Sashe 26
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sai La'asar na tashi bayan nayi sallah na Goya Ahmad na Fada kitchen. Jallop din Cousscouss nayi da Kifi Saboda acikin Cefanen da Jamal ya kawo har da kifi,Sai na Dibi Naman jiya da ya rage nayi musu Ferfesu da shi. Kafin mangariba na gama komai Lokacin Haruna ya Dauko su Amir Daga makaranta sai da suka cire kaya muka yi sallah sannan na zubo musu abinci suka ci Anum sai tambayan ina Daada yake shi da Sabuwar Umman su nace sun fita ammh yanzu zasu dawo wasa waasa sai wajen tara da wani abu suka Dawo Lokacin ma ina koya ma Amir Haruffa ne Anum kuma suna ta wasa da Musty suka shigo suna ganinsu suka tashi suka nufesu gabadayan su suna musu oyoyo ita ta Daga Musty shi kuma ya Daga Anum sai ya Rungume Amir.. Daga inda nake ban tashi ba nayi musu barka da dawowa shi ya amsa ita kuma Hannu ta Dagamin saboda bazata iya Daga murya ba ammh Tana da Fara"a sosai nima sai na Daga mata Hannu. Su da yaran shashen shi suka shiga sai na mike na Shiga kitchen na kwaso musu abincin su na bisu da shi sun baje afalo yaran suna ta wadaka da Ice_cream da su Sweet har da gashishiyar kaza,Zeey din tana zaune gefen Ya Ishaq har kafadunsu na dukan juna tana mgana a waya sai dai ba Hausa take yi ba,sannan ba Turanci ba kamar dai Fullanci. Na sauke farantin Hannuna na mike kenan ya kirani na Dawo na durkusa a gabansu ya tambayeni abunda na Dafa na gayamai ya juya yana kallonta da ido suka ma juna mgana naga ta tashi tana wani Rangaji Har Lokacin tana mgana cikin Shagwaba ta shige ciki shi kuma kamar wani Sauna ya Bita da kallo ni kaina na kalleta ballatana shi. Ahmad ya tambaya nace yana barci Sai cewa yayi"Meke damun yaron nan ne..?barcin sa ya fara yawa fa! Ni dai ban ce komai ba na tashi na fice bayan nace ma Amir suzo su kwanta da Wuri Saboda makaranta gobe. Falo na koma na Tattara musu littafan da jakunkunan su na kai musu Dakin su na gyara musu in da kowanne zai kwanta na fito musu da kayan barcin su,nayi ta jiran su har goma ta wuce suna tare da su sai kawai na wuce Dakina naje na Duba Ahmad sai sharan barcinsa yake haka kawai na kasa barci batare da ya'yana sun kwanta ba,Ban samu natsuwa ba sai da naji Hayaniyar su afalo na fito falon Amir nayi ma fad'an meyasa basu zo sun kwanta da Wuri ba su san gobe suna da makaranta"? Anum ya kallah yana fadin"Umma Anum ce taki tasowa." ina kai kallona wajenta ta wani kwabe Fuska tana Fadin"Umma ni wajen Anty da Daada zan kwana" Sai yarinyar ta bani Dariya in ban yi wasa ba Anum ta Dauko iyayi wajen Ubanta to in ba Salo ba da shi ta Saba kwana ko yaushe ta san Anty ma..? Dariya nayi, da yasa yaran suka Tsaya suna kallona hannunta na kama da na Musty Amir na bayan mu zuwa Dakinsu Lokaci daya ina Fadin"Baki san ba kyau yaro ya kwana inda Babba yake kwana ba. ? Na fada ina zama gefen karamin gadon Anum cikin kallona tace"Umma to ba Ahmad na kwana a wajen ki ba..? Kai na girgiza ina Dariya Anum akwai kalkalin baki cikin Mgana ta nace"Shi bai girma ba ai bai kai ku girma ba..Da shima ya kai kamar Mutsy ko Anum dina zan daina kwana da shi zai Dawo Cikin yan'uwansa" Zata kara mgana na Dakatar da ita da Fadin"Shii..Sai gobe sai mu karisa Anum yanzu Dare yayi gobe akwai makaranta ku sauya kaya Mai jin Fitsari ya shiga yayi kafin ku kwanta" Suka amsa min da Toh ni na saka ma Anum da Musty kayan barcin su araina ina Tunanin in na yaye Ahmad ya kara girma zai dawo kwana wajen su Amir ita kuma Anum Lokacin ta kara girma ita macece sai na cireta cikin yan Maza na koma muna kwana tare. Sai da na tabbatar da sun kwanta Mun yi addu'an barci na taya muka Shafa jikinsu sannan na baro Dakin na koma nawa nima nayi shirin kwanciya yau da wuri barci ya kwasheni,Kila Saboda na gaji ne sosai sannan abun mamaki har barcin rana nayi ammh kuma na samu ishashen barci da Daddare. Da Safe ma kamar jiya ne har su Amir suka tafi makaranta basu fito ba Haruna mai adaidaita sai da yayi min mganar kudinsa yace ayi ma megidan Tuni Tunda yaga yana gari nace zan gayamai in sha Allahu yayi hakuri. Kamar jiya yau ma har kuryar Daki na kai musu abun karyawan su ita Zainab din tana Tiolet kamar yadda yace ban jira ta ba nayi fitowa ina gasgata mganarsa da yace bata aikin komai bata ma iya ba ganin yadda komai kuma ta kara Birkitasa kamar jiya ban gyara ba yau din basu fita da wuri ba sai yammah,Suna cikin Shashen sa sun kule,Ga shi nayi ta Dakon sa nayi masa mganar Haruna