Sashe 171
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
na saba. Shawaransa na bi ban kira kowa ba,To in ma zan kira bani da zabi Tunda wayar tana cikin Password ne Dole sai in ta farka tukunnah. Ba ta kuma tashi ba sai da asuba,Cikin ikon Allah ta tashi da kwarin jiki Daki daya muka kwana na bar mata Kan gado ni na kwana saman Cafet. Ba tare da taimakona ba tayi wanka ta Dauro alwala ta fara rama salolinta ni kuma na fita zuwa kitchen tunda na saba bana barcin Safe,Wani lokacin tare da su kafaya muke abun kari wani Lokacin sai dai su fito su ga nayi musu komai. Yau ma hakan ce ta kasance,Indomie na Dafa sai na dafa musu kwai ni kuma daman na fi son sayayye sai na soya na Dafa Ruwan tea mai kayan kamshi,Na kuma soya Buredi,ina da Sauran Soyayyan Nama sai nayi musu pepe. Ko kafin takwas na safe na gama komai na goge kitchen din daman na fi yin abincin rana da yawa tunda ina aika ma su Maa da shi su yi ta saka albarka shi kan shi Engr bai sani ba sai dai in su Maa din suka fad'amasa domin ya yi min mgana ba Dawaniya ba ce..? Nace masa ba Dawainiya bace,daga karshe sai yace Allah ya ba da Lada. Koda na koma Daki Badariya na kwance ammh ba barci take yi ba,gaisawa muka yi na tambayeta jiki cikin sakewar murya tace min taji sauki.. Gefen gadon na zauna ina fadin"Kin kira yusuf kin fadamai halin da kike ciki..?wai ma tsaya da sanin sa kika yo wannan Doguwar tafiyar..?kuma baki fad'amin jiya zaki kamo hanya ba" Shuru tayi kafin ta yamutsa fuska tace"Bai sani ba" Kai tsaye na kalleta da tambayan"Bai sani ba..? Bangane ba..? Sai ta koma ta lumshe ido kafin tace"Miye baki gane ba..? Nace miki bai san na taho ba,bama shi ba ba wanda ya sani" Ban yi mamaki ba ganin yanayin yadda ta zo sai na muskuta kafin nace"To sai ki kira yanzu ki fad'a masa" Kai tsaye tace"A"a.." Mamaki ya isheni na mike ina fadin"To ni bani lambarsa na kirasa na fad'amasa kina wajena kada hankalinsa ya tashi in yaji bakya gida" Da sauri tace"Bazan baki ba Anty Fa'iza" Ina kallonta nace"Saboda menene..? Sai ta muskuta ta mike ta gyara zama kafin tace"Saboda bana so yasan inda nake. Na gaji Anty Fa'iza Ina so na rabu da auran Yusuf ko na huta da wannan bala'in da nike ciki" Ta karishe fada cikin gunjin kuka sai naji Tausayinta ya fad'amin. Na karisa gareta na zauna gefenta na rumgumota jikina ina Lallashinta Fadi take yi"Nagaji nagaji. Bala'in yau daban na gobe Dabam,ga na Matarsa ga na mahaifiyarsa ta tsaneni bata son ganina bata barina nayi girki ta karbe makullin Store sai taga dama zan ci abinci,matarsa kuma har gidan take zuwa tamin Tijara,ban ce komai ba shi ma kamar ta shanyesa baya iya Daukan mataki in nayi mgana sai yace nayi hakuri yana raga mata ne Saboda Hajiyar su, Wlh nagaji ne Anty Fa'iza gwara ya sakeni na koma gida yafiye min zaman auransa na rashin kwanciyar Hankali" Tana gama fad'amin haka ta fashe da kuka ma ban tausayi ga wanda ya Saurara ni kaina ta rauna na min zuciya ina tuna a baya nima fa na Fuskanci iri wannan rayuwar da Badariya take fuskata. Cikin Bubbuga bayanta