Sashe 66
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wajen Antyn su fiye da zama a inda Umman su take sun rage zumud'in zuwansa. Zainab ta kara haihuwa an samu Fadil ita ta matsamin ta kuma matsa ma Mijinta naje har Abuja karo na Farko sunan fadil kuma nayi mata abun arziki kamar yadda take yi ma ya'yana Anty Binta kamar ta kasheni haka takeji sai dai ba dama Saboda Dan zaki ya riga ya girma, duk da basu daina cin zarafina ita da Mama ba,ammh sun rage suna shakkar min wani abun ganin yarana sun girma sannan nima na wuce Tunaninsu yanzu Fa'izar yanzu ba Fa'izar da suka saba tozartawa a baya ba ne. A sunan Fadil di'n zainab da mahaifiyarta sun sakarmim komai ni nayi gabacin girke girken da akayi kuma ba'a ji kunya ba, abokan aikin Zainab suka zo suna ta santi,Dani da yara dukkanmu mukaje mun fi Sati a Abuja,kuma Uban gayyar na Abujan lokacin, ammh yadda ban gabansa nima haka na nuna masa tuni na daina masa ma karan,Sai mu had'u in ban ga dama ba, sannu bana ce masa,shi kuma mamaki da girman kai yasa ya ke nuna kamar bai ganni ba. kwana Goma muka kwashe a garin Abuja Sannan muka Dawo katsina, har kums gobe Zainab bata tab'a min wani abu na Tozarci ba,sai kanwarta ita kuma ance bata kasar ta tafi kasar waje karatu. Mama ta samu labarin Daukakata Daga sama ne, bata yarda ba sai da tazo ta ganin ma idonta komai ta koma gida tana fada,ta kira Yaya ishaq ta tirkesa kan ya barni ina tara mata agida sannan ina yawon zuwa gidaje da sunan yin girki, tunda aikin abinci sana'a ce da zai bar ni ina gantali da sunan girki. Badariya ke fad'amin a gaban Anty Binta yace bazai iya hanani abunda nake so ba,kamar yadda shima ban taba hanasa abunda yake so ba. daganan sai ya kashe bakin su,Nasan sun yi min abubuwa da Dadama ammh ban rike su a raina ba, Mama har gaban abada matsayin uwa take gareni ina yi mata alheri sai dai bata tab'a karba ba har Atamfofi na taba siyan musu dukkan su Har Hajiyar Dala Mama ta Dawo min dashi tace a Fad'amin ban yi arzikin da zan siya mata zani ta Daura ba.tun kafin Ubana Sidi yasan kudi ta sani bazan Rud'eta da abun duniya ba. Bana damuwa da mganganunta,Anty Binta dai ta amshe tana fadin nima haka na rika tatsan kaninta abun nasu ma kamar sun haukace Koda yaushe Goggo ke nuna min Ribar Hakuri tabbas kuma nima naga Ribar wannan hakurin da nayi shiyasa nake nuna musu komai ba komai ba ne. To ni ina naga lokacin biye musu ma..? Ina da abun yi lokaci na sana'ata ne da ya'ya na,ko D'an nasu da suke takama da shi Fa'iza ta daina ara masa lokacinta yanzu ballatana su. **** Kiran sunana da Amir yake yi ne ya Dawo dani Daga tunanin da na shiga Firgitgit na sauke Tagumina ina fadin"Uhm me kuke fad'i..? Amir yace"Umma wannan dogon Tunanin fa..? Gyara zama nayi ina fadin"Ina tunanin watarana zakayi aure ka kawomin suruka nima" Sai ya bata rai su Anum suka saka Dariya ya daka musu tsawa Hafsah tace"A"a kyalesu su dara Mallam" Sai ya yi fushi ya wurgar da Sandar Hannunsa ya wuce fuu ya shige Dakinsu,Na bisa da Dariya Saboda shi yasha fadi'n bazai yi aure ba sai yayi kudi ya kaini Saudiya. Su