← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 175

Sashe 18

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bai yi rigima ba Tunda naji su Anum shuru nayi Tunanin Babansu ya Dauko su suna gidan Mama. Shiyasa na idar da sallah sai na fara jera ma kowanne kayan sa a dirowansa ina Dakin wayata na kara ammh ban ji ba sai chan sama sama naji karan a cikin kaina. Na daukota na Duba Goggon Karofi ce Ina hada Hausa Ina karantawa wanda bai da wahala sosai in dai kamar na sune ko mgana wacce ba'a rubuta tayi tsawo ba. Ina Daukan kiran na sakata a speaker Hafsah ce muka gaisa tace ta Sauka lafiya taje wajen Tamadina taji sauki tana ta godiya Daganan ta bama Goggo muka gaisa ta yi tamin nasiha daman ita nata kenan Fadi take yi "Fa'iza ki yi hakuri kin ji ko..?Allah bai manta dake ba..In sha Allahu zaki ci Ribar wannan biyayyar taki" Shuru nayi ban ce komai ba ta yi ta bani Misalai da matan da suka yi Biyayya agidan aure sannan suka Rabuta ranar Lahira hawaye suka kawo Cikin idanuwana ina tuna Baba a mganarta shima duka kalamansa ne..daga karshe tace min"Naji Isahaq zai kara aure ko..?to sai kin kara Hakuri Fa'iza daman abunda Saudatu take nema ne ya samu ki koma gefe ki rumgumi ya'yanki Allah yayi albarka Allah ya baki Dangana" Ina share hawayena nace"Ameen Goggo ammh dai zaki zo ko..? Goggo tace"To sai nagani in zan samu zuwa ammh yara zasu zo su zauna Dake" Daga haka mukayi sallama na koma na cigaba da aikina naki bari Tunanin auran nan ya shiga zuciyata. Tun ina saka ran dawowar su da wuri har na sare gani har Tara tayi nayi sallar isha'i nayi ma Ahmad wanka har yayi barci nima wanka na Sake yi na saka Riga da wando masu taushi na barci Diyar Goggon karofi Anty Nasara ta kawo min su Tsaraban Umra. Ina zaune afalo ni kad'ai kamar mayya naji Hayaniyar yaran da shigowar su dukkansu jikina suka fado suna murna nima na rike su ina Mirmishi Tun kafin nayi mgan Amun tace"Umma Gidan Mama fa Daada ya kaimu" To daman yana da inda yafi gidan Maman ne..? Suka fara gwadamin Tsaraban Kayan lashe lashen da ya siya musu sai ga shi ya shigo yana shigowa da sallama bai ko bari na amsa ba ya fara fada yana fadin"Don iskanci kina ji ina ta Hon bazaki iya fitowa ki budemin get ba..? Ni wlh har ga Allah ban ji ba cikin sanyina nace"Ban ban ji ba wlh..kayi hakuri" Tsaki kawai yaja ya wuce Shashensa yana fadin"duk kin ji..ai ba hayaniya a inda kike balle ki fake da Lalurarki" Ina jinsa ban ce komai ba sai ma kirkiri mirmishi Saboda yaran kada su Fahimci wani abu,ni ke kokarin kauce ma wasu abubuwan ammh yadda Ya ishaq baya jin kunyar tozartani gaban ya'yana in da ina Biyesa da tuni yaran tun tashi da shi a ransu,sai dai in dai suna wajen da ya fara fadansa zan yi saurin ba shi hakuri na nuna komai ba komai ba ne. Kayan makarantan su nace suje su cire kafin su ci abinci sukace min sun sha tea agidan Mama. Suna shigewa d'aki ni kuma nabi Ya Ishaq Shashensa kada yace ya dawo nayi banza dashi daman na hada mai abincin sa tuni na kai mai shashensa. Koda na shiga yana Cire kayan jikinsa sallamanta ma aciki ya amsa min na Rankwafa ina mai Sannu da zuwa ya amsa sau d'aya ya dauke kai ya Tura kofar Tiolet ya shige ni kuma sai na karisa cikin bedroom din na Tattara kayan daya cire na ninke mai na bude Wardrope dinsa na sakamai na gyara mai Dakin Dazu daman saboda bai bar key din bane shiyasa. Ina Dakin ya fito yana Digan ruwa da Sauri na Dauko mai Towel na basa ya amsa yana Goge jikinsa Lokaci d'aya yana kallon kayan jikina ni kuma ban ma Lura ba wardrope dinsa na Bude ina Fadin"Jallbiya zan dauko maka..? Kai tsaye yace"Bar shi kawai" Ban damu ba na rufe na koma gefe na Tsaya kaina na kasa kamar Daga sama naji yace"Ina kika samu wad'anan kayan barcin kuma..? Shuru nayi kafin nace"Anty..Na..Nasara ta kawo min Tsaraban Um umra." Tabe baki yayi kafin yace"Shi yasa da zata baki sai da ta zabo kalan da zai yi daidai da yanayin ki.. Green wannan kayan ba su yi ba ammh ke kin ga abun sawa da sunan ki yi ma mijinki kwalliya dashi.." Sai naji na muzanta duk da ya saba kusheni ammh na yau sai yafi Dafani barin ma da ya kara fadin"Kwata kwata na rasa wani abu ne zaki saka ya Dace dake Fa'iza..Alhamdulillah da Allah ya bani Zeey yarinyar mayar dressing ne komai tasa ajikinta sai kin ga kamar don ita aka Hallici kayan zata zo kuga juna don Allah in kun had'u ki fara D'a ukan gyara daga kanta" Kaina sai da ya yi Dum jikina sai yayi min ba Dadi ammh ban nuna ba kayan jikina na kallah har ga Allah ni ban ga Aibun su ba kore