Sashe 69
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dai..?ba ku gani ina lafiya, Daddy ka fad'a musu ba wanda ya Dake ni fa" Dr.Lawal bako na zaune a gefe ya murmusa kafin yace"Tun muna Abuja nake fadama Jamal haka,ammh bai bar kuka ba kamar wani mace" Sai aka juya ana kallonsa yana ta sharban Hawaye Ishaq yamika masa hannu yazo kusa da shi Cikin karfin Hali yace"Kun gani ina lafiya basu dake ni ba in baku bar kuka ba,Mama ba zata bari ba" Ni ko ina gefe daya ban tusa kaina ba Farhan ne a sabe a Hannuna yana ganina ya kirani"Umma.." Ni kuma na Chabesa da yake har Hutu an taba kawosa wajena kuma indai suna garin to yana wajena sosai yaron ya saba dani. Sai dai nayi hamdala da godiya acikin raina da ya kubutar da shi Lafiya,duk da an rasa aiki da dukiya sai dai an gode Allah Yaran dake d'akin Badariya basu san abunda ke faruwa ba,suna tare da Halisa,Su na kyalla ido su ka gansa sai suka nufesa suna kiran sunansa "Daada.." Da sauri duka ya Tare su Anum ce akan gaba sai musty da Ahmad Amir dai a gefensa ya zauna yana fadin"Alhamdulillah Daada ya dawo" Mirmishi ya saki ya shafa kansa yana fadin"na dawo Baba na" Anum ta fashe da kuka su Ahmad na tayata Ishaq ya fara lallashinta sai ta tsagaita tana fadin"Daada.." Sai shesshekan kuka ya tareta sai ya rumgumeta yana fadin"Ina fatan baku yi kuka da baku ga Daada ba ko..? Anum tace"Bamu yi ba da mun fara Umma zata hanamu sai tace mu yi maka addu'an Allah ya kubutar dakai,mu addu'a muka yi ta maka" Amir ya karbe da fadin"Umma nata karatun Qur'ani ta d'aga hannu ta na ta maka addu'a Daada nima nayi maka sosai" Gabada'yan falon sai yayi tsit ana Sauraran yaran Yaya ishaq jikinsa ya karayin sanyi kaunar ya'yansa ya kara kamasa ya kamasu duka ya Rumgume yana Dagowa muna Had'a ido ina shirin na gaisheshi tare da barka da arziki karo na farko a Rayuwata tun da na san Yaya Ishaq da ya taba ambaton sunana cikin Tausasawa. "Fa'iza.." Idanuwana a bude na dago ina kallonsa shima ni yake kallo, ba ma shi kadai ba.kaf mutanen dake falon sai kallon su ya dawo kaina,mamaki da al'ajabi basu bar ni na iya amsa mai ba, sai ya kara shayar dani wani gumbar mamaki cikin karin Laushin da yayi ya sake fadin"Nagode..Nagode sosai da baki bari ya'yana sun yi kukan rashi na ba.ko achan in na Tunasu nakan shiga damuwa ammh da zarar na tuna kina nan sai naji sanyi a raina ina da yakinin zaki Kula da su fiye da yadda zan kula da su'" Ya karishe fada yana kallona da zurmamun idanuwansa da suka zurma Saboda wahala abun mamaki baya karewa har da mirmishi yayi min na Daskare a tsaye na kasa mgana Sabon Ishaq nake gani a gabana ko kuwa dai tsohon ne wanda na sani..? Ni kaina baki na yayi nauyi,Nauyin da dakyar na iya fuzgo mganar dake bakina sannu da arziki nayi masa, sannan na hada da Allah ya kyauta cikin yanayina nace"Allah ya baka ikon cin wannan jarabawar Allah kuma yasa a mizani" Cikin Muryansa mai cike da sanyi da Haiba ya amsa min da fadin"Ameen Fa'iza Ameen Ameen" Tare da su Goggo suma da suka amsa