Sashe 164
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da kayan barci ruwan toka masu Taushi,yana rumgume dani kamar wani zai kwace masa ni sai na shiga wani yanayi yanayin da ban taba sanin akwai sa ba, na miji ya Rungume matarsa su yi barci tunda na auri Ishaq bamu taba kwana waje daya daga farkon Dare har karshe ba. koma wani abu yake bukata yana samun natsuwa zai tsallakeni ya barni wani lokacin ko na koma Daki ko kuma shi ya koma Falo ya kwana ammh sai ga shi bingiren rayuwata ya kawoni inda ban sani ba. Ina yin motsi ya kara saurin rikoni ya maida kaina saman kirjinsa yana Fadin"Nima nagaji Faa'izaa ki barmu mu yi barci" Yafad'a cikin wata irin murya ashe yaji motsin tashina,sai kawai na bi Umarninsa na koma na lafe saman kirjinsa ina sauke numfashi nayi barci cikin salama barcin da na jima ban yi kamarsa ba. Da asuba shi ya jamana jam'i bayan mun idar muka zauna ya yi ta mana addu'an zaman lafiya,bayan nan kuma yace na dauko Qur'ani daman nazo da shi,shima yana da nashi ya fito da shi,shi ya fara jawomin aya daga cikin suratul bakara na dauka sai da na karanta masa shafi biyar sannan ya yi kabbara yace na Dakata yayi min tambayoyi kan abunda ya shafi sallah,alwala da Tsarki ba domin ban iya ba yasan na iya domin cike wani bangaran sunnan ma'aiki. Muna gamawa shi ya karbi Qur'ani ya ijiye saman Side drower din gadon yana juyowa nayi saurin cewa"Ina kwana" Mirmishi ya yi min irin mirmishinsa mai narkan da zuciyata. Kafad'a ya noke min kamar karamin yaro kafin yace"Bana son wannan kalan gaisuwan Tife bana so. kada mu fara haka da ke" Cikin kallonsa nace"To wata iri kake so..? Tsam ya mike ya iso gabana ya saka Hannuwannsa ya Dagoni ya rumgumeni kam na wani Lokaci kafin ya sakeni ya dago kaina ya sumbaci Goshina kafin ya tsaya yana kallona nima ina kallonsa gira ya dagamin kafin yace"Ki rama ma kura aniyarta mana" Kunya ta kamani na Sadda kaina saman kirjinsa da sauri ya Dagoni yana Fadin"A'ah Faa'iza ni bana son haka sam kunyar me..?ni fa mijin ki me Sirrin ki wanda iyayen ki da yan'uwanki suka damka amanarki a Hannuna ni kuma na karb'a da alkawarin zan iya yi na wajen ganin na rike wannan amanar sai ki bari kunya ta shigo zamantakewar mu ta Cutar dani..?A'ah Faa'izaa..! Bana so..bana son kunyar nan fa" Ya fad'a har cikin zuciyarsa sai naji jikina ya yi sanyi na Dago ina kallonsa sai ya lakuci hancina yana Fadin"Nayi miki afuwa na yau ammh daga gobe zaki fara Duty" Sai na gyada masa kai sake Rumgumeni ya yi ina jin wata natsuwa acikin raina da gangar jikina. Hijabin da nayi sallah ya ciremin yana Fadin"Jiya kika yi min wayau kika yi barci kika barni ko..? Ina sunne kaina nace"Nagaji ne" Shima kai tsayen yace"Nima ai na gajin Faa'izaa sati nawa nayi ina bin Hanya ba kuma tafiyar Jirgi ba" Sai na kasa mgana Tabbas gaskiya ya fada ya fini gajiya da Sauri nace"To kayi hakuri" Ina rufe baki ya amsani da fadin"Waya fad'a miki laifi kika yi..? Sai na rausayar da kaina kafin nace"Nayi laifi mana. muje ka kwanta nayi maka Tausa" Dariya ya saka lokaci daya yana rike hannuwana ja na yayi muka koma kan gado muka kwanta ya Dora kaina