Sashe 156
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta rame ta lalace kamar ba Halisa ba Daga gani dai tana ji ajikinta a raina nace Allah ya kyauta. Anty Binta ke tambayan ina shi Ishaq din.?Badariya tace"Jamal yace ya wuce kano ta chan zai siyi ticket na komawa Lagos. tunda yasan tsiyar da yayi" Mama tace"To ina shi Amir.? Sai da akayi mgana na Tuna da Amir cikin Damuwa nace"Ko dashi ya tafi ne..? Badariya na shirin mgana sai ga Jamal da Amir sun shigo tare,yana ganina ya Rugo ya rumgumeni yana kiran"Umma." Mu kadai ne afalon su Goggo suna ciki,Ammi ta gama warware musu komai kowa yaji sai yace gwara da ya rasa Fa'iza bai chanchanta ba. Mama har ciki ta shiga tana basu hakuri tana sharan kwallah Goggo tace bakomai kansa yayi mawa ga shi ya rasa Fa'iza ita kuma Allah yasa gidan arzikinta ne. Ganin yanayin sa yasa nasan Amir na cikin damuwa sai najashi Daki bayan mun gaisa da Jamal shima hakurin yake bani nayi yake,nace bakomai a raina ko nace shi ke da Hakuri kuma yanzu ammh har abada bazan taba yafe masa da kazafin da ya kullamin ba sai mun yi Hisabi a gaban Ubangiji ranar gobe kiyama. Tambayan Amir na yi da yaci abinci sai ya dagamin kai kafin yace"Naci ai ina tare da su Abba ne a sabon gida" Sai nayi shuru na kasa mgana saboda nasan yaji mganganuna da na Babansa kuma wasu kalmomin masu nauyi ne a Tunanin yaro karami kamar Amir. Ba zato kawai naji ya riko hannuna kafin yace"Umma ki yi hakuri" Sai hawaye sharr da sauri na rikosa ina fadin"Kai Amir menene yasa kake kuka..? Sai na rumgumesa ina Lallashinsa cikin shesshekan kuka yace"Umma ki yi hakuri kin ji ko.? Sai naji kaunar d'ana ta kara ratsani na Dago fuskarsa ina share masa hawaye,ina fadin"To shikenan na hakura kai ma ka daina kuka" Mirmishi nayi masa shims ya maidamin kafin yace"Umma gwara da kika auri Baba baki auri Daada ba. Tunda yace miki ke datti ce" Cike da mamaki nake kallonsa kafin na samu bakin mgana yace"Baba yace yana son ki Umma. Muna yace yana son mu" Sai ga hawaye sharr sun zubomin rike hannayensa nayi ina fadin"Nima ina son ku ya'yana ka kula da kannen ka Amir kuma kada ka kuskura ka fada musu abunda ya faru kaji ko..? Sai ya gyad'amin kai alamun bazai fada ba,kansa na dafa ina fadin"Yauwa Sannan ka lallashesu in zasu yi kuka saboda ban dawo ba kaji ko..? Nan ma kai ya gyadamin nima sai na jinjina kaina kafin nace"Allah ya yi muku albarka gabadaya" Ya amsa da Ameen,mun dade muna Hira da shi yawancin labarin rayuwar su a lagos ne ina jin sa ina mirmishi gefe daya ina sharan kwallah Haka Allah ya kaddara bazan zauna da ya'yana har abada ba. domin nasan Ishaq bazai bani ko daya Daga ciki ba. Sai bayan La'asar su Mama suka wuce katsina an rabu zukata ba Dadi,kamar kada mu rabu da Amir da yaga ma Ina Damuwa sai yace"Umma ki daina damuwa fa zan lallashi su Anum kuma ma ai Baba yace zai rika kawo ki,kina ganin mu muma yace zamu rika zuwa muna ganin ki" Sai na rumgumesa ina kuka Kaunar Engr da ta boye acikin raina ta sake Fitowa a cikin zuciyata,ance mai d'a wawa daman ya Fad'amin shi baya