ni Ni dai tsabar mamakin da nake ci bai sakeni ba naji ana cewa ya kamata a barsa yayi wanka yaci abinci ya huta zuwa gobe da Safe. Mama da kanta ta rakasa har dakin Jamal ita da su Anty Binta,Mazan kuma fita suka yi Hotel zasu kama su kwana,Sai alokacin muka gaisa da zainab muna ma juna barka da arzikin Farhan na wajena ya makaleni tana Dariya ta bar min shi ta shige Dakin Mama inda ta saba sauka. Ni kuma daman ba ni da wannan gatan Dakin Badariya ne wajen saukata nan muka shige ni da yaran,basan ya suka kare ba ni dai daganan bayan na gama shirya yara sun kwanta nima na kwanta,Kafin nayi barci na dade ina tunanin Yaya Ishaq da Sabon Tausasawarsa gareni, wata zuciyar ta ankarar da ni da cewa kada na sakankan ce kada na manta Hukuma ce ta tsare shi na tsawon Lokaci yana cikin firgicin da bazai yin wani abu ba kada hakan ya rud'eki daganan na watsar da wannan Tunanin na kwanta barci,ammh sai da na tashi wajen uku na Dare na Dauro alwala nazo na yi nafilfilun godiya ga Allah. Washegari da na tashi,na riga na saba da aikin da jikina bazai iya zama haka ba,Hafsat bata nan tana Hostel wajen wata kawarta ta kwana tun jiya,Mun dai yi waya da asuba na fada mata Yaya Ishaq ya dawo sai tace ma ta gani a waya Badar ta saka,Sai da nayi sharan duka Dakunan na gyara nayi abun karyawa sannan na kama yaran nan duka nayi musu wanka, Goggo nata min sannu da kokari Su Anum nata Tambayan Daada Hajiyar Dala tace yana Hutawa ba'a so a damesa. Sai bayan na natsa na kira Yaya Asiya na gayamata sai da tayi hamdala,ta nuna alamun murnanta ammh Yaya Mariya ko ajikinta cewa kawai tayi Allah ya kyauta da nace ko zata zo ne..?sai tace min zaria zata tafi suna, kanwar mijinta ta haihu ban ja mganar ba, sanin bazata zo din ba Yaya mariya akwai kafiya da riko Daman sau d'aya tazo shima ba wai jaje tazo ba,Goggo ce ta dinga mata fada yasa tazo kuma har tatafi Allah ya kyauta bata iya ce ma Mama ba, Da Yaya Asiya ta mata fad'a bude bakinta sai cewa tayi"wani Jaje kuma Yaya Asiya..?Alhakin Fa'iza ne fa ke bibiyan Ishaq da danginsa" Bige mata baki Yaya Asiya tayi ta na mata fada sai bata kara mgana ba, kuma tunda tatafi bata Dawo ba. Chan da rana sai ga su Anty Nasara da mutanen karofi gida ya cika da yan Taya murna kamar Biki kawayen Mama har da yan'uwanta na yamai da suka yi sammakon tasowa da makota ammh Yaya Ishq din na barci har alokacin bai tashi ba, ana ta dai yi ma Mama barka da arziki bakinta Har kunne Hajiyar Dala tun safe ta bi mijinta suka koma Bayan Mama tayi ta Godiya,Kuma duk wanda yazo sai ta nuna Zainab tace ayi mata Godiya mahaifinta ne ya tsaya ma Yaya ishaq har aka sako shi,sannan sai ta zauna ta bada labarin sharri a ka kulla ma Danta,kawayenta na tayata mugayen addu'o'i ga wanda yayi sanadiyar haka. Ni dai ina gefe ban tusa kaina ba,Da kaina na kira Hajiyar su Raliya na fadamata tace sun yi mgana da kaninta ya fadamata an sakesa tace min zata shigo in ta samu sarari yanzu harkokin sun yi mata yawa ne,muka rabu bayan nayi mata fatan