wayayyin yan Boko daganan kowacce ta Dauke kanta. Ni ce muka cigaba da mgana da ita,ban tambayeta ba tace min"Gobe zan wuce lagos fa Maman Amir" Cikin murnata nace"Allah sarki..Kin gama shirin naki kenan..?. Da kai tamin mgana kafin tace"Eh nagama gobe jirgin yammah zan bi zuwa lagos shiyasa da wuri zan bar nan" Da jinjina kai na bita kafin nace"ammh tare da yaran gabad'aya ko..? Cikin muskutawa tace"Da Farhan kadai Daddy ya roki Honey ya bar masa Fadil ban san ko ya amince ba tukunnah" Da kamar bazan yi mgana ba sai nace"Naso da Fadil su Amir zasu ji dadin in kannen su na tare da su" Sai ta juya ta kalli Nana Fatima taga tana ta latsa wayarta cikin Sauke murya tace"Maman Amir wajen ki nazo..Ina so mu yi mgana ne" Ta fad'a tana kallona ni kuma kai Tsaye na gyara zama ina fadin"To ina sauraranki" Sai ta juya tana kallon Nana fatima Fahimtar da nayi na abunda take nufu yasa da sauri nace"Kada ki damu Nana Fatima yar'uwata ce ta jini zaki iya yin mganarki bata da matsala" Jin abunda nace yasa ta gyara zama tana fadin"Maman Amir sai naji mgana a bakin Honey mara dad'i" Cikin son basar da zencen nace"Mganar me..? Bude ido tayi kafin tace"Kin ki binsa Lagos sannan kin ce ya sake ki. Haba Maman Amir" Zan yi mgana kenan Nana Fatima ta katseni da fadin"Baiwar Allah kinsan fa tana kan dokar Likita ne ba'a so ana mata mganar da zata tada mata Hankali. duba da Condition dinta, da zaki yi hakuri da mganar nan sai next time da yafi" Sai naga Zainab ta mata wani Kallo kafin ma tayi mgana itama sai na tareta da fadin"Nana kyaleta ai na samu sauki" Cikin tsareni da ido tace"Dokar Abba fa..?Shi yace kada a kara miki mganar mijinki har sai lokacin da yace" Idanuwana na Lumshe kafin na bude Lokaci daya ina fadin"Fatin mu kyaleta ai mgana ce kadai ko..? Ganin nace haka yasa ta koma gefe tana cigaba da danna wayarta Zainab kuma sai tayi wani iri ta Lura dai yar'uwata bata yinta kwata kwata. Kallonta nayi ina fadin"Uhm ina jinki maman fadil" Da Sauri ta rike hannayena tana Fadin"Nazo ne tattakiya daga Abuja na baki Hakuri maman Amir wlh Honey duk ya susuce ya kasa ma natsuwa kan aikinsa yara kuma kinga sun ki zama tare da shi,Mama ita kadai ce a gida tunda Badariya na kano,Kuma kinsan sun saba dake bai kamata ki yanke hukunci cikin Fushi ba. A madadinsa ina baki Hakuri gobe ki shirya sai mu tafi tare bazan ji Dadin zama agidan nan baki ba Maman Amir" Ta karishe fada cikin marairaicewa,Sai na yi mirmishin yske kafin nace"Ba ga ki ba maman Fadil. Bani da Haufi kan su Amir zasu samu kulawarki kamar yadda suke samun nawa,mganar kuma ya susuce akan in koma ba gaskiya ba ne. Ke kanki shaida ce farkon zamanki dani kinsan wasu abubuwan kin kuma san Mijinki baya sona kece zabinsa to ki barni nima na sauwake ma kaina mana,da zama fa inda ba'a sonka gwara ka zauna inda ake sonka sau dubu Zainab" Taran Numfashina tayi tana fadin"Wlh Honey na sonki ni Shaida ce" Kai tsayen nima nace mata"Aa ban yarda ba,so d'aya ne yana wajen ki. Ke yake so kuma ke ce ki ka yi daidai da Ra'yinsa da Burinsa ni kawai na Haifa masa ya'yavne sannan na zauna na Kula da su,ko a yanzu ya damu ne Saboda haka ba domin ni din yake
Chapter 121 · 0% Book details