nace"Subhanallah har yanzu matsalolin nan basu gyaru ba..? Shi Yusuf din bai dauki wani mataki ba..? Sannan yanzu me ya faru kika taho.? Badariya na gunjin kuka tace"Yaushe zai iya daukan wani mataki yana taorin matarsa yana tsoron uwarsa,Kwanaki fa har yaji nayi na tafi lagos na kafe bazan koma ba sai ya sauyamin gida da Hajiyarsa saboda bala'in ya yi yawa da yunwa nake kwana da nayi mgana sai tace Danta ya gaji da ci da juya nazo ba na Haihuwa sai ci nayi kashi abinci fa sai dai na siya,shi bazai iya mgana ba sai dai ya bani kudi a hannuna na rika cin abinci gajiya nayi sai nayi tafiyata Tunda bata amince ya sauyamin gida ba,Dakyar ya lallasheni na dawo da alkwarin zai sauyamin gida na ni kadai ammh kuma mgana ta shiriran ce,Shekaran jiya matarsa tazo gidan tana ta zagina tana ce min Juya in sha Allahu dukiyar da na shigo ci bazan sameta ba har tana zagin Ubana dake Kabari ni kuma raina ya baci na Rama shine ta jani da Dambe har mukayi fad'a,Du keni in Daketa muka yi Lokacin Hajiyar bata nan daganan sai akace taje gidana gaishe da Hajiya bata nan najata da fad'a har nayi Sanadiyar barar mata da ciki daman ina bakin ciki. Yusuf baya nan ammh Hajiya ta kirasa a waya tace ko ya sakeni ko yaga bacin ranta. Shi ya kirani yana kuka yake fad'amin ni kuma da naji haka nace gwara a rabun kowa ya huta tunda yaki saki na sai na zabi na tafi inda bazai ma sani ba ballatana ya nemi shiyasa na yanke shawaran zuwa wajen ki Anty Fa'iza na tabbata ko kowa bai Fahimceni ba ke zaki Fahinceni" Kafin ta gama bani labari naji raina yayi wani duhu jikina duk ya yi sanyi Badariya mai kaunata ce ban so kaddaranta tazo a haka ba, ammh kuma bawa bai isa ya tsara ma kansa Rayuwa ba,muna namu ne Allah kuma na nashi nashin ne kuma na gaskiya. Kuka take yi kamar ranta zai fita ina Lallashinta da ban hakuri kfin nace"To yanzu shi Yusuf din yana ina..? Badariya tace"baya nan,Rabo na da shi tun jiya a fligth mode na saka wayata,mun rabu dai yace yayansu yace ya dawo sai a zauna kada ya sakeni sai indan ya dawo ni kuma daman na shirya tafiyata Shiyasa ban Tsaya ba" Tun daga yanayin mganarta nasan da gaske ta gajin,sai ban matsa mata ba na kyaleta sai dai nayi ta bata baki da ban hakuri kafin na barta naje nayi wanka na shirya ko da na fita falo su kafaya sun tashi suka gaisheni na amsa sun shirya zasu shiga makaranta sai nace su dibi abun karyawa su karya kafin su fita ni kuma na Dibar mana ni da Badariya na kaima har Daki. Abincin ma dakyar ta sauko taci,Tasha dai tea,sai Soyayyan Buredi shi kuma kadan taci sai amai haka ta shiga Tiolet tana kwarara shi ni dai ban ce mata komai ba ne ammh naga Ciki Sabo a tare da Badariya. Su kafaya kafin su fita har Daki suka shigo suka Duba Badariya sannan suka min sallama suka tafi makaranta Dukkansu sun iya mota,suna da kuma Motocin su yau wannan ta tuka gobe wanchan ta tuka. Suka barmu da Badariya tana bani labarin zaman hakurin datake yi a gidan Yusuf ba kwanciyar Hankali,ni kuma ina kara Tausanta da kalmar nan ta Hakuri ita na rike kuma naci Riban Hakurina. Sai