basu fito ba sanda kuma suka fito suna tare da ita Hannunuwan su sarke da juna shiyasa ban yi mai mganar ba yace min gobe zasu koma Saboda aikin su zai kaita gidan Anty Binta da gidan Anty Mahma sai kuma su zaga gari nayi musu adawo lafiya. Yace kada nayi abinci da su zasu ci a waje na amsa mai da toh sannan ya kara Umartana da in shiga bangaransa na gyara musu kamar jiya nan ma na amsa mai da toh. aiko basu dawo ba sai goma da Rabi na Dare ina Falo ina fama da guga Anum da Musty sun gaji da jiran Dada da Anty sun yi barci Amir ne ke taimakamin in na goge daman kayan su ne, sai ya rika Dauka D'aya bayan d'aya yana kaima kowa cikin Dirowan kayansa. Albarkacin Zainab har aka kawo ma su Amir Chips da su pizza,Sai kuma suka Tarar da su Anum din sun yi barci Ya Ishaq shi kadai ya shiga bangaransa ita ta tsaya tana waya naji dai Tana ta ambaton wani suna Daddy tana mgana cikin shagwaba irin na ya'yan gata..sai da ta gama sannan ta Dagamin Hannu sai nima na Daga mata Amir ta yafito da hannu yazo wajenta tana mai mgana ni ban ji me take fadamai ba. Ta mike tana kallo na inaga abun gugan da taga ina yi ya bata mamaki kusa dani ta kariso da takalminta mai Tsini ta Duka a gabana tana fadin"Sannu fa" Na amsa mata da mirmishi kallona tayi kafin tace"Hannun ki da bayan ki basa ciwo ne..?ba mai wanki da guga ne..? Sai ta karkato kanta tana Fadin"Kina jina..?. Sai ta ma bani Dariya cikin yanayina nace"Ina jin ki mana..ai ina jin mgana in kika yi a kusa dani" Kai ta jinjina kafin ta kara kallona ta ce"Sannu fa" Na kara amsa mata sai tace"kina kokari fa..na ji dadin girkin ki..In da a Abuja kike da kin samu kudi..Gidajen mu duk kukus suke d'auka sannan irin ku kuna samun aiki a manyan Restaurant wajen saida abinci kin gane..? Tafad'a tana kallona Saboda Hausan nata sai a hankali bai zauna ba sai na daga mata kai alamun ina jinta sai kawai taci gaba da fadin"Meyasa baki yi karatu ba Fa'iza..?na tambayi Honey yace kece baki so why.? Sai kawai na kalleta abunda na Lura da Zeey din macece faram faram bata da girman kai ko D'agawa sannan ita Kai Tsaye ce duk abunda ya shige mata Duhu sai ta yi mganarsa shiyasa ban damu da mganarta ba sai na yi mirmishi kafin nace mata"Ba ni ba ce ba na so..Karatun ne bai dace da Kaskantattun mata irina ba..Wad'anda basu da gata sannan masu nakasun ji irin ta Lalurata.." Kallona ta tsaya tanayi ina ganin bakinta na motsi ta kasa mgana ita kuma tana so tayi mgana ammh hausan bata san yadda zata min na gane ba,Muna cikin hakane sai ga Ya Ishaq ya leko ya kirata sai ta tashi ta tafi ammh sai da ta waigo ta kalleni nima na kalleta ina tunanin mamakin mganata take yo menene ban sanin mata ba. Daganan bamu kara haduwa ba sai da Safe da zasu tafi,misalin karfe goma na Safe yara tuni sun tsufa a makaranta,ganin har suna shirin tafiya yasa na yi mai mganar Haruna ina ga saboda a gabanta ne yasa bai yi Fada ba,ya cire dubu goma sha Hudun sa ya bani Saboda duk wata Dubu takwas ne,Sannan ni kuma ya bani Dubu uku na rike a hannuna wai bashi da kudi nidai na amsa ina godiya,Zainab ta bani Hannu mun yi musahaba tana ce min"Sai na ganki kun zo min hutu Abuja ke da yarana" Mirmishi kawai nayi mata ta Dauki Ahmad har Haraban gidan na Rakasu ko Saboda ganinta ne yasa ya bude get din da kansa Dubu biyar ta bama Ahmad sabbi tace ya raba shi da su Anum,Har motar su ta bar Haraban gidan tana Dagamin hannu nima ina Daga mata bayan sun fice sai na maida get din na kulle na koma cikin Gida ina Sauke Numfashi. Ban zata haka amaryan tasa zata karbeni ba sai ga shi na sameta a yanayin da ban zata ba. Da yammah da Haruna ya Dauko su Amir daga makaranta na basa kudinsa yana ta godiya Anum har zata min kukan banza don nace Daada da Anty sun koma Abuja sai da nayi mata jan ido sannan ta shiga Taitayinta. Tunda suka tafi bai kirani ba,nima ban kira ba nadai san shuru lafiya ne in da ba Lafiya da naji Labari sai nima na kama kaina na cigaba da kula da kaina da ya'yana tafiyar su da Sati Daya Sai ga Goggon karofi tazo min kamar Daga sama nayi murnan ganinta har bansan yadda zan kwatanta ba. Tazo min da su kuka,Kubewa garin kunu garin Danwake,kayan miya da kuli kuli,Sai ta zo ma da su Amir gyada da mai gishiri da mai bawo,Sai alewan yara,Suna makaranta ko da ta iso da rana ne Lokacin nama zata ko Daga gidan Mama take sai tace min Daga Dutsemah take ta biya ta gaida ta Madina ta dade bataje ba naji Dadin jin Tamadina tana lafiya. Bakina