ai kalan yan aljannah ne sai dai daman shi tozarcin sa ba inda baya tashi. Da naga zai saka kaya sai na fice abuna na zauna afalo ina jiransa haka ya fito yazo ya zauna ya fara cin abinci sai da ya gama sannan na kwashe komai na kai kitchen na koma nayi mai sai da Safe naga yana waya da Hannu kawai yayi alamun naje ni kuma na fice na koma Dakin yarana na iske Amir na koyama Anun aikin da aka bata a makaranta Musty har yayi barci na gyaramai kwanciya na mai addu'a na koma cikin su Anum na zauna ina ganin abunda suke yi ina mirmishi sai da suka gama na saka Amir yaje yayi fitsari shi da Anum suka kwanta muka karanta addu'an barci atare suka Shafa na gyara musu kwanciya na rage musu fanka na kashe musu wutar Dakin na fita zuwa D'akina na gyarama Ahmad kwanciya nima na kwanta agefensa ina addu'an barci. Karfe uku na dare yau na tashi nayi Nafilfiluna sannan na fita naje na tashi su Amir,sai ga Baban su ya fito suka tafi masallaci ni kuma muka yi tamu ni da Anum agida. Kamar yadda n Saba kafin bakwai din Safe sun shirya cikin kayan makarantar su Ahmad na bayana sai rigima yake yi,Ba ya ishaq zai kai su ba Haruna mai adaidaita ne wanda ya saba kai su baban nasu yau zai koma Abuja. Shashen shi suka je suka mai sallama sannan suka fito ni na saka Hijabi na rakasu har waje muka gaisa da Haruna sannan suka shiga suka wuce ina Dawowa a gurguje na had'a ma Ya Ishaq abun karinsa buredi da kwai na Soyamai sai ruwan tea na kai mai Shashensa ya fito cikin shirin Tafiya sanye da Suit bakake ya tsuke kamar ba shi ba har da wani damfararen bakin glass na ba mutumci. Yana zaune yana karyawa ina Gabansa Ahmad na Hannuna ina Lallashinsa sai da ya gama sannan ya mike yana fadin"Fa'iza zan tafi kuma kila sai satin biki zan shigo.karbi ki ga." Kudi ya miko min yan Dubu na saka Hannun na karba ina godiya Karamar Jakarsa ya Dauka na mike ina Sabe da Ahmad zan karb'a da Sauri yace"Kada ki damu da wannan..Ki kularmin da yarana in akwai wani abu ki kirani a waya..koda yake nasan zaki kira indai kina da bukatar wani abun" Nidai ina biye dashi har Haraban gidan Ahmad ya karba yayi masa sumba kafin ya miko min shi Sai da ya shiga mota sannan ya Leko yana fadin"Anty Binta zata aiko miki da kayan fitan biki da wasu kaya da ta matsa sai na siya miki in ma da wani abu zaki ji wajen su Mama na tafi..Ban da yawo..Fa'iza gidan Mama da Gidan Anty binta kad'ai kike da izinin zuwa ki Kiyaye" Daga haka ya rufe motarsa lokaci daya yana fadin"Ki budemin get" Haka na tafi zugwi zugwai ga goyo a bayana,na saka karfina na bude mai get ya fice na bisa da Allah ya kiyaye hanya na maida get din na Rufe ina Haki sai da na koma falo sannan na Kirga kudi Naira dubu biyar itama nasan Saboda matsalan yara ne daman duk sati in yazo haka ya ke bar min. Kuma kafin ya Dawo ta kare ko Kudin motar da nake zuwa gidan Mama ko Anty Binta sannan ga Dawaniyar yara yau Anun tace bata da pensil gobe Amir yace zai siya Drowing duk anan kudin ke tafiya. Tunda ya tafi sai na maida Hankalina wajen kula da ya'yana Kwana Hudu Tsakani da Tafiyar Ya Ishaq Anty Binta ta kirani a waya mu hadu agidan Mama ranar jumma'a da Safe bayan su Anum sun tafi makaranta na shirya na tafi bayan nace ma Haruna gidan Mama zai kawo su Anum in ya Dauko su daga makaranta. Naje na iske gida cike da kawayen Mama ana ganin kayan lefen da za"a tafi dasu Abuja agobe. Akwatuna goma shake da kayan alfarma ni ko Aleda Anty Binta ta bani nawa Less d'aya atamfa biyu sai takalmi sai Hijabi na karba da Hannun Biyu ammh sai Mama ta harareni tana fadin"Naga kin karba a wulakance kin raina ne..? Kaina na kasa na kasa mgana Hajiya Barira aminiyar Mama tace"To ina Laifi wannan kayan Hajiya Saudatu..?ai wlh naga kokarin Ishaq ma matar farko ai ba kowa ke wani wahalar da kai akan su ba" Mama ta tabe baki kafin tace"Matar ma irin wannan abar ba.." Suka kwashe da Dariya suna nuna ni, Anty Binta ta kyabe fuska tana Fadin"In ma ta raina ita ta sani..Kila wad'anan take kalla ai inda suka dace za'a kai su Yarinya ba inda basu dace ba" Ni dai kazil ban ce ba Saboda suna so naji cin mutumcin su da karfi suke mganar su,Haka suka sallameni na kwashi kayana zuwa Dakin Badariya bata nan tana makaranta. Ba domin nace Haruna ya wuto da su Anun nan ba da gida zan koma saboda su yasa na jira sai da suka Dawo nazo musu da kaya suka sauya ni nayi girki daman indai nazo to kamar jaka haka take komawa agidan Mama. Sai La'asar na koma gida ni da ya'yana da kayan da Anty Binta ta bani duka an
Chapter 18 · 0% Book details