alheri da nasara,Yaya Ishaq bai tashi ba sai yammah ya rama Sallolin dake kansa yaci abinci Lokacim Tuni Goggo da iyalanta sun wuce Karofi sai ga Mama nayi mata godiya Goggo tace bakomai an yi ma zumunci ne. Ya iske Dangin mama da makota da kawayen mama da su Anty Binta,ana ta yi mai barka da arziki,yana amsawa kayan Jamal ya saka riga da wando sai naga yana yawo acikinta ahalin yafi jamal cikan namiji a baya sai dai zama waje d'aya da Tunane tunane yasa duk ya zabge. Ni aikina shine Saukewa da Dorawa da an yi baki Mama tace a kawo abinci da ance ya kare sai tace ina nake da bazan sake dora wani abu ba? ko meye amfani na.?daman nasan ba ni da amfani shiyasa ban damu ba Zainab kuwa yar gatace tun safe tana ciki tana hutawa tace min Kanta ke ciwo saboda tafiyar Mota Fadil ma ni ta bama shi nayi mai wanka na goyasa duk wanda ya ganni da goyo sai yayi mamakin sanin Tunda Ahmad ya girma ya wuce Goyo,Sai na juya aga Fadil ne,ni renon yara bai dameni ba kafin ma nasan zafin Haihuwa na iya kula da yara ballatana yanzu da na haifa nasan zafin su,Ni nake Dawainiya da yaran manyan da zasu iya cin abinci da kansu suci wadanda baza su iya ba na zaunar da su na basu,Zuwa Dare gidan ya watse sai na jiki jiki bayan sallar isha'i mahaifin Zainab ya iso daga chan inda ya kama yana Hutawa shima a falo aka taru har da ni ina chan gefe fadil na Hannun kakansa yaran kuma suna jikin Baban su. Mgana yake akan gobe zai koma Abuja Mama da su Anty Binta suna ta mai godiya ya kada kai yana fadin"Bakomai Ishaq kamar Zeey na Dauke sa shima D'ana ne,Ina so na shaida masa kuma ku zama shaida,Na basu gidana na Abuja su zauna da Zeey Saboda bazata iya zaman wani waje ba in ba Abuja ba,nan ta saba sannan yaran nan sun fara rayuwarsu achan bazau yuyu a sauya musu muhalli ba sannan ta na aiki,Sannan kada ya damu nauyin komai ni zan Dauka kafin ya samu wani aiki zamu iya bakin kokarin mu bazai gagara ba In sha Allahu" Mama ta hau godiya har da Hawaye shi ko Yaya Ishaq mama ya kallah kafin ya kalli mahaifin zainab yace"Daddy ban ki mganarka ba,ba kuma don na raina kyautatawarka a kaina ba, sai don yanzu ba da ba ne.In a baya aiki ya kaini Abuja yanzu fa..?Ina ganin zamana a Abuja yanzu bamai yuyu ba ne" Kai tsaye batare da Damuwa ba yace"Why da bazai yuyu ba Ishaq..?ai auran soyayya kuka yi da Zeey, kai ka ganta kace kana sonta itama ta amince dakai na aura mata kai,kuma kai ka zabeta na tabbata zaka bita a duk inda take ballatana ma wannan ba abun damuwa ba ne kada kaji komai aikan ka ya kusa dawowa ko ba wannan ba wani zai samu kaji ko..? Zai sake mgana Mama ta Dake masa Hannu da kafarta ina lura da su ya Dago yana kallonta yana so yayi mgana ta hanasa har ga Allah sai da naku sa yin Dariya. Mama ta juya tana fadin'"Kai Alhaji mungode sosai Allah ya bar zumunci shirmen sa kawai yake yi me zai hana ya bita chan in ya zauna anan me zai yi..?mungode sosai Zainab ki tayamu godiya fa" Tana mirmishi tace"Bakomai Mama" Niko ina gefe araina nace wai me mata da iyalai