son ya'yansa su kirasa wani Daddy yafi son Baba na gargajiya. Nasan Engr na da kirki ammh sai da Amir ya kalleni yace"Umma ki daina Damuwa shi Baba na da kirki bazai rika sakaki kuka kamar Daada ba" Har suka tafi da na tuna da mganarsa sai naji hawaye sun kawo min Allah Sarki ya'ya Rahma ne Allah ya bama wadanda ba su da ya'ya masu albarka mu kuma da muke da su Allah ya tsare mana su sannan ya kara shiryawa,katsina zasu kwana Gobe su tafi kano Jamal Dole zai siya musu Tiket zuwa lagos tunda Uban gayyar ya watsar da su ya yi gaba. Tunda dai na tabbatar da cewa Engr na aura sai duk wani Fargaba na ya kare na saki jikina da yammah Nana Fatima na cewa na sake wanka ba Gaddama na Sake yin wanka na sauya kaya zuwa atamfa Doguwar riga. Da naga bata ce zatamin kwalliya ba kai Tsaye nace"Fatin mu kwalliyar fa..? Cikin shagwaba na fada ai sai ta rike baki tana fadin"Eyee lalle na yarda ana son Engr ammh ai dazu har kina mana Boren baki so" Ina Dariya nace"Dazu kika ce. yanzu ai komai ya sauya". Duka ta D'akamin tana fadin"Zaki sani ne bazan yi kwalliyar ba". Dariya na fara ina bata Hakuri sai ta rumgumeni tana fadin"Naji dadin ganin ki cikin farinciki Fa'in mu Allah ya saka ki yi farinciki fiye da yadda kike Tsammani, Allah yasa Engr ya juyar dake Dadin da sai kin manta sunan ki" Tsungulinta nayi ina fadin"Ba'a gasa bakin nan naki ba" Na fad'a ina dariya ni da ita ina tuna Dazu da Yaya Mariya tace gwara da Ishaq ya furta haka akansa wasu hallayansa tasa Inno ta mata dakuwa tana fadin bakin ki kamar bai ji gashi ba Mariya, muna ta dariya shine na tuna na fad'ama Nana Fatima" Sai da mukayi sallar mangariba sannan Nana Fatima ta min kwalliya mai sauki sai tunani nake yi ko Engr yayi Fushi ne bai nemeni ba. Abunda ban sani ba suna tare da su Abba har Dr.Lawal sai washegari zai koma Abuja,bazai iya barin su ba,kuma wayata ban kunna ba amnh yafi kowa son ganina da jin muryata. Abincin har sai da aka bama almajirai tunda ba wasu jama'a ni ko su Sa'adatu hana su dawowa yau nayi alokacin bansan lamarin zai sauya ba Ammi ko bakinta har kunne ammh da Safe ko Fara'a batayi. Taruwa suka yi Nana Fatima da Raliya suna min tsiya Badariya na taremin daman tana nan bata koma ba,Yusuf din zai turo Direba yazo ya Dauketa jibi. Muna cikin hakane Abba ya kira wayar Nana Fatima akace a bani ina karba yace"Fa'i ki kunna wayarki Engr na son mgana da ke" Cikin sanyin jiki na amsa mai da toh wayar na cikin karamar jakata ta hannu na fiddota na kunna,naga tarin sakonnin Engr ban bude ba sai na goge su nasan ma magiyane tun a baya yanzu kuma mun taka wani mataki basai mun koma baya ba. Ina kunna wayar kamar yana jira sai ga kiransa gabana ya fadi ga su Badariya sai na lallaba na fice ashe suna Lura dani sai suka kwashi shewa na fice ina girgiza kai kawai. Tsakar gida na fita sai naji akwai sanyi sai na shige dakin Karikitan goggo da nawa ni kaina,na samu saman Freezer na haye har kiran ya katse sai ya kara kira ina Dagawa bai jira nayi mgana ba yace"Alhamdulillah Faa'iza ta zama ta Tosin har Abada" Mirmishi