saman kirjinsa yana shafawa kafin yace"Menene na sauri..? Tausa ai sai kin gaji da yi yanzu dai ki gama Hutawa ni zan kula dake ammh ki sani bashi ne zaki biyani kayana" Ina mirmishi nace"Kada ka damu Tife zata biya Tosin bashin sa" Dariya ya saka yana kara rikeni a jikinsa da karfi har sai naji zafi nayi yar kara sai ya sausasauta rikon da yayi min yana Fadin"Ina ji kamar in nayi miki karamin riko zaki iya kubcemin ni kuma bana so nayi rauni wajen rike amanarki Tife na" Kai tsaye nace"Nasan ai zaka iya.Zaka iya" Shuru ya yi na wani lokaci ammh bai sakeni ba,har sai na dago kaina ina kalllonsa sai naga shima ni yake kallo maida kaina yayi saman kirjinsa kafin ya kira sunana. "Faa'izaa..'" Cikin wata kasalalliyar murya nima a kasalancen na amsa masa,da Na'am sai kuma ya yi shuru har sai da nace"Umh menene..? Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace"Wata alfarma zan roke ki Faa'izaa..? Kai tsaye nace"Wata irin alfarma ce wannan..? Kai tsaye yace"Rokon ki zan yi. Don Allah Faa'izan a zaman da zamu yi in nayi miki wani abu wanda ba daidai ba ki yi gaggawan sanar da ni na baki Hakuri,kada kice zaki yi fushi da ni ko ki yi min horan kusantar in da kike,Zan fi jin zafin hakan fiye da Laifin da na aikata miki. Ina so komai nayi miki ki tareni ki fad'amin ba kunya ba tsoro ni mijin ki mai sonki da kaunarki ba bautar juna zamu yi ba,bautar Ubangiji zamu yi Ni dake ladan mu na wajen Ubangiji,kada mu zama bakin juna mu dora zamantakewarmu kan tafarkin koyarwa sunna da addini. nima in kika min ba daidai ba zan fad'a miki Domin ki gyara nima don Allah ki ankarar dani a inda na kuskure ba iya amanar kan ki ba Faa'iza Amanar junan mu dukkanmu zamu rike don Allah" Ko kafin ya gama mgana Hawaye sun cika idona yana gama mganarsa suka kwaranyomin ashe akwai ranar da wani namiji zai daukeni nima kamar Sauran mata masu daraja da kima..? Yana ji na fashe da kuka,kukan dake fitowa daga kasan raina jikinsa na rawa ya mike zaune ya tarairayoni ya Rumgume yana fadin"Kuka kuma..? Ko na fadi mganar da bata yi miki Dad'i ba ne..? Yafad'a yana kara rikeni acikin jikinsa ammh na kasa daina kuka saboda abun daga kasan zuciyata yake fitowa,gani nayi ya rude yasa na kara rumgumesa kamkam cikin shesshekan kuka nace"Kukana na farinciki ne. Ina kukan samun abokin rayuwa irin ka,sannan ina kukan da na rasaka ni ko wani irin asara na Tafka a rayuwata..? Sai da ya Dagoni muna kallon cikin Idanuwan juna sannan yace"Ni ne da na rasaki da nayi babban asara Faa'iza ina sonki. Soyayya ta gaskiya" Runtse ido nayi sai ga hawaye sharr,kafin na bude su akansa yana kallona da kaunata acikin idanuwansa sannan ga mirmishin nan nasa mai tsuma zuciyata. Cikin muryan kuka nace"Me ka gani a tare dani..? Kyau.?kudi.?ilimi..? Bani da komai fa. Bani da komai anya na chanchanci wannan kaunar daga gareka..?kana da komai,ko ta ko'ina bamu dace da juna ba..ban chanchanta ba..ban.." Bai barni na karisa ba ya kariso ya hade space din dake tsakanin mu lokaci daya yana sumbar bakina na bude baki zan yi mgana ya tura harshensa cikin bakina da ya yi sanadiyar Daukewar mganata Lokaci daya