Anum na bari suna rubutu kan karamin allon na koma kusa da Hafsah ina fadin"Hafsah inaga fa hostel zaki koma ki fara bincikawa tun yanzu" Sai ta dakata da abunda take yi ta kalleni tana fadin"Meyasa..? Mikewa nayi ina fadin"Ba yanzu zaki san dalili ba.Ki dafa ma yaran nan indomie ki hada da kwai,kuci ni cikina ya cika" Da Toh ta amsamin tabi ni da kallo tana mamakin meyasa nake wasu abubuwan kwana Biyu haka fa Sa'adatu tace na gayamata zan bar mata sana'ar zobo da Kunin aya nan da Lokaci kad'an,kuma naki cewa komai, bayan haka Ni kaina nasan Hafsat ta fara zargin wani abu ni kuma bazan bari ta fahimci komai ba ko Goggo bata san abunda na Kudura a cikin Raina ba, har gobe ina jin bakinciki da Yayata mariya bata kara takowa inda nake ba sai dai mu had'u a karofi ko in naje gidanta tunda yanzu na samu sake Fita free,to ina ma jiran sa kenan..? Shi da sai ya yi wata uku bai zo ba,nima ko nake gaban kaina. ammh indai gidana ne Ya mariya ta daina zuwa tun sanda mai shi ya yi mata iyaka da shi. Cikin Sati d'aya na gama Had'a kayana waje daya,Ranar ma cewa nayi basai anyi zobon yammah ba, na safe daga daya kare a barsa haka,Da Daddaran nace ma Hafsat gobe zan tafi karofi tare da ita su Anum kuma Gidan Mama zan kai su,mamaki ya sa ta kasa mgana nima ban kara ce mata komai ba Domin ta shiga D'akina taga kayana a had'e waje daya kamar wacce zata tashi,ko zata yi Hijira. Ni ko da na koma D'aki sai na shiga Tunane tunane na tuna sanda na saka Ahmad a makaranta har barazana Ishaq ya yi min in ina nuna mai iko kan ya'yansa sai ya rabani da su ya kai ma Mama su,niko a lokacin sai nace mai kada yayi gaggawa ya bari Lokacin da zasu koma karkashin kulawan maman ai ya kusa, sannan na fad'amai suma ya'ya na ne, sannan komai nayi musu ban fadi ba ni uwace garesu kuma in yana ganin don yace na kula dasu ai baya biyana, balle yace aikin kudi nake yi masa.daga Lokacin bai kara tada mganar ba. Na kwana sallah da neman zabin Allah duk da zuciyata naso ta karye Saboda in na kallesu bansan yaya zasu ji in yau suka wayi gari bana tare dasu ba sai dai ko bana so lokaci yayi da zan hakura da rayuwa tare da Ishaq kabir karofi. Allah mai aiko da kaddara a lokacin da yaso washegari da safe su Anum na shirin tafiya makaranta ni kuma ina dakina ina faman jan casbaha ina hawaye,Kirjina yana ta zafi Saboda yanayin da nake ciki naji Hayaniya afalo da Mganganu sama sama,da Sauri na fito da Hijabina sai naga Jamal hankalinsa tashe yara duk sun yi cirko cirko a falo. Hankali tashe na karisa ina fadin"Lafiya Jamal me ya faru ne..? Cikin wani irin yanayi yace"Wlh Yaya Ishaq ne EFCC suka kama shi Daga Wajen aikin su na Abuja. tun jiya yana Hannunsu,Zainab ta kira Mama ta na kuka take fad'amata" Sai naji na Rude yara ma suka fara tambayan me ya samu daada. Cikin Tashin Hankali nace"Me yayi..?su waye EFCC..? Cikin tashin hankali yace"Wata hukuma ce ta federal goverment da ke kula da sace sacen kudad'en gwammatin kasa,To abun dai kamar shiryawa akayi ance wasu miliyoyin kudi ne suka yi batan Dabo a ma'aikan su Yaya ishaq da aka tsannanta