nayi ban yi mgana ba sai ya cigaba da fad'in "Ki ce wani abu mana karo na farko da aurane na akan ki Faa'iza" Dakyar na iya fadin"Ina mana Fatan alheri" Ina jin Sautin mirmishinsa kafin yace"Kin gama mgana gabadaya..? To Ameen ykk..?kin ci abinci kuwa..?kin daina kuka..? Ina dariya nace"Duk ni kadai wanne zan fara amsa maka..? Kai tsaye yace"Duka nake bukata" Cikin karya murya da bansan na iya ba nace"ina lafiya kamar yadda kake. abinci kuma ban ci ba kila sai an jima kuka kuma na daina tun daga Lokacin da naji Labarin na zama matarka" Ni kaina in ina tare da Engr bana sanin ma ina sakin baki ina mgana. Sai da naji yace"Da gaske Faa'iza..? Ni kaina bansan adadin Halin da na shiga ba nayi ma Allah godiya Sosai har Umra zamu Faa'iza domin mu kara godema Allah" Jin nayi shuru yasa ya cigaba da fadin"Papa da sweetheart sun ce na gaishe ki sosai tare da Sister dina. Suna ta min magiyan gobe na taho dake Abuja" Da sauri nace"Ni kuma..? Sai ya marairaice kafin yace"Eh suna so su ganki ne. Ni dayake ma kinga jibi zan yi tafiyata bama ganina zaki rika yi ba" Dariya ya bani kafin nace"Ai sai jibi ne Tafiyar goben bazan ganka ba ne..? Sai ya yi saurin fadin"Nufina daga goben nake so nace" Yafad'a yana sosa keya kamar ina ganinsa yana jina ina yar Dariya wani irin farinciki ya mamayesa kafin yace"Wlh da na son da auran nan Visa zan yi miki kafata kafarki zuwa America Faa'izaa" Ina mirmishi nace"Ayya sai kuma ga shi kafarka kafarka zaka tafi" Kai ya kada kafin yace"Kin ci ba shi. Zakuma ki sha wahala wajen biya' Ni dai dariya nayi masa hira ya dinga min yana bani labarin granny din su ta kirashi tana fadan meyasa aure cikin gaggawa haka? bai fad'ama kowa ba yana cemin"Kinsan me na gayamata..? Sai na girgiza kai cikin Danne Dariyansa yace"Ce mata nayi gaggawan na rabo ne,gwara ayi ayi auran kada na haifa mata yaran da take son gani a titi" Sai na rufe baki ina salati shi kuma yana Dariya kafin yace"To karya nayi..?haka tsohon mijin ki yace nawa na biyaki kika bani jikin ki..? Ni wlh ban ji haushinsa ba ga shi Sanadin mganarsa ya sa jikin ya zama nawa har Abada, in a baya ina biya ne yanzu a kyauta ma za'a bani sai ma ina yanga" Kasa mgana nayi ina toshe bakina kada nayi dariya shi ko ajikinsa cikin Kada harshe yace"Wayyo na tausaya masa sosai" Kai kawai na girgiza kafin nace"Ba kai kayi masa kwacen mata ba" Da sauri yace"A'a daman ai Faa'iza ta Abdulbasit ne shi kadai ban cika neman abu na rasa ba Faa'iza,ni da kika ganni nan ina da sa'a duk abunda na nema ban Samu ba to ki tabbatar da ba Alherina ba ne" Cigaba ya yi da bani labarin sa kad'an da wasu abubuwa na shi,ya yi mganar yana dawowa zan tare na zabi in da nake so na zauna kaduna ko Abuja,ko Edo Saboda na Zolayesa nace"Lagos nake so"Da sauri yace"Ban da nan. Ni bana zuwa Lagos" Yafada har da hade rai sai na kyakyalce da dariya shima tayani yayi kafin yace"In domin yaran mu ne kada ki damu tare zamu rika zuwa ganin su bazan lamunta da barin ki ke kad'ai ba. gwara ki zabi kusa dani wlh kika zabi nesa korata za'ayi a aiki Tunda