da wani yanayi da ya zirgamin. Tun ina rawan jiki sai ga shi na saki jikina har ina rumgumesa cikin samun natsuwa da na samu tun a ranar da auren Engr ya sauka akaina. Sai da ya yi har ya gaji yana ganin zai rasa control dinsa ya sakeni ni kuma na koma na lafe ina runtse idanuwana Saboda kunyar data Lullubeni. Rumgumeni ya karayi kam kafin yace"Na rufe wannan mganar. Kada na karajin kin ce baki chanchanta ba. Bana so, raina na kuna,in kuma kina so raina ya rika kuna ne shikenan ki cigaba da fad'a" Yafad'a har a muryansa ina jin ransa na kuna nasan na ji kalmar bana so din da yasa nayi saurin cewa"Na bari bazan kara ba" Saman kaina ya sumbata idanuwansa na lumshe yace"Yauwa Tife na" Mun jima rumgume da juna yana zayyanamin kalaman kauna da Soyayya,yana kuma rarrashi na domin yana yi yana shafa kaina zuwa bayana bansan Lokacin da barci ya kwasheni ba shima dai kusa dani ya koma ya kwanta muka kamkame juna sai Sha d'aya na rana muka tashi ina ta mamakin barcin da na sha. Yana dariya yace"To kin samu jikin Tosin mana ga Taushi dole ki yi barci baki sani ba" Dariya nayi masa ban ce komai ba Tunda nasan gaskiya ya fada,Wanka muka fara yi dagani har shi sannan ya fita ya siyo mana abinci nikan sai da nace"Ka siyo cefane na fara girki baka yi ta siyan abinci a waje ba" Yana dariya yace"Sai yadda kika ce Hajiyata. Siyan abinci kuma daman an saba ganina." Kai tsaye nima nace"Eh lokacin baka da mata yanzu kuma kana da mata" Cikin dagemin gira yace"Ehyee! ya sunan matar tawa..? Nasan zolayarsa yasa na masa fari kafin nace"Tife mana. Tife sunanta" Dariya ya kwashemin dashi kafin yace"Ah'a su Tife an waye an zama yan gari" Dariya nayi masa ban biye masa ba tare muka ci abincin yana bani a baki ni da naji kunya nace zan basa sai yace'"Miye na sauri kuma..? Ai har wanka zaki yi min gama zama dai yar gari. duk ina yi ne na bashi zaki rama ma kura aniyarta" Ban ce masa komai ba sai dai na sunne kai nayi mirmishi. Ranar yini ya yi bai fita ba sai da yammah ya fita siyo mana abinci bayan ya tayani mun gyara gidan mun gogesa na saka turaran wuta na da na had'a mai kamshi tunda duk Ammi ta sako min su kamar tasan ko zasu yi amfani. A burner na saka turaran tunda nazo da kananun abubuwan da nasan zan nema da Engr ya shaki kamshin sai da yayi mgana cikin yanayin mganarsa yace"Kai Turaren nan akwai kamshi" Ina gyada kai ban ce komai ba sai shine yace"Ke kika had'a..? Na kara gyadamai kai sai yace"Tab. Masha Allah Zuwa zamu yi mu bud'e gidan Turarukan wuta nan da wani Lokaci sai kiji mun fi Dangote kudi" Kai kawai na girgiza ina dariya nasan Halin Engr in ya fara zolayarsa sai cikina ya nemi ya kulle saboda Dariya. Ranar ma tare muka kwana,bai nemi wani abu ba,Sannan shi ya karamin Tausa har nayi barci,abinci ma in ya siyo a baki yake bani gatan duniya dai ba wanda bana gani tun ina Tunanin zai nemi wani abu ina jin kunya har na saki jikina da shi na koya irin gaisuwansa komai kuma yace yana so shi nake yi masa,Sai da muka kwana uku da zuwa na bude wayata na kira su Ammi muka gaisa nayi musu bangajiya nan take gayamin a Abuja suka kwana gidan surukaina sai