yammah Dr din yazo ya kawo sakamakon bayan ya yi mata bayanin tana da shigar ciki na wata Biyu da wasu kwanaki ta kiyaye aikin wahala sannan ta rika cin abinci ta samu Hutu Badariya ta kasa mganar har bayan Tafiyanta ni ce nace mata"To ina zaki kai wannan rabon Badariya..? Baki san abunda Allah ya kaddara Tsakanin ku ba tace ke da Haihuwa sai dai kiga anayi tun ba'aje ko'ina ba sai Allah ya nuna mata bata isa ba. Kinga sunan juya da suke kiran ki sai ya kare daga yau" Bata ce min komai ba sai dai tana ta sharan kwallah Saboda matsalan Badariya yasa sai dare muka yi waya da Engr da ya tambayeni ya ake ciki na Fad'amasa yadda ta fadamin da kuma cikin da aka gano a jikinta. Engr ya fara fad'a yana fadin"Shima dai kamar wani sakarai haba .Ba'a haka sai ya sulhunta lamarin ita matarsa ai karkashinsa take in bata son a zauna lafiya ya yi mganinta mana ita kuma mahaifiyarsa matsayinta Dabam ya kamata in dai yana son matarsa ya san yadda zai iya gyara kowani bangare ammh a bar yarinya na Fuskantar wannan matsalan bai Taso ba Faa'izaa ki riketa a wajen ki Sati mai zuwa zan dawo da kaina zan kira mijinta mu yi mgana, in yana sonta ya gyara gidansa in kuma bazai iya ba to kowa ya kama hanyarsa" Har mamakin Engr na rika yi haka yake da fad'a sai dai nasan shi baya Daukan re ni jarumi ne kuma jajirtattace ne,Da na fad'ama Badariya abunda yace sai taji dadi jin yace zai Shiga mganar zuwan Badariyq yasa su kafaya suka koma gida nima da Badariya ta kara jin sauki munje da ita ta gaida su Maa muka yini achan sai Dare Direba ya maidamu gida. Badariya sai fadi take yi"Gaakiyan dangin mijin ki masu karamci ne Anty Faa'iza" Sai dai nayi mirmishi Saboda abunda na sani ne aka sake fad'amin. Kafin satin da Engr zai dawo Badariya ta murmure tunda ina takura mata taci abinci duk da tana amai ga laulayi da Zazzabi take kwana,wayarta tana Kashe shiyasa bamu ji labarin irin neman da Yusuf ya yi mata har Lagos ba,Da kuma irin yadda Hankula suka tashi tunda duk an nemi kowa bata wajen su ni kuma kila ana tunanin ina amarci kila Badariya baza ta zo wajena ba. Sai ana gobe Engr zai dawo zainab ta kirani a bakinta nake jin hankulansu duk a tashe suke Badariya ta bar gidan mijinta ba'a san inda take ba. Tana bani Labarin yadda Hankalin Mama da su Yaya ishaq ya tashi da shi kan shi Yusuf din sai naji kamar na gayamata gaskiya sai kuma na fasa akallah dai na jira dawowan Engr sai na tada Hankalina na nuna Damuwata da Alhini na. Bayan mun gama wayar na fad'ama Badariya sai ta tabe baki tace"Mama da yan'uwana kawai na damu ammh ba domin Yusuf ba" Ban biye mata ba,ganin yadda tayi fushi illah na rika ce mata"Ke dai fad'i gaskiya kin yi kewarsa sosai ma ko baki yi don komai ba kya yi saboda abunda ke cikin ki" Gajiya tayi ta kyaleni tunda taga na Rike mganar na ki saki,Washegari da Shirye Shiryen Dawowar Engr muka tashi,Badariya ta kama mun muka yi masa abincin kala kala na saukansa jirgin yammah ya biyo sai bayan mangariba ya iso gidan. Lokacin n cakare cikin Riga da sikat na Atamfa mai ruwan ganye