Bincike sai aka gano da saka Hannanunsa kudaden suka fita, shine hukumar tazo ta kamasa ance ko ganinsa basu bari an yi ba har yanzu.." Sai na sulale na zauna kan kujera ina salati Amir ne yabi bayana da Salatin su Anum kuma kuka suka saka suna Kiran sunan Daada cikin kad'uwa nace"Hafsah cire mu su kayan makaranta mu..mu tafi gidan Mama" Jamal Ahmad ya Dauka yana Lallashi ni kuma sai na koma D'akina na kalli kayana da suke had'e waje d'aya sannan na Maida su gefe a Fili na Furta"Ashe har yanzu Lokaci bai yi ba..? Shin sai wani Lokaci ne ya Dace na Fara wata Sabuwar rayuwar..? *Karshen littafi na D'aya* *Nan na kawo karshen Littafi na D'aya na KANA NAKA,akwai sauran gwagwamarya,ga dai Ishaq a hannun EFCC,ko ya zata kaya..?* *Ya matsayin aikin sa?Ina kudurin Fa'iza..?Zata tafi ne ko zata sauya ra'ayi..?ya makomar auran Zainab da Ishaq..?tunda da yuyuwar Abuja zata gagareshi shiga wannan karon?ya Mama zata yi..?Ishaq shine duka karfinta,Wani irin Daukaka ce take Bibiyan Fa'iza..?* *Duka tarin amsoshin ku suna cikin Littafi na biyu da na uku,akan farashi mai sauki regular N500,sai kuma tsarin VIP1000,wannan karon bana son tsarin kati,a turo ta POS, akan wannan acct no din 0552179550 Jamila Umar gt bank,Zamu tafi Hutun sallah,sai bayan sallah in muna Raye zamu dora daga littafi na biyu,ammh in dan kun cika adadin ku na Mutane 250 da suka siya,ni nasan ina da masoya Fa'iza ma nada masoya ku yi Dafifi wajen rakata har border domin jin Abunda zai cigaba da gudana a rayuwarta da Ishaq,Janafty tace ta gode Allah ya hadamu a aljannah Ammen* *Janafty* *KNKB2001* *Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 05521790550,ban da tsarin kati wannan karo a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488* Duka na tattara yaran muka bi Jamal zuwa gidan Mama hankali tashe,Har da Hafsah muka iske gidan cike da mutane,Kawayen mama da su Anty Binta,Anty mahma da sauran makotan abokan arzuka. Yadda naga Mama na kuka sai da ta karyamin zuciya ni kaina na shiga tashin hankali mai tsanani. na kasa dora wannan sabuwar kaddarar data bullo mana lokaci d'aya a kan mizani. abu d'aya na sani ina da yakana da yakinin na yarda da Allah sannan na aminta garesa kowani tsanani yake,kuma dukkan sauki daga garesa ne. ban bi ayarin yan kuka ba. Na koma gefe ina hailala da yi ma Allah kirari da istigifari,domin nema ma Yaya ishaq mafita da salama acikin sabon halin da ya wayi gari acikinsa. Ganin ba wanda ya tuna da kiran mutanen karofi sai na Dauki wayata na fita daga falon Mama nayi nisa da Hayaniyar mutane,na kira Goggo na shaida mata abunda ke faruwa Allah Sarki dan'uwa rabin jiki sai Goggo ta Rud'e hankalinta ya tashi ta dinga Daukan Salati tana Direwa,mun rabu tace gatanan zuwa bari ta shaida ma su Yaya Isa halin da ake ciki. Ni da kaina na kira Yaya Asiya na gayamata Halin da ake ciki. itama tana ta salati tana Direwa,kowa in yaji abunda ya faru sai ya tambayi garin yaya..?mu kuma bamu da masaniyar yadda abun ya faru,abu d'aya muka sani ana Tuhumarsa da Batar wasu makudaden kudad'en gwamnati, lamarin akwai